Ko da ake cewa babu abinda lokaci baya tafiya dashi, Abida bata daya daga cikin mutanen da suka yarda da wannan zancen. A wajenta akwai abubuwan da basa taba wucewa, wannan abubuwan harda tsanar da Hajiya tayi mata, a cikin wannan abubuwan kuma harda halayen Asabe da kamar lokaci kara mata su yake. Lokacin dai wannan karin ya zo da sauyi kala-kala a gare su, ciki harda na muhalli saboda kadan da wannan yayi musu, iyali sun karu, duk da a cikin Bachirawa dai suka sake samu, mai daki hudune, sai wani karamin daki a soron gidan da ya. . .
Oh Allah Asabe Kinga takanki wlh,
Muje zuwa dai.
#haimanraees
Allah yakara basira da hazaka