A cikin abubuwan da suke bawa Sa'adatu dariya harda wasu karin maganar ko maganganun da suke nuna yanda mutum yakeji da hausawa suke yawan amfani dashi, musamman ace anji saukar aradu, aradun fa ance tsawa ce, daga nisanta ma, tana sama kana kasa idan kaji karar wata tsawar ai saika nemi maboya, tsoron Allah ya shigeka saboda firgici. Ina kuma ace kaji saukarta aka? Anya zaka rayu harka bada labari kuwa? Duk idan taji an fada sai tayi dariya, tana kuma jinjinawa hikima irin ta bahaushe wajen zakulo magana. Sai dai kuma da wani zaice zata taba amfani da. . .