Skip to content
Part 20 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

A cikin abubuwan da suke bawa Sa’adatu dariya harda wasu karin maganar ko maganganun da suke nuna yanda mutum yakeji da hausawa suke yawan amfani dashi, musamman ace anji saukar aradu, aradun fa ance tsawa ce, daga nisanta ma, tana sama kana kasa idan kaji karar wata tsawar ai saika nemi maboya, tsoron Allah ya shigeka saboda firgici. Ina kuma ace kaji saukarta aka? Anya zaka rayu harka bada labari kuwa? Duk idan taji an fada sai tayi dariya, tana kuma jinjinawa hikima irin ta bahaushe wajen zakulo magana. Sai dai kuma da wani zaice zata taba amfani da kalmomin a karin kanta zasu kwana musu tana karyatawa, sai gata yau a zaune take, amman da kalaman Aisha suka dirar mata kamar aradu sai taji kamar ta sake zama, kamar kuma kafet din ya baje, tayil din dake kasan shima ya murmushe ya zama gari, ya barta zaune akan turbayar da take dibarta tana shawagi da ita shisa takejin har wani lilo kanta yakeyi.

Zuciyarta da taki nutsuwa da Aisha duk yanda take kokarin janta a jiki a cikin wata dayan nan ashe gargadi ne takeyi mata, kokari takeyi ta kareta daga wannan babban al’amarin da bata da wuyan dauka?

“Kinga nace a turomun ke ko? Wai tuwon alkama nake marmari nace kizo ki tukamun”

Girke-girken duk basu bama Sa’adatu mamaki ba, ko ba’a fada maka ba, gidan, da ita kanta Aishar zasu hanaka mamaki idan akace duka tsayin rayuwarta bata taba rike muciya da sunan tuka tuwo ba, tana da gatan daya bata damar jingine duk wani aiki da ake ganin ya wajabta akan mace, musamman mai sauki kamar girki da ko ba’ayi mata a cikin gida ba tana da kudin da zata fita taci a ko ina, ko ta siya a kawo mata har kofar gida. Yanda Aisha take tsayawa tana janta da hirane yaki kwanta mata, akwai haduwar jini, amman ba irin wannan ba, tazarar dake tsakaninsu tana ganin tayi nisan da zata dinga sakar mata fuska tana dariya da ita irin yanda takeyi

“Kinsan bansan ina Bachirawa take ba, kuma tunda kika tashi anan kuke?”

Kamar wadda aka yiwa dole haka takan amsa duk tambayoyin da Aisha takanyi mata, a takaice, tana kokarin sakewa da ita kamar yanda taga tana so, zuciyarta ce taki bata hadin kai. Musamman idan taji dawowar Jabir, sai komai ya tsaya mata, sanyin gidan baya taba hana zufa karyo mata, sau goma sha daya ta hadu dashi tunda Aisha ta fara rakitota gidan, bakinta na rawa take gaishe dashi

“Lafiya, Nagode”

Shine amsar shi, kuma bai taba kallonta ba a duka wannan haduwar, asalima da ace bata kallon hanya to zasuyi karo saboda nashi kan a kasa yake ko da yaushe, ko a cikin gidan ne yana zaune a kujera, to sau hudu ma tana wuce shi a falon da bataji ya amsa maganar Aisha ba zata dauka bacci yakeyi, saboda idanuwan shi a rufe suke a duka lokuttan, sau daya Aisha ta taba ce masa

“Jay ko zaka fita titi da Sa’adatu…”

Saboda tana kitchen din tana tattara rabin abinda ta dafa a ranar da Aisha ta dibar mata dama wasu kayan kwalam da makulashen, saida robar tayi barazanar subucewa daga hannunta da ta juyo wannan maganar, ita dashi? A mota daya? Harma ta shaki iskar da zai fitar? Anya zata iya?

“Nope”

Amsar shi ta daketa a bazata, haka kawai kuma sai taji wani abu a zuciyarta ya sosu matuka. Wani yanayi na rashin jin dadi ya saukar mata, cikin rashin kuzari ta tattara komai, ko murnar kudin da Aisha ta bata batayi ba. Kuma ko da ta koma gida ranar ma duba duk wani dalili da yasa take damuwa da al’amuran shi tayi, amman ta rasa ko daya. Haka ta tashi washegari babu wani karsashi, da Aisha ta kirata kuwa kamar kar taje haka ta dinga ji, yau kuma tana shiga takejin zuciyarta na bugawa sosai, muryarta can kasa suka gaisa da Aisha

“Me za’ayi?”

Ta tambaya a hankali

“Kizo ki zauna Sa’adatu, magana zamuyi”

Bugun zuciyarta daya karu, ta tabbata in da za’a saurara za’a ji sautin shi, kujera ta nuna mata, saita tsinci kanta da zama akan kafet a kasa, saboda jikinta na bata kowacce magana ce, tafi karfin ta sameta tana zaune a kujera

“Bansan ko zaki yarda dani ba idan nace miki na juya maganar nan, na sake juyata tun kafin insan ke zan furtawa, amman har yanzun na rasa ta inda zan fara”

Cewar Aisha tana wasa da yatsun hannunta, tata zuciyar nafin ta Sa’adatu dokawa

“Kiyi mata magana ke kadai Tasha, bani da karfin halin jin tace a’a, ke kinsani bani da wannan karfin zuciyar”

Jabir yace mata cikin muryar nan tashi da tasan ko taja maganar babu abinda zata fada da zai canza masa ra’ayi, sai dai itama yanzun kwarin gwiwar da take ta tattarawa tunda ta yanke shawarar tunkarar Sa’adatu take neman rasawa. Makoshinta ma ji takeyi ya bushe kamar ta yini bata sha ruwa ba, taja numfashi ta fitar

“Abinda zan fada abune da yake da muhimmancin da nake so ya zamana tsakanin ni da ke ne kawai Sa’adatu, ba zan miki barazana ba, inajin bana bukatar hakan…”

Kallonta Sa’adatu tayi, a matsayin Aisha, da nata matsayin da gaske bata bukatar bude baki tayi mata barazana akan komai, bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane tabbas

“Bansan ko kinsan abinda ake kira surrogacy a harshen turanci ba”

Kalmar “Surrogacy” ta dira kunnuwan Sa’adatu tana isa cikin kanta kafin ta fara shawagi tana neman ma’anarta da kuma hadinta da maganganun Aisha, kafin taci gaba da wasu maganganu cikin harshen turanci da fassararsu ta riski Sa’adatu kamar

“Mahaifarki zaki ara mana mu ajiye da, ki haifo saiki bamu, ba kyauta zakiyi mana ba, zamu biyaki, kuma za’ayi komai ne a rubuce da lawyanmu, kudi zamu baki masu yawa Sa’adatu”

Bata san ta inda dariya ta taho mata ba, danko da taji sautin dariyar ma bata dauka ita takeyinta ba, kallon da Aisha takeyi mata ne yasa, da kuma ganin ita bakinta baya motsi yasa ta gane ita takeyin dariyar, ta dauki kusan minti biyu kafin taji sautin ya daina fitowa, haka saukar aradun take ashe? Ba zaka taba ganewa ba sai ta diro maka, irin dirowar da tayi mata hade da maganganun Aisha. Littafin hausa nawa ta karanta? Na turancin ma ta karanta wadansu bama don neman nishadi ba, sai don ta kara gyara turancinta, ta kuma gwada nisan da tayi a fahimtar yaren, sai kuma suka bata mamaki yanda suka nishadantar da ita, fina-finai kuwa ba zata iya kirga adadin wadanda ta kalla ba, daga na soyayya, fada, tsafi, abubuwan al’ajabi da suka bata mamaki, suka sakata tunani.

Amman bata taba cin karo da abu daya girgizata irin maganganun Aisha ba, ta basu aron mahaifa fa, zasu ajiye da, to tayaya? Kanta ya kulle gabaki daya, watakila hakan Aisha ta gani shimfide akan fuskarta shisa ta cigaba da fadin

“Mun rigada mun gama tsara komai, yardarki kawai muke bukata, sai kuma saka hannunki a jikin wasu takardu”

Kallon Aisha dai Sa’adatu takeyi, idan kuma tunanin ta bai samu matsala ba, magana ce akeyi ta daukar ciki da haihuwa, kuma taga Aisha na sallah, Jabir dinma tana da tabbacin musulmi ne, kuma su duka duk da suna hadawa da turanci sosai, suna hausa, idan ka cire Jabir da har yanzun ba zatace ga yaren shi ba, Aisha dai tayi mata kama da bahaushiya. Kudin da suke dashi baya nufin ko yaya ne basu san kadan a cikin al’ada irin ta bahaushe ba, in kuwa hakane taya suke tunanin zasu ajiye da a mahaifarta, zata daukar musu ciki tsayin wata tara, ta haihu ta mika musu abinda ta haifa, ta kuma koma ta cigaba da rayuwa kamar komai bai faru ba? Sai kace a film din America ko Indiya? Ko da tacewa Aisha duka iyayenta sun rasu, bata tunanin akwai inda tace mata ita kadai take rayuwa, bata da mafadi, ko wanda zai dora ayar tambaya akan rayuwarta da zabukanta.

“Kamar magana kike ta daukar ciki da haihuwa”

Ta tsinci kanta da bude baki, muryarta na fitowa da wani yanayi, har lokacin kuma idanuwanta kafe suke akan Aisha, sai dai wannan karin ba zatace ga mintunan da Aisha ta dauka tanayi mata karin bayani ba, ta dai san lokacin da ta mike, da kuma lokacin da Aisha tace

“Ki dauki duk lokacin da kike bukata don yin nazari, amman karki dauka da yawa…”

Kuma kamar akwai alamar roko a karshen maganar ta Aisha, ta kuma fita daga gidan, tana jin kamar wani abune yake turata tana tafiya saboda yanda tunaninta yayi nisa zango. Adaidaita sahun data tare ma ta shiga saida ya tambayeta inda zai kaita tukunna ta tsinci kanta dayi fada masa kwatancen unguwar. Data fita kuwa dubu dayar data bashi, da hannu ta nuna masa alamar ya tafi, ina zata iya tsayawa wani karbar canji bayan so take ta jita kwance a cikin daki, idan da hali ta turo kofar ta rufe ko zatayi nasarar rufewa da wannan rudanin daya yi mata dirar mikiya. Ko tayi sallama ba zata tuna ba, sun daiyi magana da Fa’iza da take zaune tana yanka salak, kafin ta wuce daki, ko hijabi bata cire ba haka ta kwanta.

Tunani take so tayi ta kasa, inda duk ta duba cikin kanta babu sauran sarari, maganganun Aisha ne suke ta mata yawo. Sallar azahar dai sau biyu tayi, ita da kanta bata aminta da ta farkon ba, abinci da Fa’iza tayi mata tayi kuwa haka tace ta koshi, kanta ne yake dan ciwo idan tayi bacci ta tashi zataci, batayi baccin ba, bata kuma yi tunanin daya kamata ace tanayi ba, la’asar, magariba, isha’i duka ta fita tayo alwala ne tana sake komawa daki. Ta fita ta dauki abincin da Fa’iza ta zuba mata ne saboda bataso Abdallah ya dawo ta fada masa bataci abinci ba, bata shirya tarin tambayoyi da tuhumar me yake damunta da zai tsareta dashi ba, kuma sosai tayi kokarin tura abincin da bata gane dandanon shi ba. Ta koma kan katifa tayi luf kamar tana bacci, tanajin Fa’iza ta shigo dakin ta dubata bayan dawowar Abdallah, tana kuma jin tana fada masa tayi bacci.

Watakila gajiyar da kwakwalwarta tayi ne, yasa wani wahalallen bacci ya dauketa. Washegari ma haka ranar tazo mata ta wuce batare da ta kulla wani tunani ba, sai juya maganganun Aisha da take tayi, sai kuma alamun zazzabi da takeji kamar yana son kamata. Ta daiyi kokari wajen taya Fa’iza ayyukan gidan, daga baya kuma ta koma tana kallon yanda take jan turtsetsen cikinta kamar batajin nauyin shi, kafin kuma ta tuna irin wahalar laulayin da Fa’izar ta sha lokacin da cikin yake karami. Ko yanzun ma kamanninta duk sun canza, batayi katon hancin nan da yawancin masu ciki sukeyi ba, sai dai akwai rama a fuskarta, tabbas baiwar da Allaah Yayi wa mace mai yawa ce. Hidima kawai Fa’iza takeyi, a zauna ayi hira, tayi dariya, duk kuwa da tarin labaran da taji da wanda ta gani game da masu ciki da hatsarin da yake cikin nakuda.

Duka mai rai mamaci ne, amman kuma yawo kakeyi da sanin cewa ajali zai iya riskarka kowanne lokaci, a wajen mace mai ciki kamar abin ya bambanta, rayuwa take a cikin wata duniya ta taradaddi, kamar cikin na tare da wani tikiti ne na karewar rayuwa ko akasin hakan, gareta da abinda take dauke dashi, duka wata taran nan da wahalar, nakuda na iya riskarta ta haihu, dan ya koma, ko ita ta tafi ta barshi. Sosai Sa’adatu a yau take ganin babu wanda ya kai mace mai ciki mika dukkan lamurranta a hannun Allaah, shisa ma har take da sukunin gudanar da al’amuran yau da kullum batare da tunani da firgici sun kassarata ba. Saita tsinci kanta da yiwa Fa’iza sannu tana sakata yin dariya. Haka ta kwanta ranar ma tana rasa zaren da zata kama ta kulla a matsayin tunani, da kiran Aisha ya shigo wayarta kuwa bugun da zuciyarta tayi da bata da wadatacciyar lafiya tabbasa saita samu matsala, ba iya kiran kawai ta kashe ba, gabaki daya wayar ta kashe.

Sai bugun zuciyarta ya zama wani sauti daya hana mata bacci, idan ta rufe idanuwanta sai taji kamar ya karu, wayarta a kashe yake, ta gane baccin bai fara daukarta ba sai gab da asuba, saboda yanda akayi kiran sallar farko akan kunnenta, dakyar taja kafa ta fita tayi alwala. Akan dardumar data idar da sallah ta kwanta, bacci mai nauyin gaske ne ya dauketa, shisa ta dauka a mafarki take jin muryar Abdallah yana tashinta

“Fa’iza nakuda takeyi Sa’adatu, kizo ki zauna da ita in samo abin hawa mu tafi asibiti…”

Babu shiri kuwa ta wartsake, inda Allaah Ya taimaka unguwar tasu cike take da masu dan sahu, kuma da sanyin safiya ne, lokacin ma wasu suke wanke adaidatar, wasu kuma suna fita. Da yake hausa sunce zaman lafiya wani abune daban, kuma duka matasan da suke unguwar da ma bayan layin nasu, har kuwa da wadanda suka ma girmi Abdallah, suna girmama shi da ganin kimarshi saboda yanda yake mu’amala da kowa a mutunce, nan da nan ya samo wani dan unguwa suka koma kofar gidan tare. Da yake duk wasu kayan haihuwa da za’a bukata Fa’iza ta jima da hadawa a jaka, dauka kawai Sa’adatu tayi, suka kulle gidan suka nufi asibiti gabaki daya, babu wani bata lokaci aka karbesu, sai da aka shiga da Fa’iza dakin haihuwa, su kuma suka koma inda ake zama ita da Abdallah tukunna ya ciro waya ya fara kiran ‘yan uwa yana fada musu.

Kafin karfe tara su Nabila duk sun iso asibitin, kuma duka da abinci sukazo, suka karya gabaki daya a asibitin suna zaune suna jiran tsammani, Abdallah dai yana saka baki a hirarsu ne, amman inda zasu kalle shi da kyau, dariyar shi bata kaiwa cikin idanuwan shi saboda zullumin da yake ciki, da an fito an kira wasu sai gabanshi ya cigaba da faduwa. Wasa-wasa har la’asar suna nan zaune, shine ma yake zuwa yana samun daya daga cikin Nurses din da duk yanda suke ta dakawa mutane tsawa suna musu izgilanci, kwarjini da sanyin Abdallah ya hana ko daya daga cikinsu yi masa wulakanci, duk kuwa yanda amsar da suke bashi take nuna ya dame su. Abu kamar wasa, tun suna hira har tsoro ya fara shigar kowa, musamman ‘yan uwa na nesa da suke ta kira ana ce musu har yanzun.

Basu sake shiga tashin hankali ba sai da aka kwana ana neman sake yini, kafin ma aka kira Abdallah da batun za’a yiwa Fa’iza aiki, su kuwa duk wanda ya samu ya shiga ya ga halin da take ciki da kuka yake fitowa, musamman yanda take ta rokon da su kamata su fita da ita taga Abdallah suyi bankwana dan tanajin ba zata rayu ba. Gefe Sa’adatu ta koma tana share hawaye, ko da taga yanda jikin Abdallah yake rawa, idanuwan shi dauke da kyallin hawayen da yake dannewa sai zuciyarta ta sake karyewa, da taji kudin da ake nema kuma na aikin, taji maganar Abdallah da Nabila, da kudaden da yake wajen shi basu karasa cika ba, saboda ya karasa bayar da kudin rago a wajen wani dan ajinsu da yake kiwo, saita mike ta same su, itama akwai yan kudi a wajenta duk da ba masu yawa bane saboda wadanda ta fara tarawa lokacin zaman makokin Abida duk ta fito dasu, cikin albashinta kuma in dai wani abin zai burgeta batayiwa kanta kwauro.

Gaggawar da akace suyi ce take neman gagara saboda yanda aketa kokarin hada kudin aikin. Kaiwa da komowar da Abdallah yakeyi kuwa wani abune da Sa’adatu ba zata taba mantawa ba. Wani hukunci na Ubangiji, ya gama tattaro duka kudin, harya saka hannu ya biya, Fa’iza ta haifo katon yaronta. Zuwa Magriba kuwa har sun koma gida. Kamar basu shiga wani tashin hankali ‘yan awanni kadan da suka wuce ba. Kamar kowa ya manta ma anata hira ana hada-hada, sai Abdallah da yake a sanyaye har lokacin, sai kuma Sa’adatu da babu abinda yake mata yawo sai yanda da ace dole-dole aikin za’ayiwa Fa’iza fa? Kuma kudin aikin sukaqi haduwa, shikenan? Sai dai su kwaso su dawo gida ko kuma su zuba mata ido har Allaah Yayi ikon Shi? Mutane nawa ne hakan ta faru dasu? Tabbas idan rayuwarsu bata canza ba suma wata rashin kudi zai zama sanadin ajalin wani a cikinsu

“Miliyan biyar zamu baki Sa’adatu”

Maganar Aisha ta dawo mata, miliyan biyar ko ba’a fada mata ba zata canza rayuwar su, miliyan biyar kuma kudine da in bata wannan dalilin ba watakila a danginsu dai babu wanda zai taba hada hanya da ita balle ya mallaketa, daki ta shiga ta dauko wayarta ta kunna, ta lalubo lambar Aisha tana tura mata sako mai dauke da kalmomi biyu kacal

“Na amince”

Kalmomi biyu masu sauki a rubuce

Kalmomi biyu masu sauki wajen karantawa

Kalmomi biyu da suke dauke da kaddarar da babu wanda ya hango faruwarta a cikinsu

<< Tsakaninmu 19Tsakaninmu 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×