Hausawa sukace duk abinda baizo ba to ba'a saka masa rana bane ba. Sa'adatu kuwa ji takeyi kamar tana yawo a cikin wata duniya ta daban, ko da sukace aure, ta dauka taruwa za'ayi a masallaci a daura, kowa ya watse, sai kuma yar walima ta al'ada da tasan 'yan uwanta zasuyi a gida dole, sai komai daga bangaren su Jabir ya girgiza ba ita kadai ba harma da ahalinta. Kudine aka saka mata a account har Naira dubu dari wai ko da zatayi wata bukatar. Data nunawa Amira sai tace ta barsu a ciki, idan. . .