Skip to content
Part 24 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Hausawa sukace duk abinda baizo ba to ba’a saka masa rana bane ba. Sa’adatu kuwa ji takeyi kamar tana yawo a cikin wata duniya ta daban, ko da sukace aure, ta dauka taruwa za’ayi a masallaci a daura, kowa ya watse, sai kuma yar walima ta al’ada da tasan ‘yan uwanta zasuyi a gida dole, sai komai daga bangaren su Jabir ya girgiza ba ita kadai ba harma da ahalinta. Kudine aka saka mata a account har Naira dubu dari wai ko da zatayi wata bukatar. Data nunawa Amira sai tace ta barsu a ciki, idan aka natsu sai ayi tunanin wani abu mai muhimmanci da za’a sai mata da zata mora. Sai kuma lokacin da suka kawo lefe, da yake maza ne suka kai, kuma gidan Anty Talatu, sai daga baya aka kawo musu nan, mamaki saida ya kusan daskarar dasu, abinda ita Sa’adatu take gani a waya yana girgizata, shine yau a cikin gidansu a matsayin mallakinta, akwatuna saiti uku, akwatina da idan za’a tambayo kudinsu tana da tabbacin ya ishesu su shekara suna lallabawa.

Akwatuna masu shidda-shidda, su kansu jikinsu anyi masa wata kwalliya da wani ribbon me daukar hankali, harda wasu kwanduna kamar na saki guda uku suma da aka zuba wasu kayan a ciki, ita kam ko bayan an gama tururuwar gani, Fa’iza tace mata tazo taga lefenta sai ta kasa budewa, har Fa’iza na tsokanarta, jikinta ne yayi mata wani iri, yanayin hidimar da bikin ya fara sakata jin inama-inama. Sai kuma da ‘yan uwan Jabir da yasan ko yayi kokarin hanasu shagali ba zasu hanu ba sukazo da motoci suka dauketa da ‘yan uwanta wai sun shirya wata ‘yar walima. Haka suka bata wani leshi da tunda take ganin leshi, harna lefenta kuwa lokacin Tahir, bata taba jin mai laushin shi ba, ruwan kwai ne, Nenne tayi mata kwalliya, cikin kankanin lokaci sai gata ta wani irin fitowa kamar ba ita ba, ko su Nabila mamakin kyan da tayi sukeyi, gashi dai ba wata kwalliya akayi mata me yawa ba, haka daurin nata da wani irin yadine mai kalar ruwan madara, kamar duwatsun jikin leshin nata.

Yanda ‘yan uwanshi suke ta janta, ayi nan da ita ayi hoto, ayi can da ita, sai taji wani irin yanayi ya lullubeta, kamar abubuwan da takeji a lokaci daya sunyi mata yawa ita kadai, shisa ta rasa samun takaimamen yanayi daya da zata kama ta rike, duka basu fi su dari ba a wajen taron, amman ji take kamar su dubu ne, fuskoki daban-daban, maza da mata, amman kuma idan ka natsu zakaga kamannin da jini ne kawai yake samarwa a tsakanin su duka, sai kaga taron babu wasu bare da yawa, yasu-yasu ne kawai. Bata sake jin komai ya hargitse mata ba saida ta daga ido taga Jabir, yana dariyar wani abu da Badiya da take tsaye a kusa dashi ta fada masa, shadda ce ruwan madara a jikin shi, kalar dankwalin kanta, ya saka hula mai duhu, batasan meye a tare dashi ba, dariyar da yakeyi har hakoranshi suka bayyana da bata taba gani ba, ko manyan kayan da yake jikinshi, sai kawai taji wata kwalla na nan cika mata idanuwa.

Da suka jawo shi zuwa kusa da ita kuwa, sai taji zazzabi ya rufeta, ashe zuciyarta bugun wasa takeyi da, ashe duk yanayin da take tunanin yayi mata yawa shirme ne, da Jabir ya saka hannun shi cikin nata yana hade yatsunsu guri daya, saita rantse ta narke tabi filin taron da suke, shisa ta daina jin nauyin jikinta sam, take jin tana juyawa kamar fallen takarda duk inda Jabir da ‘yan uwan shi sukayi da ita, hasken camera kuwa da yake ta dalle su na haskawa ne har cikin kwakwalwarta da tayi wayam, kamar babu komai sai fili, ba dan rashin agogo ba, wannan baya hana lokaci tafiya, kawai a wajenta ne komai yayi tsaye

“Kaina na ciwo da gaske Adda…kince fuskata kawai zan nuna, nayi kusan minti talatin fa, wanne kaya kuma zan sake? Dan Allaah ki barni inje in kwanta”

Muryar Jabir ta ratsa ta cikin kanta, duk da batajin ta fahimci abinda yake cewa, saboda ya saki hannunta, ya saka taji wani irin kadaici da bata taba sanin akwai shi ba yayi mata rumfa, ta kuma ji anja hannunta, wannan karin ma fiye dana farko, yanda akayi da ita haka takeyi, kayane ta canza, bata da natsuwar gane kalarsu, haka aka sake janyota aka fito da ita, daya sake rike hannunta sai taji dai-daito ya ziyarce ta, batasan lokacin data sake dumtse yatsunshi cikin nata ba, shisa bata ga yanda ya juyo ya dan kalleta ba, a lokacin kuma camera ta haskesu tana daukar har yanayin da yake cikin idanuwan shi. Hotuna aka sake yi sosai, bayan su kadai, yan uwan shi da nata duka. Kafin ya rankwafa kamar zai fada mata wani abu mai muhimmanci yana saka abokan wasan shi yin wata sowa, ga wayoyi a sama sunata haske su

“Kaina ciwo yake, tafiya zanyi, kiyi hakuri wannan baya cikin yarjejeniyar mu, yan uwana suna san shagali sosai, bansan ya zanyi in hanasu ba, ki samu ki gudu kema kafin su gajiyar dake”

Kanta ta sadda, tana jin tsikar jikinta na mikewa, tana kuma karanto duk wata addu’a da zata iya tunawa kar ace kowama yana ganin yanda jikinta yake kyarma

“She’s so shy (Tana da kunya sosai)”

Taji wata murya ta fada daga gefensu, kafin kuma Jabir ya saketa ya fara takawa da nufin barin wajen

“Dan Allaah ku maidata gida ta huta”

Taji yana fada har lokacin bai daina tafiya ba, wasu a cikin ‘yan uwanshi na bin bayan shi, idanuwanta na biye dashi har saida ya bace mata, tukunna ta sadda kanta kasa, a hankali ta saka dan yatsa ta dauke kwallar da ta kasa mayarwa. Motar da yazo wajen da ita yaje ya bude ya shiga, hankalin shi gabaki daya yayi gida, yayi wajen Aisha daya baro cikin wani sanyi da bai taba gani tare da ita ba, a lokaci daya kuma yanajin yatsun Sa’adatu cikin nashi har lokacin, baisan me yasa ya riko hannunta ba, kamar hannun nashi ya bar karkashin ikon shi yana ganinta, tana dago idanuwan nan ta sauke su akan shi, babu wanda ya taba kallon shi yanda ta kalle shi yau, kamar akwai wani abu tare dashi da ita kadai take gani, har so yayi ya kalli kanshi yaga abinda take kallo amman babu halin hakan.

Daya fara takawa zai karasa kusa da ita kuwa, zai rantse kamar jikinta rawa yakeyi, kamar kuma yana ganin bugun zuciyarta a cikin idanuwanta da tayi saurin saddawa kasa duk da baiji sautin bugun ba, kamar kuma idan bai riketa ba tayi raunin da zata iya faduwa, watakila shisa hannun shi bai tsaya ya gama yanke shawara ba ya rikota, yana jin yatsun da suka kasa bace masa yau, sai dai ba karamin yaki yayi da kanshi ba lokacin karya murza yatsun nata, musamman da suka fara zufa a cikin nashi, so yake ya murza ya goge mata zufar da nashi yatsun da tafin. Kai ya girgiza ko yanayin zai bace masa. Yasan yan gidansu da son shagali, yaga kuma yanda suketa shiryawa bikin, harda wasu anko da sukayi, duk da Zaitun ce kawai ta karbi kudi a wajen shi, wannan kuma duk wata dama da zata samu ta karbar kudi a wajen kowa ma a cikinsu bata bari ya wuceta.

Tana da wani irin son rayuwa mai tsadar gaske, komai nata ya bambanta dana kowa a gidan. Ya kuma bata, amman wani lefe, wata hidima duk ‘yan uwanshi sukace sun dauke masa. Abokan guda daya ya turawa katin gayyata, da yake duk ba’a garin Kano suke ba, suna Abuja, yasan shi zai turawa sauran, kuma yasan duk abinda sukeyi da yammaci juma’ar zasu sauka Kano, tunda washegari asabar daurin aure, bayaso suji a garine su dame shi da mitar ya kara aure bai fada musu ba. Ya dai ce musu babu wani abu da za’ayi banda daurin aure, su dai sunce zasuyi walima idan an dawo daga daurin auren, kuma su zasu taho da kayan da za’ayi amfani dasu wajen daurin aure, ya amsa su da to yanda yake amsa yan gidansu da duk wani abu da sukazo dashi game da bikin, so yake ayi a gama ko zasu wuce wannan bigiren su shiga wanda ya zama dalilin auren gabaki daya.

A daki ya samu Aisha, ta kashe hasken dakin, ta kuma ja labulayen masu kauri, dakin yayi wani duhu kamar babu haske a waje, taja bargo ta rufe kusan har kanta, kayan jikin shi ya fara cirewa yana barin na cikin kawai kafin ya karasa kan gadon shima ya kwanta a bayanta, yana zagaya hannun shi a jikinta, ko motsi batayi ba, idanuwanta a rufe suke, wasu hawaye masu zafi na saukar mata. Farkon gano matsalarsu da likitan nan ya basu shawarar ko su dauki yaro a gidan marayu, wato adoption a turance, ko idan kasar da suke dokar bata hana ba, su samu wadda za’a dasawa kwan Jabir din ta haifa musu, sai ta dinga jin kwan Jabir a jikin wata? Wata daban ba ita ba, wata daban ta raini kwan nan ta haifo, jininta dana dan Jabir zai kasance a gauraye har abada. Ai gara ma suje gidan marayun su dauko, duk da tana da yakinin yan gidansu Jabir zasuce su bashi nasu da ya tsallaka gidan marayu.

Sai dai bayan sun dawo, tayi tunanin Hajiya Hasina zata saka Jabir ya karo aure, tashin hankalinta saiya ninku, ga Jabir yaki bude bakin shi yace mata zai zauna da ita da matsalarta, ba zai kara aure ba, shekara ta tafi, dari-darin da take saiya fara raguwa da aka doshi shekara ta uku shi ko dangin shi babu wanda ya taba nuna mata wani abu a fuska, asalima masu kananun yara sai suka daina kawosu gidan, kamar suna tsoron kar ganinsu ya tuna mata da nakasar da take tare da ita. Sai dai ko sun kawo, ko basu kawo ba, inta dauki waya sai taga yara, inta fita saita gani, kuma hakan tuni yake mata sosai na abinda ba zata taba samu ba, ga zuciyarta kamar kara mata son rike yaron da zata kira da nata takeyi kullum.  Saita fara jin kamar wata ta haifo ta basu bakomai bane ba, jinin Jabir har abada zai zamana nata ne, tana masa wannan soyayyar, kuma haihuwar yaro ko yarinyar ne kawai ba zatayi ba, amman zata so shi, zata dasa mata soyayyar shi saita goge masa wannan tunanin na cewar ba ita ta haife shi ba.

Abune mai sauki, abune kuma da yake faruwa, daga ita har Jabir misali ne na hakan. Da rana daya basu taba jin basu fito daga jikin iyayensu ba. Suna zaune suna cin abinci tace masa

“Jay…”

Ya dago ya kalleta bai amsa ba

“Me yasa ba zamuyi considering surrogacy din nan ba?”

Wata magana da tasha mamaki akanta saboda Jabir din daya bude baki da wani tsari kamar ya jima yanayin shi, kuma ya jima din, yana jiran lokacin daya kamata ne yayi mata maganar saita rigashi, ada yara da yawa yake so, amman yanzun ko daya ya samu zai gode, ko daya ya gani da zai kira nashi zuciyar shi zata natsu. In yaso saiya kara dana ‘yan uwanshi duk ya hada ya rike. Kuma tare suka tsara komai ya faru karkashin inuwar aure zaifi sirri, babu wanda zai zargi wani abu, kuma babu wanda zaisa ayar tambaya dan Jabir ya karbi da ko yar shi, aure na mutuwa ko da yaushe, da dalili ko babu. Har dariya ta dingayi da Adda Farhana ta tafi bayan ta sameta tana kokarin kwantar mata da hankali, tanajin da sun san irin auren da Jabir zaiyi duk da sun daina damuwa.

Ko data samu Hajiya Aisha, Mummynta da zancen ma, tana ganin har kwalla saida ta cika mata idanuwa, balle kuma Alhaji Fu’ad daya fara fada kamar zai ari baki, saboda duk wani abu da zai tabata baya kaunar shi, fadanshi kuma duka na son kaine, son ace Jabir zai zauna da yar shi da lalurarta batare daya nemi ya kara aure ba, yanda taga ya daga hankalin shi saida taji kamar ta warware masa komai ko zai samu natsuwa. Ada zasuyi waya biyu zuwa uku, amman yanzun sai yayi mata kira biyar dan yaji lafiyarta, yanda duk take biyawa ta gidan daga wajen aiki dan ta nuna masa bata cikin wani tashin hankali bai gamsar dashi ba, haka ‘yan uwanta ma, su kai tsaye suke tambayar in tana da wata damuwa. A lokacin da gaske take bata da wata damuwa, ko Jabir zai kalli wata mace tana da yakinin ba Sa’adatu ba, yar karamar yarinya haka, kuma mai matsayi irin nata. In ba kaddarar rashin haihuwa ba ya za’ayi mace irin Sa’adatu ta amsa sunan matar mijinta?

Kuma ganin Jabir din baya wata hidima, suna tare ko da yaushe kamar hidimar karin auren shi bata faruwa a gefe, ya dai fada mata ya siyi wani karamin gida a rijiyar zaki, inda ‘yan uwan Sa’adatu zasuje su duba, inda kuma zasu kaita, har neman suje taga gidan yayi, tace masa ba lokacin ba, tunda tana ganin babu abinda zataje tayi. Sai dai ranar larabar satin bikin Nenne da kanta tazo tana gayyatarta walimar da zasuyi, har tana ce mata a dinka mata nata leshin ko a kawo mata ta bayar da dinki da kanta? Tace a’a ba zata samu damar zuwa ba

“Na fahimta”

Nenne tace tana mata sallama, kawai ta sauke wayar taji wani abu ya daki kirjinta, yarjejeniya ko akasin haka fa da gaske wata macece zata amsa sunan matar Jabir bayan ita, kuma ko da sakinta yayi a tarihin rayuwarta dai akwai shafukan da zasu zamana ta kasance mata a wajen Jabir. Saita nemi wanna natsuwar da takeji ta rasa, wani yanayi na rashin jin dadi da kishin da take dashi akan Jabir yayo mata sama. Kawai kuma ranar juma’a sai yace mata su Adda Farhana sun matsa masa saiya je wajen walimar sunyi hotuna, kenan har tarihin da ko ya taso ta manta Jabir ya auri wata bayan ita ba zai yiwu ba zasu kafa, taga yanda yan uwanshi suke da son shagali, bawai akan nasu bikin da akayi kwanaki bakwai ana shagali ba, tun a shekarun baya kenan, ko murnar zagayowar ranar haihuwa ma lamarine mai girma a wajensu, sam basa raina shagali.

Da kananun kaya ya fita a jikinshi yana ce mata ba zai dade ba, sai taji wasu kananun hawaye da tun ranar laraba take fama dasu sun zubo mata, lemon data dauko ma dakyar ya wuce makoshinta a kurbar farko, saita mayar ta ajiye, ta koma daki, tsautsayi, shine abinda ya sakata daukar wayarta, tsautsayin kuma ya sakata bude status din Nenne data dora wani gajeran video, inda ta dauko Sa’adatu tun daya kafarta har zuwa saman kanta, a zaune Aisha take saida ta mike tsaye batare da ta sani ba, da wanne irin idanuwa ta dinga kallon Sa’adatu? Ita ba haka ta ganta ba sam, yar yarinyace fa, yar shekaru goma sha, ba wannan macen data amsa sunan mace ba, ba wannan kyakkyawar matashiyar da zatayi gogayya da kowacce mace ba, ba wannan Sa’adatun da zata saka ayi watsi da kwalin PhD bama degree ba idan akazo hadata da wata mace, wayake ta kwalayen karatu yana ganin wannan a gaban shi.

A haka Jabir zaije ya ganta? Babu mayafi? Babu hijabin da ya lullube komai har bata gani ba ta zabi tayi wautar hadata da mijinta? Da yarjejeniya ko babu, yardar da take da ita akan Jabir ce ta ruguje, ita kanta da take mace inta ga Sa’adatu tasan me kyauce, tana kuma da halittar da ita bata da ita, tana da duk wani abu da zai iya motsa zuciyar lafiyayyen namiji, harda baudadde irin mijinta kuwa. Ta rasa ya akayi ta kasa ajiye wayar, ta dinga bin status din yan gidansu Jabir tana budewa, aikuwa zazzabi mai zafin gaske ya rufeta lokacin da taci karo da video din Jabir a kusa da Sa’adatu, rike da hannunta, numfashinta har wani sama-sama ya dingayi, data tashi gabaki daya wayar ta kashe ta kwanta, hawaye na zubo mata, ciwon kai, na jiki dana zuciya duka ya saukar mata lokaci daya, sai kuma taga kamar Jabir ya yini bai dawo ba, ya za’ayi ya dawo yana tsaye kusa da mace irin wannan?

“Tasha”

Ya kirata a hankali

“Kinsan ina sonki ko? Kinsan kafin ke da bayanke ban taba kallon wata mace da idanuwan da nake kallonki ba…dan Allaah karki fara dora ayar tambaya akan wannan yardar da kikayi mun, naje saboda bana so su zargi wani abu, naje saboda abinda kowa yake tsammani daga wajena ne, kuma anyi angama na dawo wajenki, where I belong, tare dake”

Wannan karin shessheka ce ta kwace mata

“Tana da kyau Jay, naganta, tana da kyau”

Sake riketa yayi sosai wannan karin

“Ba zance bangani ba, kinsan ba zanyi miki karya ba ko da don kiji dadi ne, tana da kyau, amman iya idanuwana hakan ya tsaya, bana jinta anan…”

Ya fadi yana jan hannun Aisha ya dora akan kirjinshi, inda zuciyar shi take

“Ina sonki, babu wani abu da zai taba canza hakan, kinsani ina da dama da halin auren duk macen da nake so, bani da ra’ayin hakan, ke kadai kin isheni, dake kadai kuma nake son karasa rayuwata, ko da wasa ban hango sake auren wata ba, wannan ma kinfi kowa sanin akwai dalili”

Bata san ko kishin da takeji bane take so ya barta ko zata huta shisa zuciyarta ta kama duk wasu kalamai daya dingayi tana rike mata su gam-gam, kafin kalaman su kare, ya jaddada mata har abada shi din nata ne ta hanyar da yafi kalamai tasiri

Shekara daya zuwa shekara daya da rabi yace
Sa’adatu zata zauna dasu
Kafin ta fice daga rayuwar su kamar hakan bai faru ba

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 23Tsakaninmu 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×