Skip to content
Part 26 of 55 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

“Disappointed”

Kalmar tazo masa cikin kai, zai kuma iya kirga mutane nawa ne a rayuwar shi masu matsayin saka shi jin wannan yanayin amman basu taba amfani da matsayinsu ba, ko yaushe cikin kaffa-kaffa sukeyi dashi da kuma abinda zai sosa masa rai. Amman da tsakiyar dare, kamar marar gaskiya, haka ya zame Aisha daga jikin shi ya mika hannu ya dauki wayar da ya bagarar tun dawowar shi gidan, bayan sunje dakinsu, yazo sake kaya ya cirota daga aljihu, kamar ko da yaushe idan Aisha tana gabanshi, idan kuma suka kadaice haka, duka sun sabama kansu ko ba zasuyi hira ba, basa daukar waya, kowa zai kwanta ne ya dan bari kwakwalwar shi ta sarara. Sai dai yau babu abinda yake so yayi saiya duba wayar, yaga me Sa’adatu ta turo masa. Hannun shi har kaikayi ya dingayi, haka ya kauda kai, kawai kuma saiya dauka yaga ba ita bace ba? Yaga MTN ne sukeyi masa tallarsu marar amfani?

To ko dai bata ga sakon shi bane? Gashi ya rigada ya goge balle ya duba yaga ko sakon yaje mata, ta bude ko bata bude ba. Cikin sanyin jiki ya ajiye wayar ya gyara kwanciyar shi a bayan Aisha da take bacci, shima rufe idanuwanshi yayi, ya dai jima kafin bacci ya dauke shi saboda tunanin daya cunkushe masa. Sai dai yau bayan Asuba saiya kasa komawa baccin safen daya saba kafin lokacin fitar shi, haka ya dinga kallon Aisha tana shirin fita aiki, suna dan kananun hira harta gama, shifa shisa bai taba sha’awar aiki a karkashin wani ba, saboda irin wannan takurar, musamman kuma aiki irin nata da har ranakun karshen mako basu da wani hutu. Dan dai tana so ne, amman me ma zatayi da albashin? Yana da halin biyanta ninkin shi duk watan duniya bayan duk wata hidimarta, sannan kasuwancin da takeyi a gefe ya tabbata yana kawo mata kudi fiye da wannan dan albashin da ake biyanta, kawai son aikin ne yake danne mata ganin wahalar da take cikin shi.

“Fitar na sakani nishadi, kuma yana ragemun tunani, ina son aikina sosai Jay, saboda kai na tsaya anan, kafi kowa sani”

Tace tana saka shi yin shiru lokacin da ya tabayi mata mita, kuma gaskiya ta fada, saboda shi ta tsaya a wannan gidan Radio din. Tun lokacin fatan shi in sun haihu yaransu kaf su dauko kwakwalwa irin ta Aisha, tana da kokari, irin kokarin da in har tace maka sakamakonta baiyi kyau ba, to zaka samu ta gaza samun cikakken makine da guda biyar ko sama da hakan, wannan faduwa ne a wajenta, shi bai damu ba, ba dakiki bane ya sani, amman kuma bashi da kokarin nan, yana cikin mutanen da za’a iya kiran kwakwalwarsu da tsaka-tsakiya. Ta gama makaranta da sakamakon da zata iya aiki a ko ina ta zaba, kuma iyayenta na da sanayyar da zasu samo mata gurbin aiki, da kudin da ko nawa ne zasu siya mata idan akace ciniki za’ayi. Saboda shi saita hakura, ta tsaya iya gidan radio din nan na Kano, idan yace shima zai hanata zai so kanshi da yawa.

Gefen fuskar shi ta sumbata, kafin ta rataya id card dinta a wuya tanayi masa sallama ta fice. Gyara kwanciyar shi yayi, sai dai yanda duk yaso bacci yaki bashi hadin kai, yanda kuma duk yaso ya karyata ya damu yaji yanda Sa’adatu ta tashi saiya kasa, ya dauki wayar shi, ya lalubo lambarta, ko babu komai dai yanzun a karkashin kulawar shi take har sai yarjejeniyar su ta kare, kuma a ciki akwai alkawarin zai kula da ita, jin ya ta tashi na cikin wannan kulawar. Sai dai harta yanke bata daga ba, ya sake kira a karo na biyu nan na haka. Saiya saka ma ranshi watakila bacci takeyi, ko bata kusa da wayar. Farhana ya turawa sako kan maganar maigadi da kuma mai’aikin da za’a samo musu. Ya ajiye wayar ya tashi ya shiga bayi da niyyar watsama jikin shi ruwa, watakila inya dawo ya samu ya dan runtsa.

Sa’adatu kuwa baccin da Jabir ya hasaso shi take kwasa, kusan rabin daren rabashi tayi tana kuka, kadaici da tsoro duka sun tarar mata waje daya, ga wani irin shiru mai saka firgici, motsi in ba nata ba, batajin alamun motsin komai. Hanjinta da ya tattare waje daya da alamun yunwa, da kuma cikin nata daya fara kara yasata saukowa daga kan gadon da take kwance tana jan ledojin da Jabir ya ajiye gabanta ta fara budewa, kaji ne a guda daya, wasu irin yoghurt da kuma lemuka a dayan, harda ice cream din da duk da bata bude ba tasan ya narke, tarkace ne sosai da zatayi tsalle ta kara inda a cikin yanayi mai dadi take. Robar yoghurt daya ta kwance tana hadawa da kazar, sai gata taja kasan skirt dinta ta goge fuskarta sosai, ta kuma gyara zama yanda taji komai na wuce mata. Anya ta taba cin kaza mai dandanon wannan kuwa? Harda wata miya miya a gefe da tasha albasa. Da cikinta ya dauka, saita tattara komai ta kulle, abinda duk take tunanin zai iya lalacewa, taga karamin fridge anan dakin baccin nata sai ta nufe shi da ledojin, sai dai lemukane a ciki da wasu irin cake, sai ruwa kadan, ta fiffito dasu tunda ba wani girma gare shi ba tana saka kajin da ice cream, da safe sai ta fita ta duba idan akwai babba ta mayar can.

Yanzun kam babu abinda zai sakata fita, yanda ta murzawa dakin mukulli ai sai gari ya waye. Ko kayan jikinta bata sake ba, haka ta kwanta, ita da batason haske in zatayi bacci, yau tsoro ya hanata kashewa, sai dai ta dinga juye-juye, lokaci zuwa lokaci tana sauke ajiyar zuciya, dabarar saka dankwali ta kulle idonta ne yazo mata, hakan kuwa tayi, saiga bacci ya soma fusgarta. Baccin da taga kamar tana farawa aka soma kiraye-kirayen sallar farko na Asuba. Dakyar ta iya raba jikinta da gadon ta nufi bayi, ta samu ta dauro alwala ta fito, akwai hijabin da saka mata lokacin da za’a kawota, shi ta dauko tazo ta gabatar da sallah, tana idarwa bata iyayin azkar ba ta koma ta kwanta. Bata tashi ba sai wajen goma saura, ta jima a kwance tanajin kamar idanuwanta ne kawai a bude, amman sauran jikinta bai gama tashi daga baccin ba a yanayin nauyin da yayi mata.

Wanka tayi da ruwa mai zafi kafin ta wartsake, ta samu wata doguwar rigar atamfa, itama sabuwa ce ta saka, sai taji inama zata samu hula, kan ta bari a haka, taje saloon an gyara mata shi duk da ba tsayi gare shi ba, a cike yake sosai, kuma tana da yalwar shi, tunda har kusan goshinta akwai wani da ya kwanta yayi luf-luf. Ba’ayi mata kitso ba saboda tana ta musu mitar kan nayi mata ciwo. Sai suka kyaleta, a lokacin kuma babu wani ciwon kai, kananun kitsone bataso suyi mata su barta da tsifa. Bude dakin tayi ta nufi falon, tana kare masa kallo, yayi mata kyau sosai, kayan ruwan toka, sai kafet da labulayenta da basu kai kujerun haske ba, data karasa sai data shafa kujerun, murmushi na kwace mata, ko ina da ina ta shiga, har kitchen, inda ta bude fridge din tana mamakin ganin kayan miya, nama harda kifi a ciki. Kuma taga store dinma iya ganinta duk wani nau’i na danyen abinci akwai, kuma harda dankalin turawa tagani cikin wani matsakaicin kwando, ga wajen dining dinta ma daga wani lungu akwai wani fridge din.

Nishadi ta tsinci kanta a ciki marar misaltuwa, ta koma daki ta kwaso kayan data ajiye a fridge. Sai lokacin kuma ta tuna da wayarta da take a vibration, ta duba tana daukota, da ta bude sakon Jabir sai da zuciyarta ta buga, ta karanta a hankali, sakon haka kawai saiya rage mata nishadin da take ciki, saboda ya tuna mata duka gidan nan da kayan shi basa nufin mallakinta ne har abada, lokaci take dashi kayadadde a cikin shi. Ga kuma kira nan har guda biyar da bata duba taga su waye ba, ta cire wayar daga vibration, ta fita tare da ita. Robar ice cream daya ta dauka, tayi kankara, anan dining ta zauna ta shanye, tana jin sanyi na kadata, amman bata damu ba, sun dai dauke wuta, a gidansu Jabir da tayi aiki ta iya amfani da microwave, kuma taganta a kicin dinta, data dumama namanta na jiya. Harda ma shawarmar data gani, kan kujera ta koma ta kwanta, ba yunwa takeji can ba, watakila su dawo da wutar.

Bacci ne ma yake soma fisgarta sai taji kamar ana hon, data saurara kuwa sai taji an soma jerawa babu kakkautawa, haka kawai gabanta ya fadi cike da tsoro, wayarta data ajiye a gefe ta hau ruri, ta dauko wayar tana ganin lambace da bata adana ba, ta daga ta kara a kunnenta

“Kizo ki budemun Sa’adatu”

Muryar Jabir ta daki wani abu fiye da kunnenta, data sauko kafafuwanta daga kujerar ta mike kuwa sai taji kamar jikinta na dan rawa, daren jiya ya fado mata, hannunshi daya daga ya share mata kwalla kamar ya damu da ita sai yanzun yake dawo mata, taushin muryarshi da yake mata magana. Zafin da taji a kafarta yasa ta tuna babu takalmi ta fita, a gefe daya tana mamakin ranar data fara budewa, gata nan a wasu sassa na gidan, ashe gate din haka yake da nauyi, data zare suka sakatun, sai ta raina karfin da take tunanin tana dashi wajen budewa, hannuwanta har wani jini-jini taga sun tara, data koma gefe ta bashi waje dan ya shigo da motar, saita tura baki kadan cikin sabon da tayi in tana cikin yanayin rashin jin dadi, tana kuma murza hannuwan nata da suke mata zafi. Haka Jabir yayi parking din motar ya fito sanye da wasu riga da wando na kanti masu laushin kallo a ido, daga inda take kuwa tana iya ganin kyallin da gashin kanshi yakeyi, gashin da yake kara tabbatar mata da cewar yana da wani yare daban ko da kuwa akwai Hausa a ciki, to da wani sirkin.

A nutse ya tako zuwa inda take, saita sauke idanuwanta, har lokacin bata daina murza hannuwanta ba, hakan yasa shi kallon hannuwan da suke dauke da kunshinta kamar lokacin aka zana, ja da baki, ya kara kawata hannuwan nata a idanuwan shi

“Me ya samu hannun?”

Tambayar ta kubce masa

“Kofar na da nauyi, dakyar na bude”

Ta amsa cikin sangartar da bata sanin tanayi duk idan an nuna mata kulawa, sangartar data saka shi kamo hannun nata daya ya dan jata gaba ta hade wani yanki cikin tazarar da take tsakaninsu, dubawa tafin nata yayi, ya dan saka babban yatsan shi ya murza hadi da fadin

“Sannu”

Kafin ya saki hannun nata kamar wanda ya tuna wani abu yana fadin

“Yau za’a kawo maigadi…akwai zafi sosai”

Yana fitowa daga mota zafin ya dake shi, irin dukan nan na wanda yana fitowa daga AC ya shiga mota ya kunna wata, yanzun kuma ya sake fitowa, so yake kawai ya karasa cikin gidan, shisa ma ya fara tafiya, Sa’adatu na bin shi a baya, tana kallon inda ya cire kafa hadi da mayar da tata a wajen, sai dai me, yana shiga cikin gidan wani zafin ya sake dukan shi

“AC din a kashe yake ne?”

Ya tambaya tunda yasan akwai, kai Sa’adatu ta girgiza masa

“An dauke wutane”

Da rashin fahimta yake kallonta, kaifin idanuwan shi na sakata janye nata a hankali

“Wanne irin an dauke wuta kuma?”

Saboda shi bai taba sanin wani abu dauke wuta ba tunda yake a rayuwar shi, ko kafin solar manyan janareta ne ke aikin a gidansu, bai taba ganin babu wuta ba in ba kwai aka kashe ba, hakama gidajen ‘yan uwan shi. Shisa ya zaro wayar shi yana fara danna lambar Farhana ya kara a kunne, idanuwanshi nakan Sa’adatu da takejin duk ta takura da tsayuwar da tayi a gabanshi, tana kuma tuna rashin dankwalin da bata dashi

“Adda…”

Ya fadi a madadin amsa sallamar da tayi masa, yana kuma katse soma tambayar lafiyar shi da ta amarya data soma

“Bana ce a saka komai daya kamata a gidan nan ba?”

Daga dayan bangaren tace

“Akwai wani abu da baku gani bane? Har kayan abinci duka na tabbatar an saka fa”

Kai ya girgiza a hankali, sosai zafin ya fara damun shi

“Babu wuta”

Ya fadi yana saka Sa’adatu kallon shi kadan

“Daukewa akayi”

Ta gyara masa

“Meye bambancin babu wutar da daukewar da akayi?”

Ya tambayeta yana kuma cewa Farhana

“Akwai zafi sosai Adda”

Cikin sanyin murya ta amsa shi

“Tunani na ne bai kai ba, sai dai a saka muku solar”

Shi koma meye dai

“Dan Allaah Adda, yau fa…”

Baima damu daya ce mata nawa za’a kashe ba, tunda yasan ba karba zatayi ba, kusan kowa a gidan in dai yana bukatar ayi masa komai cikin hanzari to Farhana yake nema, tasan wani da yasan wani da za’a kira azo ayi maka komai cikin kwanciyar hankali, da har tsokanarta sukeyi, yanzun ne suke ganin amfanin hakan sosai da sosai. Yana sallama da Farhana bayan tace masa anma samu maigadin, zata hado shi da direban gidanta yazo ya kawo shi tunda yasan wajen, ya kalli Sa’adatu

“Zafi nakeji”

Dan ya fara zufa ta kasan rigar shi, da tayi yunkurin bude bakinta saita rasa abinda zatace masa, dan ita batajin zafin da yake magana akai, asalima ji tayi gidan na da iska sosai, gidansu na farko fankar samace, irin tada din nan da zaka kure gudunta, amman in ba wuta bace mai karfi aka kawo saika manta ma akwai wata fanka, in zafi yayi zafi kuwa ka saka mafici kayi fifita, ko a daura net a kwanta a tsakar gida. Karshen abinda zakayi ka samawa kanka sauki shine ka watsa ma jikinka ruwa, to wannan dinma ba kullum yake samuwa ba, tunda ruwan siyen shi suke, ba suda rijiya ko famfo, garama unguwarsu ta yanzun, akwai gidan da suke da irin rijiyar nan, kuma suna bari dul meso ya diba, almajiri Abdallah ya samu, kullum ya cika musu ko ina a biyashi, kuma ita ta siyi fankar kasa ta saka, to a sati sau nawa ne ake kwana da wuta?

“Ki zo mu koma mota, mu jira maigadin yazo”

Jabir ya fada, dan ba zai iya zama cikin dakin nan ba, sai dai maimakon hanyar waje saiya nufi wajen dining ya bude fridge ya dauko ruwan da harya fara kankara, batare daya kalleta ba yayi hanyar waje, ita sai taga kafafuwanta sunyi daki, hijabin da tayi sallah ta dauka ta saka, ta fara neman takalmi, cikin na lefe da aka jera mata wajen ajiye takalma ta dauki wani filat mai kyau, sannan ta fita, a motar ta samu Jabir, ya kunna yana zaune yana kokarin kwance robar ruwan daya dauka, saita bude gaban a hankali itama ta shiga, kallonta yayi yana mamakin hijabin da take jikinta, shi da yake neman maraba da kayan jikinshi saboda zafin daya sha, duk da yanzun ya kunna AC din motar, kuma ta fara daukar sanyi

“Haka kika kwana jiya? Cikin wannan zafin?”

Murmushine ya kwace mata

“Nifa banji zafin ba…”

Ta amsa shi da dukkan gaskiyarta, sanda ta kwanta da wuta, har rufe jikinta saida tayi saboda sanyin AC da bata saba dashi ba

“Saboda baki da lafiya”

Wannan karin dariya tayi, Jabir ya kurbi ruwan hannun shi yana rufe robar

“Da gaske in kina da lafiya dole zakiji zafin”

Wani irin sama-sama take jinta, Jabir din da take gani daga nesa, Jabir din da amsa gaisuwarta yake masa wahala, Jabir da take ma kallon wani mutum maiji da kanshi, irin mazan littafin nan da matansu ma sai sunyi sa’a sukejin hirarsu, shine suke zaune a mota daya yau, da kamshin shi daya cika motar, yake mata magana haka, har yana sakata dariya. Lallai, wata kaddarar dole ne ta baka mamaki. Yunwar da yaji na saka shi cewa

“Me zakici?”

Kai ta dan girgiza

“Ina da sauran kayan jiya, banajin yunwa tukunna”

Shikam yanaji, burger ce guda daya a cikin shi da ruwan shayi, tun daren jiya, Aisha kuwa ruwan shayin ne tasha sai kwai guda biyu data soya. Yanzun din baima san meya kamata yaci ba

“Zakaci ne?”

Ta tsinci kanta da tambaya, ya girgiza mata kai a hankali, wani irin shiru na ratsa motar, shirun da yasa ta fyskancin bugun da zuciyarta yakeyi, Jabir kuwa saiya kara gyara zaman shi sosai, yanajin sanyin motar na ratsa shi, a gefe daya kuma wani dumi da baisan na menene ba yakejin yana mamaye shi a hankali, ta gefen idon shi yake ganin Sa’adatu na wasa da yatsunta, yatsun da yake so ya kara kamawa, saboda akwai wani abu a tare da hannun nata da yayi masa. Sosai yake kokarin mallakar kanshi wajen ganin baiyi kwakkwaran motsi ba, sai zuwan direban Farhana ya cece shima, hakan yasa shi ya fita sukayi magana da maigadin da yace sunan shi Danlami, dattijo ne mai cike da kamala da dattako.

Daya koma motar sai ya dan kalli Sa’adatu yace

“Tafiya zanyi…”

Ita data kalle shi sai yaga rauni a cikin idanuwanta, in ba kuma yaudarar kanshi yakeyi ba, kamar bataso ya tafi

“Za’azo a saka miki solar din, nasan ba zai wuce yau ba. In kina bukatar wani abu kiyimun text”

Kai ta daga a hankali, data bude murfin motar ta fita, ta mayar ta rufe, sai taji ta rufe da wani abu da batasan menene ba, tana kallon Jabir din yaja motar, maigadin nasu ya bude masa ya fita, zata rantse kuma ya saka idanuwan shi cikin nata, har murmushi yayi mata kafin ya juya motar

Haka kawai taji wani irin kadaici ya lullubeta

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 25Tsakaninmu 27 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×