Lissafi ya cakude masa a kwanakin, saboda kusan duk wasu kaya da suka saka oda dinsu daga kasashen ketare sai sukazo a lokaci daya. Saukin shima bashi yake zuwa Legas din yin clearance ba, yana da amintattun daya wakilta dan hakan kawai, kuma tun fara kasuwanci dasu, bai taba kamasu da rashin gaskiya ko kankani ba. Sai dai akwai abubuwa da suke bukatar dole sai yana tsaye akai, a gefe daya kuma ga hidimar neman asibitin da yakeyi, dan Aisha kamar ta sakar masa komai ne, kafin yayi tsegumi kuma saita rigashi da kawo tarin uzurin aiki ko tace ciwon. . .