Skip to content
Part 27 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Lissafi ya cakude masa a kwanakin, saboda kusan duk wasu kaya da suka saka oda dinsu daga kasashen ketare sai sukazo a lokaci daya. Saukin shima bashi yake zuwa Legas din yin clearance ba, yana da amintattun daya wakilta dan hakan kawai, kuma tun fara kasuwanci dasu, bai taba kamasu da rashin gaskiya ko kankani ba. Sai dai akwai abubuwa da suke bukatar dole sai yana tsaye akai, a gefe daya kuma ga hidimar neman asibitin da yakeyi, dan Aisha kamar ta sakar masa komai ne, kafin yayi tsegumi kuma saita rigashi da kawo tarin uzurin aiki ko tace ciwon kai, ya bita yanda yaga tana sone kawai, amman yana hango kwantacciyar damuwar da take dannewa a kasan idanuwanta, kishi hadi da wasu abubuwa da ya kasa karanta. Sunyi magana da Farhana tace masa an rigada an kammala komai tun washegarin ranar da sukayi magana.

Yaso ko wannan damar ce yayi amfani da ita dan yaga Sa’adatu da tunaninta bai barshi ya huta ba a kwanaki biyar din nan, sau biyu ya kirata suka gaisa, sai dai bayan gaisuwar da tambayar ko akwai abinda take bukata, idan ta amsa da babu sai su duka suyi shiru cikin rashin abin fada, gashi haka kawai sai yaji yana so ta cigaba da magana, balle kira na biyun nan da ta amsa shi muryarta can kasa, dauke da wani yanayi daya saukar masa da kasala, tace masa bacci takeyi. Haka ya wuni tana fado masa lokaci zuwa lokaci ranar, idan haka muryarta take idan ta tashi bacci ta cikin waya, tabbas zaiso yajita batare da wani shamaki ba, tunda yana da yakinin tazarar ta ragewa muryar armashi. Ganin yanda tunanin nata yake damun shine yasa bai kara kira ba, don ji yayi kamar yana bukatar yar tazara a tsakaninsu, saboda idan ya hada idanuwa da Aisha, sai yaji wani yanayi na rashin gaskiya na tsirga masa, kamar akwai abinda yakeyi da bai kamata ba, kamar kuma baya kyauta mata.

Wajen la’asar ya samu kanshi yau din, yana zama mota ya sauke numfashi yana dan gyara zama saboda bayanshi daya rike, ya kama mukullin mota da nufin murzawa, wayar shi da take aljihu ta sake daukar vibration, ya jita tun yana shagon shi na kayan jarirai, yasan ba Aisha bace ba saboda tana aikin rana ne zuwa dare. Kuma kamar sakone ma ya fara shiga sau biyu, kafin wasu mintuna kuma kiran ya biyo baya, dan karamin tsaki yaja yana karkatawa ya zaro wayar daga aljihun shi. Zuciyar shi ta tsinke ganin Sa’adatu ce, kawai sai yaji a jikinshi akwai wata damuwa, ya cire key din wayar kenan, yaga sakonta daga sama, da hanzari ya bude

“Bani da lafiya”

Ta rubuto a takaice, sai kuma na biyun

“Dan Allaah kazo ko ka turo a kaini asibiti, cikina na ciwo sosai”

Jikinshi har rawa yake lokacin daya danna lambarta yana bin bayan kiran, sai dai harta yanke bata daga ba, ya sake kira yana murza mukullin motar ya tayar da ita, yaja yana nufar titi da gudun daya wuce ka’idar shi. Sa’adatu bata daga kiran ba sai ana hudu, muryarta can kasa kamar tayi kuka ko kuma tana cikin yinshi ma, saboda

“Hello…”

Din data furta a shake ta fito, kuma can kasa

“Gani na zuwa, sannu, yanzun ina hanya, minti goma zuwa sha biyar zan karaso In Shaa Allaah…”

Batayi magana ba, amman yaji a jikinshi kai ta daga masa, sai kawai ya katse kiran, yana mayar da wayar aljihun shi ya maida hankalin shi kan tukin da yakeyi. Cikin kasa da mintinan daya fada mata kuwa ya karasa, saboda kamar ansan yana da uzuri mai karfi, haka ya dinga samun hanyoyin da saukin cunkoso kamar ba yammaci ba, kuma kamar ba garin Kano ba. Wani irin hon ya dinga dannawa a jere a jere harya tsorata maigadin daya bude masa cikin hanzari, ya shiga da motar yana kashewa ya fita, cikin sassarfa ya karasa yana tura kofar da zata hadashi da falon batare daya damu daya kwankwasa ko kuma yayi mata sallama ba, kan kujera ya hangota ta saka hijabi a jikinta, ya taka ya karasa, yanda ta lafe a cikin kujerar yasa zuciyar shi sake bugawa, tsugunnawa yayi yana kallon fuskarta, idanuwanta a rufe

“Sa’adatu…”

Ya kira a hankali, cike da wani taushi da yasa ta bude idanuwanta da sukayi zuru-zuru ta kuwa sauke cikin nashi da taji kaifinsu ya ratsa har kwanyarta, yana kuma sakata dan rissina nata idanuwan

“Tashi…”

Ya fadi yana mikewa, ganin yanda take yunkuri kamar an zare mata lakka yasa ya kama hannunta yana taimaka mata ta mike, sai lokacin ya kula akwai takalmi a kafarta, sosai yayi mamakin ganin bata da kwari ko kadan, saiya riko damtsen hannunta sosai yana bata tallafin daya kamata, ya jata suka fita daga gidan zuwa motar shi, ya bude gaban yana taimaka mata ta shiga, ya rufe, ya zagaya ya shiga shima. Tukunna ya kunna motar yayi baya da ita, ya fadawa maigadin zasuje su dawo. Tambayoyine fal a ranshi, tace cikinta ne yake ciwo, tun yaushe? Me yasa tunda ya fara bata kira shi ba? In har tayi laushi haka bayajin yanzun ne ya fara mata ciwon, sai yakejin kamar ranshi na so ya baci, cikin abubuwan da bayaso, wasa da lafiya irin haka na daya daga ciki.

Komin kankantar ciwo yana son ya sani, kuma za’aje asibiti, tun Aisha na gwada hakurin shi akan haka har tazo ta daina saboda wani tashin hankali da yayi mata sanda tayita fama da ciwon kai da kasala, saita sha paracetamol tayi shiru, saida ta tashi ta yanke jiki ta fadi, ashe jininta ne yayi kasa. Farkawa tayi ta ganshi yana kai kawo a dakin da take kwance, bayan ya kira mata likita, ya tabbatar da taji sauki ya kuwa rufeta da fadan da watakila da ta mayar masa da magana ko tayi kokarin yin wani bayani, ranar zai karyata maganar kannen shi da suke cewa basajin kome ya faru Jabir zai iya dagawa ko namiji dan uwanshi hannu, balle kuma mace, barshi dai da fada, shima idan an kure hakurin shine.

Wani asibitin kudine nan kusa da unguwar tasu daya gani, kuma yaga alamar kamar zaiyi kyau ya shiga yana samun waje ya ajiye motar, aikuwa tun daga ma bakin kofa wata Nas tazo tana taimaka musu, ta rike Sa’adatu tana zaunar da ita, Jabir kuma ya fara kokarin bude mata kati, sai dai da akazo tambayar shekarunta ne saiya dan kalleta

“Sha tara”

Ta fada cikin harshen turanci, ya maimaita a hankali, sai yaji kamar ba ma’aikacin kawai ya fadawa shekarun Sa’adatu ba, harda kanshi. Ya sake kallon Sa’adatu da yaga tana yiwa Nas din nan magana a hankali, ita kuma tayi mata nuni da wata yar hanya, kafin suka mike kusan a tare tana kamata ta tayata zuka nufi hanyar, daya gama komai, ya biya saiya zauna da dan karamin katin da suka bashi yana jiran su Sa’adatu, Nas dince dai ta sake yi musu jagora bayan sun dawo har inda zasu ga likita, akwai mutum biyu a wajen jiran, hakan yasa suka zauna suka jira, duk minti Jabir na satar kallon Sa’adatu data sadda kanta kasa tana dan buga kafarta cikin yanayin da baya bada sauti. Sai dai baisan addu’a takeyi a cikin ranta ba, karya bita dakin likitan, ya barta ta shiga ita kadai, saboda bata san yanda zata bude baki tace cikinta ne ya rikice ba tun wajen karfe sha biyu na safe, take zirga-zirgar shiga bayi, kuma tun a shiga ta biyar cikinta ya fara murdawa.

A kwanakin nan zatayi karya idan tace bata dinga baza ido tana kallon kofa cike da tsammanin shigowar Jabir ba, haka kuma zatayi karya idan tace ranta bai sosu ba, ta dauka ko dan aikin solar din da akayi zaisa yazo ya gani, ko da ita bai dauko kafa takanas dan ya ganta ba. Kuma taga ya kirata ranar da safe, washegari ma ya kirata, tana ma bacci taji wayar na ruri, ta janyo da nufin latsewa ta kashe saita dan bude ido daya taga shine, shisa ta daga, da ta sake dubawa kuwa duka maganar da sukayi sakan arba’in ce, bata ma kai minti ba. Bata kuma ganshi ba, ta wuni kallo har saida ya fita daga ranta, ta dinga zagaye-zagaye cikin gidan, ta shiga wannan dakin ta fito ta koma nan, ga wayarta dai akwai data da kati, amman kuma duk wanda ta kira a cikin ‘yan uwanta in suka gaisa sai suce ta gaishe da Jabir su takaita wayar, kamar suna gudun shiga lokacinta dashi.

Lokacin da basu san bata dashi ba, wayarma ta danna, amman kuma zuciyarta a cushe take, kadaici ne da bata taba sanin irin shi ba ya lullubeta, saima da daddare data kwanta, duk da babu tsoro a ranta tun ranar da aka kawo maigadi, sai dai kadaicin, da tunanin Jabir na tare da Aisha a wannan lokacin. Jabir da yake amsa sunan mijinta kamar yanda yake amsa na Aisha, amman kuma tazarar da take tsakaninsu a wajen shi babu zaren da zai iya auna tsayinta. Shisa ta maida hankalinta kan kayan kwalam da makulashen da bata da shamaki dasu a yanzun, kamar tana son huce takaicinta akansu, danma duk tarin naman nan, kajin da kifin, bata san yanda zata sarrafa su ba idan ya wuce a soya, a saka a miya, a kuma yi farfesu.

Ita da maigadi kuwa morewa sukeyi sosai, shima batayi masa kwauro tunda taga komai a wadace, kuma Jabir yace mata duk abinda take da bukata ta fada masa. Sam ba zatayi wasa da wannan damar ba, morewa zatayi kafin lokacin da take dashi ya cika. Safiyar yau din dankalin turawa ne ta soya musu da kwai, data dibarwa maigadi ta dawo, taga waken gwangwani da yawa a store, taje ta dauko daya ta bude tana zubawa a gefe, ta hada dashi taci iya abinda zata iya ta mayar. Ba’ayi minti talatin ba, bayan tayi wanka ta saka wata Abaya marar nauyi, saita zo ta dauki yoghurt tana sha tana kallo, zuwa can kuma ta tuna da soyayyen kifin da take dashi a kitchen da wani yaji mai dadin gaske data gani a roba, dan data duba yar takadar jiki batayi mamakin ganin harda nama a kayan hadin yajin ba, shisa dadin shi ya isa. Ta dinga dangwalawa tana ci, bata gane illar da tayiwa cikinta ba sai da ta mike dan dauko ruwa taji tana wasu numfarfashi.

Koshine tayi da ya saukar mata da rashin jin dadi, saboda cikinta yayi mata bake-bake, data kwanta kuma ba’a rufa minti sha biyar ba taji cikin kamar ya kumbure mata, tunda ya fara wasu kananun kara, daman da dare ma Allaah ne dai ya dubeta, ta kwaba madarar data gani kusan rabin kofi da Milo ta dawo ta zauna kan gado ta dinga sha, saida ta gamane ma ta dinga addu’ar Allaah Yasa kar cikinta yayi ciwo. To gashi yau ta dinga gamje-gamje, aikuwa data fara shiga bandaki, tun tana ganin kamar idan ta gama fitar da duka abinda yake cikin nata zaiyi mata sauki harta fara galabaita, ta duba jakarta tana da kudi wajen dubu bakwai, tun sauran na hidimar biki, ta dauki dubu daya taje ta samu maigadi ta bashi tace ya siyo mata flagyl, ya jima sosai kafin ya dawo, sao dai babu aikin da yayi mata, zuwa uku na yamma da hawaye ta fito daga bayi tana bin bango, kafafuwanta har rawa suke, da ta sake shiga kuma taga ya hado da amai sai tsoro ya kamata.

Tana tuno yarinyar makotansu lokacin ma basu da wayau sosai da ta rasa rayuwarta sanadin amai da gudawa. Dan abin ya dinga bata mamaki har take cewa Amira

“Daga mutum yayi gudawa shikenan saiya mutu?”

Duk bayanin kuma da Amira tayi mata ita dai ba wani fahimta tayi ba, sai da ta dan fara hankali ne sosai ma ta gane, tunda Kano na daya daga cikin jahohin da duk zafi sai anyi fama da annobar kwalara. Sai dai duk sanda zata ga ta fara shiga bandaki fiye da misali sai abin ya fado mata. Sosai cikinta yake murdawa kamar ana kulle mata hanjin ciki, shisa tunanin kiran Jabir ya fado mata

“Taso…”

Jabir da bata ga mikewar shi ba ya fadi yana katse mata tunanin da takeyi, hannunta ta saka cikin nashi daya mika mata, ya dagata suka shiga dakin likitan, ta zauna, shikuma yayi tsaye a bayan kujerar da takeyi, yana yawo da idanuwan shi tsakanin ita da likitan daya fara jera mata tambayoyi tana jinta a takure lokacin da take amsawa

“Kina zawo?”

Ya tambaya kai tsaye babu wani sakayawa bayan ta fada masa cikinta na ciwo kuma tayi amai, wata irin kunya ta rufar mata, a hankali ta daga masa kai

“Zaki iya tuna tun wajen karfe nawa kika fara?”

Kan dai ta sake dagawa, sai da ta ga ya kalleta tukunna ta bude baki

“Wajen sha biyu”

Daya tambayi ko ya kai shiga nawa tayi sai tai kasa da kanta sosai saboda ta bace lissafi, goma? Sha? Ko fiye da haka. Muryarta a raunane tace

“Goma ko fiye da haka”

Jabir da yake bayanta ya rike kujerar da hannun shi yana kokarin danne bacin ran daya taso masa, goma ko fiye da haka, ashe bata da hankali? Tun wajen sha biyu? Sai karfe hudu da wani abu tayi tunanin neman a taimaka mata, ita kadai a gida, inda wani abu da a sameta fa? Ya kalli danginta yace musu me? Saboda auren yarjejeniya sukayi ko me? Baiyi mamaki ba da likitan yace zasu riketa zuwa safe jikin tunda da ya tambayeta ko taci wani abu haka tace dankali kadai taci da wainar kwai. Sai da sukaje dakin da Jabir ya bukaci na mutum daya yake so, tukunna aka fara bata taimakon daya kamata, ganin yanda Jabir ya tsareta da idanuwa ne yasa ta daure lokacin da za’a daura mata kanula, duk da idanuwanta sun cika da hawaye, bata kaunar asibiti da duk wani abu daya dangance shi, wasu zasuce basa son allura, to ita har maganinma bata so.

Ko gidansu ana cewa in anga tana neman magani to tabbas ta fara ganin farin haske ne. Saima kuma Allaah Ya dubeta Yasa bata daga cikin mutane masu yawan ciwo, inka cire ciwon kan da zai wahala ko Panadol ta sha masa, sai dan abinda ba’a rasa ba, ita ko period takeyi, dan ciwon marar na awanni ne, shikenan kuma sai wani watan. Ruwan flagyl aka fara daura mata, ta kwanta, idanuwan Jabir akan duk wani motsinta, shisa ta lumshe nata idanuwan, da yake dan karamine kuma bude shi sukayi, nan da nan ya kare, aka sake saka wani, sai da suka saka mata guda uku irin shi, tanajin wani daci-daci a makoshinta, tukunna suka saka mata babba, akayi allura a ciki, allurar da take tunanin itace ta sakata bacci.

Hakan yasa Jabir ya fita ya siyo ruwa, lemuka, kayan marmari, da kuma abincin da yake tunanin zata iya nema idan ta tashi, baisan me zataso ba, sai ya siyo mata fried rice da kaza, shikuma ya siyi plantain da kifi, dan yunwar yakeji. A hanya ya tsaya yayi Magriba, ya turawa Aisha text cewar wani abu ya dan rike shi ba zai koma da wuri ba. Har yaja motar shi ya koma asibitin kuma yana tunanin dalilin da yasa ya boye mata ciwon Sa’adatu da kuma cewar yana tare da ita a asibiti.  Har lokacin bacci takeyi, yaja kujeru biyu, ya zauna a daya, dayar kuma yayi amfani da ita wajen dora robobin abincin shi, tunda komai na Sa’adatu ya ajiye shi inda ya kamata. Kafin ya fara cin abincin shi a tsanake. Ya gama ya hada komai da wanda ya rage ya mayar a cikin ledar, wannan karin sosai yaja kujerar wajen gadon Sa’adatu yana kallon fuskarta da yanda take mayar da numfashi.

Akwai hula akanta, dan ta cire hijabin, sai dai hular tayi baya, yana kuma ganin gashin da yake kwance luf-luf har a goshinta, dama gefen fuskarta. Aisha na da yalwar gashi, sai dai bata dashi a wajajen da yake gani yanzun a fuskar Sa’adatun, sosai yakai kanshi ya leka, dai-dai lokacin data bude idonta tana saka shi yin baya babu shiri saboda kwata-kwata bai tsammaci zata farka ba, ita kanta ta tsorata, tana kuma da yakinin karfin bugun zuciyarta ne abinda ya mayar da ita ya kwantar da saita mike zaune. Sai da ya maida numfashi, ya samu ya tattaro nutsuwar data kwace masa

“Kin tashi?”

Kai ta daga masa, tana amfani da dayan hannunta ta janyo hularta ta sake rufe kanta sosai, tanajin idanuwanshi sun takurata sosai. Shiya fita ya kira likitan, ya dubata, kuma cikin ikon Allaah ciwon cikin ya fada mata, sai bakinta da takejin babu dandano, da kuma rashin karfin jiki. Hakan yasa shi cewa babu wata matsala, ya rubuta magani guda biyu da kuma ors daya dinga jaddadawa Sa’adatu kar tayi wasa, har zuwa washegari ya zamana bata sha wani ruwa ba ko abu mai zaki, shi zata dinga sha. Idan ruwan da yake hannunta ya kare sai a cire ya sallameta. Duk wani abu da Jabir yayi mata tayin shi kai ta dinga girgiza masa, sai kankana ta sha. Har takwas da wani abu kafin aka sallame su, lafiya kalau ta mike da kanta, shikuma ya dauki abinda zai iya ya kai mota, kafin suka tafi. Wani irin zaman shiru sukayi har suka karasa gidan, ta bude motar ta fito, ledar abinda ya rage ne da kuma ta kayan marmarin Jabir ya bawa maigadi.

Sannan ya shiga gidan, inda ya samu Sa’adatu harta zauna, akan kujera a gefenta ya ajiye mata ledar abincinta, ya dan ja numfashi

“Sa’adatu…”

Ya kirata da wani yanayi da yasa ta daga kai ta kalle shi, ta kuma kasa saukewa kamar wadda aka rike

“Lafiya na cikin abubuwa masu muhimmanci a wajena, musamman lafiyar mutanen da suke karkashin kulawata, a iya zaman da zamuyi, yau ya zama na karshe da zaki zauna da ciwo komin kankantar shi bansani ba, ko cikin dare ne, ko da yaushe ne, call me”

Ya karasa muryar shi na kara sauka, amman cike da kashedin da taji jikinta ya amsa, wani tsoro-tsoro na ratsata, a hankali ta daga masa kai, tana kuma samu ta sauke idanuwanta kasa

“Dare nayi, zan tafi, in kira wani yazo ya kwana dake?”

Kai ta girgiza masa, saboda haka kawai taji in bashi zai kwana ba, to zata kwana ita kadai, babu abinda ya cinyeta sauran ranakun, yau ma batajin wani abin zai sameta danta kwana ita kadai. Nazarinta Jabir yakeyi, sunanta makale a harshen shi, yana dannewa karya kirata, saboda yanajin inta dago zaiji kamar ya kamata ya zauna tare da ita, wani abu da yasan ba zai faru ba saboda bashi da kalaman da zaiyi amfani dasu wajen yiwa Aisha bayani.

“Ki daure kici abincin ko kadan ne, kisha maganinki kuma saiki kwanta. In da wani abin kiyimun text ko ki kirani”

Kan dai ta sake daga masa a hankali, bata yarda da muryarta ba shisa batayi magana ba, tana kallon kafafuwan shi ya juya, ta daga kai ta kalle shi harya fice daga dakin, taja numfashi tana kokarin mayar da hawayen da batasan dalilin taruwarsu ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.6 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 26Tsakaninmu 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×