Skip to content
Part 31 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Ba zatace ga lokacin data dauka a zaune ba kafin Jabir ya fito, ya sake kaya, ya saka wasu ruwan madara da suka nuna alamun na bacci ne da ake kira da pyjamas, a idanuwanta ma tana iya ganin laushinsu batare data taba ba

“Ke ba zaki watsa ruwa ba? Ga sallah kuma”

Mikewa tayi, sai taji dadi da shi yayo cikin falon, ita kuma ta wuce zuwa dakin daya baro. Sai dai alwala tayi, ta fara yin sallah, tukunna ta murza mukullin da yake ta cikin dakin, ta shiga wanka data fito jakar kayansu na gefe, haka kawai taji ba zata iya saka kayan baccin data dauko ba, kuma tasan ba zata iya bacci da doguwar rigar data mayar ba, ko a gida tana da kaya kala biyu data ware suka zama na baccinta. A gwanjo ma ta siyesu lokacin. Turaren Jabir ta dauka kala daya ta dan fesa, sannan ta bude dakin ta fita. Samun shi tayi yaja teburin dake cikin dakin zuwa gab da kujerar da yake zaune, gabanshi kuma robobin takeaway ne masu kyalli da ya bubbude wasu, wasu kuma suna rufe, hannun shi daya da tsinkaye guda biyu da a fim kawai take ganinsu.

Wani abu mai kama da taliya ne yake ci, sai kifin da take tunanin an rigada an gyara shi saboda yanda yake cinshi hankali a kwance, gabaki daya falon ya gauraye da kamshin abubuwan daya bubbude, idanuwanta kafe suke kan hannunshi da yanda yake sarrafa tsinkayen nan kamar wani abu mai sauki.

“Na kasa jiranki, yunwa nakeji.”

Ya fadi yana sake cika bakin shi da abinda ya dibo, a kasa ta zauna gab da teburin, saita rasa abinda zata dauka, sauran da bai bude ba ta fara bubbudewa, ta dauki farfesun kayan cikin data gani da dankalin turawa ta ajiye a kasa, ta kuma sake dubawa ta dauki cokali mai yan yatsu sai robar ruwa da wani lemon kwali, a nutse ta fara ci, farfesun yayi mata dadi. Tayi mamakin yawan wanda taci, ta kuma riga Jabir da harta gama yana cin kifin shi, wayar shi da saida ta fara vibrating tukunna Sa’adatu ta kula da tana ajiye akan teburin ya kalla, ya mika hannu ya danna gefe kafin yaci gaba da abinda yakeyi. Yayi hakan kuma sama da sau biyar, ko dai katse kiran da yake shigowa yakeyi, ko kuma wani abu yake dannawa ta daina vibrating har sai kiran ya yanke da kanshi. Kusan sau goma ana kiran nashi amman bashi da alamun dagawa. Daya karasa cinye kifin ma saiya dauki wayar ya mike ya koma dakin da suka fito yana bugo kofar kamar tayi masa wani laifi.

Wajen Sa’adatu ta dan tattara sai dai tabar komaine akan teburin, akwai kayan kallo a dakin, amman batason yin karambanin kunnawa. Sai kawai ta dauko jakarta da take falon ta zaro wayarta, kan doguwar kujera ta koma ta kwanta. Batason tunani yayi mata yawa shisa ta lalubo wani littafi na Batul Mamman, Gumin Halak, ta soma karantawa. Yanda littafin yaja hankalinta ne yasa bata kula lokaci ya tafi ba, sai taga kamar daga kwanciyarta ne har tara ta wuce. Mikewa tayi, fitsari ma takeji, ga kuma sallar isha’i, yar hijabin data hado cikin kayanta duk suna dakin, haka kawai takejin batason shiga dakin, sanin bata da wani zabi yasa ta sauka daga kujerar ta taka zuwa kofar dakin data kwankwasa a hankali.

“Yes…”

Jabir ya amsa daga ciki, da sallama ta tura ta shiga, yana kwance daga can gefen gadon yaja bargo ya rufe rabin jikinshi yana danna wayar shi da hannu daya, baiko raba fuskarshi da wayar ba, da hanzari ta shige bandakin tayi fitsari ta dauro alwala, datazo daukar hijabin saita hada harda kayan baccinta tana ficewa. Jabir baima kula da ita ba saboda hankalin shi nakan wayar shi, Aisha tafi kowa sanin shi, rigimar da take nema dashi tasan ba riba zataci ba. Shi zata kalla tace masa.

“Banajin zuwa Abujan nan Jay, kuje ku dawo kawai.”

Yanata mata uzuri ba dan ya fahimceta ba, saboda baiga dalilin da zasu dauki watanni suna tsara abu tare ba, ta kuma nuna masa ta aminta da duk tsarin nasu dari bisa dari tazo ta zare jikinta tabar shi yana komai shi kadai ba, asalima wani kallo take masa yanzun kamar yayi mata laifi ko kuma yana shirin yi mata laifi. Sa’adatun ma ita ta zabota da kanta, to meye matsalarta? Duka ita yake dubawa a cikin abin nan, saboda ita ne ya zabi yayi auren wucin gadi, saboda ita ya zabi wannan hanyar alhalin yana da lafiyar da zai samar da yaron da kanshi, baisan me kuma take so dashi ba, da ta zabi ta rufe idanuwanta tana neman shi da rigima haka. Yayi mata shiru, ita ta cigaba da magana har saida taja sukayi fadan da yaketa gujewa, to me yasa take kiranshi yanzun? Me zatace masa?

“Kayi hakuri, na rasa ya zan danne zuciyata ne. Inajin kamar da mun zabi a ciri kwai a jikina a cira a jikinka sai a hada, saita daukar mana, bansani ba, bansan daga inda tunanin yake zuwamun ba.”

Shine abinda ta zabi ta turo masa, inda tun daga farko tayi masa wannan maganar, tasan zaiyi komai wajen ganin idan hakan mai yiwuwa ne kuma zai bata abinda take so, sai yanzun? Da suka rigada suka zabi wani tsari?

“Yarona ba naki bane kome kike son gayamun? Sai kin hada jini dashi zakiji shi kamar naki?”

Kiranshi ta cigaba dayi bayan shigar sakon shi, sai dai wannan karin kashewa ya dingayi, bayason jin muryarta ko cigaba da jan magana da ita, saboda ranshi a bace yake sosai, ko muryarta bayason ji. Karshe ma duka wayar ya kashe, ya juya kwanciyar shi, jin ranshi na kara baci yasa shi saukowa daga gadon ya nufi falo da nufin dauko ruwa, sai yaga Sa’adatu takure akan kujera, kuma da alama bacci take shirinyi tunda ta sake kayan jikinta.

“Ke me kikeyi anan?”

Tambayar tashi ta saukar mata kamar daga sama, dan juyin da tayi da kujerar ba mai girma bace tabbas data fado.

“Na kwanta ne.”

Ta amsa a daburce, saboda yanda Jabir ya tsareta da ido kamar yana shirin kai mata duka, ko wadda tayi masa wani gagarumin laifi.

“Saboda me?”

Ya tambaya yana kallonta, kaifin idanuwanshi nasa ta sadda kanta, gadon da yake dakin na da girman da zasu kwanta su biyu batare da wani ya takura dan uwan shi ba, ya dauka taga hakan, ta kuma ga a gefe ya kwanta. Me yasa to zatazo ta takure a kujera? Itama bata masa rai take so tayi yaga alama

“Baki jini ba? Saboda me?”

Ya maimaita muryarshi na rage amo, tana kuma jiyo amon tarzomar dake jiran kiris ta tashi a yanda ya sauke muryar, batasan me zatace masa ba, saboda me zata kwana a falo? A kujera? Saboda sanin cewa kyaure ne kawai a tsakaninsu yasa taji idanuwanta sun bushe babu alamar bacci a cikinsu, ko fada masa zatayi yanda ko da tanajin baccin sautin bugun zuciyarta kadai ya isa ya hana mata samun shi? Duka wadannan dalilai ne ma? Tunda duk yanda zata jujjuya komai, karshe dai saboda shine, shine matsalar, kwana waje daya dashine damuwarta, kuma ba zatace ga dalili ba kamar yanda batajin zata iya fada masa saboda shine.

“Kina so jikinki yayi ciwo? Ya zakiyi bacci a kujera?”

Ita bacci a kujera ba matsalarta bane, baiga katifarta ta gida bane ba, bai kuma san zamanin da suke kwanciya su hudu akai ba, haka suke jerawa kamar an saka tsinken tsire a takarda, duk kuwa da fadan da za’ayi, a dinga zungurin juna, bacci suke su tashi kalau, har a ranakun da sauro yakan so yaga hakan bai samu ba kuwa. Sai wannan luntsumemiyar kujerar?

“Ki tashi kafin ranki ya baci”

Yayi maganar cikin wata muryar data sa tajita tsaye kan kafafuwanta, kafin su jata zuwa dakin cikin wani irin sauri kamar zata kifa. Ko gidansu kannen shi na fada, baya duka, babu wanda ya taba dagawa hannu, amman sunce gara duka da fadanshi idan ta hadoku, kuma baya ma bukatar ya daga muryar shi, akwai wani yanayi tattare da yanda zaiyi maka magana da ba zata san lokacin da zaka bi umarnin shi ba ko tsoro zai cika maka zuciya. Yau abinda ya faru da Sa’adatu kenan, ko data shiga dakin ma bata tsaya duru-duru ba, a farkon gadon ta kwanta taja duvet din ta rufe jikinta har kai, zuciyarta sai bugawa takeyi cike da tsoro, da taji shigowar shi dakin, taji takun tafiyar shi da kuma alamar ya kwanta a gefe sai wasu hawaye masu dumi suka silalo mata, yaushe rabon da ayi mata fada haka? Ko Abdallah duk yanda zata bata masa rai a nutse yake magana da ita, zata kirga lokuttan daya yi mata tsawa.

Amman yanzun ji take kamar ma data tsaya har mangareta sai Jabir yayi. Batasan sheshsheka da ajiyar zuciya na kwace mata ba, ta dauka kukan zuci takeyi sai hawaye kawai dake sauka. Jabir yaji ajiyar zuciyar ta farko, kafin sheshekar dake nuna alamun kuka takeyi, irin kukan sangartattun yaran nan, mamakinta ya sa shi tashi zaune yana kallon saitin datake ta rufe har kai tana kukan da yake neman dalilin shi ya rasa. To ko dai duka mata ne haka? Idan basu ga sun bata maka rai ba sam basajin dadi, in ba haka ba me yayi mata da zata saka shi a gaba tana kuka?

“Sa’adatu…”

Ya kira a hankali saboda haka kawai yaji ba zai iya shareta ba, dif ajiyar zuciyar da sheshekar suka dauke, sake kiran sunanta yayi amman bata amsa ba, saiya saka hannun shi yana jan mayafin data rufa dashi, hadi da matsawa sosai kan gadon yasa hannuwan shi duka biyun ya mikar da ita zaune, wani yanayi da yaji ya tayar masa da tsikar jiki, musamman fuskarta da take jike da hawaye, ta kuma turo labbanta da suke a jike suma kamar haka halittarsu take tun asali, idanuwan nan sun rine, taki kallon shi, sai hannu data sa tana goge fuskarta hadi da sauke ajiyar zuciyar data sa shi ya kusan kamata ya riketa a jikinshi ya lallasheta

“Menene? Nine?”

Sai lokacin ta kalle shi, zuciyarta ta natsu a kirjinta, ta nemi bugun nan da take tayi ta rasa, babu abinda take so sai lallashin da batasan dalilin shi ba, shisa ta daga masa kai a hankali

“To na daina”

Ya furta yana kamo hannunta hadi da murzawa kadan, sai wani hawaye a idon dama ya silalo, hannunta ya saki yakai shi fuskarta yana gogewa, bada yatsan shi ba, da duka tafin hannun shi, yanajin dumin da fuskarta ta dauka kamar zazzabi takeyi, saiyayi hanzarin saukar da hannunshi zuwa wuyanta yana tabawa.

“Zazzabi kikeyi?”

Kai ta girgiza masa duk da itama tanajin dumin da jikinta ya dauka.

“Jikinki yayi zafi”

Batace komai ba, shima sauke hannun shi yayi

“Ki kwanta to, bana son kuka kinji?”

Kai ta daga masa tana kwanciya

“Kiyi addu’a”

Ya furta, saboda yanayinta ya fito masa da yarintarta a fili, yana kuma saka shi jin babu abinda yake so daya wuce yayi mata rumfa, ya bata kariya daga komai da zai iya, ciki kuwa harda shi da kanshi, shisa yayi duk wani kokari da zai iya na ganin bai rungumota ba, filo hudune akan gadon, guda daya ya dauko yana saka shi a tsakaninsu ta kasan duvet din, ya mika hannu ya kashe musu hasken dakin, ya kwanta yana jan bargon, wannan karin shi bacci ya kauracewa, ita kuma cikin ikon Allaah bacci ne mai nauyin gaske ya dauketa, daman duk idan tayi kuka haka to zai wahala batayi bacci ba. Har wanka saida ya tashi ta karayi amman ya kasa bacci, duk wani abu me rai a jikinshi yasan da zaman Sa’adatu da take kwance a gefenshi.  Ya dade sosai kafin bacci ya dauke shi, cike da mafarkin yayiwa Sa’adatu rumfar da yake tunani, da jikinshi da wani abu da baisan meye ba.

“Mun makara, shidda da rabi, ka tashi kaji”

Sa’adatu dake bubbuga gefen filon Jabir din take fadi, dan itama kawai gani tayi ta bude ido, da farkoma ta manta inda take, sai a hankali komai ya dawo mata, ta kuwa sauko daga gadon kamar wadda take kan kaya, ta shiga bandaki, alamun hasken data gani a bandakin tasan garin ya waye. Saida tayi alwala tazo ta tashi Jabir daya fitar da wani sauti ta kasan makoshin shi yana juya kwanciya hadi da sake rungume filon da yake rike dashi, saita wuce falo kawai, ta dauki doguwar rigarta ta mayar, tayi sallah, ta dauki wayarta kuma tana duba lokaci, taga cajinta ma yayi kasa, ta nemi soket a falon ta saka caji tukunna ta koma dakin dan ta tashi Jabir, dakyar ya bude idanuwan shi dake cike da bacci.

“Bacci nakeji, kibarni.”

Ya furta yana kokarin sake rufe idanuwan shi

“Kayi sallah saika koma baccin, mun makara”

Mirginawa yayi yana sakin filon, idanuwan shi rabi a rufe, rabi a bude ya mika hannu kafin ta tantance me yake shirin faruwa tajita kwance akan gadon, Jabir ya dora kafarshi daya kan nata duka biyun

“Ki rabu dani bacci nakeji”

Ya furta yana riketa sosai, sai dai yana saka kanshi cikin wuyanta, yanda ya saba, akwai inda yake jingina gabaki dayan fuskarshi a wuyan Aisha, yakance an halicci wajen ne kawai saboda shi saboda yanda yake jinshi dai-daita, sai ya zagaya hannun shi ya sakala yatsunshi cikin nata yayi mata kyakkyawan riko, a haka zasuyi bacci, idanuwanshi yaji ya bude gabaki daya jinshi a bakon waje, rike kuma da bakon abu, babu shiri ya mike gabaki daya yanajin kamar jiri na neman mayar dashi ya kwantar, abinda bature ke kira da head rush, yakan same shi duk idan yayi kokarin mikewa da sauri haka, shisa inya tashi bacci saiya jima a kwance kafin ya tashi, a hankali komai yake dawo masa. Yana Abuja ba Kano ba, yana tare da Sa’adatu ne ba Aisha ba. Sa’adatu da ta yunkura ta tashi zaune, jikinta ko ina na bari, dakyar ta rarrafa ta sauka ta dayan bangaren, sai rarraba manyan idanuwanta takeyi cike da firgici tana sa Jabir fadin.

“I’m sorry.”

Cikin hanzari tace,

“Sallah zakayi daman, mun makara.”

Kai ya daga mata yana ganin yanda take a firgice har lokacin, sai dai kafin yayi yunkurin fadin wani abu harta fice daga dakin. Kanshi ya dafe da duka hannuwanshi biyu yana mayar da numfashi, kusan mintina uku kafin ya samu ya mike ya nufi bandakin. Sabon burushi ya dauka ya bude ya fara wanke hakoran shi, yayi wanka, tukunna yayi alwala ya fito, wando ya sake ya mayar da rigar yayi sallah. Kanshi yayi wani irin nauyi, ya kuma san bacci ne da bai wadace shi ba, idan baiyi baccin ba kuma nauyin kan zai juye ne zuwa ciwo, shisa ya koma ya kwanta. Sai dai me, daya rufe idanuwanshi sai fuskarshi a wuyan Sa’adatu ta dawo masa, sai kuma yakejin kamar hucin numfashin data ja, kafin firgicin dake idanuwanta su sauka cikin nashi dake rufe, dole ya budesu yana sauke numfashi me nauyi. Kamar wasa sai juye-juye yakeyi ya kasayin baccin da yakeji sosai da sosai.

Daman kona awa biyu ya samu, karfe goma zasu fita, awa daya ya ishesu su shiryawa, shi bama lallai ya karya a lokacin ba zai iya bari sai sun dawo. Amman fur baccin yaki bashi hadin kai, dole ya hakura, ya dauki wayar shi ya kunna, sakon Aisha ne farkon shiga tana gaishe dashi da tambayar yanda ya tashi kamar ba fada sukayi ba, shareta yayi ya cigaba da duba sauran sakkonin da suka tarar masa. Suma din saiya rasa cikakkiyar nutsuwar yin hakan, dole ya ajiye wayar. Lokacin bakwai da kusan kwata, gwara su shirya ma su fita zaifi, suyi su gama abinda zasuyi a garin Abuja, saboda baisan yanda zai iya cigaba da mallakar kanshi ba idan abinda ya faru yau ya sake faruwa.

Kuma yana so yayiwa Sa’adatu rumfa ne. Rumfar da zata kareta daga abubuwa da yawa.

Ciki harda shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 30Tsakaninmu 32 >>

1 thought on “Tsakaninmu 31”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×