Inda duk ya duba status din yan gidansu a satin, tallar zobo ne da kunun aya, suna cewa azo a siya, matar Yayansu ce takeyi. Yasan suna da kara, suna kuma da kirkin da duk lokacin da mutum daya ya fara wata sana'a ko wani abu, to duk za'a taru a karfafa masa gwiwa har saiya cimma wannan burin nashi. Idan kasuwanci ne kuwa, sune farko-farko wajen siye. Ba zai manta lokacin daya wayi gari yaji yana son fara siyar da kayan yara, daga dan kwana daya zuwa shekaru bakwai. Tare suka dinga zirga-zirgar nan da. . .