Skip to content
Part 36 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Inda duk ya duba status din yan gidansu a satin, tallar zobo ne da kunun aya, suna cewa azo a siya, matar Yayansu ce takeyi. Yasan suna da kara, suna kuma da kirkin da duk lokacin da mutum daya ya fara wata sana’a ko wani abu, to duk za’a taru a karfafa masa gwiwa har saiya cimma wannan burin nashi. Idan kasuwanci ne kuwa, sune farko-farko wajen siye. Ba zai manta lokacin daya wayi gari yaji yana son fara siyar da kayan yara, daga dan kwana daya zuwa shekaru bakwai. Tare suka dinga zirga-zirgar nan da ‘yan gidan nasu, daga samun wajen da zaifi dacewa da ya siya, haka gyara wajen, babu wani abu da zaice yayi shi kadai, kayan farko kuwa da aka cika shagon dasu, bayajin sunyi sati biyu, kuma in da za’a kirga a wadanda sukayi masa wannan cinikin to kaso mafi girma ahalinshi ne.

Haka a shekarar farkon nan, fiye da rabin kwastomominshi ta sanadin ‘yan uwanshine, idan suka siya sukaga saukin kayan, suma sai su jawo masa wasu. Yanzun gashi yana daya daga cikin wadanda masu kananun shagunan siyar da kayan yara suke sari a wajen shi. Saboda haka sai yake tajin kamar shine kadai ba’a taya koma wacece ta fara sana’ar da tallatawa, balle kuma ace ya siya. Kullum da abin a ranshi, sai dai idan gari ya waye, hidindimun shi sukan dauke masa hankali, sai idan ya natsu ya dauko wayar, saiya tuna. Yau kuwa wajen biyar da rabi na yamma abin ya fado masa a rai, gashi kasancewar ranar ta Juma’a, ranar da akeyi me zafi ce, a cikin AC ya kusan wuni, sai dai idan wani dalili ya dan fito dashi ya tsaya, duk da haka makoshin shi yayi wata irin bushewa.

Ga hanjin shi ya daure waje daya saboda yunwa, yanda azumin ya fara bashi wahala tun kafin a shiga masallaci yasa duk shagonshi da yaje yace musulmin suyi aikinsu daga cikin shago, kuma su rage zirga-zirgar da sukeyi, sauran kiristocin da ba azumi sukeyi ba suyi wannan din. Ya kuma ga jin dadinsu karara. Dan yana duk wani kokari wajen ganin ya kamanta adalci ga masu aiki a karkashin shi. Gida ya nufa kanshi tsaye, yana kuma shiga ko Aisha da take masa sannu hannu ya iya daga mata ya wuce bedroom, saida ya shiga bayi ya watsa ruwa, ya jika kanshi sosai, ya fito ya samu kaya marassa nauyi ya saka, tukunna ya dauki wayarshi ya fito falon ya kwanta kan kujera, yanajin Aisha da take ta kai-kawo a kitchen din, yasan kayan shan ruwa ne take kokarin hada musu.

A irin ranakun nan yana jinjinawa kokarinta, shi me zai kaishi? Ina yaga karfin nan? Baije kusa da wuta bama yanaji a jikinshi, bayan duk wani abu da zasuci zata iyayin order a kawo musu. Ya daina bata bakinshi ne wajen nemar mata saukin da yaga bata maraba dashi

“Inajin dadi idan nice na shirya maka abin buda baki Jay, kuma wani abin ai ina siye idan naga zan wahala wajen yi.”

Sai kuwa ya kyaleta, yana dai binta da sannu ne, koya bita kitchen din yana tayata hira, yau kuwa bashi da karfin yin ko daya. Wayarshi ya soma daddanawa, status din Kamil ne a sama, ya bude, video ne, Kamil din na zuba kunun aya cikin kofin gilashi da yake dauke da wasu kankaru, kunun fari kal dashi kaman an zuba madara, ganin shi saiya kara masa kishin da yake ji, kuma talla ce Kamil din yakeyi. Akwai flyer din da yayi saving, ita yaje ya lalubo ya dora, saiya rasa abinda zai rubuta tunda baisan waye ma yake siyarwa ba, kawai saiya saka “Book us for Eid” yayi posting din abin, ya kuma duba lambar wayar dake jiki yana kokarin haddacewa dan yayi dialing

“Tashaa…”

Ya kwala mata kira

“Jay kayi hakuri ka shigo, kifi nake wankewa, na bata hannuwana duka biyun”

Gyara kwanciya yayi

“Zaki sha kunun Aya da zobo inyi mana order?”

Ya fadi cikin daga murya yanda zata jiyo shi

“Ehh”

Ta bashi amsa, dan ta gaji da shan duk lemukan da suke cikin gidan, tanata tunani ne, ko tayi musu smoothie, ko kuma tayi musu order din wani abin shan tunda gashi nan birjik a cikin family sai wanda ka zaba, to wannan dinma tasan dai ba zai wuce a wajen wani na gidan ba, tunda har Jabir ne da kanshi yake cewa zaiyi musu order. Abinda yasa ma ita bata ga tallar ba, saboda wata dabi’a data tashi a cikinta, duk lokacin da watan azumi yazo, to sukan tattara komai ne su ajiye gefe su fuskanci ibada, da ita bata iya rabuwa da wayarta, sai da taga yan gidan sai su sauke Qur’ani sau wajen biyar a cikin watan ita dakyar take hada daya, babu wanda yayi mata magana, kunyar kannenta da yanda suke iya jingine komai su nemi dacewa yasa ta yakice wayar, to duk wani social media kuwa ajiye shi takeyi, dan ko aiki ma a lokacin azumi ne take daukar hutunta, sai abinda ba’a rasa ba, idan an kirata babu yanda zatayi take zuwa.

Balle kuma wannan azumin da takejin tafi kowa bukatar shi, tana cikin rudu da hargitsin da take bukatar kara samun kusanci da Ubangiji. Kuma sosai nutsuwar zuciyar data rasa ta fara dawo mata. Jabir kuwa lambar ya dauka, sai dai yana fara rubutawa sai yaga sunan da yayiwa Sa’adatu saving din tata lambar dashi ya fito, mamaki yasa shi tashi zaune, ya sake dubawa, saiya kara komawa yaga ko shine bai riko lambar dai-dai ba, ya kuma duba yakai sau hudu, lambar Sa’adatu dai ce yake gani. Sakonnin daya ga suna ta shigo masa ta whatsapp din yaje ya duba, sai yaga tsokana ce daga wasu a cikin gidansu, da ma abokan wasa, suna cewa sai dai ya sai musu, wasu na fadin dole ayi musu family discount tunda su na gida ne, maganganu dake tabbatar masa da gaske Sa’adatu ce take siyarwa.

Wani kuzari da baisan daga inda ya fito ba yaji ya shige shi, lokaci daya ya mike ya nufi bedroom ya dauko mukullin mota, ya nufi kitchen ya samu Aisha na saka kifin data gama gyarawa a cikin wani bowl, karasawa yayi yana sumbatar gefen fuskarta

“Fita zanyi, karki jirani zan dan saka wani abu a cikina, a dai ajiyemun kifin nan”

Kai ta daga masa, dan tasan tunda ya shigo gida, ko menene zai sake fitar dashi abune muhimmanci, kuma ma ita din ba mai yawan saka ido bace ko tsare shi da tambaya kowanne lokaci, wani hali nata da Jabir yake girmamawa

“To zobon fa? Ko mai delivery zai kawo?”

Dan jim yayi

“Zan taho dashi kawai in babu damuwa.”

Yayi maganar yana kallonta.

“Ba damuwa, zan hada wani abin. Allaah Ya tsare.”

Ya sake sumbatar gefen fuskarta a maimakon ya amsata ya fice. Kanshi tsaye gidan Sa’adatu ya nufa, yana tukin ya rasa kalar tunanin da zaiyi, yana shigar da motar shi kuwa ya ajiye, ya bude ya fita, har sauri yake karawa wajen ganin ya shiga cikin gidan. Ya murza hannun kofar sai dai jinshi a rufe yasa shi kwankwasawa, Sa’adatu da take wajen dining dinta tana manna sticker a jikin robobin kunun ayarta ta mike, daman shine matsalarta, saboda kaf layin tasa maigadi ya tambayar mata, babu gidan da ake markade, sai daga bayama ta dinga yiwa kanta dariya, ai ta fita, kuma taga yanda gidajen suke, ina ne za’a samu injin markade? Ayar kuma nada yawan da ba zaima yiwu tace zatayi amfani da blender ba. Kawai sai ta tsaya tayi lissafi yanda zata fita, ta kuma fitar da Fa’iza idan tayi mata kunun ayar, Abdallah kuma ya samar mata mai napep dan can unguwar tasu ne. Shi yake zuwa ya kawo mata, kuma yanzun matashin da ake kira da Ashiru, shine ya zama mai delivery dinta idan an siyi abu.

Da yake yaga yana samu, sai shima ya maida hankali, babu bata lokaci, tana kiranshi yake zuwa. Ko kunun ayar ma yau shiya kawo mata, roba hamsin ne. Tasan babu wanda zai kwankwasa mata gida haka sai Jabir, ‘yan uwanshi da take jinjina karamci irin nasu yanzun, duk wanda yazo wayarta yake kira, da wahala su kwankwasa, saboda su kuma ta koyi sakama kofar mukulli, tunda akwai maza, ta kuma ajiye yar karamar hijabinta kan kujera, saita saka kafin ta bude. Ko yanzun ma da jikinta yake bata Jabir ne, saida ta saka hijabin tukunna ta karasa ta bude masa kofar, idanuwansu na shiga cikin na juna, sai taga nashi kamar sun dan fada, fuskar tashi ma ta sakeyi mata fayau, ko kuma dan ta kwana biyu bata ganshi bane ba? Dan matsawa tayi, ya shigo, ita ta mayar da kofar ta rufe tana gaishe dashi, gaisuwar daya amsa a takaice ya kafeta da idanuwa

“Bari in dan karasa saka abu a fridge”

Ta fadi tana juyawa, duk da akwai sanyi a jikin kunun ayar, shi abune da baya shiri da zafi sam, yanzun saiya samu matsala. Tsintar kanshi yayi da bin bayanta, tana ta dibar robobin data manna ma sticker tana kaiwa kusa da fridge, sai yaja kujerar data tashi ya zauna, ya dauki sticker daya yana dubawa na wani lokaci, kafin muryar shi can kasa yace

“Business kika fara Sa’adatu?”

Kallon shi tayi, shima ya dago ya kafa mata idanuwa

“Kowa ya sani bandani, kowa ya sani, ni kadai ne bansani ba.”

Ya karasa maganar yanajin wani abu na mamaye shi, yanzun daya dauki flyer din nan ya saka a status, daya rubuta wata magana da zata nuna baisan ita bace bafa? Ko kuma yaje ya tambayi wani a cikin masu posting din waye yake siyarwa? Sai ya koma yace me? Da wanne kalamai zaiyi amfani wajen kare kanshi, ai daya shiga bakin danginsu ma, dole za’a jinjina yanda matar shi zata fara sana’a bai sani ba.

“Bakazo bane”

Cewar Sa’adatu tana cigaba da jera sauran kunun ayar, harda wanda bata sakawa sticker din bama, saboda Jabir daya keta kallonta kamar tayi masa laifi, ta kuma fara jin tayi laifin.

“Baki da lambata? Dan banzo ba, ba zaki iya fadamun ba? Ba saikin kirani ba, ko text ne zaki iyayi mun, me yasa nine na karshe da zan sani?”

Da duk yanda yake maganar, da yanda ranshi yake kara baci. Dole sai yazo gidan zaiga abu, ko kuma zai sani. Numfashi Sa’adatu taja tana saukewa, ko da ba zatace tasan Jabir ba, yanayin shi duka ya nuna zuwa yayi ya sauke mata fada, jira kawai yakeyi ta fadi wani abu da zai bashi wannan dalilin, zata iya kiranshi a waya, ko tayi masa sako ta sani, ita duka wannan tunanin ne baizo mata ba, da kuma ta fara jin kudade a asusun bankinta sai shi da kanshi Jabir dinma tunanin shi yayi mata nisa, balle kuma tunanin ya kamata ya sani

“Kayi hakuri…”

Ta furta cikin wata karamar murya, ganin yana kallonta har lokacin, idanuwan shi cike da tarin rikici yasa ta dorawa da

“Kaji, kayi hakuri, tunanin ne baizo mun ba, kuma kaga azumi akeyi, ba kyau fada da azumi…gashi ma na baka hakuri…”

Ya numfasa duk da baisan abinda zai fada din ba, aka kira sallah. Da sauri ta bude fridge din, zobon da tayiwa kanta roba hudu, ta kara su abarba da mangwaro ta dauko roba biyu, ta dora daya kan fridge, ta kwance guda daya tana mikama Jabir, ga mamakinta saiya makale mata kafadu yanda yara sukeyi, idanuwan shi har lokacin na kanta, dariya ce take son kwace mata.

“Yi hakuri, kaji…yayi sanyi fa, kuma an kira sallah.”

Kallonta ya cigaba dayi, abune da bai taba tunanin zai faru dashi a gaban wata mace ba Aisha ba, macen ma yarinya karama kamar Sa’adatu, wato yaji rigimar da yake bukatar a lallashe shi. Da Aisha ce, babu ma yanda za’ayi ta fara bashi a robar, zata zuba a kofi, idan kuma a robar ne, irin robobin nan ne masu hade da abin zuka a jiki. Yanda kuma taga yanajin rikici zata kama hannun shi, ko ta zauna a jikinshi ta sauke murya tana masa magana, suna iya shafe lokaci me tsayi tana binshi yana dauke kai. Ga mamakin shi robar Sa’adatu ta daga ta kai bakinta tana kwankwada, ta kuma sha ya kusan rabi, kafin ta sauke numfashi tana yin hamdala

“Kai Alhamdulillah…”

Ta sake fadi tana kara kaiwa bakinta, batama san taji kishi haka ba, wannan karon rikicin ya bace daga idanuwan shi, mamaki ya maye gurbin rikicin. Mamakin Sa’adatu data dan kalle shi.

“Ka sha kaji Allaah, yayi sanyi sosai.”

Sai dai ba miko masa tayi ba, sake kaiwa bakinta tayi tana karasa shanye sauran, ta rufe robar, ta dauko dayar, ganin ta fara kwancewa, kuma makoshin shi kamar anyi wasan kasa yasa shi mikewa tsaye, yaga alama yarinta na damunta, bai kamata ya biye mata ba, shisa ya mika mata hannu, saita bashi robar, sha yayi sosai. Ya kuma wuce da sauran a hannun shi, bedroom dinta ya nufa, ya karasa shanye zobon, yana ajiye robar kan drawer din kusa da gado ya shiga bayi ya daura alwala ya sake fitowa daga dakin, ficewa daga gidan yayi, shida maigadi suka nufi masallacin da kwana ce kawai zasu sha bayan sunyiwa juna barka da shan ruwa. Da aka idar da sallah, saida ya gama azkar dinshi tukunna ya fita daga masallacin, dan ya samu maigadi ya rigashi komawa.

Ya samu Sa’adatu zaune a falon da plates guda biyu a gabanta sai bowl, tayi tsammanin zai dawo daman, tunda ta leka ta window taga motar shi. Pritata tayi na plantain, a status din Badr tagani, kuma batayi kwauron baki ba, ta tambayeta yanda zatayi, wasu kayayyakin ma da tace mata ta yanka a ciki ita bata sansu ba, mai delivery din Badr din ne ta aiko shi ya kawo mata da yawa, taga kala-kalan tattasai, dan koren ciki ma ranar ba irin koren tattasan da aka saba siyo musu bane in zasu yanka a wake da shinkafa. Sai kuma doya data dafa da sauce din kifi daya sha ganyen ogu, kamshi duk ya cika falon. Tana jin dadin mu’amala da Badr, tana kuma koyon abubuwa da yawa, danma wasu tace zaifi kyau tazo gidan suyi tare sai tafi ganewa, ta waya ba zai ba, idan ta samu lokaci zuwa bayan sallah sai ta shigo.

A kasan shima Jabir ya zauna yana kallon plate din data tura gabanshi, ta saka masa pritata din data yayyanka slices kamar na pizza, guda biyu ta saka masa, doya a gefe, sai kuma sauce din a bowl, ita nata plate din komai ta hade a ciki, sai cokali mai yan yatsu, sai kuma robobi guda uku, zobo, kunun aya, sai kuma robar ruwa, harda kofi ta ajiye masa.

“Sannu da shan ruwa, ko kana bukatar wani lemon ne in dauko maka? Akwai na kwalaye da ka aikomun dashi.”

Kai ya girgiza mata tun kafin ta karasa maganar. Daya bude robar kunun ayan, bai tsaya zubawa a kofin da ta ajiye ba ya sha sosai, dan shi idan akayi buda baki yafi bukatar abu mai ruwa, sai kuma kayan marmari, sai yayi sallar asham ya dawo ne yake cin abinci sosai. Amman yau yaci pritata din duka slices din da Sa’adatu ta zuba masa, miyar ma ta shigar masa ido, sai yaci yankakkiyar doyar guda hudu, ya karasa shanye duka kunun ayar. Ya kalli Sa’adatu data cinye duka abinda yake nata plate din, tana kuma kurbar zobo kadan-kadan

“Na koshi. Thank you”

Ya furta yana ture plate din gabanta kadan

“Zobon da kunun aya za’a bani, nawa ne?”

Dariya ta danyi

“Bari a dibo maka”

Kai ya girgiza

“Siye zanyi…a bani kowanne roba goma”

Dan ware idanuwa tayi, dan kusan duka na cikin fridge dinma na mutane ne da aka rigada aka tura kudin, wanda zasu karba washegari, gwara ma zobon shi saita sakeyi da safe, amman kunun ayar sai yamma Fa’iza zata aiko dashi, ba kuma zata iyayi mata tashi na kamaka ba, ta sakata yin wani aiki tunda ga yanda suka tsara da farko

“Anya kunun ayar zaka samu guda goma.”

Kallonta Jabir yayi

“Bana ganshi da yawa ba”

Kai ta dan daga.

“Eh na mutane ne da sukayi booking, gobe idan Allaah Ya kaimu zasu karba.”

Ta karasa maganar tana mikewa, nacan saman fridge din banda shi a lissafi daman, sune take so ta kirga taga ko roba nawa ne, bin bayanta Jabir yayi.

“Nifa sai an bani.”

Taji ya fadi gab da ita, kurkusa yanda ba zata iya juyawa batare da ta shiga jikinshi ba, kamshin da yakeyi ya hade dana kunun aya da zobon da yake fitowa daga cikin fridge din, kamar baiji bugun da zuciyarta takeyi ba, ya mika hannu yana kirga kunun ayar

“Gashi nan guda goma…”

Dan juyawa tayi.

“Matsa in fito maka dasu to.”

Ta fadi cikin wata murya da bata gane tata bace ba, matsawar yayi kadan, sai dai bata daina jin kamar dumin shi a bayanta ba, dumin da sanyin dake fitowa daga cikin fridge din ya kasa dishe mata. Fito masa dasu tayi duka, kafafuwanta kamar an bugesu sanda ta nufi kicin ta dauko babbar leda ta zuba masa a ciki tana mika masa, daya karba saiya mayar dayan hannun, ya kuma riko nata hannun da daya yana kallon fuskarta

“Banason ina zama karshe wajen sanin abu, musamman mutanen da suke da muhimmanci a wajena, ina so in zama na farko da zan san duk wani abu daya dangance su, zamuyi fada sosai idan na kara tsintar wani abu naki a wajen wasu kafin ni in sani, bana so, karki kara…”

Kai ta daga masa tanajin idanuwanta sun cika da hawaye duk da ba da hargowa yakeyi mata maganar ba, kuma baiyi kama da fada ba, asalima muryar shi a tausashe take, wani irin taushi da take zaton shine yake neman hawayenta.

“Thank you. Allaah Yasa albarka, zan turo da kudin ta account.”

Kan ta sake daga masa, tunda harshenta ya nade, yatsunta daya sake murzawa ya kara mayar mata da duk wasu kalmomi da tayi kokarin hadawa balle ma tayi tunanin furtasu. Shima so yake ya saki hannun nata, tunda wani abu cikin kanshi ja cewa ya dago hannun ya sumbata, dakyar ya iya mallakar kanshi, yana sakin hannunta kuma ya juya yabar wajen, kujerar dining ta laluba ta zauna.

“…musamman mutanen dake da muhimmancin a wajena…”

Haka kunnuwanta suka jiye mata Jabir ya fada, kenan tana cikin jerin mutanen da suke da muhimmanci a wajen shi?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 35Tsakaninmu 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×