Skip to content
Part 35 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Ledar kayan marmarin kawai ta dauka, shi ya dauki kwandunan, inda ya saka kafarshi nan take mayar da tata, a dan zaman aikin da tayi zatace tasan gidan da, sai dai da suka shiga babban falon da sallama dauke a bakunansu, sai taga kamar komai ya sake mata, yawan mutanen da suke cikin falon yasa taji duk ta tsargu, musamman yanda kowa ya bar abinda yakeyi ya zubo musu idanuwa, ba kirgawa tayi ba, amman sunfi su ashirin a cikin dakin, daga mai kofi sai mai plate da cokali a hannu, wasu a zaune kan kujera, wasu a tsaye, wasu kuma bata gama tantance me sukeyi bama saboda kanta data sauke kasa, tana iya kokarinta wajen ganin inda duk Jabir ya cire kafarshi nan take saka tata, saida taga alamar ya tsaya itama ta tsaya, ta dan daga kanta, kafin kuma tayi kasa tana zama kan kafet, ledar a gefenta, kafin su fara yi musu sannu da zuwa cike da rakadin da yasa Jabir dan runtsa ido ya karasa inda Hajiya Hasina take

“Hajja…”

Jabir ya fada yana kama hannun Sajjad, dan Yayan Hajiya Hasina din da yake zaune a gefenta, ya kuma yi amfani da karfinshi yana dago shi ya zauna kusa inda ya daga shin

“Yoo”

Cewar Sajjad yana daga hannuwan shi cikin alamun nuna rashin yarda da abinda Jabir din yayi masa

“Kowa yasan wajena ne ka zauna”

Jabir ya fadi yana kallon Hajiya Hasina da take dariya

“Ina wuni”

Sa’adatu ta fadi da karamar murya

“Sa’adatu, lafiya kalau…ya gida?”

Sake sunkuyar da kai tayi, wata irin kunya na lullubeta

“Alhamdulillah, an sha ruwa lafiya”

Saida Hajiya Hasina ta amsa, tukunna ta dan daga kanta tana kallon sauran da furta

“Ina wuninku, barkanmu da shan ruwa”

Nan kowa ya fara amsawa, har bata ma gane me suke fada saboda hayaniyar data kaure, kwandunan da Jabir ya ajiye ya janyo gaban Hajiya Hasina yana fadin

“Nakine wannan”

Da fara’a sosai Hajiya Hasina taja kwandunan duka biyu gabanta

“Kai Ma Shaa Allaah, me na samu”

Surukanta suna zuwa gaisheta sosai, kuma sukan zo da tsaraba, musamman in sun dawo daga wata kasar ko wani garin, sai dai in ba biki ake ko suna ba, wannan yace shi zai dauki dawainiyar kawo abu kaza, babu wanda ya taba dafo abinci ya kawo mata, saboda wannan al’ada ce da basu saba da ita ba, kuma ko da dafowar akayi tasan yan aikine zasuyi, balle gani suke meye zasu kawo naci da ita bata dashi? Tana bude kular dambum kamshi ya bade dakin, ta daga kai ta kalli Sa’adatu da take wasa da hannun jakarta, tanajin wani dadi na ratsata

“Hajja me aka kawo miki?”

Anwar ya tambaya yana zagayowa, hannunta Sa’adatu taji an kama, data daga kai sai taga Hibba

“Tashi daga nan kafin su fado miki, yanzun zasu fara halinsu”

Mikewa tayi tana karasawa kan kujera mai zaman mutum daya da Hibban ta kaita, aikuwa kusan su duka zagaye Hajiya Hasinan sukayi, da tana wajen tabbas yanda suke turereniya wani zai iya fado mata

“Wai ba zaku barni in fara diba bane? Ku aka kawowa koni?”

Hajiya Hasina take fada tana doke hannayen da suke ta kaiwa. Ita bata san zata samesu da yawa haka ba data kara, taji dadi sosai yanda taga kowa naso yaci abinda ta kawo, ita fa, ba kowa ba, Sa’adatu yar Abida da Habibu, itace cikin yan gayun nan da suketa zuba kamshi kala-kala suna rububin abinda ta dafa da hannunta

“Matar Jb ko meye wannan yayi dadi sosai”

Cewar wani farin matashi, daya tara sumar da take a nannade daga gaban

“Nagode”

Ta fadi a kunyace, ya daga mata danyatsa alamar jinjina yana sake dibar dambun da cokali me yatsun da yake cikin plate din dankalin shi, a gefe ya zuba, ya fara waige-waigr kamar wanda yake neman inda zai zauna, ya hangi wata budurwa da robar zobo a hannunta, ya kuwa nufeta yana kokarin kwacewa ta matsa

“Dan Allaah ki bani in kurba Badr”

Ya fadi yana sake mika hannu, ta daga robar sama

“Kaje can ka dauka”

Kai yake girgiza mata

“Ba zan iya ba kinsanni, kina ganin su Fahad a wajen, ki dai bani in dandana”

Saida ta sauke numfashi tukunna ta mika masa, ya kurba, ya sake kurba kamar yana son tantance dandanon, da ya sake kurba saiya mikawa yarinyar daya kira da Badr, ita kuma ta karaso ta zauna gefen hannun kujerar da Sa’adatu take

“Muyi magana Antynmu…ko kinsan idan zaki siyar da abin nan kudi zaki samu?”

Ta karasa maganar tana jinjina robar zobon, da mamaki Sa’adatu take kallonta, da kuma nauyin jin ta kirata da Anty, alhalin ta girmeta, zata kusan shekarun Nabila, koma ta fita

“Ina nufin za’a siya sosai, saboda yayi dadi, ki bani number dinki muyi magana sosai”

Wayar Sa’adatu ta karba ta sakama Badr lambar wayarta, ta karba ta mike. Kusan kowa magana yake tayi da Sa’adatu, wasu kuma sun bude ledar kayan marmarin sun dauki abinda yayi musu, sunje sun dauraye sun dawo. Yanda duk taji dadin yabawar da suke tayi mata bai kai na Hajiya Hasina da tace mata.

“Nagode sosai Sa’adatu. Allaah yayi albarka, naji dadi fiye da zatonki, kuma dambun ma yayi dadi, idan kinyi a dinga aikomun dashi, ina sawa anamun amman gaskiya naki ya yi dadi.”

Ta kuwa kudurta a ranta, ko da sau dayane a sati ko sati biyu zata dingayi ana kawo mata har lokacin da take dashi a cikinsu ya kare. Mazan duka suka fita sallar isha’i da kuma asham, suma sai suka tashi, tabi su Hibba sukayi sallar. Hibba data fita ta dawo dakin, ta mika mata wani kofi mai matsakaicin girma, irin mai murfin nan da kuma abin zuqa a hade, farine shisa take iya ganin abinda yake ciki, wani purple din abune mai wasu mulmulallen abu a ciki, saman ne ma kadai purple, daga kasan farine tas, sai mulmulallun abubuwan kuma bakake ne a iya ganinta, a tsorace ta dan zuko tana gudun karta kasa hadiyewa saboda rashin sabo, wani irin dadi ya gauraye bakinta yana wanke mata makoshi, ta kuwa sakeyi masa kyakkyawar zuka.

“Abin nan akwai dadi.”

Ta fadi tana saka Hibba yin dariya

“Bubble tea ne”

Kai ta jinjina, koma meye yayi mata dadi sosai. Haka suka sake fita falon inda hira ta kaure anata gardamar da bata gane kanta, saboda akan kasashen ketare ne da sukaje, suna gardama kan wani abinci da taketa kokarin ganin ta maimaita sunan, ganin zata tauna harshenta yasa ta hakura. Sai wajen goma saura Jabir ya mike yana fadin.

“Idan na biye muku zamu kwana a gidan nan. Sa’adatu tashi mu tafi.”

Mikewar tayi itama, tayiwa Hajiya Hasina da tace,

“Ke in za’a je gida aida babbar jaka ake zuwa Sa’adatu, kawo ta hannun naki ku jirani ina zuwa.”

A kunyace ta mika mata, tana tabin ‘yan uwan Jabir da suke cewa zasuzo gidanta, amman zobo zatayi musu, wasu kuma suce kunun aya

“Saboda ajiyeta kukayi dole ku dinga lissafa mata abinda kuke so, bama zakuyi magana dani…”

Jabir ya fara, sai dai kafin ya karasa, wajen mutum hudu sun hadu sun tura shi baya suna cigaba da magana da Sa’adatu da take kokarin danne dariyarta ganin fuskar Jabir din, ashe suma masu kudin dai suna wasa da tsokanar juna yanda sukeyi, harma wani ya harzuka abin ya zama fadan da karshe dai an tsawatar, ta dauka basu da wannan lokacin, suna can suna kashe kudin da suke dashi. Da Hajiya Hasina ta dawo jakar ta mika mata

“Allaah Yayi albarka. Nagode kwarai”

Hajiya Hasina ce kawai bata bisu ba, amman duka har wajen mota suka rakasu. Saida suka ga fitar su sannan suka koma ciki. Ya rigada ya fadawa Aisha zaije gida, amman duk da haka sai danna wayarshi yake ganin goma tayi. Yanajin wani iri, saboda yanda harshen shi yayi nauyi wajen kasa fada mata shida Sa’adatu zasuje gaishe da Hajiya Hasina, bayan tunda ya yanke hukuncin tare zasuje ya gama tsara kalaman da zaiyi amfani dasu, zai gaya mata duk cikin cover dinsu ne tunda babu wanda yasan irin auren da sukayi. Saida yaje gabanta ya bude bakinshi yace

“Zanje gida yau bayan shan ruwa…”

Sauran kalaman suka makale masa, har saida ta daga ido ta kalle shi ganin kamar akwai sauran abinda yake son fada, sai yayi mata murmushi yana shigewa daki ya barta a falo tana fuskantar aikin da takeyi. Tayi masa kira har biyu suna gidan ya kasa dagawa, saboda rakadin da suke tayi, zata iya jiyo muryar wani a cikinsu yana kiran Sa’adatu, zai iya tashi ya amsa wayar ya sani, ya dai rasa abinda ya zaunar dashi

“Rashin gaskiyarka”

Wata murya da yayi kokarin yakicewa ta fada masa

“Kowa yaji dadi. Sannu da kokari…sai dai ni baki bani dambun ba”

Murmushi tayi

“Kuma ya kare, duka na juye musu, sai dai idan na sakeyi In Shaa Allaah”

Dan ciza lebe yayi

“Kawai daman ba’ayi niyyar bani ba”

Sai tayi yar dariya tana kallon gefe, yanda ko ina yayi hasken fitilu kala-kala, bata taba fita da daddare haka ba tunda take, sai yanayin garin yayi mata dadi sosai. Da suka karasa a motar tayi masa saida safe ta fice tana rufe masa murfin, tabarshi yana bin bayanta da kallo, saboda yana kokarin kwance belt din daya daura ne ya taka mata har cikin gidan tayi masa sallama, sai yaji wani iri, jikinshi yayi masa sanyin daya kasa fahimta. Haka yaja motar da ko kashewa baiyi ba ya fice daga gidan, maigadi nayi masa a dawo lafiya ma baiko kulashi ba.

*

Kwana biyu tsakanin zuwa gidansu Jabir, Badr ta kirata suka gaisa, tayi saving din lambar Badr din. A Whatsapp status din Badr ta dinga ganin wasu kalolin abinci, anan ta fahimci cewar abinda Badr din takeyi kenan, dan ga logo dinta nanma shine ta saka a profile, Dine with B. Sosai Badr din ta burgeta, inda zata samu wani kasuwanci da zai dinga kawo mata kudi sosai ai da taji dadi, ita irin kasuwancin da Abida tayine bataso, saboda gani takeyi nawa ne ribar? Ga inda ake siyar da abinci nan wajen Badr, harda na dubu goma fa take gani. Harta kasa hakuri tayi tagging din wani status da.

“Kai Badr, inajin daman nice nake kasuwancin nan.”

Emoji din dariya Badr din ta tura mata, ita mahaifinta da Marigayi Alhaji Paki, abokan wasa ne. Kawai son zumunci ne irin na Ahalin Paki da tarin dukiyarsu baisa sun kyamaci danginsu masu karamin karfi ba, haka suke hulda da juna babu wani bambanci, duk da itama Badr din suna da rufin asirinsu, mahaifinta ma’aikaci ne babba a water board kafin yayi ritaya, sannan yana dan taba kasuwancin da yanzun shine kawai hanyar shi ta samun kudi. Suna da yawa a gidansu dan matan baban nata uku, su kadai mata su goma sha dayane, ga kananun yara da tasan su ake haifarwa yanzun. Shisa ta tashi da burin tsayawa da kafafuwanta. Hajiya Hasina ita ta biya mata duk wata makarantar girki data ke alfahari da shigarta yanzun.

Ko makaranta Polytechnic ta samu, inda ta karanci Business administration har matakin Higher national diploma, bata kuma cigaba ba saboda yanzun kasuwanci na gara mata sosai da sosai. Kasuwancin abinci data gina da taimakon ‘yan uwan nata da suka san manya, bakuma su taba gajiya da taimaka mata ba. Yanzun tana daya daga cikin sanannun masu siyar abinci daga gida a cikin garin Kano. Bayan tafiyarsu Sa’adatu ne take jin labarinta a bakin Hibba, cewar talakawa ne sosai, ita tanaso taga mace ta tsaya da kafafuwanta. Musamman irin Sa’adatu, ya kamata ace tayi amfani da auren Jabir ta samu ta tsaya da kafarta yanda ba zai zamana da auren kadai ta dogara ba, dan rayuwa bata da tabbas.

To kuma gashi yanzun Sa’adatun ta nuna mata da gaske take son yin kasuwancin.

Shisa bata amsata ta whatsapp ba, saida ta samu sarari tukunna ta kirata sukayi magana sosai. Tace mata za’ayi roba 50 zatayi amfani dashi wajen yin tallah, manya kwastomominta, wanda duk sukayi order din abinci saita hada musu. Sosai Sa’adatu taji wani nishadi na shigarta da son abin, nan da nan ta kira Fa’iza ta bata labari, sukayi magana kan za’a siyowa Sa’adatun zobo buhu, inda Fa’izar take siye, da duk wasu kayan hadin da tayi amfani dasu, dan wancen zobon na musamman ne tayi ba kamar na siyarwa ba, to wannan dinma tunda ba irin cinikinsu bane na cikin lungu, roba naira dari, saina leda hamsin da kuma naira ashirin, dole za’a tsaya shima a Inganta, haka kunun aya.

Lissafi sukayi na duk abinda za’a kashe, akwai kudi sosai account din Sa’adatu, gashi randa sukaje gidansu Jabir ma, kudi ne Hajiya Hasina ta saka mata, rafar yan naira dari dari guda biyu.

Kudin na nan a dirowar gefen gadonta, saboda ganinsu kawai na saka mata nishadi, shisa ta ajiyesu kusa, kullum saita bude ta kalla. Haka robobin da za’ayi amfani dasu, da kanta Fa’iza ta shiga kasuwa, saita dinga daukar su a hoto tana turawa Sa’adatu, ita kuma tana turawa Badr, har saida suka zabi guda daya da tayi. Da Badr tayi mata maganar za’ayi logo ta zabi business name, ga kuma su sticker da ledar da zata dinga amfani da ita, duk saita diririce tana rasa sunan da zata zaba, karshe da taimakon Badr din suka zabi SH Treats. Tace da lambarta zata dinga amfani, harda su shafin Instagram na kasuwanci saida Badr tasa ta bude da sunan. Cikin kwana biyu akayi komai, ta biya duk wasu kudi da Badr din take mata lissafi, Fa’iza da kanta tazo ta tayata suka hada zobon dan ta kara ganin yanda ta hada wancen, suka gyara ko’ina, dan anan sukayi abincin buda baki tare, ta diba ta tafi dashi.

Washegari kuwa saiya Badr tazo gidan, da ledojin da kuma sticker da za’a manna a jikin robobin. Ta tayata suka manna, ta kwashe ta zuba bayan mota ta tafi. Haka ta koma cikin gida bayan sunyi sallama da Badr, tunda tace ta tsaya ta lissafa ta saka kudin roba, sticker da leda, taga idan an siyar da roba daya 500 zata fita. Ta kuma ga kuma za’a fita, harma kunun ayar idan an fara. Daman da dare data tashi yin sallah, addu’arta duka akan kasuwancin ne, Allaah Ya bata sa’a Ya kuma sa ya samu karbuwa. Aikuwa tana ganin Badr na musu tallah, tana fadin kuma mutanen da zasu samu dandanawa sune na farkon da suka saka order din abinci a ranar. Ta dingajin kamar ta rungume Badr din ta waya, wannan lissafin shiya dauke hankalinta daga kan Jabir da ma auren gabaki daya.

Saboda kwana take tana tashi da lissafe-lissafe daban-daban, ga wasu hotuna da Badr ta turo mata, ita kanta bata gane zobon bane, tace ta zabi daya a ciki ta saka a shafinta na Instagram, har abinda zata rubuta idan ta saka saida Badr din ta turo mata, tana ce mata akwai wani aji da akeyi na koyar da kasuwanci ta yanar gizo, bayan sallah za’a fara dibar sababbin dalibai, ta zama cikin shiri, saita biya a sakata dan ta koyi dabarun da zata dinga amfani dasu, dan tana so ya zamana Sa’adatun ta iya komai, inyaso taimakon da zai dinga shiga tsakaninsu shine na tayata yin tallah kawai. Kafin wani lokaci saiga ‘yan uwan Jabir sunata magana ta manhajar WhatsApp, harda masu kiranta a waya, duk wanda ya fadi sunanshi intazo adana lambar saita kara masa da Paki a gaba yanda zata gane cikin sauki.

Haka Adda Farhana ma ta kirata, tanata tsokanarta

“Ai Jabir bai fadamun an fara business ba Sa’adatu, ko Hajiya zan fara cewa tun yanzun.”

Dariya ta dingayi.

“Kinga kuwa Daddynsu Khalid na son kunun aya sosai, mun huta da zuwa siye a wani waje tunda anayi a gida. In zamu samu yau ina son roba goma.”

Mikewa tsaye Sa’adatu tayi

“Adda sai dai gobe idan Allaah Ya kaimu.”

Dan jim Adda Farhanan tayi

“To babu damuwa, ki turomun da lambar account dinki sai in saka kudin, da kuma gudummuwata a kara jarin aya ko?”

Godiya tayi mata sosai, tana dauko littafin da maigadi ta ba ya siyo mata shi a bisa shawarar da Badr ta bata, na ta dinga rubuta sunan kowa da adadin order din da ya saka, gudun rudewa. Cikin kwana biyu saiga kudi nata shigowa asusun bankinta, saboda ‘yan uwan Jabir haka suka dinga yi mata ciniki, suna kuma dora mata a kafafen sada zumuntarsu. Saiga shi ta sake samun abinyi cikin azumin nan, ta tattara komai ta hade a fridge daya, dan dayan cike yake da zobo da kunun aya. Ciniki ya fara kankama, data kalli kudin dake asusun nata sai nishadi ya kamata, gashi Badr tace mata bayan sallah za’a hada harda dambun nan irin wanda ta kaiwa Hajiya Hasina. Sai kawai ya zamana zobo, kunun aya da kuma dambun takeyi, tana ce mata saita samu masu aikin da zasu dinga kama mata. Ita kuwa gani takeyi in dai da wannan kudin da take ganin shigowarsu, ina zataji wata gajiya?

Kuma ga Fa’iza ma, wanne yan aiki zata dauka, sai ta dinga kama mata, suna samun alkhairin tare, tunda idan Fa’iza ta samu, to a jikin Abdallah da kuma danshi fiye da rabin abinda ta samu din zai kare, ita kuwa ba zata taba mantawa da Badr ba, dan ta zame mata wata hanya ta samun mafitar data jima tana nema, mafitar da sanadinta kaddara ta fado da ita hannun Jabir, ashe rabon arzikin nata ba daga hannun shi kawai zai fito ba

Daman bahaushe yace in da rai da rabo

<< Tsakaninmu 34Tsakaninmu 36 >>

1 thought on “Tsakaninmu 35”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×