Skip to content
Part 37 of 67 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Hankalinta a kwance yake, dan lokacin sallah Aisha babu wani abu da takeyi daya wuce tayi wanka, kwalliyar sallah sai kuma tarbar baki, idan kuma taje gidansu, sai randa ake haduwa gabaki daya a gidansu Jabir. In duk angama wannan kuma suna ware rana daya daga safe har zuwa dare suna yawo ne ita da Jabir din. Yau ma daya rage saura kwana biyu sallah, karamar wayarta ta dauka tana lalubar lambar Wahidah 08039154314, tunda a wajenta ta saka order din masa, wannan karin dai ta sakane fiye da waccan sallar, dan data kai gidansu, sai aka ajiye kowanne abinci aka dirarwa masar, har kaji ma ta siya, tana dai tunanin hadawa da samosa ne, tunda meatpie ma duk a wajen Wahidar ta siya. So takeyi ta roketa ta taimaka tayi mata miya, tasan masar kawai takeyi da sallah, banda miya.

Data kira sai bata sameta ba, dan haka ta tura mata da sako, tana fatan kuma ta samu sararin da zatayi mata miyar. Sai kuma ta koma kan abin sha, ta tashi ta dauko daya daga cikin robobin da yanzun baka raba fridge dinta dasu, duk kwana biyu sai Jabir ya sai musu, ita ko rantsuwa tayi ba zatayi kaffara ba, bata taba shan zobo da kunun aya masu dadin nan ba, da ba azumi akeyi bama wuni zatayi tana sha. Yanzun kuwa har Mummy zatayi wa order, yanda take son kunun aya. Lambar ta fara dauka, zuciyarta tayi wani tsalle, ta sake ganin sunan Sa’adatu ya fito, ta kurawa lambar jikin wayar data robar ido tana so ta tabbatar, ba gizo idanuwanta sukeyi mata ba, lambar Sa’adatu ce, zuwa yanzun bugun da zuciyarta takeyi bana wasa bane ba. Jabir bai fada mata ba amman, ba delivery akeyi musu ba, shine yake zuwa ya karbo da kanshi.

Wani abu ya soki zuciyarta, wani abu da inta dorashi akan kishi batajin zai iya dauka. Tanata so ta tambaye shi, ya ake ciki, amman ta kasa, tunda ya dawo daga Abuja, taga ya jingine fadan da sukayi kafin tafiyar, fushin da yake mata lokacin da yake Abuja, duka ya ajiye su a waje daya kamar basu faru ba, ya riketa a jikinshi da kamshin shi, kalamanshi, da zuciyarshi da take addu’ar ta kasance mallakinta ita kadai. Sai itama ta rike tambayoyinta, duk da sunata nukurkusarta. Sauran kwana biyu azumi, tana kitchen, ta dafa garin Habbatussauda tana tacewa a kofi, wani abu da shanshi ya zame mata jiki yanzun, tunda Mummy tace mata maganin mutuwa ne kawai bayayi in dai zaka juri sha, kuma ka sha din da yardar cewa babu wani abu da yafi karfin Ubangiji, haka kuma babu wata cuta da Allaah Ya saukar batare da maganinta ba, sai dai rashin rabo, dacewa, ko kuma rubutacciyar kaddara.

Sai ya zamana tana iya shan kofi biyar ma a rana, dan Jabir ya tambayeta menene, ta fada masa, daya karba da nufin kurba yana kaiwa bakinshi kafin ma yasha ya ajiye mata kofin yana runtsa idanuwa.

“Bana son kamshin, kamshin wani iri, yana juyamun kai.”

Ta dingayi masa dariya, itama hakan taji daga farko, dakyar ta iya shan rabin kofi, amman yanzun ta rigada ta saba, tasha shi kamar shayi, ga kuma wanda ta kwaba da zuma, kullum da sassafe tana shan cokali uku kafin taci komai, sai cokali uku idan zata kwanta bacci, da ta kare take sake hadawa. To ranar ma ta gama tacewa, tayi tsaye tana sha tana danna waya a kitchen din, Jabir ya sameta, shi kofi ya dauka ya hada tea suna dan hira, shine tayi karfin halin ce masa.

“Sa’adatu fa?”

Dariya yayi, dariya me sauti yana kurbar shayin shi.

“Kaji…”

Kallonta yayi.

“Babu yanda za’ayi ki nunamun ita da duk wani abu nata matsalata ce kuma kizo kina tambayata…abune da ba zai yiwu ba, in ba rigima kike nema dani ba zaki bar maganar nan.”

Sai dai kafin ma tace wani abu ya fice ya bar mata kitchen din, saita rasa kwarin gwiwar binshi, saboda bata neman rigimar sam, tasan shi, fiye da kowa. Babu riba a rigima dashi ko daya, da azumi yazo kuma saita maida hankalinta kan ibada, duk da bawai tambayoyin sun barta bane ba, abinda sukaje yi Abujan anyi? Komai yayi dai-dai? Sa’adatu na da ciki? Ko babu? Ko ya ake ciki? Tana so ta sani da duka zuciyarta, amman yin maganar da Jabir na nufin tashin hankalin da bata shiryawa ba, yana nufin su koma yin komai su biyu, kamar tsarin farko, amman anya ta gama shiryawa? Ita zata rike yaron ko yarinyar, tanajin ta shiryawa wannan, amman ganin Sa’adatu da ciki, cikin Jabir, abinda ita ba zata taba samu ba. Karya ne da yaudarar kai tace ta shiryawa wannan, hasashen shima barazana yakeyi wa numfashinta.

Yanzun ma numfashin ne yake fitar mata a wahalce. Wacce irin sakewa Jabir yayi da Sa’adatu da zata dinga ganin shi duk kwana biyu? Da harya yake siyo abinda take siyarwa yana shigo mata dashi cikin gida? Kamar kuma yasan abinda take tunani, saiya zabi wannan lokacin ya shigo gidan da sallama a bakin shi, kallo daya yayi mata da yanda take masa kallon tuhuma yasa shi tsayawa.

“Sa’adatu ke zobon nan?”

Ta jefa masa tambayar da tayi masa bazata.

“Eh ita takeyi.”

Ya amsa a takaice kuma kamar hakan ba wani babban abu bane, yana kallonta, saboda kallo ne ita takeyi masa na tuhuma, kallo na yayi mata laifi, bai fada mata ba, baikuma san dalili ba, amman ba zai bata damar da zata saka shi jin yayi wani babban laifi na kin fada mata din ba.

“Takardun dana shigo dasu jiya fa?”

Ya tambaya.

“Suna inda ka ajiye.”

Ta amsa shi, saiya wuce ya barta zaune a wajen, zuciyarta da kirjinta gabaki daya nayi mata zafi. Kuma ya samu karfin halin takawa har inda take ya sumbace ta ya sake ficewa ya barta cikin rashin sanin abinyi.

*****

A bangaren Sa’adatu ma shiri takeyi sosai, saboda inda tana so har gidan Anty Khadi taje, rabonta da ita tun bikinta, sai taje ta gaishe da Anty Talatu ma, zumunci take so tayi sosai wannan sallar, shisa ma zata cewa Jabir zatayi kwana biyu a gidansu. Zata dibi komai, suyi girkin da zasu rike ita da Fa’iza. Kuma tana so taga Abdallah, maganar da zasuyi mai muhimmanci ce. Sauran kwana hudu sallah taga alert din daya sa ta samo abin sakatar hakori a daki tana kirga sifirin da yake hade da dayar, dan ta tabbatar ba dubu goma bace, dubu dari ce take gani. Kafin text din Jabir ya shigo mata.

“Kudin hidimar sallarki.”

Text din da bata iya ta bashi amsar shi ba sai daren, darenma badan abinda ta tura ya gamsar da ita ba, saboda ta ina zata fara yi masa godiya? Idan kuma addu’a ce kullum sai tayi, tana daijin ita kanta addu’ar ya kamata ta sake karawa ne. Ba wasu kaya zata dinka ba, tunda na lefenta ta kaisu ina? Ciki ta zabi kala goma ta fito dasu, dinkakku, haka ta zabo takalman da zatayi amfani dasu, jakunkuna da kuma mayafai. Da tayiwa Jabir text ma ta tambaye shi, bai hanata zuwa tayi kwananta biyu ba, dan ko Aisha inba rikici yakeji ba, baya hanata fita unguwa. Ko ba haka ba, inta zauna gidan me zatayi masa? Gara taje tayi nishadinta da ‘yan uwanta, batama jira sanar da ganin wata ba ran daren sallar tayi miyarta da ta sha kaji sai kamshi takeyi. Washegari kuwa tun karfe takwas ta gama shiryawa, ta dibi cefane mai yawa da take dashi, dan duka wanda ya rage ne ta kwashe, ta raba biyu a manyan ledoji, saita kara da naman kaji da kuma kifi, ta dauki dubu biyu kuma.

Da ta zata kaiwa maigadi abincin safe saita bashi tana dorawa da fadin.

“Gashi Baba ayi abincin sallah, zanje gidanmu nima sai jibi idan Allaah Ya kaimu zan dawo, inajin babu wata matsala dan an kulle gidan, kaima kaje gida ko?”

Albarka ya dinga saka mata.

“Ai ba’a bar gida ba kowa ba Hajiya, sai dai zanje din kamar yanda kikace, da magriba sai in dawo.”

Kai ta jinjina tayi masa sallama ta koma gida, bata wani dade ba, direban da zai kaita gida yazo, ita ta dinga fitowa da duk kayanta waje, shikuma ya saka a mota, saida sukaje gidan, ya fara tayata shigowa dasu taga harda wasu karin ledojin manya manya, yace Jabir ne yace ya kawo. Zuwa yanzun kuwa bata san wanne yare zatayi amfani dashi tayi masa godiya ba. To ko dai muhimmancin da yace tana dashine yake ta kokarin nuna mata? Haka Fa’iza ta dinga yabon kirki irin na Jabir din, Sa’adatu na tayata da murmushin amincewa.

“Dan Allaah ki kara kyautata masa Sa’adatu, kin daiga irin son da yake miki, da baya sonki babu yanda za’ayi ya dinga wannan hidimar damu.”

Tuwon shinkafa Fa’izar tayi, Sa’adatu ta kama mata suka karasa komai. Cikin kayan da Jabir ya aiko da wanda ta dibo suka dibarwa Anty Khadi masu dan dama, suka hada mata da abincin sallar, sai na Anty Talatu itama, gidan Anty Khadi din dai suka fara nufa, adaidaita sahu suka samu. Taji dadin ganinsu ba kadan ba, sai dai Sa’adatu tayi kuka, abinda yasa Anty Khadin bata son zuwa kenan, ko Abdalllah Ya ganta saiya kama yi mata kuka, duka kamar ganinta din wani fami ne na rashin Abida. Har saida ta saka su Anty Khadin kuka ita da Fa’iza, nan aka dinga hirar Abida da tarin alkhairinta. Haka gidan Anty Talatu da sukaje, inda ta dinga ina taka sa dasu, kamar zata goya Sa’adatu sabo da jin dadin yanda ta ganta tas, kamar ma batayi azumin ba, dan lafiyayyen abincin da take samu ya hana mata yin ramar nan. Har dubu biyar Sa’adatu ta bata, ta dinga saka mata albarka, haka ta hadosu da su daddawa da kuka, harda dambun naman da tayi.

Da Abdallah zaiyi mata fada ya za’ayi gari daya tace zata baro gidanta tazo ta kwana, tace masa Jabir ne yace ta taho saboda yana wajen Aisha kwana biyun, kuma maigadi ma zaije gida, sai ita kadai. Shine yace ta taho gida, sai gashi kamarma yafi Fa’iza murna, dan har sha biyu sunata hira, Fa’iza wajen goma tace musu bacci takeji ta shigewarta dakinta ta barsu, kuma su duka sunsan ta basu waje ne ko akwai abinda zasu tattauna, lokacin ne kuma Sa’adatu ta samu tayi masa maganar kudaden da suke cikin bankinta.

“Inaso ka samu wani business ne da zaka dingayi Yayaa, da ayita ajiyar kudi haka gara ace ana juyasu wasu suna shigowa.”

Shima ya yarda da shawararta.

“To dole sai nayi tunanin meya kamata Sa’adatu, sai a juya miki su In Shaa Allaah.”

Kai ta girgiza masa, dan taga kamar bai fahimci inda ta dosa ba duk bayanin da tayi masa, ya juya mata me? Bayan ita tana da tata sana’ar.

“Yaa Abdallah bani zaka juyawa ba, duka dubu dari da hamsin din kai na ba, ka dinga juyawa kana hidima da kudin, idan na kara tara wasu sai in kara maka.”

Shiru yayi, shiru kuma mai yawa, kanshi a kasa, kafin ya dago ya kalleta.

“Kudine masu yawa Sa’adatu.”

Kai ta jinjina.

“Amma tace kai kadaine namiji da muke dashi, ko da Abba Ya rasu, muna da wani bangon a tare da kai, idan ka tsaya Yayaa muma duk zamu samu wajen jingina.”

Ya kasa magana, zuciyarshi tayi masa wani irin nauyi, duka iyayenshi suna cikin addu’o’in shi, ba kuma sai a lokutta sallah ba, hakama duk fita in zaiyi ko babu yawa sai yayi sadaka da niyyar Allaah Ya kai musu ladan, yanayin kewar Habibu, sosai, haka Asabe, yana tunanin lokuttan daya rasa masu yawa tare da ita, musamman sanda ta sake aure, duk wani lokaci daya kamata ace yaje ya gaisheta baije ba, yana kuma dana sanin wannan rashin zuwan sosai. Amman Abida, duk yanda zai juya alkhairinta yake gani tare dashi, ko Fa’iza ya kalla sai yaga kamar Abida na tsaye a bayanta, saboda badan goyon bayanta da tsayuwarta ba bayajin zai samu Fa’iza, badon Abida bama bayajin zai samu abubuwa da yawa a rayuwar shi.

Cikin abubuwan kuwa harda Sa’adatu da gata nan a gabanshi, ta tattara duka wasu kudi data tara ta mika masa, ko zai iya magana me zaice? Godiya zaiyi? Ko addu’ar da daman bata yankewa a tsakaninsu?

“Dan Allaah karka ce komai Yayaa…zan maida kudin cikin account dinka.”

Kai ya daga mata, itace tayita kokarin jan shi da hira har ya sake. Zata ce kwanaki biyun nan wasu kwanakine da zata jima wasu basu zo sun goge mata su ba, ko sun dishe tasirin haskensu. Taji daman ta tambayi Jabir fiye da kwanakin nan biyu. Kuma da jagorancin Fa’iza sukayi dambu mai yawan gaske, ta kira direba dan Jabir ya bata lambar shi yace ko da tana bukatar wani abin, kar wata rana baya kusa taita jira, shi yazo ya dauketa taje gida ta dauko kuloli, tazo aka zuba, shi din ta ba kuma, tare da kunun aya da zobo, shima kuma ta zuba masa nasa, ta bayar aka kai gidansu Jabir din. Sai gashi Hajiya Hasina da kanta ta kirata a waya tanata godiya da saka albarka.

Haka ta koma gida cike da kewa, haka kuma sallar ma tazo ta wuce kamar bata faru ba. Sai dai cinikinta karuwa yakeyi kullum, saboda tana kara samun sababbin kwastomomi ne. Bayan sallah da kusan sati biyu dai saiga Jabir, rabonta dashi tun kafin sallah, sai dai a waya, shima fadan Fa’iza taji, duk da ba duka ba, tana dai gaishe dashi duk bayan kwana biyu ta hanyar tura masa sakon da yake amsawa a takaice kamar tata gaisuwar, kuma tun sauran kwana biyu sallah, sau biyu ya siyi zobo da kunun aya, kuma duka lokuttan bashi yazo ya dauka ba, ya bata address ne yace a aika masa dashi a wajen. Sai yau, da ya shigo mata falo da yamma, ya cika mata shi da kamshin da yaketa bazawa, yana sanye da wandon jeans baki, karo na farko in bata manta ba, data ganshi da jeans, sai riga mai dogon hannu ruwan madara. Yayi kyau, gani ma tayi kamar yayi aski, ko gyaran fuska ne, ya daiyi mata kyau ba kadan ba.

Shima kallonta yakeyi cikin riga da skirt din data saka, kanta da hular data tura baya, gashinta daya sha gyara ya dan fito, bakikirin dashi yanata kyalli, yaji kamar ya karasa yaja hular yaga gyaran gashin duka, tunda tace masa zatace saloon yake tunanin me akayi mata, iya wankin kai? Ko an hada da kitso, to gashi ya gani babu kitso. Daman yana neman dalilin da zaizo saiga kiran Likitan shi a jiyan, magana sukayi sosai, yace za’a dora Sa’adatu din akan magani na sati biyu, amman idan kwanakin period dinta sun gaza sati biyun to ta jira sai tayi tagama tukunna ta fara sha. Da yake da daddare ne lokacin saiya bari sai yau din daya siyo maganin, gaishe dashi tayi, ya samu kujera ya zauna yana sauke numfashi.

“In kawo maka ruwa?”

Ta tambaya

“Yanzun Sa’adatu ruwa zakiyi mun tayi? Inzo gidan mai kunun aya da zobo ayi mun tayin ruwa.”

Yanda ya karasa maganar ya bata dariya sosai.

“Daman ai zan hado maka da ruwan ne.”

Tabe baki yayi yana kara sata dariya, lokaci daya ranakun da sukayi a Abuja suka dawo mata, wani abu ya dan daki zuciyarta.

“Tunda na karya ajina na tambaya ba.”

Tashi tayi taje ta dauko masa, ta hado da kofi tazo ta ajiye gabanshi.

“Taliya na dafa, in zubo maka?”

Kai ya girgiza mata, a koshe yake. Aisha tayi girki saboda bata da aikin rana, yana shago ma ta kirashi, sai yace zai aika a karba, ita da kanta taje ta kai masa, suka zauna a ofis dinshi sukaci tare, suka danyi hira tukunna ta tafi. Ya kuma ce mata ko babu kayan cikin da tayiwa wata irin dahuwa ta sake dafa masa irinshi, kunun ayar ya fara zubawa yana sha, sanyin da gardin suka saukar masa suna saka shi sauke numfashi. Sa’adatu kuma ta dauki remote tana dan kara maganar data shigowar shi tasa ta rage, india ne take kallo, tanajin dadin kallon sosai. Saida ya kusan shanye kunun ayar shi tukunna yaja ledar da ya shigo da ita ya mika mata.

“Zaki sha daya kullum, na sati biyu…”

Bata bude ba, tadai ga alamar kwalin magani, ga kuma ledar da tambarin wajen siyar da maganin a jiki, sauran bayanin ya karasa yi mata, yana sakata yin lissafi cikin kanta, baifi saura kwana shida ya rage mata ba, tayi period din.

“Saura kwana shida ko biyar.”

Ta fadi a kunyace, kai Jabir ya jinjina.

“Ba damuwa, in kin fara sha, ki fadamun.”

Nata kan ta jinjina masa.

“A karomun kunun aya guda biyu, kisa mun a leda, in da wanda ya fara kankara ki sakamun shi.”

Mikewa tayi, akwai wanda sukayi kankara ma, su ta saka masa guda hudu, ta kara masa da zobo biyu, tazo ta kawo masa, harya mike tsaye. Ya karba.

“Inda wani abin kinyi mun magana.”

Ta daga masa kai, tun randa Aisha tayi masa maganar Sa’adatu takeyin zobo da kunun aya, bai sake zuwa dashi gidan ba, duk da yana so. Batayi magana ba, amman bayason kureta, tunda ranar yanayinta ya nuna rashin jin dadi karara, ya siya sau biyu da yana shagunan shi, da yawa harma yaran shagon duk ya raba musu. Sannan ya gane gidansu basa rabuwa dashi sam, da kanshi yake nufar fridge ya dauka. Yanzun kuwa tsayawa yayi ya siyi kayan zaki da tarkacen biskit-biskit saboda zai biya gidan Adda Farhana ya kara duba yaronta da yayi zazzabi. Yana ma dai son yayi wani abune da zai dauke masa hankali har lokacin da Aisha zata koma gida, sai shima ya koma, dan tunda ya sauke wayarshi jiyan bayan sun gama magana da likita ya kasa hana kanshi lissafi.

Lissafin kwanakin aurensu da Sa’adatu, da yanda ma sukayi masa gudu sosai, yanzun fa suna cikin wata na hudu, duka yaushe akayi auren? Yanzun yasan tana gama shan maganin nan zasu koma Abuja ne a sake gwadawa, idan an dace, abinda yasan zaiyi wahala ma ace ba’a dace dinba, shikenan sai a fara lissafin lokacin haihuwarta ko? Lokacin da zai rike danshi ko yarshi, wani abu ya mamaye zuciyarshi yana cikata fam da wannan tunanin, wanda bai wani dade ba, tunanin fitar Sa’adatu ya maye gurbin shi, tunanin da yaji ya dagula masa lissafi harya sa ya daina jin dandanon zobon da ya bude yana tukin yana kurba. Saiya dan rage gudun motar ya rufe robar ya ajiye, ya cigaba da tukin, yana jawo tunanin Aisha cike da son danne na Sa’adatu, itama lissafin ne, na kwanakin da suka rage mata, za ta koma aikin Hajj ne da Umra gabaki daya.

Shita fara yiwa magana, yace mata ba zai koma ba wannan shekarar, watakila dai yake Umra kafin azumi ko cikin azumin, sai baije ba. Dan haka suka tsara tafiyar zasuyita ita da Mummynta tunda yace ba zashi ba, sai kewarta ta fara danne shi, dan zasu jima tunda harda Umra zasu kara hadawa, zata tafi ta barshi shi kadai.

“Ba ga Sa’adatu ba.”

Wata murya ta fada cikin kanshi tana saka zuciyarshi wani irin bugawa…

<< Tsakaninmu 36Tsakaninmu 38 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 37”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.