Tsaye take a kicin, rabonta da dogon tunani kan abinda zata dafa harta manta, ba kullum take sanin me za tayi ba, amman data shiga kicin din duk abinda idonta ya fara cin karo dashi shikenan. Matsalarta kawai taji abu mai dadi a bakinta, kuma a zagaye take dashi. To yau Jabir yana nan, kuma a iya dan zaman da tayi dashi ta kula yana da zabin abinci sosai. Kuma da tace masa mai zaici saiya daga mata kafadunshi yana bin bayan hakan da wata doguwar hamma, kafin ya gyara kwanciyar shi yaja bargo ya rufe jikinshi, alamar bacci zai. . .
Allah ya gaparta mana zunubanmu