Skip to content
Part 39 of 64 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Tsaye take a kicin, rabonta da dogon tunani kan abinda zata dafa harta manta, ba kullum take sanin me za tayi ba, amman data shiga kicin din duk abinda idonta ya fara cin karo dashi shikenan. Matsalarta kawai taji abu mai dadi a bakinta, kuma a zagaye take dashi. To yau Jabir yana nan, kuma a iya dan zaman da tayi dashi ta kula yana da zabin abinci sosai. Kuma da tace masa mai zaici saiya daga mata kafadunshi yana bin bayan hakan da wata doguwar hamma, kafin ya gyara kwanciyar shi yaja bargo ya rufe jikinshi, alamar bacci zai koma, saita ja masa dakin ta fito kawai. Dan ita ta fara jin yunwa, da tayi tunani ta rasa, ta kuma ga yana son kifi, sai ta dauko shi kawai ta wanke, tana dubawa taga tana da sauran plantain da dankalin turawa da yawa, farfesun kifi zatayi sai ta soya dankalin da plantain din, idan yana shan shayi to, in kuma da lemo zai hada ko wani abinma dai bata da matsala.

Ta dai barwa Fa’iza sako, tayi mata zobon da kunun ayar duka acan wajenta, dan ta rigada ta hango yau din zata kasance mata rana mai tsayin da ba lallai ta samu sararin yin zobon ba. Jabir ne a gidanta, kuma alamu sun nuna bashi da niyyar tafiya tunda ya koma bacci, idan ma ya tafi din zai yiwu yace zaici abincin rana anan, kona dare, koma ya kara kwana. Wani sama-sama take jinta da tayi wannan tunanin. Tana kwashe kaskon karshe na dankalin Jabir ya shigo kicin din, ya maida kayan da yazo dasu a jikinshi, yayi mata wani irin haske na ban mamaki, hasken kwan lantarkin da yake kicin din yasa kalar fatarshi yi mata wani iri, har bata san lokacin da tace masa.

“Kana Hausa, ka kuma iya, amman abubuwa da yawa tare da kai basuyi kama da na Hausawa ba.”

Dariya yayi mai sauti, yana karasawa kusa da bowl din data ke zuba plantain, dube-dube ya fara.

“Ina cokali? Kar in saka miki hannu a ciki.”

Kallonshi tayi, bata jima da tsame nata hannun ba, dan ta fahimci babu yanda za’ayi ka soya plantain kuna kallon juna batare daka dinga dauki dai-dai ba.

“Yana cikin drawer din can, ka sa hannu mana.”

Fuskarta ya leka yana sata kallonshi da girarta duka biyun a dage, ko da ya kai hannu ma jira yake yaji ta bige masa hannun yanda Aisha takeyi duk idan tana soya abu yazo yasa hannu, idan ma yana gidan to zai samu cokali mai yatsu a ciki, sai dai in yana jin neman tsokana ne zai saka hannu

“It’s not hygienic.”

Ta kan fada, to a wajen Aisha komai ma ka’ida gare shi, yasan wasu abubuwan tana daurewa ne saboda tana zaune dashi, babu yanda zatayi, plantain din ya dauka guda biyu ya saka a bakinshi.

“Meye nawa baiyi kama dana Hausawa ba?”

Ya tambaya yana tauna plantain din.

“Abubuwa da yawa…”

Cewar Sa’adatu tana dorawa da.

“Kalarka…kaga ni za’a ce ina da haske, amman ba can ba, kaima kuma ba fari bane ba, amman kalarmu ba iri daya bace ba, naka hasken yayi wani duhu da baiyi kama dana mutanen yankin nan ba.”

Dariya Jabir yayi.

“Da gaske nake, haka gashinka, ganin shi nake me laushi sosai…”

Gas din ta kashe danta kammala, hakan Jabir ya gani, ya kamo hannunta yana dan dukar da kanshi ya dora hadi da yawo da hannun, kafin ya sauke mata shi, gashin ma yafi yanda take gani laushi.

“Dan wace kasa ce kai?”

Ta tambaya, tana amfani da dayan hannunta ta murza wanda ya saki, saboda jinshi da takeyi wani iri, kafadu ya dan daga.

“Nigeria mana…kingama? Me zan tayaki dauka? Yunwa nakeji”

Kai ta jinjina masa

“Shayi zaka sha?”

Da sauri ya girgiza mata kai yana tambayar

“Akwai kunun aya?”

Maigadi ta zubawa

“Ko zaka mikawa Baba maigadi sai in fitar mana da namu.”

Kallonta yayi yana dan dakuna fuska kamar yaron dake shirin yin kwiya

“To bari in mika masa inzo.”

Cewar Sa’adatu, karba yayi, shifa kwata-kwata ba aike yake so ba, idan bashi ya saka kanshi ba. Ko a gida bakinshi yana kusa taba bango duk lokacin da wani a cikin Yayyenshi zai saka shi dauko wani abu, ko a cikin gidan ne, balle kuma aiken ya hada da saiya fita. Yana juyawa ta samu wajen data zuba musu farfesun, ta dauka da dayan bowl din data hade dankalin da plantain din ta fita daga kicin din, a tsakiyar falo ta ajiye musu. Ta koma ta dauko kofi da kunun aya roba biyu tazo ta ajiyewa Jabir da harya dawo. Ita kicin din ta koma, dan shayi take so ta hada dashi. Data hada ta koma falon ta ajiye, saita je ta kunna tv din, tana nemo tashar da tafi so, saboda yanda suke saka fina-finan India masu kyau. Sai kuma har Jabir din ya mayar da hankalin shi kan tv, suka karya cikin shiru. Ta rigashi gamawa, sai da ta jira ya karasa tukunna ta kwashe kwanonin ta kai kicin, sanda ta dawo Jabir harya mike.

“Zan fita…”

Kai ta jinjina masa

“A dawo lafiya. Allaah Ya tsare.”

Tayi kokarin danne harshenta dan karta tambayeshi ko zai dawo.

“Kiyi abinci dani, idan akwai kunun aya ki bani in tafi dashi.”

Ya fadi, zuwa tayi ta dauko masa roba biyu masu kankara, ya karba yana wucewa batare daya sake ce mata komai, tabi bayanshi da murmushi a fuskarta, ya fice daga gidan, ta sakawa kofar mukulli ta koma ciki, sai dai duk yanda taso, ta kasa maida hankalinta kan cigaba da kallon fim din, saboda yayi wajen tunanin abinda zata dafa da zaiyiwa Jabir dadi. Ta dauki waya da niyyar tambayar shi yafi a kirga tana fasawa, saita koma daki da niyyar ta kara runtsawa, nan dinma baccin bai samu ba, ta tsurawa wajen da Jabir ya kwanta ido tana jinta wani sama-sama, tunanin duk data kama zatayi sai taji ya kwace mata. Hakura tayi, ta mike, zanin gadonta babu abinda yayi, amman sai taji tana so ta sake shi, hakan tayi, ta wanke bandaki, ta share dakin. Ta fita ta karasa gyara gidan, har wanke-wanke tayi, ta kunna turaren wuta. Tukunna taje tayi wanka itama, ta samu doguwar riga ta wani leshi marar nauyi, bama zata iya cewa ga asalin sunan kalarshi ba, amman duka leshin da aka saka mata a lefe, haka kalolin suke, idan jane, to sai taga kamar bai kamata ta kirashi ja kai tsaye ba.

Saboda zata dinga hasko jajayen abubuwa a idonta, dakyar zata samu kalar ja guda biyu da leshin zai tsaya a tsakiyarsu, wasu irin kaloline masu laushin gani a idanuwa, basu cika haske ba, kuma ba suyi duhu ba, wasu kaloli a tsakiyar wadannan abin biyu. Ta kara gyara gashinta, ta kara masa abin daure gashi, saita ajiye dankwalin kan gado, itama ta zauna tana mike kafafuwanta bayan ta feshe jikinta da turaruka. Wayarta ta dauka, a karo na farko ta lalubo lambar Jabir ta manhajar WhatsApp, batayi wani dogon tunani ba ta tura masa

“Me zakaci?”

Tana ganin sakon ya nuna mata ya shiga, amman bai bude ba, ta fita ta amsa wasu sakonnin da suka shigo mata, harta gama Jabir bai bude sakon data tura masa ba, sai da aka dauki mintina ashirin tukunna ya amsa da

“Komai ma”

Numfashi Sa’adatu taja tana saukewa, inda tasan me zata dafa ai da ba zata wahala tambayar shi ba

“Tuwo?”

Wannan karin da saurin shi ya dawo mata da amsa

“A’a, banaci”

Saita tsinci kanta dayin dariya

“Fankaso?”

Tana ganin alamar yana rubutu, sai kuma ya dakata, saita sake ganin alama, yayi hakan yafi sau bakwai, kenan kome yake rubutawa, fasawa yakeyi yana gogewa, dariya tayi me sauti

“Baka sanshi ba ko? Baka san Fankaso ba”

Ta karasa rubutun tana dorawa da emoji na dariya kafin ta tura, yayi kusan mintina biyar, gashi ya nuna ya karanta, amman bai amsa ba, dariya Sa’adatu takeyi ba kadan ba

“To alkubus”

Ya amsa wannan karin, da kalma daya kawai

“Sa’adatu…”

Amman sai taji kamar ba sunanta kawai ya kira ba, ba sunanta kadai ta karanta ba, harda yanayin fuskar shi sanda ya kira sunan nata, cike da kashedi, ya sauke idanuwanshi cikin yanayin dashi kadai yasan ya yakeyin shi, shisa taketa dariya. Ko a gida tana da tsokana kowa ya sani, amman tafi tsokanar Amira duk da jibgar da takan sha, saboda yanda Amiran take da saurin shaka, ta ga alamar Jabir dinma yana daya daga cikin mutanen nan da tsokana ke saurin shakar dasu, shisa abin yakeyi mata dadi

“Bari kawai inyi dashishi to”

Ya kusan mintina uku kafin ya amsa

“Taliya, Sa’adatu…”

Ya kara da

“Taliya da koma me yayi miki”

Dariya ta sake kwace mata

“Abinda yayi miki wanda zan iya ci, abincin mutane”

Sosai take dariya

“Wanne iri ne ba abincin mutane ba?”

Ta tambaya, sai ya koma sama yana nuna mata dashishin data rubuta

“Yanzun wannan sunan yayi miki kama da abincin mutane?”

Emoji din dariya ta tura masa

“Na zama abokin wasanki ko? Ai nasan ba abinci bane daman”

Emoji din ta sake turawa kafin ta amsa da

“Abinci ne fa, wasu suce Burabusko”

Ta tura

“Ko Biski”

Emoji na harara ya turo mata

“Get out of my phone Sa’adatu”

Dariya tayi a fili, tana jan datarta ta kashe. Wayar Badr ta kira da suka gaisa cikin raha, sannan Sa’adatu ta dora da

“Anty Badr taliyar yan gayu zaki koyamun”

Sosai Badr tayi dariya

“Daman akwai taliyar yan gayu Sa’adatu?”

Itama dariyar tayi

“Eh mana, irin wadda nake gani a Instagram”

Yanayin raha da rashin girman kan Sa’adatu yana burge Badr din sosai, kome zata gani batajin shakkun Badr din tayi mata kallon tayi kauyanci, zata tambaya, haka idan bata gane ba zata sake jera mata wasu tambayoyin har saita fahimta, ko kalma ce ta turanci tagani da tayi mata tsauri ko bata fahimceta ba to tambayarta takeyi. Shisa ita kuma duk wani abu da take tunanin zaiyiwa Sa’adatun amfani take tura mata shi. Yanzun ma sallama sukayi, tace taje ta duba WhatsApp, ta tura mata videos har kala biyar, na yanda zata sarrafa taliya, daga kasa kuma tace ta duba da kyau, inta zabi wadda zatayi, abinda bata dashi sai tayi mata magana zata sa a siyo a aiko mata dashi. Cike da farin ciki Sa’adatu ta bude videos din, kafin ta fara kallo a tsanake.

Jabir kuwa da murmushi ya ajiye wayar ganin ta sauka, murmushin da ya kasa barin fuskar harya kammala duk hidindimun shi na ranar, ya wuce gidanshi. Jaka ya samu ya shiga hada duk wani abu da yake tunanin zai bukata na kwanaki bakwai, idan yaji zaiyi fiye da hakan saiya koma ya sake dauka. Yanayi yana atishawa, kafin ya gama kuwa ya fara dan tari, daman tun safe yakejin kamar wani abu a cikin makoshin shi, bai dai kawo mura bace sai yanzun. Haka Aisha ta kirashi video call yana dan tari

“Jay mura ko? Kasha abu mai kankara”

Ta karasa cike da tuhuma, dan hade fuska yayi

“Injiwa yace na sha abu mai kankara?”

Jabir komin tsananin sanyin da akeyi sai da AC yake iya bacci, sai dai ya rufe jikinshi, ita kuwa haka take tashi da hanci a toshe, shisa lokutta da dama sai dai su raba wajen kwana, ta koma wani dakin ta kunna abin dumama daki, amman in dai zai sha abu mai kankara, musamman ya jera kwanaki, sai mura ta kamashi. Gashi bai iya mura ba sam, ga gardamar shan magani

“Kasha abu mai kankara, kar muyi gardamar da kasan baka da gaskiya”

Idanuwa ya lumshe mata yana sake budesu a kanta

“Kaina ya fara ciwo”

Numfashi ta sauke daga bangarenta, kewarshi na mamayarta, tanajin kamar ta miko hannu ta cikin wayar ta taba fuskarshi

“Kasha magani, dan Allaah, kuma karka zauna a gidan, ka tafi wajen Hajja”

Kai ya daga mata

“Kaci abinci?”

Ya girgiza mata kai, yana kai dan yatsa ya shafa wayar

“Nayi kewarki”

Ya furta da dukkan zuciyarshi, sun kusan mintina talatin suna magana, duk ya shagwabe mata, ita kuma ta biye masa, sai dai taga lokaci na tafiya gashi yace baici abinci ba ta lallaba sukayi sallama. Ya mike ya dauki jakarshi ya fita yana kulle gidan, a gaban motar ya dora jakar kan kujera, ya shiga ya zauna yana kunna motar. Sai dai ko titi bai fita ba yaji tsikar jikinshi na tashi alamun zazzabi na son rufe shi. Ga makoshi da kirjinshi sun fara masa zafi. Haka ya karasa gidan Sa’adatu da wani irin nauyin jiki. Dan daya kwankwasa, ta bude masa, ta kuma mika hannu, bata jakar yayi yana wuceta ta shige falon ya nemi doguwar kujera ya kwanta. Anan cikin falon ta ajiye jakar tashi, tana binshi da idanuwa, kafin tace

“Yunwa?”

Yanajin yunwar ma, tun abincin da sukaci, sai kunun ayar da ya karba, bai kara cin wani abu ba. Gashi yanzun la’asar ta wuce.

“Akwai yunwar ma”

Cewar Jabir, wucewa Sa’adatu tayi, shawarar Badr ta dauka, da yake jalof ce, tace mata ta tafasa, da ta danyi laushi saita tace ta rufe, ta hada komai ta kashe gas din, idan yaso Jabir din na shigowa sai taje ta hade komai ta juya, mintina biyar zuwa goma ya turaru saita sauke. Dan ita tafi gane taliya daga tukunya sai plate. Hakan kuwa tayi, ta dai dibi komai ne ta hada musu nasu ita da maigadi, saita dinga mamakin dadin da taliyar tayi, tana ta shima Badr albarka, tabbas zama da ita ta koyi abubuwan fita kunya irin haka. Shisa kanta har rawa yake sanda take hadawa Jabir, cike da yarda da kai da kuma alfaharin abinda tayi din. Ga taliyar tayi kyau, tasha yanke-yanken tattasai kala biyu, kore da yellow daya kara kawatata. Haka ta samu filet mai kyau ta zuba, ta saka masa cokali mai yan yatsu ta dauko zuwa falon, tun kafin ma ta ajiye kamshin spices din da tayi amfani dasu ya daki hancin shi.

Lokacin data ajiye kuwa harya mike zaune

“Ki janyomun table in dora akai Sa’adatu”

Abinda yace tayi, ta dauki filet din ta dora masa, ta koma ta dauko robar kunun aya data ruwa, ta sake komawa kicin ta dauko kofi bayan ta dauraye shi ta ajiye masa. Ta nemi kujera ta zauna tana kallon yanda Jabir din yake cin taliyar, kafin a hankali ya dago kai yace mata

“Tayi dadi sosai… kizo ki zubamun kunun ayar”

Tashi tayi, taje ta kwance ta cika masa kofin, a nutse yakecin abincin yana korawa da kunun ayar, sai gashi kadan ya rage

“In karo maka?”

Dan ware idanuwa yayi

“Kina so inyi amai, na koshi har wuyana”

Dan baima yi zaton zaici da yawa haka ba, tazo ta dauke filet din takai kicin. Tana tunanin wani abu marar nauyi da zatayi musu da daddare. Data dawo falon ta zauna, saita dauki wayarta tana bubbude videos din girke-girken da Badr take turo mata, ko zata samu wani abin mai sauki da zata iyayi. Jabir ma tashi wayar ya dauka, yana dannawa yana dan kurbar kunun ayar, sanyin shi na saka shi yin tari lokaci zuwa lokaci hadi da gyaran murya saboda makoshin shi da yake ciwo, haka kuma duk lokacin da zaiyi tarin sai Sa’adatu ta raba idanuwanta daga wayar da take dannawa ta kalle shi, sai kuma taso ta tambaye shi ko mura yakeyi, amman kuma ai tare suka kwana, duk jiya, har wayewar gari bataji yayi tari ba, in ba a fitar shi murar ta taso masa ba, ganin yanda hankalin shi kacokan yake kan wayarshi yasa bata tambaya ba. 

Akan kunnuwansu aka kira sallar Magriba, Jabir ya rigata mikewa, dakinta kuma ya nufa, sai ita ta shiga daya a cikin sauran biyun. Saida ya fara kama ruwa, tukunna ya daura alwalar da yana fitowa daga bandakin zuwa daki, sanyin da dakin ya dauka ya hadu da danshin ruwan alwalar da yayi yasa tsikar jikinshi wani irin mikewa, sanyin na ratsa shi har cikin ciki, dan saida duka jikinshi ya amsa. Ya sauke hannuwan rigar yadin jikinshi daya ja sama. Amman jikinshi sake amsawa yayi, barin jikin yanaji ba a waje bane kawai, har can cikin hanjin shi. Haka ya fita masallaci, amman kafin ma a karasa idar da sallar, fankar cikin masallacin ta kara gigita shi. Lokacin da aka idar kuwa zazzabi ya gama rufe shi, yanata faman tari, har na kusa dashi saida yayi masa sannu, ya amsa ya mike batare da yayi dogon azkar ba.

<< Tsakaninmu 38Tsakaninmu 40 >>

1 thought on “Tsakaninmu 39”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×