Skip to content
Part 40 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Babu abinda take tunawa sai lokacin da take hangen Jabir daga nesa a gidanshi, lokacin da zata rantse ko wuka aka dora masa ba zai ko iya fadin baka bace ita ko fara, saboda yanda baya kallonta, gaisuwarta ma daga kasan makoshi yake amsawa. Shisa ta tattaro mazaje da yawa da taci karo dasu a litattafan Hausa, ta tsamo halaye daban-daban na kowanne a cikinsu, ta tattara ta hadawa Jabir din. Bayan kasancewar shi mai girman kai, yanda take tunani a lokacin, rashin magana, irin miskilancin nan da mazan novel suke dashi, miskilancin da za’ayi musu magana daya, sai suyi mintina goma kafin su amsa, dan akwai littafin da taji shi jarumin tsabar miskilanci da shiru-shirun da yake dashi, idan yayi maganar data wuce hudu a jere sai yayi ciwon kai. Dan ko mamanshi ma haka yake amsata dai-dai, matar shi shekararsu shidda tare, amman sai tayi sati biyu bata ga dariyarshi ba.

Kawai dai taga Jabir tare da Aisha ne, taji tayi masa magana, tana kuma sauke numfashi yana amsata, ba amsa kalmomi kadan ba, cikakkiyar amsa, tana daga kicin kuma tasha juyo dariyarsu alamar hira sukeyi, saita kankare masa hali daya data makala masa, da kaddara tasa shi matsowa kusa da ita kuma, sai taga ai babu wani hali guda daya data makala masa da yayi dai-dai da nashi, sai dai rigimar da bata hasaso masa ba, itace taga gilminta a Abuja, ta ga kadan daga cikinta, bata kuma fatan wani abu da zai faru yasa ta ganta gabaki daya. Bayan rashin girman kai, ya iya hirar da zata saka manta da komai, ko dariya ba zaka dinga sanin lokuttan da zataita kwace maka ba. Sai dai a duka hasashenta, ko yanayin zubin shi na namiji mai cikakkiyar halitta a ido, tana masa kallon jarumi, irin jarumin namijin nan da ko lokacin kuruciya yara sa’anninsa zasuyi tsoron takalar shi da fada.

Jarumi ta fuskoki da yawa, ko alamar sangartar da yakan nuna lokaci zuwa lokaci baisa ta daina yi masa wannan kallon ba, sai a kwanaki hudun nan, yau cikon na biyar da takejin inta kara minti biyar daki daya dashi, tabbas zata saka masa filo akai tabi ta zauna, tasan ya mura take, tunda inta riketa batayi mata da wasa sam, ita ba iya hancinta zai dinga zuba ba, tari, zazzabi, ciwon kai duka saita hada dashi lokaci daya, da ta kwana biyu kuma ciwon makoshi zaisa muryarta tayi wata irin budewa ko kuma ta shaqe taqi fita gabaki daya. Sau nawa ma duk gudunta da allura sai anyi mata ta zazzabi idan tana mura. Amman Jabir yabi ya narke, ya shagwabe kamar wanda motar itace tabi ta kanshi. Ranar farko tabbas da zazzabi ya kwana, daga sallar Magriba daya dawo daga masallaci, ko isha’i bai fita ba, sai wajen goma data ga bacci na shirin daukar shi ta matsa masa ya tashi yayi isha’i ya koma ya kwanta.

Ta kuma damu, duk da yayi bacci haka ta dinga leka fuskar shi har karfe sha biyu, lokaci zuwa lokaci kuma zata taba goshin shi, sai da taji yayi zufa, alamar saukar zazzabi tukunna ta samu tayi bacci. Amman batajin tayi cikakkun awa biyu dayin baccin taji Jabir yana tabata hadi da kiran sunanta, dakyar ta bude idanuwa

“Sa’adatu…”

Ya sake kira, takai hannu ta murza idanuwanta, tana budesu akanshi, ba ganinshi takeyi ba saboda duhun dakin

“Zan sha ruwa. Ki bani ruwa, ni bani da lafiya”

Ya karasa maganar muryar shi na sauka, wayarta ta laluba, ta kunna fitilar

“Zazzabin ne?”

Ta tambayeshi tanajin ta wartsake gabaki daya, saida yayi tari tukunna ya daga mata kai

“Kaina na ciwo, haka makoshina…kina da tissue?”

Sauka tayi daga gadon, ta kunna wutar dakin, sannan ta fita, ruwan a store ta dauko masa marar sanyi, ta kuma dauko masa tissue babba, ta dawo dakin ta mika masa duka biyun a tare, saiya karbi tissue din yana kallonta da robar ruwan

“Ga ruwan, ko ka fasa sha?”

Kallonta ya cigaba dayi, haka kawai sai kewar Aisha ta taso masa, da ba ruwan kawai zata kawo masa ba, zata hado masa shayi mai citta da kanamfari, ta zauna ta biye masa, yanda ya kasa bacci su hadu su shiririce har gari ya waye, amman ruwan ma Sa’adatu ba zata bude masa ba, ko dan batasan ya yakeji bane? Zagayawa tayi ta dora ruwan a gefen drawer din bangaren da yake.

“Mura ce ta kamaka, ina da maganin mura, harda na tari ma, in dauko maka?”

Da mamaki yake kallonta.

“Kinyi mura ne? Yaushe? Waya kaiki asibiti”

Saida taje ta kashe kwan dakin, ta bar na wayarta, ta koma kan gadon tukunna ta amsa masa da.

“Kwanaki ne, asibiti? Mura ce fa, Baba maigadi na aika chemist yayo mun wani hadin mura, ina sha nayi bacci, dana tashi sai naji dadin jikina, tarin ma sai daga baya daya dameni ne na bashi ya siyomun maganin tari.”

Daga kwancen yake kallonta, yake kuma jinjina ma rashin hankalinta, magani ta bayar aka siyo mata kai tsaye, maganin da ba likita bane ya rubuta mata, kuma har take masa tayin ko zaisha?

“Maganin da ba likita bane ya rubuta miki Sa’adatu?”

Ya karasa maganar tari na kwace masa, bashi dama karfin magana saboda makoshin shi da yake masa zafi

“Murar ce saina tsaya likita ya rubuta mun magani?”

Su da inba tsanani ciwo yayi ba, iyakacin su chemist din Bala. Kusan duk unguwarma nan ake zuwa, har dan karin ruwa sai yazo gida ya saka maka. Sai ciwo yayi ciwo ne ake tafiya asibiti. Hamma tayi tana jan bargo, ta mika hannu ta dauki wayarta ta kashe fitilar, dan idanuwanta sunyi nauyi sosai. Idan ta tsaya magana baccin zai iya guduwa. 

“Bacci zakiyi ki barni?”

Jabir ya fadi cike da mamakin ganin Sa’adatu taja bargo tana gyara kwanciya

“In dauko maka maganin?”

Ta bukata, shiru yayi yana kallonta ta cikin duhun dakin, ya mika hannu ya lalubi robar ruwan ya bude ya kurba ya rufe yana mayarwa ya ajiye. Ya matsa sosai ya hade tazarar dake tsakaninsu, sosai ya shige jikinta, dan kusan rabinshi akanta yake, yana hana mata baccin da ya fara neman daukarta saboda nauyin daya dora mata da kuma wani bakon yanayi da yake mamayarta, tarin da yayi a bayan kanta yasata fara kokarin zamewa daga jikinshi

“Dan Allaah, zaka shafamun mura.”

Bude baki yayi yana rufewa cike da mamaki, kafin yayi amfani da kafafuwan shi duka biyun yayi mata rumfa, sosai take kiciniyar kwacewa ta kasa

“Allaah da gaske zaka shafamun.”

Ta fadi tana haki, idan ya shafa mata murar nan ai ya gama da ita

“Kinga sai muyi jinya tare…”

Cewar Jabir daya hada hannayenta ya kara nadeta tsaf a jikinshi yana maida numfashi shima, wato gudunshi ma takeyi. Yanda duk Sa’adatu taso ta koma bacci kasawa tayi, dan Jabir bai saketa ba saida ta yarda zataje ta hado masa shayi, baima zauna a dakin ba, ya bita kicin din inda duk ta cire kafarta nan yake mayar da tashi. Ba ita ta samu ta runtsa ba sai bayan da tayi asuba, shima daya dawo daga masallaci saiya kwanta a bayanta, ko jinshi batayi ba saboda baccin daya dauketa. Ashe abin zaifi yawa washegari, Jabir langabewa yayi, ko bandaki zashi saiya mika mata hannuwa ta tayashi mikewa tukunna, haka ya samu waje yayi zaune, ko abin goge baki ita ta matsa masa a jikin brush ta bashi, taga alama inta tsaya a dakin wankan da zaiyi ma ba zaiki tayi masa ba.

Gashi ko paracetamol sai da suka kai ruwa rana tukunna Jabir yasha, tunda tayi masa tayin maganin mura yaki, suje asibiti yaga likita yaki, kuma ya narke kamar kiris yake jira ya sume mata. Bai fara cika mata ciki ba sai washegari da babu zazzabi ko kadan a jikinshi, tarin ma ya fara sauki tunda ta hada masa shayin citta, ta zuba zuma da lemon tsami ya kusan wuni yana sha, amman haka ya kara narkewa, ko girki batayi ba, sakawa yayi sukayi order din abinci wajen Badr har maigadi saboda yana so ta zauna a kusa dashi

“Ba zakice mun sannu ba ko?”

Zai furta lokaci zuwa lokaci, yana kamo hannunta ya dora a saman kanshi, cinyoyinta kuwa sun zame masa filo, koya zata zauna nesa dashi zaice ta matsa kusa dan ya kwanta yana fada mata yanda makoshin shi yake zafi har cikin kirjinshi, kanshi yayi nauyi, jikinshi duka baya masa dadi. Shisa da yamma suna falo, data zare jikinta da sunan zata dafo masa shayi, ta dawo taji yana waya da Aisha, saita lallaba ta koma kicin din ta zauna, tana juyo shi yanata fadawa Aishar yanda yakeji, yanda kuma yake zayyanawar sai kayi tunanin Ebola yakeyi ba mura ba, da alama kuma biye masa tayi. Ta saka Sa’adatu tunanin cewa ita Aishar ce ta sangarta shi, shisa yake abinda yakeyi. Bata sake shiga mamaki ba, sai wajen karfe takwas da ta ‘yan gidansu Jabir din suka cika mata falo, babu kuma wanda yazo hannu biyu. Harda wanda bata ma taba ganinsu ba, maza manya, da duk wasu alamu suka nuna suna da iyalai.

“Ya sha wani magani ne?”

Mus’ab da yake likita ya tambayi Sa’adatu

“Yaki sha, sai paracetamol kawai”

Haka Mus’ab din ya tashi yaje ya taba goshin Jabir kamar wani karamin yaro, yana jera masa tambayoyi da sannu kamar sauran. Farhana kuwa tana gefenshi tana mika masa kayan marmarin da tasa Sa’adatu ta daurayo ta kawo mata da wukar data yayyanka masa dai-dai sha.  Gefe Sa’adatu ta koma tana kallon ikon Allaah, yanda gabaki daya hankulansu yake kan Jabir, ga damuwa bayyane a fuskokinsu, daya a cikinsu ne ya fita ya siyo magungunan da Mus’ab ya rubuta. Har goman dare suna gidan, da zasu tafi kuwa Mus’ab da Farhana suka dinga jaddada mata ta kula dashi, ta tabbatar yasha magungunan dan baso yakeyi ba. Farhana kamar ta dauki Jabir din ta tafi dashi

“Ko dai in turo miki mai aiki ne Sa’adatu? Tunda kinga shi bayajin dadi, kar hankalinki ya rabu gida biyu, ga kula dashi ga kuma hidimar gida”

Ta girgizawa Farhana kai, duka aikin guda nawa ne? Bayan saita ga dama zatayi girki. Haka dai sukayi sallama tana ta kara jadda mata ta kula dashi sosai, dan mura batayi masa da wasa. Bayan sun tafi saida ta kimtsa wajen, ta kwashe abubuwan da suka kawo din, ta saka komai inda ya kamata, tana mamakin ganin harda ice cream cikin tarkacen da suka kawo, shida yake mura. Washegari kuwa, kamar tasani da tayi wanka saita saka doguwar rigar atamfa, tayi daurinta mai sauki, saiga Hajiya Hasina a gidan, tazo duba Jabir. Sa’adatu ta rasa inda zata sakata, kome zata kawo mata tunda zuwan bazata tayi, Surayya ce ta rakota. 

“Karki damu kanki Sa’adatu, nima ba dadewa zanyi ba, zanga jikin nashine dan naji muryar shi tayi kasa sosai da safen nan dana kira”

Zuwan Hajiya Hasina yasa ta kewar Abida sosai, wato uwa daban ce, tasan ko kusa basa irin sangartar da Jabir yake yiwa Hajiya Hasina, bata kuma jin ko da suna yara sunyi irinta, amman tabbas sun taso cikin kauna da tsantsar kulawar Abidar, kamar kowacce uwa, in dai zasu kwanta ciwo, komai nata tsayawa yakeyi har sai sun samu sauki. Maganin da Sa’adatu tayita fama dashi yaki sha, Hajiya Hasina tasa ta kawo mata, ita ta bashi da kanta, Sa’adatu na kallonsu. Da yasha kuwa saida ta shafa kanshi alamun yayi abin kirki, sai gashi da zata tafi ya mike, dashi aka rakata har bakin mota, bayan Sa’adatu ta hadasu da zobo da kunun aya. 

Yau daine ya isheta, tunda ko tarin ma babu, amman yakiyin kwari da jikinshi, ko da tace masa tana son cin dankali sai yace su duba idan Badr zatayi ranar su siya ko su siya a wani waje, dakyar ya yarda ta soya da kanta, daman so takeyi ta bar masa dakin tasha iska. Daya gaji da zaman sai gashi ya fito falo, ya kunna tv, sai dai ya kasa tsayawa tasha daya, sai wasa yakeyi a tsakanin tasoshi, kafin ya barshi wata tasha da ake wasan tseran motoci, yayi kasa da maganar sosai. Dankalin da sauce din kwai Sa’adatu tayi, ta zuba masa shima tana hada masa shayi, baima ci da yawa ba don bayajin yunwa, yana ta bin Sa’adatu da duk wani motsinta da idanuwa. Jiya ba karamin kokarin mallakar kanshi yayi ba, balle a yan kwanakin nan ta fara sabawa da zama a jikinshi, bata dari-darin nan da yake hange cikin idanuwanta ko da hannunta ya rike.

Jiyama kafin yayi wani motsi, data hau gadon saita matsa kusa dashi sosai ta kwanta, kamar hakan abune da takeyi kullum, bayajin tasan ma tayi din, daya zagaya hannunshi, saita saka yatsunta a cikin nashi kafin ya riko da kanshi, tasa yanajin babu abinda yake so irin ya tsallaka duk wata katanga da ya gina a tsakaninsu tun daga ranar walimar nan daya fara jin hannunta cikin nashi. Ba zaice wanne labari take bashi ba, ya daiji Twitter, ya kuma ji kaza, amman yanayin dariyar dake cikin muryarta da kuma yanda tayi kasa da ita saboda dare ya hadu ya karasa hargitsa shi. Sai gashi ya manta da murar da yakeyi, sau biyu yana watsa ma jikinshi ruwan sanyi kafin gari ya waye. Yau kuma saita zabi ta saka wata doguwar riga da baisan kota yadi bace ba, na kanti ko dinka mata akayi, ruwan kwaice mai haske, sai akayi mata zanen wasu ganye manya masu launin kore da ratsin ja, dankwalin rigarne ta daura, ya daizo goshinta sosai, ya kuma zauna kamar an dasa mata.

Baisan man lebe ta shafa ba, ko kuma maikon dankalin da takeci bane yake walkiya a labbanta, amman tayi masa kyau, wani irin kyau daya sa yaji tsoron zama a kusa da ita, daga karshe ma ya sake watsa ruwa ya canza kaya yace mata zai fita, watakila rashin shakar iskar data gauraya da numfashin Sa’adatu da kamshinta ne yasa shi jin abinda yakeji. Sosai kuma fitar ta sama masa nutsuwa, har gidansu yaje suka zauna suka sha hira, bai koma ba sai bayan isha’i, abinci ma a wajen Hajja yaci, shisa ko da Sa’adatu tayi masa sako tana tambayar shi abinda zaici yace mata babu komai, zaici a wajen Hajja. Yana shigowa gidan yayi bedroom yana barin Sa’adatu a falo bayan tayi masa sannu da zuwa, daya watsa ruwa sai yayi kwanciyar shi suna chatting da Aisha data turo masa hotunan da tayi, sai ya sauka yana kiranta

“Baki da lafiya?”

Ya tambaya, tayi dariya

“Kin rame, idanuwanki sun rame…meya sameki?”

Ya sake fadi muryarshi cike da kula da kuma damuwa

“Babu komai fa, kasanni da canjin yanayi, amman ya fara dai-daituwa”

Hira sukayi sosai, dan Sa’adatu ma tana can wani fim da take kallo ya dauke mata hankali, in ba gamawa akayi ba batajin zata iya tashi. Ko da sukayi sallama da Aishar ma sai suka sake komawa WhatsApp, shi ya fara fada mata yanda yake kewarta yana kuma tambayar kwanaki nawa ya rage kafin ta dawo, da kuma yanda kwanakin sukayi masa yawa, cikin son ta kwantar masa da hankali ta soma biyewa hirarrakin shi, sai dai ya fara jin son ko ita ta biyo ta cikin wayar, ko shi yabi ya sameta, shisa yayi mata sallama, ya ajiye wayar a gefe ya kwanta yana maida numfashi a hankali a hankali. Bacci ne ya soma daukar shi yaji shigowar Sa’adatu, da kwanciyarta, yanajinta tayi addu’a tana tofawa a hankali, ta gyara kwanciya sosai, ba can nesa take dashi ba, haka kuma akwai tazara a tsakaninsu, sosai yaso yabar wannan tazarar kamar yanda Sa’adatu ta samar da ita, dan har juya kwanciya yayi.

Da ya sake juyowa ya kuma matsa yana rikota, sai muryar da take fada masa ba wani abu zaiyi marar kyau ba ta rinjayi muryar da take ta fada masa babu abinda yake sonyi din cikin yarjejeniyarsu, da muryar ta numfasa da nufin kira masa Aisha, sai Sa’adatu ta sauke numfashi tana gyara kwanciya a jikinshi da alamun baccin ya karayi mata dadi, tana saka muryar nan yi masa wani irin nisa.

A lokacin ne kuma yayi tsalle yana haura duka wasu katangu daya gina a tsakaninsu

Kaddara kuma tayi aikinta, ta bude musu shafin da babu wanda yasan da zaman shi a cikinsu.

<< Tsakaninmu 39Tsakaninmu 41 >>

1 thought on “Tsakaninmu 40”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×