Babu abinda take tunawa sai lokacin da take hangen Jabir daga nesa a gidanshi, lokacin da zata rantse ko wuka aka dora masa ba zai ko iya fadin baka bace ita ko fara, saboda yanda baya kallonta, gaisuwarta ma daga kasan makoshi yake amsawa. Shisa ta tattaro mazaje da yawa da taci karo dasu a litattafan Hausa, ta tsamo halaye daban-daban na kowanne a cikinsu, ta tattara ta hadawa Jabir din. Bayan kasancewar shi mai girman kai, yanda take tunani a lokacin, rashin magana, irin miskilancin nan da mazan novel suke dashi, miskilancin da za'ayi musu magana daya. . .
Nice