Skip to content
Part 46 of 66 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

A karo na farko, yake tunanin dalilin da yasa duk kalolin duniya, asibitoci da yawa suke zabar fente bangwayensu da farar kala, bawai bayason kalar bane ba, ai yana da kaya da yawa farare. Amman yau kalar ce yakejin akwai wani abu na rashin jin dadi a cikinta, kamar tana fassara wani abune da ba alkhairi ba, waiting area ne, ba zaice kuma ga yanda akayi yake zaune ba. Abubuwan ne sukazo suka wuce masa kamar a mafarki, daga durkushen da yake yanajin tashin hankalin da yake mamayarshi, wayarshi da take aljihu tayi haske, ya kuma rasa inda ya samu azancin ganin hasken wayar, ko dan duhun da yake dakin ne? Ya dai zaro wayar, ya kuma daga kiran ya kara a kunne, inda yaji muryar Mus’ab, bai tantance me yake cewa ba.

“Hamma…”

Ya kira, akwai wani abu a muryarshi da yasa Mus’ab din sanin ba lafiya ba

“Aisha…Hamma matata.”

Ya karasa numfashin shi na masa barazana

“Kana ina?”

Mus’ab din ya tambaya cike da natsuwa

“Daki…gida…ina gida…bata motsi Hamma, tana kwance…bansan me ya sameta ba.”

Cewar Jabir cikin rashin natsuwa

“Gani nan, ka zauna inda kake, tare da ita, ka zauna anan gani nan zuwa gidan.”

Bai kuwa yi cikakken minti ashirin ba ya karasa gidan Jabir din, ya kuma wuce falon zuwa dakunansu, yana kwankwasawa har sai da ya karasa dakin da yaji muryar Jabir yana cewa ya shiga, da fitilar wayarshi yayi amfani yana kunna switch din dakin, zuciyarshi ta buga, ta sake bugawa ganin Aishar kamar babu rai a jikinta, ga kuma jinin da yake kwance a dakin, jinin da yake yawata idanuwanshi a jikin Aishan yana neman daga inda yake fitowa saboda rigar jikinta duk ta baci dashi, iya ganinshi kuma baiga daga inda yake fitowa ba

“Daukota Jabir.”

Ya fadi muryarshi na rawa, sai dai kallonshi Jabir yakeyi kamar bai gane abinda ya fada ba

“Ka daukota mu tafi asibiti nace maka”

Yayi maganar cike da umarni wannan karin, sai lokacin kuma Jabir din yaji shi, duk da asibiti ne kalmar da tafi karasa masa. Haka ya dauki Aisha yana bin bayan Mus’ab har motarshi. Bai tsaya tambayar Jabir komai ba, da dai ya bude masa baya ya kwantar da Aisha, ya bita, saiya rufe murfin motar ya zagaya ya shiga. Asibitin dashi yake zuwa da iyalinshi, wani asibiti na wadanda sukaci suka tada kai a garin Kano, can ya nufa dasu, ganin yanda suka shiga da Aisha yasa akazo aka karbeta babu bata lokaci, Jabir dai yabisu, har dakin da aka shiga da ita, juyin duniya ya fita kuma yayi kamar bayajinsu. Saida Mus’ab ya karasa ya kamo hannunshi ya fito dashi, yazo ya zaunar dashi inda yake yanzun. Haka ya fita ya siyo ruwa mai sanyi ya kwance robar ya dawo yana mikawa Jabir, baiyi musu ba ya karba, yayi mamakin yawan wanda yasha, ya mikawa Mus’ab robar ruwan, ya karba ya rufe yana ajiyewa anan kasa. 

Sai dai shi bai zauna ba, tunani yakeyi, abinda ya faru, wanda kuma zai iya bashi amsar kuma alamunshi sun nuna baya cikin natsuwar da zaiyi hakan. Lokaci suka dauka, sosai, dan tun Mus’ab na tsaye harya zauna, kafin akazo aka kirasu ofishin likita, tare suka shiga, Jabir ya zauna a kujera, Mus’ab ya tsaya a gefenshi

“Ya kuke da marar lafiyar?”

Likitan ya tambaya

“Mijinta ne ni, wannan kuma Yayana ne.”

Daga ido likitan yayi yana kallon Mus’ab su duka kuma sunsan ma’anar kallon, asibiti da ka’idojin su

“Kayi magana kawai…”

Jabir ya bashi izini

“Mun samu mun tsayar da zubar jinin, ta bugune sosai akanta, ga kuma ciki da take dauke dashi…an yi sa’a babu abinda ya samu babyn, sai dai tana bukatar hutu saboda…”

Likitan bai karasa magana ba saboda dariyar da Jabir ya kwashe da ita, dariyar da shi kanshi baisan ta kwace masa ba. So yake ya gane tun daga yaushe ne yake ta yawo a mafarki? Tun tashin shi da safe daman bai tashi ba? Kawai bacci yakeyi yayi mafarkin ya tashi, harya karasa gidan Sa’adatu, daga can kuma ya dawo gidanshi ya samu Aisha yanda ya sameta. Ya jinjina kai yana sake kwashewa da dariya

“Mafarkina har dakai ya kwasomun Hamma, ko dan mun kwana biyu bamu hadu bane ba?”

Jabir ya fadi yana kallon Mus’ab, shikuma likitan su duka yake kallo, yana soma tantama akan hankalin Jabir din.

“Wai Tasha ce da ciki, koni kadai naji abinda ya fada”

Duk da shima Mus’ab din yana cikin rudani, saiya dafa kafadar Jabir din, cikin taushin murya yacewa likitan

“Marar lafiya da muka kawo fa, Aisha Lukman Arabi…ko dai anyi musayar file dinta dana wata?”

Cikin mamaki likitan yake kallonsu

“Wanne irin musaya? Ita dince nake magana akai…”

Mikewa tsaye Jabir yayi

“Kace tana da ciki, ko ba ciki kace ba?”

Likitan ya jinjina kanshi

“Daga awan jinin da mukayi matane ya nuna akwai ciki, shisa mukayi gaggawar yin scanning dan tabbatar da lafiyarshi, kuma scanning din ya nuna mana lafiyarshi kalau, cikinta sati takwas…”

Mus’ab din dai Jabir ya sake kallo, ba dariyar da yake bace kawai ta dauke, har jinin da yake kai kawo a jikinshi ji yakeyi ya tsaya, fuskarshi ma da tayi haske kamar takarda ta nuna haka, ta nuna jinin ya daina karasa mata, cikin wata irin murya ya furta

“Hamma son ganin dana har yakai kaddara tayimun wannan wasan?”

Kai Mus’ab yake girgiza masa, ba zaice ya tuna duka abinda akace akan matsalar Aisha da Jabir ta haihuwa ba, ya dai rike na Jabir din, ya kuma san ya rigada ya samu waraka daga tashi matsalar, amman idan ba ciwon mantuwa bane ya sameshi, Hajiya Hasina da bakinta take fada musu matsalar Aisha bamai magani bace ba, matsalace da zata kasance da ita har karshen rayuwarta, shisa ma ta damu a lokacin akan Jabir ya kara aure ko zai samu rabo, har suka dinga tausarta suna cewa ta saka masa ido aga gudun ruwanshi, da kanshi yake ce mata.

“Gashi ya kawo maganar auren da kanshi da lokaci yayi Hajja, haka kawai kika dinga damun kanki.”

Lokacin da maganar Sa’adatu ta taso, to yanzun kuma me likitan yake cewa, idan kuma abinda yake fadin ya sakashi a rudani, dole zai kidima Jabir, dole kuma ya fara tabbatar da babu kuskure a maganar likitan, kafin ya dora Jabir akan benen burin da idan maganar ta zamana ba gaskiya ba, babu wanda yake da tabbas din rauninkan da zai samu idan ya fado. Shisa ya kama hannun Jabir ya fitar dashi waje, ya kuma koma ya kalli likitan cikin idanuwa yana fadin

“Kayi hakuri, maganar da kayice duka ta sakamu a rudani, saboda ita wadda kake magana akai tana da condition din da likitoci suka tabbatar samun cikinta abune mai wahala”

Kallonshi likitan yake

“Haka sukace ba zai yiwu ba gabaki daya?”

Dan jim Mus’ab ya yi.

“Ko ma ca sukayi ba zai yiwu gabaki daya ba, ya yiwu, kaima musulmi ne kamarni, mun sani fadar likitoci baya nufin Allaah ba zaiyi ikonShi ba, balle kuma magana ta haihuwa.”

Numfashi Mus’ab yaja, duka maganganun likitan akan hanya suke, amman hakan baya nufin zasu kore shakkun da yake tare dashi.

“Ko dai za’a kara dubawa?”

Ran likitan ya soma baci.

“Ba’a son yawan scanning a satikan cikin, amman idan kuna shakkune sai a kara gwadawa a gabanku dan ku tabbatar.”

Kai Mus’ab ya daga masa, daya fito, inda yabar Jabir nan ya sameshi, yana tsaye yana jiran wani abinda zai gifta ya tasheshi daga mafarkin da yakeyi. Haka kuma yabi bayan Mus’ab da likitan har dakin da Aisha take, inda yasa wata Nurse ta kira masa wata mata itama sanye da farin kaya, Jabir bayajin abinda yake fada, saboda idanuwanshi na kafe akan Aisha da take a kwance, gefen kanta da wata babbar plaster, hannunta daure da karin ruwa, da alama batama san inda kanta yake ba, Mus’ab ne da likitan suka fice, suna barin wannan macen, Aisha da kuma Jabir, ita ta bashi kujera tace ya zauna, baiyi musu ba ya zauna. Ta kuma janyo wani abu mai yanayi da karamar Tv, kamar kuma na’ura mai kwakwalwa. Ta karasa wajen Aisha taja mayafin da take lullube dashi, sun sake mata riga zuwa ta asibiti, wani abu ta shafa akan cikinta, tana ma Jabir magana

“Ka saka ido sosai, kaga…kaga nan”

Ta nuna masa wani dan abu da yayi masa kama da wake

“Ga Babynka anan…”

Kurawa abin ido yayi baya ko kiftawa, sauran maganganunta na bacewa cikin rudani da shakkun da ya lullubeshi

“Baby…babyna”

Ya furta a hankali, matar tayi murmushi ganin yanayin fuskar Jabir din, kafin ta tashi, ta gogewa Aisha cikinta da tissue, taja mata rigar, ta kuma janye na’urar tana gungurata ta fice daga dakin. A hankali Jabir ya juya,.ya fuskanci gadon Aisha, daya ja kujera ya matsa ta bangaren da babu karin ruwa a hannunta, saiya kamo hannun, ya dora kanshi a gefen gadon yana wani irin sauke numfashi. Ashe akwai rabo a tsakaninshi da Aisha? Ashe garaje suka dingayi? Ashe da sun kara hakuri, hakurin da bai kai shekara ba, duka da basu wahala ba. Ba zaice ga iya lokacin daya dauka ba, haka bai gama tantance abinda yakeji ba, sun daiyi magana da Mus’ab, ba kuma zaice ga duka abinda sukace ba, a ciki dai ya tsinci cewa Mus’ab zaije gida, sai kuma ko za’a kawo abinci. 

Sai wajen sha daya saura na dare Mus’ab din ya koma, da tarkacen duk da yake tunanin zasu bukata, harda kayan canzawa ya tsaya ya siyawa Jabir, ya kuma hada musu da dardumar sallah. Sai kuma lokacin Jabir ya tuna baiyi isha’i ba, ya samu ya shiga bayin, ya dauro alwala bayan tafiyar Mus’ab. Yayi sallar, ya zuba ruwan tea a kofi, dan har lokacin Aisha bata motsa ba, duk da likita ya shigo ya dubata babu adadi, yana tabbatar masa da bacci takeyi, har ruwan ma sun cire mata. Yaji dadin shayin, yasha kayan kamshi, ga sikarin yayi masa dai-dai yanda yake so. Daya gama saiya koma kan kujerar, wannan karin yana kama hannun Aisha ta motsa, da sauri ya sake dumtsa hannun, sai gashi ta bude idanuwanta da suke cike da bacci har lokacin

“Hey…”

Ya furta muryarshi a shake

“Jay”

Ta amsa cike da rauni, wani rauni daya daki zuciyar shi, tunda ta bude idanuwanta tasan a asibiti take, ta kusan sati uku batajin dadin jikinta, sai dai rashin sanin takamaiman abinda yake damunta yasa bataje asibiti ba, to yau kuma tun safe data tashi, taje wajen aiki, ta kuma bada uzuri ta koma gida, ta kasa cin komai, ko tunanin abinci tayi sai taji zuciyarta ta tashi, ruwama saida ta zuba coke a ciki, data sha sai taji yayi mata dadi sosai da sosai. To lokacin data kira Jabir, tana zaune taji wani irin yanayi da bata tabajin shi ba tunda take, ga sanyin AC amman zufa ta dingayi, zuciyarta sai bugawa takeyi da sauri-sauri, ga amai, sai taga kamar ma dakin yana jujjuya mata, numfashin kirki ma yana neman gagararta, da bai daga ba, sai ta tashi da nufin zuwa bayi tayi aman, tasan ta sauka daga kan gado, ta kuma ji wani irin jiri ya kwasheta, daga nan kuma sai duhu, duhun da ta bace a cikinshi sai yanzun data bude idanuwanta

“I’m so so sorry…kin kirani…kin kirani…”

Hannunshi ta dumtsa, taso ta girgiza masa kai, amman yayi mata nauyi, kuma gefe nayi mata zugi sosai. Daman tasan laifin zai dauka ya dora akanshi

“Karka fara, ba laifinka bane ba, ba lallai kana tare da waya duk sanda zan kira ba, kuma haka kawai ai ba zakaki dagawa ba, musamman idan kasan ina bukatarka…”

Rashin gaskiya ne abinda ya lullube Jabir, wani irin rashin gaskiya da bai tabajin shi ba, saboda uzurin da Aisha take kokarin yi masa, tamayi masa, bayan babu wani dalili daya hanashi daukar wayar, tunda yana waya da ita a gidan Sa’adatu, asalima yana daukar wayar ya ambaci sunanta, Sa’adatu zata tashi ta bar masa wajen, sanda ya gama shi zaije ya sameta. Haka kawai yaki dagawa, ya gani, saiya ma saka wayar a silent.

“Kuma daman zanzo asibiti, banajin dadi a kwanakin nan.”

Cewar Aisha tana kallon Jabir da yanayin da yake lullube da fuskarshi, sai lokacin ya kalleta, sosai, kallo irin wanda ya kwana biyu baiyi mata shi ba, idanuwanta da sukayi zuru-zuru sunfi karfin ace cutar yau ce kawai, ita da bakinta tace ta kwana biyu batajin dadi, amman bai kula ba, a karo na farko a shekarun zamansu da ya kalleta a kwanakin amman kwata-kwata bai fahimci akwai wani abu na daban a tare da ita ba, saboda ba duka hankalinshi bane a kanta, saboda ya raba hankalin nashi da Sa’adatu.

“Aisha”

Ya furta, sunanta, cikakke, abinda ta manta rabon da taji shi a bakin Jabir din, abinda kuma yasa kirjinta bugawa haka kawai.

“Ciki gareki, we are going to have a baby, ni da ke.”

Wannan karin ta nemi nauyin da kanta yayi ta rasa, girgiza masa shi takeyi tunda ya fara magana.

“No…”

Ta iya fadi

“Yes…da gaske ne, naga babyn, dazun, naga babyn.”

Hawaye, hawaye wani na bin wani, kafin kuka ya kwace mata, kuka na samun abinda ta riga ta cire rai dashi, kuka na jinjinawa Kudira irin ta Ubangiji Mai zabar wanda Yaso badan yafi kowa ba, kuka na godiya, kuka na al’ajabi, kuka na abubuwa masu yawan gaske, kukan da yasa idanuwan Jabir suka fara yi masa zafi, sai dai shi ya manta yanda hawaye suke, yanzun da yake son tunawa kuma abin ya gagara

“Ina nan, tare dake, nayi miki wannan alkawarin, babu wani abu da zai sake daukemun hankali har in kasa daga wayarki…”

Cewar Jabir, kai ta daga masa kawai, kafin ya matsa sosai yana saka dayan hannunshi a cikinta, ta dora dayan nata akai, duk da hawayenta sunki daina zuba. Sai da Jabir ya tabbatar ta dan samu natsuwa tukunna ya fita ya kira likitan, ya kara dubata, yace babu wata matsala a yanzun, ta dai samu ta saka wani abu a cikinta. Shiya taimaka mata ta shiga bayi, tayi alwala, ta fito, akwai hijabi a kayan da Mus’ab yazo musu dashi, tayi sallar Magriba da isha’i, sai dai ruwan shayin ta kurba itama, Jabir daya matsa matane yasa ta dan sha fruit. Anan kan dardumar suka zauna, Jabir ya jingina bayanshi da bango, ita kuma tana tsakanin kafafuwanshi, nata bayan jingine da kirjinshi, ya zagayo hannuwanshi da tafukansu suke kwance a cikinta, lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciyar kamar shine yayi kukan ba ita ba. A jikinshi tayi bacci, bai kuma mayar da ita kan gadon ba, sai gyara mata kwanciya da yayi yana mikar da ita, rabin jikinta kuma akanshi. Wayarshi daya ajiye ya dauka, sakonni ne da yawa suka shigo masa, yawanci duk na yan gidansu ne da suke tambayar jikin Aisha.

Duka kuma suna fadin da safe zasu zo, sai dai babu wanda ya nuna yasan wani abu daya wuce cewar suna asibiti bata da lafiya, ya kuma san basu sani din ba, Mus’ab ba zai taba fada ba, ya bar musu wannan zabin ne, idan sunaso kowa ya sani a lokacin, ko kuma akasin hakan. Sai kuma guda daya daga Sa’adatu

“Babu abinda ya sameni, amman inajin wani rashin natsuwa tun fitarka. Fatan komai lafiya”

Baisan meyasa ya kalli Aisha ba a wannan lokacin, kallo na sosai. Kirjinshi ya dauki wani irin zafi da bai taba sanin akwaishi ba a duniya, lokacin daya fara danna wayar kuma, sai hawayen daya dauka ya manta dasu suka cika idanuwanshi, har baya ganin abinda yakeyi sosai, saiya ajiye wayar yana mayar da numfashi

Sai dai numfashin ne kawai ya koma

Hawayen sun zubo

Sirara

Masu zafin gaske…

<< Tsakaninmu 45Tsakaninmu 47 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 46”

  1. Ummulkhair Abdullah

    Toh Toh Masha Allah Tasha an yi baby, Allah ya sauke ki lafiya. Mallama Lubna muna nan tafe da ke muna jiran update. Dan Allah ayi mana nan kusa

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×