Skip to content
Part 51 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Idan zai zauna, ya kuma natsu, ko da bai iya kirga adadin hakurin daya taba bayarwa ba a rayuwarshi, to zai iya tuna da yawa a cikin lokuttan da hakan ta faru. Bawai yana daya daga cikin mutanen nan da bayar da hakuri yake yiwa wahala bane ba, in dai zakace yayi maka laifi bakinshi baya nauyi wajen baka hakuri, saboda bai dauki hakan a bakin komai ba, to laifukan nashi ne ne gabaki daya a idanuwan ‘yan uwanshi basa yin girman da har za’a gangaro bigiren da zai bada hakurin, mutanen da sukeyi masa uzuri kafin ma ya numfasa ya bude bakinshi. 

“Kinsan Jabir harda kuruciya da take damunshi.”

Shine maganar da yawa daga cikin manyan gidan idan yayi wani abin. Amman a satin nan, daga zuwanshi gaban Hajiya Hasina zuwa yau baisan adadin kalmomin,

“Kuyi hakuri.”

Daya furta ba, da duk wani yare kuwa da yakeji, ya furtasu ya sake maimaitawa, amman ya kasa ganin laifinshi yana raguwa a idanuwansu, a ciki kuwa harda kannenshi da duka baisan lokacin da sukayi sabo da Sa’adatu har haka ba. Duka yaushe ta shigo rayuwar tasu? Shi ya akayi ma bai lissafa da wadannan abubuwan bane tun daga farko? Watakila daya lissafa dasu daya takaita yanda zasu mu’amalanci juna su da Sa’adatun, balle har su dinga kallonshi cike da tuhuma, suna gaishe dashi daga kasan makoshi kamar wanda yayi musu wani babban laifi.

Saima da Babangida ya kirashi gidan saukar bakinshi, ya kumaje ya sameshi harda kawunansu guda uku, shi Babangidan cikon na hudu, kuma ko sallamar shi basu amsa ba suka fara binshi da kallon tuhuma, hakan yasa shi bai duba hasken yadin da yake jikinshi ba ya zauna a kasa kan kafet din dakin yana lankwashe kafafuwanshi, laifine yayi, ko basu fada masa ba ai yanajin girman laifin a jikinshi.

Yasan dai fada, irin wanda bai taba tunanin su duka sun iya ba, sunyi masa shi, har bai rike wani abin kirki daga cikin fadan ba banda

“Sai kace dai baka da manya da zaka yanke hukunci kai kadai, kasan girman saki kuwa Jabir?”

Duka a cikinsu kuma babu wanda ya taba aikata abinda ya aikata din, duk yanda suke kara kambaba lamarin, shine dai zai dorar akan girman da yake tattare da saki, ta kowacce siga akayi shi kuwa. Sai dai a karshen duka kalaman nasu da idanuwa da suka zuba masa, saiya cike shirun nasu da fadin

“Kuyi hakuri”

Babangida ne yayi karfin halin cewa

“Ayi hakuri dame? Lambar shi Kawun Sa’adatun zaka bamu ai muje mu same su mu basu hakuri, mutane masu karamci da sanin yakamata, sannan ka fadi abinda tayi maka in yaso musan yanda zamu tinkaresu a fara gyara al’amarin tunda baiyi nisa ba. “

Daya daga idanuwanshi ya sauke cikin na Babangida, yana zaton abinda yake cikinsu ya fara karanta shisa yayi saurin taryar shi da cewa

“Jabir…”

Cike da gargadin da Jabir din ya ture da

“Inda zan mayar da ita ba zan saketa ba, kuyi hakuri dan Allaah, suma ku basu hakuri, kuyi hakuri…”

Sai Kawunanshi suka saka salati, sai dai haka taron ya watse suna ganin wani taurin kai da basu taba hango Jabir din yana dashi ba, gashi yanda duk suka kadashi suka raya ya fadi abinda tayi masa, ko kuma ya hadasu sai yace suyi hakuri suyi musu fatan hakan ya zama shine alkhairinsu. Saida Babangida ya kira Hajja ne ranshi a bace take fada masa.

“Daman dan Aisha bata haihuwa shisa ya auro wannan din, to yanzun kuma ta samu ciki, ita waccen din dalilin da yasa ya aureta ya rushe.”

Aikuwa kamar ta tunzura Babangidan ne, ya dinga sababi, karshe har gida yaje ya samu Jabir din. Shi da kanshi Jabir ya tabbatar da ya bude bakinshi ya furta wani abu to abinda bai taba faruwa bane zai faru, Babangida zai wanke shi da mari a yanda yaga ranshi ya baci

“Ai daka fadamun dalilin kara auren naka tun daga farko, kaga da saimu zare hannayenmu, kaje kayi abinka kai kadai yanda inka saketa kamar yanda kayi ba zaka zubar mana da mutunci a idon mutane ba, ba za’ace munyi amfani da matsayinmu mun tauye yar kowa ba, amman ka kyauta…”

Bayan Babangidan ya tafi haka Jabir ya dauki waya ya tura masa da sakon ban hakuri, sai yayi reply da

“Nagode Jabir. Ka aikomun da lambar Wakilin Sa’adatu”

Lambar kawai ya aika masa batare daya kara da komai akai ba. Duk da fushin da suka dauka ya tabashi, babu wanda yafi dukanshi irin na Farhana.

“Nafi kowa zakalkalewa, nafi kowa korawa Hajja bayanin dalilan da zasu saka a barka ka auri Sa’adatu, ashe ni ka mayar sakarai, kai abinda yake zuciyarka daban.”

Kuma sai ya kasa yunkurin yi mata wani bayani, hakurin daya ba sauran ma bai wahalar da kanshi wajen bata ba, tunda yaga kamar hakurin kara tunzurasu yake, bayan shi kuma ai bashida wasu kalamai da zaiyi amfani dasu. Bayani suke so yayi musu, bayanin daya sha bamban da wanda Hajiya Hasina tayi musu, kuma idan ya bude bakinshi da wannan sigar tabbas abinda zai fito din irin wancen ne zai maimaita. Saboda haka lokaci zai basu, su huce da kansu. A ranar dai ya tsinci kanshi da lalubo lambar Abdallah da yake da ita, bayan sallama shima kalmomin biyu na ban hakuri ya dora akai ya tura masa. Tunda ai duka bai lissafa da wannan kalubalen ba, yanzun daya fado masa sai yayi abinda yake ganin shi ya kamata.

Aisha da ido take binshi, batayi masa kowacce irin tambaya ba. Tun daga yawan fitar shi, yawan wayarshi da ya karu da ‘yan uwanshi, suma manyan yanda suke ta zirga-zirgar zuwa gidansu tasan cewa wani abu yana faruwa, wani abu babba, wani abu kuma da bata taba ganin ya faru ba. Sai dai koma menene tsakanin Jabir dinne da ‘yan uwanshi. A fuska babu wanda ya nuna mata wani canji, yanda suka saba mu’amalantarta haka sukayi mata, ta kuma ji dadi ta wannan bangaren, ko babu komai ba zata zargi kanta da kasancewa cikin koma menene yake faruwa ba. Kawai batason kwantacciyar damuwar da take gani a cikin idanuwan Jabir din, gashi ya koma wani irin shiru-shiru, itace maganganunta suke takaitattu a lokutta da dama, amman Jabir mai son hira ne da mutanen da suke da muhimmanci a wajen shi.

Baya taba rasa wani abu da zasu tattauna akai, amman yanzun sai suyi awa daya a zaune, zai dai hadata da jikinshi, hannunshi kuma yana kan cikinta kamar a halin da yake ciki yana bukatar lallashi ne daga abinda yake cikin nata kawai, tunda wane irin kokari ne batayi ba na ganin ya dawo cikin walwalarshi amman ta kasa. Zuwa yanzun kuma data tabbatar akwai abinda yake faruwa tsakaninshi da ‘yan uwanshi sai ta karajin tsoron yi masa kowacce irin tambaya. Kuma da a daren suna kwance yace mata

“Akwai abinda yake faruwa, I don’t want to talk about it, dole zaki sani, amman ki kara mun hakuri zuwa lokacin da zan samu natsuwar fada miki.”

Bata furta komai ba, kawai kanta ta kara sakawa cikin kirjinshi tana rikeshi sosai kamar mai tsoron za’a kwace mata shi. Sai kuma ya bude abinda yayi saura a zuciyarshi da baya ciwo ya karbi lallashin da take taso tayi masa, sai dai yana lumshe idanuwanshi na Sa’adatu suka haska a cikin kanshi, cike taf da hawaye, suna kashe masa duk wani karsashi, haka ya zare jikinshi daga na Aisha bayan ya sumbaceta a kunci cike da ban hakuri, ya sauka daga kan gadon ya nufi bandaki. Ta bishi da kallo, hawayen da ba zatace ga dalilinsu ba suka zubo mata.

*****

Ba sanyi akeyi ba, duk kaunarta da fanka, da kuma dan sabon data fara da AC a zaman gidan Jabir, yau wani sanyi ne na daban yake ratsa ta duk juyin da zatayi, sanyin daya sakata kashe fankar dakin, ga mamakinta sai ta soma zufa. Dole ta tashi ta sake kunna fankar, dan ta fahimci bawai a wajen jikinta take jin sanyin ba, a cikin jikinta ne. Idan ma zata fadawa kanta gaskiya daga zuciyarta yake fitowa yana rarrabuwa zuwa sauran sassan jikinta. Duk inda ta juya akan katifar kuma sai taji kamar sanyin yana karuwa, ta kuma kasa danne zuciyarta da take ta fada mata babu inda zata samu maganin wannan sanyin sai tare da Jabir. Juye-juye take tayi ta kuma rasa inda zata saka ranta taji wani sauki, ga lokacin ma yaki yi mata sauri ko gari zai waye.

Har wani numfashin godiya ta dinga saukewa lokacin da ta fara juyo kiraye-kirayen sallar asuba, sai dai me? Ai wannan daren guda dayane, kuma kamar kofa ya bude mata, kofar kewar wani irin sabo da Jabir yayi mata. Sai ga dauriyar da take takamar tana da ita ta baje tabi iska, kudin da take lalubo sakon shigowarsu a cikin wayarta tana kallo tana fada ma kanta ko babu komai ai dai ta tsira dasu, harda karin gida na alfarma sun kasa tsaida hawayenta lokacin da suka fara zuba. Daman daga nesa ne take hango kudi, bakomai suke magani ba, farin cikin da zasu iya sakata yana da iyaka. 

Ashe akwai daren da zata gani da idan aka ajiye kudin da suke account din nata aka kuma ajiye Jabir a gefensu zata ruga da gudu ta rike Jabir saboda yana da abinda take bukata da kudin ba zasu iya yi mata shi ba. To me yasa ma? Akan wanne dalili zaiyi mata sabo da kanshi har haka bayan a yarjejeniyar da sukayi babu wannan a ciki.

“Kin tabbata? Ke da baki karanta takardar ba kika saka hannu? Ko kin manta?”

Wani sashi na zuciyarta ya tambaya, ta saka hannu ta goge hawayen da basu daina zubo mata ba. Sai gata cikin ‘yan kwanaki kamar wadda tayi kashin fitowar hakora, tayi duhu, tayi zuru-zuru, idanuwanta sun kankance sunyi ja alamar bayan kuka bata samun wadataccen bacci, ga ciwon kai da babu kalar maganin da ba’a siyo mata a chemist ba amman dashi take wuni ta kuma kwana dashi

“Sa’adatu ya kike so inyi? Ina kike so in saka raina idan kin daga hankalinki haka? So kike wani ciwon yazo ya shigeki? Ina so in hada idanuwa da Amma cikin salama, amman inaji kamar hakan ba mai yiwu bane saboda na gaza wajen kula dake”

Cewar Abdallah cikin wata murya da ta saka hawaye suka zubo mata. Sai dai ya zatayi? Itama tagaji da halin da take ciki, so takeyi ta kwantar da hankalinta, amman idan batasan ya akayi yake kara tashi ba ta ina zata fara sanin yanda zata lallaba shi ya kwanta? Tana jin Abdallah ya fice daga dakin, bata iya ko daga kai ta kalli bayanshi ba. Ko Fa’iza da take masa addu’ar dawowa lafiya bai iya cewa komai ba ya fice daga gidan. Kawu shiya fara kiranshi ya fada masa wakilan Jabir din sunje sun same shi sunata bayar da hakuri

“Sai dai muyi musu addu’a Abdallah, idan akwai alkhairi a zaman nasu Allaah Ya dai-dai tsakaninsu, dan mutanen nan baka ga yanayinsu ba wallahi, su kansu abin baiyi musu dadi ba, cike suke da kunya saboda basu zo da maganar kome ba sai ban hakuri.”

Kai Abdallah ya jinjina dan sauran fatanshi yana bajewa. Yana kuma gasgata maganar Sa’adatu da take cewa saboda matarshi bata haihu bane ba, daman ai yasan ba zatayi masa karya ba. Ko randa ya koma gidan ya samu Jabir ya aiko da kayayyakin nan ranshi kara baci yayi fiye da wanda yake ciki, ya dinga jujjuya lambar Jabir din yana jin kamar ya kirashi yace yazo ya kwashe kayanshi. Su talakawa ne, akwai ranakun da sai anyi tunani an kuma lissafa dan kudin da ake dashi a hannu kafin asan dabarar da za’ayi a cikin gidan, sai dai basu taba kwana da yunwa ba, koma menene zasu samu su saka a cikinsu cike da godiya da wadatar zuci. A cikin wannan halin ya turo da wakilan shi yace Sa’adatun yake son aure, ya korota shine yake tunanin zaiyi amfani da kudinshi ya wanke laifin da yayi?

Sai kuma yaga sakon Jabir din, ya karanta ya sake karantawa, sau nawa yaga Jabir? A wannan ganin da yayi masa, kwarjinin Jabir din da shekarun da yasan ya bashi yasa duk haduwar da zasuyi yake kokarin bude bakinshi sai Jabir din ya rigashi gaishe dashi, dan ranar farko da hakan ya faru ba zai manta ba, duk girman jikinshi da ake magana akai sai yaji shi dan karami a gaban Jabir, saboda tazarar da take tsakanin matsayinsu mai girma ce, ko da aikin ban ruwan shukokin gidanshi Jabir din zai dauki Abdallah, yasan sai dai tsananin rabo, in ba hanya gare shi ba, wani ya hada shi da wani daya san Jabir din idan yasa a nemo masa.

Amman haka ya gaishe dashi kamar shi din yana da wani muhimmanci ko girman daya cancanci Jabir din yayi masa haka.

Kuma duk wata haduwa da sukayi, Jabir ne yake saurin gaishe dashi, sai daya yazo gida yake fadawa Fa’iza ashe shine yayiwa Jabir bahaguwar fahimta, amman kudi da matsayinshi abune da bai nuna sun dame shi ba, shi din mutum ne daya fito daga babban gida, ya kuma san darajar dan adam, shisa hankalin shi ya kwanta, ya saki jikinshi da cewar Sa’adatu tana hannu me kyau. Sakon Jabir din sai yasa shi jin wannan rashin kyautawar ta wancen lokacin na neman dawo masa, kamar duk da Jabir baiyi masa wani karin bayani ba ya kamata koya ne yayi masa uzuri, koyane ya kyautata masa zato

“Watakila kaddarar Sa’adatun kenan, lissafin mazan da zata aura a rayuwarta ne bai gama cika ba. Kasan kowacce mace da tata kaddarar, idan kuma maza goma ne a cikin kaddararka duk rintsi duk yanda za’a juya saika auri kowanne a cikinsu”

Haka Amira tace masa, to ko dai kaddarar Sa’adatun ce ta gifta har takan Jabir din, to amman ya zaiyi da Sa’adatu? Idan banda haushin Jabir me ya rage masa? Wa zai dorawa laifin idan ya karbi wannan hakurin da Jabir yayi masa, hakan na nufin zai fuskanci cewa da gaske kaddarar Sa’adatun ce, kaddarar da bashida yanda zaiyi ya tare mata ita. Yanzun kuma da yake ganin yanda take ta karewa a tsaye sai suke ramewar tare, tunda ko abinci yana kaiwa bakinshi ne saboda Fa’iza, saboda itama yana ganin yanda ta damu da halin da Sa’adatun take ciki, ba zaiso ya kara mata da tashi damuwar ba. Sai kawai yayi abinda shiya kamata ace tun farko yayi din.

“Allaah Ka fini son Sa’adatu, Allaah Ka duba maraicinta, Allaah Ka zaba mata abinda yake alkhairi a rayuwarta.”

Saiya rufe idanuwanshi ya jero Istigfar, ya kuma hada da salatin Annabi S.A.W, sai yaji wata iska ta daki fuskar, iska mai sanyin gaske, dan saida ya bude idanuwanshi, yana ganin kamar kwan lantarkin daya haske unguwar tasu ya kara haske fiye da fitowarshi, abubuwan da duk suka dishe masa sun kara kala, launin komai ya fito tar, daya daga kanshi sama ma, sai yayi tozali da wani tauraro mai tsananin haske, kamar ya haska dinne a dai-dai wannan lokacin yana so yayi masa bushara da addu’ar shi ta karbu. Sai fuskar Abida ta gilma masa.

“Amma sai murmushi kikeyi kamar baki da wata damuwa a duniyar nan.”

Ya taba ce mata a wani yammaci, sai tayi dariya.

“Dan Adam kuwa ai baya rasa damuwa Abdallah. Sai dai ni da nake da Allaah, ai damuwata takaitacciya ce, kaga bai kamata ta hanani nishadi ba.”

Addu’ar neman gafara da Rahmar Allaah yayi musu saiya koma cikin gidan yana shiga daki da sallama ya samu Fa’iza zaune a bakin gado.

“Matar Abdallah”

Ya kira cikin sigar tsokana, ta kuma biyashi da kyakkyawan murmushi, saiya mika mata hannunshi, ta kuwa rike ya karasa ya zauna a gefenta.

“Komai zaiyi dai-dai In Shaa Allaah.”

Ta jinjina masa kai kamar ta jima da sanin hakan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 50Tsakaninmu 52 >>

1 thought on “Tsakaninmu 51”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×