Cikin Aisha daya fito yanzun da yake da watanni biyar ne abinda yake gani da yake bashi wani karfin gwiwa duk safiya. Sai kuma fushin dasu Farhana suka dauka dashi da baiyi nisa ba duk suka sauko, musamman yanzun da hankalin kowa yake kan Aisha din da kuma abinda zata haifa. Amman a lissafe yake da kwanakin da suketa zuwa suna wucewa. A lokacin da Sa'adatu take shan maganin da zai kara musu chances din haihuwa, lokacin ne ya fara kiyaye lokuttan al'adarta, kwanakin da takeyi da kuma ranar da take gamawa. Yanzun lissafin sai yafi warware masa. . .