Skip to content
Part 53 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Cikin Aisha daya fito yanzun da yake da watanni biyar ne abinda yake gani da yake bashi wani karfin gwiwa duk safiya. Sai kuma fushin dasu Farhana suka dauka dashi da baiyi nisa ba duk suka sauko, musamman yanzun da hankalin kowa yake kan Aisha din da kuma abinda zata haifa. Amman a lissafe yake da kwanakin da suketa zuwa suna wucewa. A lokacin da Sa’adatu take shan maganin da zai kara musu chances din haihuwa, lokacin ne ya fara kiyaye lokuttan al’adarta, kwanakin da takeyi da kuma ranar da take gamawa. Yanzun lissafin sai yafi warware masa dalla-dallah, idanuwanshi akan kalanda tayi ta farko, ta biyu, sai dai ana gobe ta ukun da zatayi, kuma ta karshe da zata tabbatar da karewar zamansu da zazzabi ya kwana, ya tashi dashi

“Jikinka da zafi sosai, dan Allaah ka taimakamun ko paracetamol ne kasha”

Cewar Aisha, haka ta dinga jera masa godiya daya karba ya sha harda tukuicin sumba ya samu, tanata faman lallabashi, so yakeyi yace mata babu abinda paracetamol zaiyi masa, zazzabinshi baya bukatar kowanne irin magani. Da daddare ta hada masa shayi irin yanda yake sonshi saboda yaki cin wani abin kirki, yana wasa da cokalin a cikin kofin yace mata

“Aisha…”

Saida zuciyarta ta buga, saboda sau nawa Jabir din ya taba kiran cikakken sunanta haka?

“Na saki Sa’adatu…”

Faduwar gaban datayi lokacin da taji a bakin yan gidansu ashe bakomai bace ba, idan ya bude bakinshi ya fada mata zata ninku, ranar a tsorace tayi bacci, bama zatace ga tunanin da ta dingayi ba, duk da basuyi tsammanin zataji maganar ba, dan ta shiga bandaki ne sukuma suka shigo dakin suna magana, kuma taji sun dora da

“Haka fa ya cewa Hajja daman dan Anty Aisha bata haihuwa ne, kuma ta samu ciki shisa ya saki Anty Sa’adatun”

Yanda kafafuwanta suka dinga rawa yasa ta nemi waje ta zauna a bayin, har saida taji fitarsu kafin ta iya fitowa itama, kuma kowa saida ya gane wani abu yana damunta, sai tace jiri take gani, nan duk suka tashi hankalinsu, aka kira Jabir da bai yarda da yanda tace masa data kwanta shikenan ba saida suka biya asibiti aka tabbatar masa babu wata matsala tukunna. Su duka sunsan auren yarjejeniya daman ai, kamar yanda Jabir din ya fadawa Hajiya Hasina, amman kuma sai ta tsinci kanta da shiga wani irin yanayi mai wahalar fassarawa, kenan sunata kallon tayi sanadin rabashi da Sa’adatu, abinda yake damunshi kenan daya kasa fada mata?

Rabuwa da Sa’adatu ce ta sakashi wannan jinyar? Wannan damuwar? Kawai sai hawaye ya fara saukar mata, to da take zaune a gefe tabarshi da Sa’adatun sabo sukayi har haka? Sai ta mike zaune, ta goge hawayenta, ta kuma fadawa kanta itace a zuciyar Jabir, itace mace ta farko kuma babu wadda zata shigo rayuwar shi ta samu wannan matsayin, meye zai kaita ma kishi da Sa’adatu, tunda ance ya saketa. Daman saboda ita ya aurota, auren da basu hango abubuwan da zasu iya biyowa bayanshi ba, basu ga komai ba sai dan da Sa’adatu zata haifa ta basu. Saita warware, dan laulayin ma duk taji ya saketa, bata bukatar ko kula da kanta, hankalinta kacokan ta mayar kan Jabir da kulawa dashi, so takeyi koma menene ta goge masa shi

“Na saketa, kuma gobe zatayi period dinta na uku”

Maganar ta kwace masa batare daya taunata ba balle yayi tunanin girman da zatayiwa Aisha da take zaune tana jin kamar ya kwada mata mari. Da marinta dinma yayi ai zafin iya fuskarta zai tsaya, ko zai kai zuciyarta ma Jabir ne, Jabir dinta, abinda ba zata yafe masa ba kadan ne. Sai dai a ciki akwai wannan maganar daya furta mata yanzun kuwa? A lissafe yake da kwanakin al’adar wata macen da ba ita ba yau? Jabir fa, Jabir dinta

“Nagansu mana, suna da kyau. Ba zan hana idanuwana ganin wasu mata ba ko kyan da suke dashi, amman ni bai dameni ba Tasha, kafin ke bansan kalar matar da nake so ba, kawai kowacce mace, macece a idona, wata baka, wata fara, wata mai kyau, wata marar kyau, dogaye, gajeru, sirara, masu jiki, ina ganin duk bambancin nan, amman bani da wani zabi, ban taba jin ni sai fara ba ko baka, ina ganinki zuciya tace mun kece”

To yau kam ba ita bace ita kadai, ya dauko Sa’adatu ya ajiye a gefenta, idanuwanta takejin suna mata yaji-yaji kamar ta shafa musu barkono, tabbas kowacce mace tana bukatar ta dinga saka kanta addu’a a kowacce sallah, ta roki Allaah daya rage mata zafin kishi, ko da kuwa bata da kaddarar zama da kishiya, a yau Aisha taji kowacce mace na bukatar wannan addu’ar, harda wanda ma basu kai da yin aure ba, saboda wani abu da taji ya taso yana neman hana mata numfashi yanda ya kamata.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Ta shiga jerawa a cikin zuciyarta kafin ta dan kwato natsuwa, ta kalli Jabir, duk hasken fatar nan na dishewa a idanuwanta, yau yayi mata bakikirin, musamman daya dago ya sauke mata idanuwanshi da suke dauke da damuwar yanda daga gobe auren daya tsinke da kanshi zai karasa karewa, ko da zai sake dawo da ita to sai dai ya shiga jerin zawarawa. Wani abu da duk halin da take ciki sai ga dariya tana neman kwace mata, saboda tasan halin bakin kishi irin na Jabir, ace shine yake karakaina akan mace a tsakanin wasu mazan? 

“Ka dawo da ita mana.”

Maganar ta kubce mata kamar tarko, idanuwanta har lokacin kafe akan Jabir tana jira taga ya zaiyi da maganarta, sai ya girgiza kanshi a hankali

“Me yasa zan saketa idan nasan zan dawo da ita?”

Wannan karin a tsanake taja numfashi ya kuma wuce, ta sake jan wani, nauyin da kirjinta yayi mata yana dagawa. Da Jabir ya mike ya bar falon batayi yunkurin binshi ba. Sai kuma takejin ta cika babbar makaryaciya, randa ta dawo asibiti meye bata fada ba, tunda ta samu ciki ai ta gama samun komai, Sa’adatu ba zata dameta ba balle ma ta zame mata wani abin tashin hankali, ashe duk karyane. Bata ga Jabir din ya nuna kulawarshi akan Sa’adatu bane ba shisa take ta wasu maganganu, gashi magana daya ta birkita mata lissafinta gabaki dayanshi. Saita tashi taje ta dauko robar ice cream da cokali ta dawo ta bude, gara ma tasha abinda zai kara sanyaya mata zuciyarta.

*****

Kitso Fa’iza tace mata zataje, amman data dawo sai gata tana mikawa Sa’adatu wasu abu a guda biyu a cikin leda, Sa’adatun ta karba tana latsawa ko zata gane menene, ta daiji wani abu kamar tsinke a ciki

“Acan gidan kitson na samu yaro na bashi ya siyo, nace ya siyo guda biyu, tashi zaki, bari in samo miki roba sai kiyi fitsari a ciki, bada yawa ba ki fito kizo mu gwada”

Cike da rashin fahimta Sa’adatu take kallonta

“Abin gwajin cikine, kawai so nakeyi in tabbatar.”

Dan sosai idanuwanta suke kan Sa’adatun, ko da ma Abdallah bai roki ta tayashi kula da ita ba. Ba laulayi takeyi ba, kuma batayi wannan hasken na masu ciki ba, ramar da tayi dai ta cike, saboda abinci takeci sosai, nan da nan taji yunwa har tana cewa Fa’iza.

“Nifa matar Yaya inajin tsutsar ciki ce ta fitomun, baki ga yanda nake cin abinci bane wai? Kinsan Allaah jiya cikin dare na tashi kamar anyi mun sata, bakiji motsina a kitchen ba, na dauko flask nazo na hada shayi nasha, jikina har rawa yakeyi.”

Fa’izar sai tayi mata dariya tana fadin

“Ai in dai tsutsar cikin da nake hasashe ce to Allaah Ya tabbatar da ita.”

Kai kawai Sa’adatu ta girgiza, Fa’iza da maganganunta da inka tsaya zasu sakaka tunanin ba gaira babu dalili, wacce tsutsar ciki ce ake fatan ta tabbata? Lokaci zata samu ta shirya taje asibiti, saima tayi musu zancen period dinta da yake mata wasa. Hakan ta tsara a satin daya fita, sai yau kuma Fa’iza zata zo mata da zancen da taji yayi mata dirar mikiya. Wanne irin tsinken  gwajin ciki kuma.

“Ciki fa? Wanne irin ciki?”

Harararta Fa’iza tayi

“Koma wanne irine ba saiki tashi ba, ai zaki ganshi.”

Kai Sa’adatu take girgiza mata

“Ina can nayi period dina, kuma dana dawo nan ma nayi…wanne irin ciki.”

Sai dai tana jin yanda muryarta take rawa saboda yanayin da take jin duka jikinta ya dauka dashi. Haka Fa’iza ta sakata a gaba, kusan har kofar bandakin ta rakata, sai dai ta nemi fitsarin ta rasa, daga cikin bandakin tace ma Fa’iza.

“Na kasa, fitsarin yaki zuwa.”

Saboda da gaske komai ma ya tsaya mata, ciki fa? Cikin Jabir

“Ki kwantar da hankalinki, baki natsu ba ya za’ayi yazo.”

Kokarin natsuwar tayi, amman ta kusan mintina goma kafin tayi shi dan kadan ta fito tana ba Fa’iza robar, duk ta kasa natsuwa, haka Fa’iza ta ajiye robar a kasa, ta bude leda daya ta fito da abin, da ta tsoma shi sai Sa’adatu takejin kamar cikin zuciyarta ta tsoma, haka suka zuba masa ido a tare, sai ga layuka biyu sun fito tar

“Alhamdulillah… Inalillahi…. Alhamdulillah”

Fa’iza take fadi bakinta yaqi rufuwa, Sa’adatu kuwa kallonta kawai takeyi

“Ciki gareki, Alhamdulillah… Sa’adatu ciki gareki”

Sai taji wani jiri yana neman tikata da kasa, ta lalubi bango ta dafa, ta kuma yi amfani dashi wajen taimakawa kanta ta samu dai-daiton takawa ta koma kan tabarmar data tashi ta zauna, sai dai a zaunen ma komai juya mata yakeyi. Ciki gareta, ciki gareta, ciki gareta. Shine abinda yake ta amsa kuwwa cikin kanta yana karasawa duk wata gaba ta jikinta, batace ma Jabir ya barta ba? Ba saida ta roke shi ba itama zata samu cikin yaki yarda, to gashi nan Fa’iza tace ciki gareta. Tana jin Fa’iza din na waya tana cewa Abdallah zasuje wani karamin asibiti da yake nan kasan unguwar tasu, na kudine ma wani Unicare. Sauran kalaman bakomai bane yake karasawa kunnen Sa’adatu, har Fa’iza ta gama shiri ta goya danta, tace mata taje ta dauko hijabinta, na nan kan igiya da tayi sallah dashi ta dauka ta saka.

Suka fita, Fa’iza ta rufe gidan. Basu wani sha wahalar samun napep din data sauke su Unicare ba, kuma da yake akwai kudi a hannunsu suka bude file, bama layi ke akwai ba, tare suka shiga wajen ganin likitan, dan Sa’adatu ta zamewa Fa’iza kamar wata karamar yarinya, itace ma take ma likita bayanin cewar suna so su tabbatar da cikin ne a rubuce a takarda. Kuma Sa’adatu da batasan takaimai man lissafin cikin bane yasa likitan ya basu harda scanning. Lokacin kuma da ta fito daga wajen scanning din tana da yakinin hoton abinda yake cikinta da yaketa motsi da aka nuna mata na daya daga cikin abinda zai zauna tare da ita har karshen numfashinta.

Ta kasan hijabinta kuwa hannunta nakan cikin, babu abinda yake mata yawo sai Abida, Abida da kuma irin kaunar da takeyi mata. Bawai auna abinda takeji da kaunar da takeyiwa Abida take sonyi ba, girman kaunar da take tsakanin iyaye da ‘ya’yansu ce take jinjinawa, bugun zuciyarta na karuwa dan har yanzun abin yaki ya zauna mata yanda ya kamata. Ciki fa, cikin Jabir

“Idan lissafin scanning din nan yayi dai-dai kina cikin wata na hudu yanzun, kinsan idan ya fara girma lissafin bai cika zuwa dai-dai ba akace”

Fa’iza da murnarta taki boyuwa ta fadi cike da zumudi. Sa’adatu bata iya furta komai ba, batama dauka zata fahimci wani abu banda bugun zuciyarta ba. Sai kuma tunaninta ya fara yawo, duka matan da suke rayuwarta, matan data sani da sukayi aure, suka samu ciki har suka haihuwa, laulayi sukanyi mai zafi, sai dai na wannan yafi na wannan. Kuma idan tana zaune a cikinsu, zance ya kawo zance har aka sakko haihuwa a ciki, tofa idan kowacce a cikinsu zata bude baki irin wahalar data sha zata bayar, ko bambancin wahalar wani cikin da wani, gajeriya da doguwar nakuda, a cikin labaransu duka ba zata dorar da komai ba banda wahalhalun da suke cikin ciki da haihuwa.

Ta kuma shaida akan irin wadda Fa’iza tasha da har saida ta kasa haihuwa da kanta. Ya akayi nata yazo da bambanci? Ko dan ba abinda ya kamata ace tayi mamaki akai bane ba, ita da auren ma kacokan ba irin na sauran mutane bane ba, me yasa zata tsammaci cikin ma yazo mata kamar na kowa? Wasu magunguna da aka rubuta mata da masu ciki kanyi amfani dasune suka tsaya suka siya. Tukunna suka fito daga asibitin, har suka tare adaidaita sahu, suka kuma karasa gida Fa’iza batayi shiru ba, maganganunta kuma duka suna nuna yanda take cikin tsananin farin ciki da labarin tabbatuwar cikin jikin Sa’adatun ne. Ita dai daki ta shige ta kwanta, kuma kamar wayarta hakan take jira sai tayi kara alamar shigowar sako.

Hannu ta mika tana janyo wayar, akwai matar data siyi kunun aya, kusan ma tana daya daga cikin masu yi mata ciniki akai-akai, tace mata zata turo mata lambar wanda zata aiko ya karba yanda zata san shine idan ya kirata, wanda ta saba aikowa din baya nan, a tunaninta matarce ta turo da lambar tunda tanata jira daman, ganin sunan Jabir yasa zuciyarta bugawa kamar tana neman hanyar fitowa daga kirjinta.

“Angama miki komai na makaranta, zan bayar a kawo miki abubuwan da zaki bukata zuwa gobe dan kun kusa fara lectures”

Ta karanta sakon tana sake maimaitawa fiye da sau hudu, kamar tana neman wani abu a ciki, kuma rashin ganin abin yasata jin wani iri, ta latsa ta sakama wayar mukulli ta kifeta. Cikinta ta sake shafawa, shin da Jabir yasan akwai shi zata samu abinda take nema a cikin sakonnin shi kuwa? Zaima yi murna? Tunda ai yana neman cikin a tare da itane saboda Aisha bata samu ba, yanzun kuma ta samu. Idan yace ma baya bukatar cikin fa? Wata murya ta tambaya tana kara mata bugun zuciya, a gefen zuciyar kuma wani abu na rashin jin dadi yana lullubeta ya sauya mata yanayinta gabaki daya. Haka ta karasa ranar zuwa dare cikin rashin jin dadi, saboda tambayar ta bude mata kofar abubuwa da dama, ciki harda sakin da yake tsakaninsu da Jabir da kuma canzawar iddarta a yanzun da take dauke da ciki.

Saima da Abdallah ya dawo, ta kuma ji yana tambayar Fa’iza me akace yana damunta, tunda taji shigowarshi, taja bargo ta rufe jikinta tayi luf kamar mai bacci, sai dai bataji amsar da Fa’iza ta bashi ba, amman zata rantse taji yanda shirun gidan gabaki daya ya canja, wani canji daya sakata fahimtar Fa’iza ta fada masa maganar cikin da take dashi, kuma hasashenta ya fada mata gaskiya

“Cikine da ita har wata hudu…”

Wani fatane da Abdallah ya dauka ya mutu a zuciyarshi yaji ya yunkuro yayo sama kamar dama can wasu abubuwan ne suka danne shi, yanzun kuma labarin cikin Sa’adatu ya daga wannan abubuwan

“Ikon Allaah”

Ya furta cikin zuciyarshi, haka suka kwanta yana kara juya girman Ikon Allaah. Sai dai da safe ya kira Amira ya fada mata yana kuma neman shawararta kan abinda ya kamata yayi, shin zaije ya sanar dasu Anty Talatu ne sai a kira Jabir din a fada masa ko ya take ganin za’ayi

“Kaga wakilan shi da sukazo hakuri suka bayar Abdallah, alamun da suka nuna shi Jabir din bai nemi yana son ayi sulhu ba, bashi da niyyar mayar da ita, idan aka fadawa Anty Talatu, Kawu bawai zai nemi Jabir bane ba, wakilanshi zaice a nema a fadawa. Bana son abinda zai zamana kamar mun nace ne akan zaman nasu, kar suga kamar muna son amfani da maganar cikin nata ta koma gidanshi…”

Kai Abdallah yake jinjinawa tunda ta fara magana

“Har raina babu abinda nake so daya wuce Sa’adatu ta koma dakin mijinta, amman son da nake mata, da son ganin tana da darajar da duk muke da ita a idanuwan mazajenmu ya danne komai, ka kira Jabir din ka fada masa da kanka, danya sani, inyaso koma menene saiya rage tsakaninshi da ita Sa’adatun, mu a gefe sai mu cigaba da yi mata addu’ar abinda zaifi zame mata alkhairi”

Shawarar Amirar kuma saita zauna masa. Sai dai daya dauki waya ya lalubo lambar Jabir saiya tsinci kanshi da kasa kira, to me zaice masa inya daga, Sa’adatu na da ciki? Maganar ma tayi masa wani girma tun kafin ya kira, yana kuma tabbatar da koma meya faru, to bai dishe wannan kunyar ta surukantaka tsakanin shi da Jabir ba. Daga karshe saiya zabi ya tura ma Jabir din sako kawai, sakon daya rubuta yana gogewa fiye da sau goma cikin rasa yanda zai dai-daita kalaman suyi masa yanda yake so. Bayan sallama saiya dora da

“Ya hidindimu. Allaah Yayi jagora. Sa’adatu sunje asibiti yau, sakamakon ya nuna tana da ciki”

Ya karanta ya sake karantawa, har yanzun sakon baiyi masa yanda yake so ba. Sai dai kuma yanda duk zai juya kalmomin karshe dai sakon da zai isar ai akan maganar ciki ne, ita kuma babu wata kwaskwarima da za’a iya yi mata, haka ya tura sakon yana ganin tafiyarshi, tukunna ya mayar da wayar a aljihunshi yana jin tayi masa nauyi a ciki kamar ya saka dutse

Yayi nashi bangaren

Addu’a Amira tace su cigaba dayi

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 52Tsakaninmu 54 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×