Skip to content
Part 52 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

To Juwairiyyah suleiman. Allaah Ya aminta dake Ya soki ninkin soyayyar da kikemun da kuma litattafaina. Thank you

*****

“Ba yau bane na farko Sa’adatu, na sha fitowa injiyo sheshekar kukanki, na kyaleki ne saboda inga iya kwanakin da zaki diba kunshe a daki, kwance akan katifa duk dare hawayenki na jika pillow kamar baki da wajen daya kamata ace kina zubar dasu”

Cike da rudani ta kalli Fa’iza

“Kin saki Allaah yaushe kike tunanin zaki samu natsuwa? Ko acan gidan Jabir dinma idan kika ci kika koshi kikayi farilla saiki bi gado ko?”

Maganar karshe ta daki Sa’adatu, saboda gaskiyar da take cikin maganganun, dan tun bayan aurenta da Jabir, tana sallolinta na farilla, kowanne kuma akan lokaci, sannan tanayin azkar dinta na bayan sallah, amman bayan wannan babu kari babu dadi, asalima akwai ibadu da yawa da ta saki, yanzun kuma tama nemi dalilin yin hakan ta rasa.

“Zakiyi zamanki cikin aminci idan kika kiyaye farillan da suke kanki, amman ke baki da bukatu ne? Duniyar ma kullum muka samu kara nema mukeyi balle kuma lahira.

Maimakon ki kwanta kina jika pillow dinki da hawaye, meyasa ba zaki jika dardumarki ba? A yayin sujjada?”

Saita sunkuyar da kanta, wani yanayi mai nauyi yana saukar mata

“Ki rike HasbiyAllahu laa ilaaha illa huwa alayhi tawakkaltu wa huwa Rabbul arshil adheem, kima yi bakwai da safe, bakwai da yamma kiga yanda al’amuranki zasu canza.”

Bakwai Fa’iza tace, sai dai a daren bayan ta gabatar da Nafila, tayi kukanta iya yinta, tayi salatin, tayi istigfar sai tayi guda dubu, ta sakeyin istigfar ta rufe da salati, tasan Ubangiji yaga zuciyarta, Ya san damuwarta, kafin ta iya bude baki ta jerosu zata cigaba da yin hakan da hawayenta. Data kwanta ma addu’ar ce a bakinta, sai ga bacci mai nauyi ya dauketa, batama tashi da wannan matsanancin ciwon kan ba. Bayan sallar asuba ma dubun ta karanta, kuma da kwanaki suka fara tafiya sai gashi sai ta fara jin nauyin da kirjinta yayi ya fara dagawa, da yake ta kasance cikin mutane masu sa’a, Ubangiji Ya dubeta da wuri, duk da jinkirin da addu’ar wasu takeyi baya nufin Allaah Ya manta dasu, gwajin da akeyiwa hakurinsu ne bai gama yankewa ba.

Sai ga walwalarta ta fara dawowa, har su zauna suyi hira kamar yanda suka saba, wani zubin sai sukai sha dayan dare suna hira ita da Fa’iza da Abdallah, ta tabbata dariyarsu na damun makota a wasu dararen. Kuma shaf ta daina lissafin kwanakin da suke ta zuwa suna wucewa, kwanakin da suke kara tabbatar da nisan da Jabir yake kara yi mata, yar nutsuwar da take samu baya nufin kewarshi nata nukurkusarta. Wata ranar alhamis saiga Badr ta kirata, da murmushi ta daga tana fadin,

“Anty Badr”

Ta dayan bangaren Badr tace

“Ba wani Anty, lokaci na baki ki dan samu natsuwa, inata jira inga kiranki amman shiru…kina ina yanzun?”

Kwatance tayiwa Badr din, da yake babu wanda zata aika ya taho da ita daga bakin hanya, saita saka hijabinta taje, ta shigo motar Badr din har kofar gidansu. A mutunce suka gaisa da Fa’iza, suka shiga dakin Sa’adatun, ta fito taje shago da kanta ta siyo mata ruwan roba da lemo kala biyu, sosai suka gaisa. Duk yanda Badr ta hasaso kankanta gidansu Sa’adatu bayan sanin cewa har aiki tayi a gidansu Jabir din kafin aurensu bata zata karami bane har haka, ashe wasa takeyi da take ganin bata taso cikin wadata ba, saboda tana zagaye da attajirai shisa. Wata mata data siyi zobo da kunun aya a wajen Sa’adatu ce ta kirata, tana ce mata Sa’adatu bata daukar waya, da kanta tayi kiran Sa’adatun taji ba’a daga wayar ba, saita ba matar hakuri tunda tace saboda itane tayiwa Sa’adatun magana a Instagram, ita ta mayar mata da dubu biyar din, tana sake bata hakuri da fada mata tabbas akwai dai wani uzurin daya tasowa Sa’adatu.

Daga baya kuma idan ta kira sai taji wayarta a kashe, abin ba karamin daure mata kai yayi ba, tanata tunanin ko lafiya, data kira Jabir sai yace mata lafiya kalau, daga yanayin yanda ya bata amsar kuma tasan babu abinda zai dora akai, sai tayi masa sallama, ta kira kanwar shi, a wajenta kuma take jin sakin da Jabir din yayiwa Sa’adatu, sakin da taji zafinshi har abin ya bata mamaki, ko dan har ranta take jin kaunar Sa’adatun kamar wata kanwar da suka hada jini. 

“Ki fuskanci rayuwarki ki watsar da wani Jabir, sana’ar da kika fara zakizo ki cigaba, daman ai kince mun kina jiran admission list ya fito, to sai muyi addu’a ki samu, ki koma makaranta abinki, ki maida hankali sosai Sa’adatu yanda zaki tsaya da kafarki wani ba namiji ba zai sake taking advantage dinki har yayi miki abinda Jabir yayi miki ba.”

Sai Sa’adatu tayi murmushi, zuwa yanzun ai ita gaskiya take fadawa kanta, babu abinda Jabir yayi mata, komai daya faru rabawa zasuyi dai-dai, kusan idan ma aka duba nata kason zaifi girma tunda babu wanda ya tirsasata, da kanta ta amince da bukatarsu, amman wa zata bude baki ta fadawa daman can auren nasu ba’ayi shi dan ya dore ba?

Badr ta jima tanata bata shawarwari, daman da suka tashi da safe, akwai inda ake murza taliyar Hausa cikin unguwar, Fa’iza taje da kanta takai filawa dan sun yanke shawarar abinda zasuci kenan. Ta kuma siyo musu su cucumber, lettuce, timatiri harda koren tattasai, ga manjansu me kyaune, saboda haka cikin tsafta da tsari ta zuba taliyar, sauran kayan hadin a waje daban, sai yaji da yaketa kamshin tafarnuwa ta kawowa Badr, Sa’adatu ta kalli taliyar da tayi kyan dahuwa, amman kuma batayi tsammanin Badr zataci ba.

“Taliyar Hausa, kinsan tun ina sakandiri akwai wani gida da ake siyarwa a layin makarantarmu, sai kasha layi zaka samu, kice rabon dai zanyi kwadayi nazo yau.”

Dariya Fa’iza tayi

“Ai ita farin jini ne da ita, da wahala kiga wanda zaice miki bayaso, sai dai in bai saba daci ba.”

Mayafinta Badr ta warware da yake nade akanta.

“Aini ruwa zaki bani in wanke hannu na, ba gayu zanyi ba.”

Ko Fa’iza bayan tafiyar Badr saida tayita yabon halayenta.

“Haka fa duk suke, har yan gidansu shima, wallahi basu da matsala, ba girman kai kamar basu da wannan kudin”

Fa’iza ta jinjina kai tana fadin.

“Allaah Ya zaba abinda yafi alkhairi.”

Sa’adatu ta amsa da.

“Amin”

Ranar ta dauka jimawar da tayi bataci taliya bane yasa ta yamma nayi ta kara shako filet, dan saida Fa’iza ta kara dafa wata taliyar tanata yi mata dariya. Sai ta fara kula kamar cinta ya karu, kuma nan da nan take jin yunwa, sai dai bata tsayawa zabe, abinda duk ta samu ci takeyi, da yake akwai wadatar komai dinma a yanzun, ga kayan shayi da take dasu lodi guda cikin dakinta da biskit kala-kala, dan haka kawai Badr ma inta bushi iska saita biyo ta gidan ta kawo mata leda cike da kayan ciye-ciye. Kuma ta dauki shawarar Badr din, ta cigaba da zobo da kunun ayarta, ga Fa’iza tare sukeyin komai, har tsokanarsu Abdallah yakeyi.

“Sai kumatu kukeyi abinku, yanzun kunma fini kudi.”

Sai gashi kamar wasa har ta shafe watanni biyu, kuma a cikin watanni biyun tayi al’ada sau daya, ta dai zo mata ne ba kamar yanda ta saba ba, tunda ta gani da safe sai jinin ya dauke, bata sake ganin komai ba sai washegari shima kadan, sai dai ciwon mara daya dinga damunta kadan kadan, ta dinga mamaki, to ko sauyine ta samu. Shisa da Fa’iza ta tambayeta ma kai tsaye tace.

“Nayi wancen watan, wannan ne dai ya dan kara kwana biyu.”

Itama Fa’izar kamar Sa’adatu saita kawo canji ne Sa’adatun ta samu, balle ma ga damuwar da tayita fama da ita, duka yaushe ta fara warwarewa, wannan kawai ya isa ma yasa mata rikicewar al’ada. Duka suka watsar da maganar a wajen, cikin wannan tsukinne kuma, a gidan radio ma Fa’iza taji maganar kafe list din farko na dalibai, tayiwa Sa’adatu magana, sai dai tana tunanin yanda za’ayi ta duba, dan ta kira Badr bata sameta a waya ba, taji ya akebi a duba. Dole ta hakura tabari zuwa safe, kuma Abdallah ma yace zai tambayar mata, makarantar daya samu aikin koyarwa akwai wani da yake bautar kasa kuma BUK din yayi, zai tambayeshi yanda nasu tsarin yake.

To kafin ma duk hakan ya faru, saiga text din Jabir ya shigo wayarta, ya kuma saka zuciyarta bugawa ta sake bugawa kafin ta cigaba tana kara gudu da duk dakikar data dauka tana kallon sunan shi a jikin sakon, lokaci daya wani zazzabi ya fara kawo mata mamaya, hannunta na rawa ta bude sakon nashi.

“Admission list na farko ya fito, kin kuma samu. Congratulations Nurse Sa’adatu. Za’ayi miki komai karki damu, idan akwai inda ake bukatar sai kinje zan aiko a kaiki.”

Karanta sakon takeyi da muryar shi, kuma sai muryar tayi mata wani iri, kamar babu wata kulawa a cikinta, kamar babu wani attachment, hakan saiya karasa kashe mata jiki duk da batama san me kuma take tsammanin a tsakaninta dashi ba, wayar na hannunta tayi haske alamar shigowar wani sakon data bude da saurinta.

“Ya kike?”

Saita lumshe idanuwanta da suka cika taf da hawaye, tayi kokari ta kasa mayar dasu, sai ta barsu suka zubo, tukunna ta daukesu da hannu, ta saka wayar a key ta ajiye batare data bashi amsa ba, idan yana so yasan ya take ai yasan hanyar gidansu, yazo da kanshi ya ganta. Amman yanzun data fara samun natsuwa, ta fara dawowa hayyacinta, Jabir kogine, kuma daya tashi saida ya tabbatar ta nutse a cikin shi, can kasa inda yafi ko ina duhu, yanzun data fara ganin haske, tana neman hanyar fitowa, ba zata yarda yazo ya tsaya ya dishe mata hasken nan ta rasa inda zatabi ba. Kuma wannan natsuwar data fara samune taji Abdallah yana maganar kudin hayar da zai sake biya

“Ai tunda dai Alhamdulillah, inajin na shekara biyu zan basu sai infi samun natsuwa.”

Tunda kudin da Sa’adatu ta bashi ya juya, tunanin duniya babu wanda baiyi ba, kafin yaga wani shago da aka saki, ance da yan garuwa ne a ciki, kuma sai sun saki shagon, daman yaga duk layin babu inda ake wanki da guga, gyara yayiwa shagon sosai, akwai samarin da suke mutunci a cikin unguwar ya tuntubi daya daga ciki, sai gashi yaji dadi ya gayyato masa har mutum uku, duk da haka saida Abdallah ya taka har gidan iyayen kowanne sukayi magana, daman yaran duk an gama sakandiri sakamako baiyi kyau ba, babu kuma wanda ya damu da yanda suke gararamba a unguwa daga wannan inuwar zuwa waccan balle a dubi rayuwarsu. Sai gashi cikin dan lokaci sun gama saka duk abinda za’a bukata, sai kuma aka fara farautar neman customers, kuma zuwa yanzun zaice an fara samu, wanda duk akayiwa wanki da guga sau daya dole ya dawo tunda babu ha’inci a cikin lamarin nasu.

Ga Fa’iza itama sana’ar da sukeyi tunda Badr na hadasu da manyan mutane sunayin harna taro, rufin asiri ake samu sosai.

“Yaa Abdallah daman ina taso inyi maka magana ne fa, na fada maka ya bani gidan da muka zauna, kama ga takardun daya aiko dasu. Nace gidan yana zaune bakowa a ciki, daka biya haya har na shekara biyu me yasa ba zamu koma can ba?”

Daman da gaske tanaso tayi masa maganar su koma can din, amman tana rasa ta inda zata fara, balle kuma azo batun kudaden da suke shakare da asusun bankinta, ga mamakinta sai Abdallah yayi dariya

“Dan ya baki gidan saimu kwashi jiki mu koma? Ko kina lissafin har yanzun baki gama iddarki ba? Idan kuma ya mayar dake fa? Ai ko dama ba zaku koma ba sai dai ayi shawarar yanda za’ayi da gidan, amman ta ina zan fara komawa can Sa’adatu, rashin lissafin sai yayi yawa.”

Ita dai ta inda duk ta juya bata ga rashin lissafi a cikin komawarsu ba, bashi Jabir din bane ya bata gidan? Kuma waye yace zai mayar da ita?

“Inda fa zai mayar dani da tuntuni ya maidani Yaya, kuma menene a ciki dan mun koma tunda dai shiya bani gidan. Koma mayar dani yayi ba sai mu koma wani waje ku kuyi zamanku ba.”

Wannan karin harda Fa’iza a dariyar, sai Sa’adatun ta kule, ta tashi ta basu waje.

“Ina zaki? Dawo mana yar kanwata…”

Amman bata ko juya ba, Amira ta kira a waya take fada mata, itama dariyar ta dingayi mata.

“Kamar dai a garin mahaukata Sa’adatu, dan ya baki gida, a ciki fa kukayi zaman aure, sai aga Abdallah ya kwashi jiki kun koma ciki? Ke abinda lissafin naki ya baki kenan ko? Kuma mu ai fata mukeyi ku samu daidaito ya mayar dake, bawai kizo ki zauna a gida ba.”

Nan Amira ta fara kwaso mata wa’azin darajar mace gidan aurenta har saida taji daman bata kira ba, dan karshe ma kashe wayar tayi kamar katin ne ya kare. Batun komawa gida kenan, idan kuma ta nuna ma Abdallah wannan kudaden yanzun kuwa ta tabbata sakata gaba zaiyi suje su samu Jabir a mayar masa da kudin. Tunaninta kenan a farko-farkon daren, wani abu da bata hango yiwuwar shi ba, za dai tasan yanda tayi masa zancen kudin a gaba, yanzun suci gaba da zama tana kallonsu, amman da daren ya fara rabawa kuma sai ta fara lissafin kwanakin da ta kara bata ga al’adarta ba, tunda yanzun aiya kamata ace ta uku ta gani. Saita saka hannu ta shafi mararta da takejin kamar ta kumbura, data danna ma sai tajita da tauri har saida gabanta ya fadi

“Astagfirullah”

Ta fadi a fili, tana mikewa ma ta fita ta dauro alwala tukunna ta dawo dakin, zuciya da sake-sake, kafin taji ta fara sako mata batun ko wata cutarce take damunta, haka ta samu ta ture komai ta gabatar da Nafilarta har raka’a goma yau, tunda da raka’a hurhudu ta fara har saida ta zame mata jiki. Tana kuma jin dadin zuciyarta matuka duk idan ta idar.

Data kammala addu’o’inta, ta kwanta sai kawai Aisha da cikinta suka fado mata, koya take? Ko yanzun cikin yayi girma? Ance idan yakai wasu watanni ana dubawa aga me za’a haifa ta hanyar yin scanning, duk da wani lokacin baya nuna dai-dai. Ko an fada musu meye zata haifa, ta tabbata hankalin Jabir kacokan yana kan Aisha da abinda yake cikinta, watakila ma sunata shirye-shiryen barin kasar tunda abin nema ne ya samu.

Kuma ga mamakinta sai takejin wani duhu-duhu yana rufar mata, saita gyara kwanciyarta tana cigaba da karanta salati. 

Saboda bata ga dalilin da zata zauna ta gayyatowa kanta bacin rai tana zamanta lafiya ba, yanzun kanta ya kamata taji dashi da dalilin da yasa al’adarta keyi mata wasa, sai kuma maganar makarantarta da har yanzun Jabir bai sake ce mata komai ba, kuma kullum saita duba wayarta fiye da yanda zata iya lissafawa, waiko yayi mata sakon itace dai bata gani ba. 

Watakila ma ita kadaice take ta tsammanin ganin sakonshi.

Shi din ya manta da ita.

Sai dai ita ai batasan abinda zai faru da ita anjima ba balle kuma wanda yake faruwa da Jabir a gefe daya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 51Tsakaninmu 53 >>

6 thoughts on “Tsakaninmu 52”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×