Skip to content
Part 54 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Shi ba mai yawan rashin lafiya bane ba, ko Hajiya Hasina ma tana magana

“Jabir bashi da yawan rashin lafiya, tunda kuka ganshi kwance to tabbas yana jin jikin.”

Ko a lokuttan da yakanyi rashin lafiyar, kaso mai girma a ciki harda sangartarshi da Hajiya Hasina take biyewa. Dan abinda zai kwantar da wani a cikin ‘yan uwanshi, idan shine ya tabbata a asibiti zai kwana da likitoci kala-kala zagaye dashi. Tunda yana daga cikin mutane masu son jikinsu da kuma rakin ciwo. Shisa baiyi zaton zai jera satika yana kwana ya tashi da wani irin zazzabi ba, kuma harya dinga fita yana hidimomin shi na yau da kullum. A cikin kwanakin kuma yanda duk Aisha taso ya zauna ta lallabashi yanda ta saba idan bashi da lafiya saiya kasa zaman.

Idan ya zauna zuciyarshi da take a jagule ce zata sake shiga yanayi, zai dinga jin baya kyautawa Aisha da ta jingine nata rainon cikin ta tare akan kula dashi alhalin ta fishi bukatar kulawar. Kuma baisan ta inda zai fara hana zuciyarshi jin abinda take ji ba. Musamman daga shekaranjiya zuwa yau din da fara neman Sa’adatu a cikin duk wani abu da Aisha zatayi masa, yana ta tarawa da kwashewa akan abubuwan da suka bambanta su. A gefe daya Aisha ta sanshi, shekaru sun koya mata karantar tarin abubuwa tare dashi, a nashi bangaren, tare da Aisha yanajin wani yanayi da bashi da kalaman furtasu, kamar dai zai iya cewa, inda duk zaije, kowanne hali zai shiga, zuciyarshi kan fada masa daya gama gida zai tafi, gida kuma a wajenshi yana nufin Aisha, kuma duk shekarun nan har yau wannan din bai canza ba, yanzun haka yanajin wannan yanayin na idan ya koma gida wajenta zaije.

Kamar kuma kowanne ma’aurata suna fada, sosai suna fada, suna samun rashin fahimtar juna, matarshi ce, a karkashin ikon shi take, kawai idan ya kalleta yakanji tayi dai-dai da komai nashi. Wayewarta, gayunta, yanda take mu’amalantar shi da ‘yan uwanshi dama sauran mutane. Kusan kacokan rayuwarta da tashi tana tafiya ne kan wani tsari, kuma a cikinsu babu wanda ya taba gwada kaucewa wannan tsarin yaga abinda zai faru. Shi Jabir dinma bai hango abinda zaisa ya sauka daga kan wannan tsarin ba, tunda komai a cikin tsarin yayi dai-dai da ra’ayinshi. Sai da Sa’adatu ta shigo rayuwar shi, yanzun yake kuma tuna duk wani abu da ya samu a tare da ita wanda Aisha bata dashi.

Kai tsaye Sa’adatu takeyin abubuwanta, ba zaice a hargitse ba, amman kuma bata nuna alamar akwai wani tsari da take bi, daga farko ya dauka shekarun daya batane yake sashi ganin hakan, kamar da kuruciya a tare da ita, sai kuma ya tuna kannenshi da basu ma kaita ba da yanda suke tafiyar da rayuwarsu, sai yaga ba kuruciya bace ba, kawai Sa’adatun ce. Tunda ai ko daga idanuwa tayi ta kalle shi sai ta sa nashi shekarun daya bata subi iska yanajin shi wani matashin saurayi dai-dai da ita, baya sanin sanda yake biyewa yarintar tata. Yanzun akwai abubuwa da yawa da idan ya gani, ko da yana cikin mota ne kuwa sai murmushi ya kwace masa, wani lokacin harma da dariya.

Ko da safiyar yau dinma yana hanyar zuwa kasuwa yaga raguna suna wucewa a gefen hanya, sai babbar sallarsu tare da Sa’adatun ta fado masa da yanda ta dinga kallonshi kamar ya aikata mata wabi babban zunubi saboda ta tambayi kai da kafafuwan ragunan da yake biyu ya yanka mata, yace mata wanda suka gyara yace su dauka

“Me zakiyi dashi?”

Ya tambaya cike da mamaki

“Babbakemun za’ayi fa zanyi farfesu inci da biredi.”

Kuma da duka gaskiyarta tayi maganar. Yanda ta dinga zumbure baki yasa shi bayan ya fita da ya nufi gidansu ya samu lokacin ake yanka ragunan, yayi magana da daya daga cikin masu gyaran ragunan, kudi kuma ya bashi yace a gyara daya daga ciki saiya kawo, ko baya nan yace akai masa gidan Sa’adatu.

“Yallabai za’a sassara ne idan an gyara?”

Saiya girgiza masa kai, ba zai jawo wani rikicin ba, gara akai mata shi a hakan, sai tayi yanda take so. Sai dai baiyi tsammanin bayan kwana biyu da yaje gidan zai samu abinda ya samu ba. Tunda watansu wajen nawa tare, mamaki wanne kalane Sa’adatu bata bashi ba, ashe zatace baiga komai bane ba, tunda ya tunkari kofar yake jin karar ana dukan wani abu, da yake bata murza mukulli a jikin kofa ba, kanshi tsaye ya shiga, ya kuma nufi hanyar da zata kaishi kitchen din gidan, inda yake jin karar na fitowa, a zaune ya sameta da wata mulmulalliyar tabarya tana dukan wani abu data nade a cikin ledoji

“Sa’adatu?”

Ya kira da mamaki da kuma tarin tambayoyi, dagowa tayi ta gaishe shi, gaisuwar daya amsa da

“Me kikeyi?”

Dan tana gaishe shin ta cigaba da bugawa abinda yake cikin ledar tabarya

“Kan rago ne nake fasawa zan ciro kwakwalwar”

Kuma wai saita nuna tsananin mamaki saboda yace

“Kan rago? Kwakwalwa? Kiyi me da ita?”

Har kai ta girgiza irin lamarinshi abin a dubane tunda baisan me akeyi da kwakwalwar rago ba

“Zoka fasamun sai kagani”

Tace tana saka shi matsawa gefe

“Ni? Inje in kwankwatse hannu”

Kuma a tsakanin mamakin juna da sukeyi, da gardamar da bata dauki mintina biyar ba, bayan Sa’adatun ta shagwabe masa fuska, sai gashi tsugunne rike da tabarya yana tayata fasa kan ragon. Akwai abubuwa da yawa a tattare da Sa’adatu, abubuwan da bai taba tunanin akwaisu a tare da wata mace bama, manya da kanana da yake jin yana kewa a yanzun. Wannan bambancin da yake tsakaninta da Aisha shine abinda yake so, wani abu da baisan yana bukata ba sai da ya samu, kuma yakejin ya rasa a yanzun. To ai akwai ma ranakun da kallon Sa’adatu kawai zaiyi sai dariya ta kwace masa, fara’arshi a saukake take tare da ita, baya bukatar ayi wani babban abu, saiya fito daga gidanta har yaje inda zaije da murmushi a fuskarshi.

Watakila hakan ya farune dan ya tara memories da yawa da zai dinga tunawa yanzun da tayi masa nisa, ta kara masa nisa kuma tunda ta gama iddarta, da gaske duk wani abu daya hadasu ya raba. Kuma sako nawa yayi mata batare data bashi amsa ba? Ko ya taken daya tambaya yaga ta karanta sakon, shisa ya wuni yana jiran amsarta amman shiru. Jiyama da dokin shi ya tura mata sakon cewa komai na shirin makarantarta ya kammala, tunda har litattafan da akace kowanne dalibin da zai karanci Nursing yana da bukata ya aika an siyo mata, harda wasu tarkacen ma, tunda Farhana ya turawa kudi yace ta hada masa duk wani abu dangane da kayan ciye-ciye da dan makaranta zai bukata. 

“Na waye?”

Ta tambaya, bai kuma yi ko rawar murya ba wajen amsata da

“Sa’adatu”

Bata sake tambayar shi komai ba, saima ta kashe wayar, kuma shi kanshi saida ya jinjinawa yawan kayan data hado bayan ta kirashi tana tambayar waye zai kai kayan, yace mata zaije ya amsa akwai litattafan da zai hada mata dasu sai ya bayar akai gabaki daya. Zuciyarshi ce da takeyi masa ba dadi da rashin amsar Sa’adatun tasa shi bai aika mata da kayan ba tun jiya, yau ma kuma baiji yana da niyyar aika mata dasu ba tunda ya tashine yana wata shawara da zuciyarshi akan kai kayan. Duk da yasan dayar wayarshi da private line dinshi yake a ciki babu wanda zai kirashi da dare batare da kwakkwaran dalili ba, haka ya sakata a silent jiya da zai kwanta dan baya cikin yanayin da zaiyi magana da kowa, ko karar wayar ma bayaso, dayar kuwa kasheta yayi gabaki daya. Yanzun nema yake tuna bai kunna ba, yasan an neme shi har an gaji, sakonni kuwa baisan yawansu ba.

Haka ya dauko duka wayoyin, ya kunna dayar, ya ajiyeta ta gama lodi, ya kuma dauki dayar yana tabawa ya cire mukullin sirrin, sai kuwa yaga sakonni guda hudu, ya shiga danya duba, biyu daga bankine na fitar katin daya saka da kuma wasu kudi daya tura, dayan Aisha ce tana rokon shi da karya zauna da yunwa, sai dayan daya bashi mamaki ganin Abdallah ne, Abdallahn Sa’adatu, wata nawa yanzun daya tura masa sakon ban hakuri, yasan dai ba amsa bace ba, haka kawai yaji zufa na tsattsafo masa a tafin hannun da yake rike da wayar, daya bude sakon kuma ya karanta sai yaji wayar na neman subucewa ta fadi tare da wani abu daga kirjinshi da yake da yakinin yafi zuciyarshi girma.

Layi dayane yake masa yawo a idanuwa, kwakwalwa dama zuciya

“…ciki…”

Sauran duk sun bace masa, idan aka hada yara biyu fa kenan, shi Jabir, yara biyu a lokacin da tsammanin dayan ma yake neman kwace masa. Sai yaji wani sanyi-sanyi na rufar masa, kamar kuma daya kifta idanuwanshi yaji danshi a cikinsu. Rahamar Ubangiji mai yawa ce, tunda shi yasan babu wani abin arziki daya aikata balle yace sakayya ce. Kyauta ta yara tabbas sai wanda Allaah Ya zaba. Mikewa yayi yana kwasar wayoyin duka biyu, mukullin motar shi na cikin aljihu, sama-sama yayi sallama da yaran shagon nashi. Daya shiga mota saiya fito da kudin da yake aljihunshi, da kuma wani saura da yakan ajiye cikin mota ko da bukatarsu zata taso, haka daya hangi almajiri zai tsayar da mota ya fita ya bashi duk abinda Allaah Ya rabauta zai samu, saida ya karar da kudin nan tas yanajin sunyi kadan, abinci zai bada kudi ayi na sadaka da kaji a rarrabawa masu bukata, ai daga yau kuma shi in bai kasance cikin godiyar Allaah bama saiya zama daya daga cikin bayi masu butulci. Kyautar yara biyu fa, yara biyu.

Bai taba jin dadin tuki irin na ranar ba, ji yake kamar shi kadaine akan titin, duk cunkoson da yake kan titin unguwarsu Sa’adatu bai gani ba, baya ganin komai sai kyautar da Allaah yayi masa. Kafin wani lokaci sai gashi a kofar gidansu Sa’adatu, ya dauko wayarshi yana lalubo lambarta ya danna kira, tana fara bugawa tare da zuciyarshi, yaushe rabon daya kirata? Yaushe rabon da yaji muryarta? Sai dai har tayi ringing ta yanke, ya sake kira sau biyar a jere bata daga ba. Murmushi yayi yana tuna rikicinta, yana tuna iya karfinta kenan, taki daga masa waya, hakan ne hanyarta ta nuna masa a wuya take dashi. Sai ta ganshi tsaye a gabanta ta fara magiya tana bashi hakuri

“Ina kofar gida, ki fito inganki”

Bai ajiye wayar ba, yana kuma kan sakon, hakan yasa yaga alamar tana rubutu, saiya tsaya jiran amsarta

“Kaganni?”

Da murmushi a fuskarshi ya karanta

“In ganku”

Ya tura yana sake fadada murmushin shi

“Ni bana son ganinka, ita kuma ko shi akwai sauran lokaci, ka tafi, idan lokacin yayi saika dawo”

Dariya yayi wannan karin

“Bana son yin rigima dake Sa’adatu, ki fito”

Jira yayi wajen minti biyar, amman bata dawo masa da amsa ba, daya sake kira ma saita kashe masa kiran tana kuma kashe wayar gabaki daya. Sai kuma ya kasa jin haushinta, duk da yaso ganinta, haka yaja motarshi ya juya. Sai dai washegari haka ya dinga kiran wayar Sa’adatu amman a kashe, saiya daga kafa baije ba a ranar, ya dai cigaba da kiranta yanajin wayar a kashe. Ranshi bai fara baci ba saida ya jera kwanaki hudu bayan nan yana zuwa kofar gidansu Sa’adatu, gashi ta kunna wayar, amman kiran duniya idan yayi mata ba zata dauka ba, haka sakonnin shi bata amsawa. Yaji, bata son ganin shi, shikuma ai yana son ganinta, yana son ganinsu, ya tabbatar da lafiyarta data abinda yake cikinta, ya kuma ji ko tana bukatar wani abu, sannan ga maganar asibiti, yana son ya dauketa ya kaita asibitin daya yadda da likitocinsu gudun samun matsala.

Yana zaune a motar, ranshi a bace yaji karar dayar wayarshi, dauka yayi da niyyar ya kashe, ganin mai kiran yasa dabara fado masa, sai ya mayar da wayar ya ajiye batare da ya amsa ba, ya dauki ta kan cinyar shi da yake kiran Sa’adatu da ita yana tura mata gajeran sako

“Akan maganar makarantarki ne, daman zance zaki hakura sai bayan kin haihu.”

Aikuwa sakon na shiga yaga alamar tana rubutu, wani murmushi ya kwace masa

“Akan me? Me yasa zan hakura?”

Wayar ya ajiye a gefe yana tayar da motarshi ya juya, yanajin tanata turo masa sakonni ya share, ko dubawa baiyi ba har saida ya koma gida, ya samu Aisha na bacci a falo kan doguwar kujera. Sai lokacin ya duba sakonnin Sa’adatu da duka akan maganar fasa karatunta ne, ya bata amsa da

“Da zamuyi magana ne ni dake, to kuma bakya son ganina. Zanyi magana da Abdallah kawai. Ki kulamun da ku.”

Ya saka wayar a silent, ya mayar da ita aljihunshi, ya karasa yana tashin Aisha, ya kama hannuwanta yana taimaka mata ta mike daga kan kujerar, kusan rabin jikinta jingine yake da nashi, suka nufi daki tare, tunda ya samo kan Sa’adatu, baccin daya kwana biyu baiyi ba shi zaiyi, dan haka ya rage kayan jikinshi ya kwanta bayan Aisha yana rikota, hannunshi akan cikinta, yanajin bacin ran da Sa’adatu ta saka masa a kwanakin na wucewa. Tun wajen sha dayan suke bacci, sai karfe biyu da wani abu, dan shiya ja musu sallar Azahar a gida tunda sun makara. Aisha saida ta sake watsa ruwa, shikuwa kaya kawai ya canza suka fice, sai kallonshi takeyi, ya kuma san nishadin da yake cikine yake bata mamaki ganin yanda ya hargitse mata kwana biyun.

Shiya mayar da ita gida bayan sun gama, tukunna ya sake fita, sai da ya karasa shago ya duba wayarshi, Sa’adatu tayi masa kira goma, sakonni sha biyar. Dariya ta kubce masa, ya bude sakonnin yana dubawa, magiya ce takeyi masa akan yaje

“Saina samu lokaci.”

Ya amsa yana sake ajiye wayar. Babu kiran da batayi masa ba shima yaki dagawa, ranshi nishadi fal, sai daya sha iska kwana biyu tukunna yaje, kiran farko ta daga wayar ko sallama batayi masa ba balle kuma gaisuwa tace

“Kazo? In fito?”

Saida yayi murmushi tukunna ya amsa ta a takaice, aikuwa kamar daman tana jiran zuwan nashi, sai gata ta fito da wata hijabi ruwan madara, tana fitar kuma karasawa tayi wajen motarshi ta bude ta shiga. Kuma ga mamakinshi, suna hada idanuwa sai ta saka masa kuka, ya karkata yanda zai kalleta sosai, yana jingina da kujerar motar, sosai yake kallon shagwaba irin ta Sa’adatu, saida tayi mai isarta, ta saka hijabinta tana goge fuskarta, sai ajiyar zuciya takeyi tukunna yace mata

“Ya kike?”

Shiru tayi bata amsa mishi ba

“Sa’adatu…”

Ya kira muryarshi 

“Inata kiranka kaqi dagawa, tun rannan nake kiranka”

Murmushi yayi

“Yi hakuri to, ba zan kara ba”

Ya tsinci kanshi da furtawa saboda yanda yakejin duk jikinshi ya mutu, jan ajin daya shirya zaiyi mata duk ya sirare yabi iska

“Makarantar har an fara karatu ko?”

Kai ya girgiza mata

“Dan Allaah karkace ba zanje ba, wallahi bana wata rashin lafiya.”

Ta furta cike da roko idanuwanta na cika da hawaye.

“Sai munje asibiti an duba an tabbatar mun da cewa babu wata matsala tukunna.”

Da sauri ta daga masa kai tana dorawa da

“Zan fadawa Yaa Abdallah sai in kiraka kazo muje.”

Nashi kan ya girgiza mata, dan ya rigada yayi magana da Abdallah din kan idan ya samu lokaci zaizo ya dauketa, kuma ya amince.

“Nayi magana dashi, zamu iya tafiya yanzun ma.”

Cewar Jabir din, saita kalli kanta, hijabinta duk ya baci da hawaye, gashi saboda sauri silipas din Abdallah ne ta zira a kafafuwanta.

“Bari in sako hijabi to.”

Tayi maganar tana bude murfin motar ta fita batare data jira amsar shi ba, bakin Fa’iza har kunne jin asibiti zasuje kuma da Jabir, ita inda za’a bude zuciyarta babu komai a ciki sai fatan ace su dai-daita tsakaninsu a hanyarsu ta zuwa asibitin. Sa’adatu harda takalmi ta sake, hijabin wani ruwan tokane da ta gani a jikin Badr, dinkin ya burgeta, da tayi mata magana saita dinka mata irinshi ta aiko mata dashi, data fito Jabir ya kasa dauke idanuwa daga kanta, yana neman abinda ya canza masa a fuskarta daga shigarta gidan da kuma fitowarta, alamu dai sun nuna ba kwalliya tayi ba, idanuwanta ma har lokacin a rine suke da kukan da tayi. Tama san asibitin da sukaje din, inda ta taba kwanciya ne.

Da suka fita daga mota, babu zato taji hannun Jabir cikin nata, saida duka jikinta ya amsa, haka ta dinga saka kafarta duk inda ya cire tashi, ko da suka karasa reception, sunanta ya fada musu da cewar tana da file, basu kuma zo da karamin katinta ba, in ba’a ga file din ba to a bude mata sabo, sukace su jira za’a duba a gani, har suka zauna bai saki hannunta ba, bai kuma nuna alamun hakan wani abu bane ba, ita dai ya bari da bugun zuciya yana kuma tuna mata ranakun da zasu zauna suna kallo hannunta a cikin nashi, da wasu ranaku da riko hannun natane abu na farko da yake farayi idan ya bude idanuwanshi daga bacci, har sai daya sa ta taba zama ta saka hannuwan nata a gaba tana kallo ko zata ga abinda Jabir din yake ji a tare dasu da baya gajiya da rikesu a cikin nashi.

Da aka gano file din nata ma, tare suka shiga dakin likitan, duk wasu tambayoyi da yayi mata ta amsa cikin rawar murya saboda Jabir daya kafeta da idanuwa, ta kuma fadawa likitan taje wani asibitin har scanning anyi mata, shisa yace ba sai an kara ba, ya dai basu awon jini da kuma na fitsari, bayan yayi rubuce-rubuce yace suje su biya sai su tafi Lab inda za’a auna komai, ba sai sun jira ba, idan aka dibi jinin zasu iya tafiya, za’a sakane a file dinta. Sai kuma bayan sati hudu zata sake komawa awo

“Makaranta zata fara, babu wata matsala? Ba abinda zai same su ita da babyn?”

Kai likitan ya girgiza masa

“Ai tama fita daga first trimester dinta, babu wata matsala zatayi karatunta…”

Sai dai yan shawarwari daya bata kan takaita yawan zirga-zirga a cikin makarantar. Haka sukayi masa godiya suna ficewa daga ofishin nashi. Wajen dibar jini haka Jabir ya rike mata hannu dam kamar zai ballata, saida ya tsaya ya siya mata gasasshiyar kaza da kuma yoghurt mai sanyi tukunna ya mayar da ita gida, dan lokacin ma ana ta kiran sallar Magriba.

“Zan kiraki, ki kula sosai please.”

Ya karasa maganar yana jan kalmar karshen cikin taushin murya, kai kawai ta iya daga masa tanajin wani abu na danne mata kirji lokacin data bude murfin motar tana ficewa

Da bai saketa ba.

Da yanzun ko basu wuce gidansu tare ba zai kaita ya ajiye.

Yanzun shikenan ko? Har anyi angama…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 53Tsakaninmu 55 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×