Skip to content
Part 55 of 58 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Ba wani bane ya zaunar dashi ya fada masa cewa a rayuwa irin tasu daya sani, ya kuma taso cikinta, akwai lokacin da zaka kai ko Hajiya Hasina sai dai ta zaunar da kai ta baka shawara, balle kuma ace tsakaninsu. Duk da ko sanda yake tasowa zai iya kirga mutum nawa suka taba rufe shi da fada a cikin ‘yan uwan nashi, ba kuma don son da sukeyi masa bane kawai, sai don shi ba mai yawan yin laifi bane ba, to yaushe ma ya zauna balle yayiwa wani laifin? Yanzun kuma da yake zaunen, dukkansu kowa hidimar iyalinshi tasha masa kai, lokacin da za’a hadu din ana marmarin juna ne. Zai iya cewa akan Sa’adatu ne duk fadan da yasha a yan tsukin lokacin, na farko kan aurenta daya ce zaiyi, na biyu kan sakinta da yayi.

To me yasa daya samu Hajiya Hasina ya fada mata Sa’adatu na da ciki, bayan wani irin shiru daya ratsa dakin ma wasu dakika sai kuma sautin hamdalarta, sai dorawa da tayi da fadin

“Allaah Ya inganta, fatan ita da abinda yake cikin nata suna cikin koshin lafiya?”

Daya amsa mata kuma wani yanayi daya girmi farin ciki ya hana masa karantar asalin abinda take jine ya lullube fuskarta, saita sauya akalar zancen da kwaso masa labarin wani dan uwansu da aka fasawa daya daga cikin shagon wayoyin shi aka kwashe komai, mamakinta ya hanashi fahimtar labarin, sai ma yace mata ana jiranshi a kasuwa akwai kayan da aka kawo yana so yaje ya duba, yayi mata sallama ya tafi, yana mota ya dinga tunani yana laluben abinda yakeji ko yayi tsammani daga wajenta ya rasa. Haka daya koma gida tun Aisha na tambayar shi abinda yake damunshi harta gaji ta kyale shi.

A gabaki daya satin, duk wani wanda ya isa dashi a cikin ‘yan uwanshi, wanda suke gari haka ya dinga zuwa yana samunsu yana cewa gaishe dasu yaje yi, wanda suke nesa ya kirasu a waya. Amman babu mutum daya da yayi masa maganar Sa’adatu balle kuma cikin da yake jikinta. Ya kuma san zai rantse batare da kaffara ta hau kanshi ba sun sani, ba magana bace da Hajiya Hasina zataji ta barwa cikinta, abin farin cikine da takan raba da kowa dan su taya junansu murna. Kuma a karon farko zasuyi masa rowa? Rowar ma ta tayashi murna idan ma ba zasu kara da komai ba.

Da gaske ya kai matakin da za’a dauki ido a saka masa? To ai talatin da biyar dinma duka yaushe ya cika ta? Kafin nan ma, duka yaushe ne suka dinga kiranshi sunayi masa fada akan sakin da yayiwa Sa’adatu? Har wanda ma basu taba yi masa fadan ba sai da sukayi, yanzun kuma kowa yaja bakinshi ya dinke? Sai wani abu daya hanashi sukuni ya dinga danne masa zuciya, ya kasa ma zama kasuwa, ya kira Aisha bata daga wayar ba, tayi masa gajeran sako cewa zata kwanta ko da ya kirata bata dauka ba ta saka wayar a silent, Sa’adatu ya kira, ita kuma tata wayar a kashe. Sai yaji komai ya sake jagule masa, daman daga kasuwa sai yaje yaga Sa’adatun ko zaiji sauki-sauki, amman bayason zuwa batare da tasan da zuwan nashi ba, kar ko itama baccin takeyi yaje yasa a tasota bayan likita ya tabbatar masa hutu na daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da mai ciki take bukata.

Sai kawai ya yanke shawarar komawa gida, inyaso sai shima ya raba gefen Aisha ya kwanta, ko baiyi baccin ba zai samu sauki ta wani fannin, watakila kanshi ya rage nauyin da yayi masa. Sai dai sanda ya shiga gidan da sallama, a tsaye ya samu Aisha, ta daure gashinta da yake baqiqirin, bawai tsayine dashi ba, amman a cike yake sosai, kuma sumar har wajen goshinta duk itace a kwance, wani abu da yake kara mata kyau a idanuwan shi, gashi alamu sun nuna da ta tashi daga baccin bata karabi takan sumar ba. Idan akwai wani wando banda dan karami a jikinta to daga inda yake idanuwanshi basu hango masa ba, rigarshi ce ruwan toka a jikinta, mai dogon hannu, tana da kauri sosai rigar, ta kuma sauka har wajan cinyoyinta, sai hannunta rike da katuwar robar ice cream din ko babu ciki ita din ma’abociyar shice tun da can, ga cikinta daya fito ta cikin rigar, akwai kananun kuraje a gefe da gefen fuskarta da take yawan yi masa mitar sun bata mata fuska

“Bawani, kinyi kyau, sosai”

Kuma baya fada bane don taji dadi, shida Aisha suna da wani kusanci da suke iya fadawa juna irin wannan gaskiyar batare da rai ya sosu ba, garama shi yaji wani iri ranar farko data tusa shi gaba tana tuntsira masa dariya.

“Ni baka fadamun hancinka na kumbura inka tashi bacci ba.”

Sai daya kwana nawa inya tashi saiyayi luf ya dade a kwance yana jiran hancin ya sace daga kumburin da Aisha tace yakeyi in yayi bacci ya farka dan kar tayi masa dariya, duk da ya kalli kanshi a mudubi yafi sau nawa amman baiga kumburin ba.

“Kikace hancina na kumbura idan nayi bacci, karya kikeyi, kawai kinga na fiki kyaune shine kike neman abinda zaki kusheni.”

Ya fadi da dukkan gaskiyarshi a lokacin, amman sai Aishar ta sake sakashi a gaba da wata sabuwar dariyar har saida yayi fushi ta koma tana lallashin shi.

“To idanma hancin na kumbura ai ina sonka a haka, naji nagani, da kumburarren hancin da komai.”

Sai kuma abin ya bashi dariya, a hankali saiya saba da wannan halin nata na fadar duk abinda tayi niyya iya gaskiyarta.

“Ni da kai, zaman aure mukeyi, tafiya ce mai yawan gaske idan muna da tsayin rayuwa. Shisa nake son inyi kokarin ganin ban boye maka ko daya daga cikin halayena ba, masu kyau da marassa kyau, dan Allaah karka boyemun kaima, hakan ne zamu ji dadin zaman, idan muna gayawa juna gaskiya cikin girmamawa, sai kaga mun hadu mun gyara inda muke da nakasu.”

Hakan kuwa suka fara, suke kuma kanyi, zai iya kallonta yace kayan data saka basuyi mata kyau ba, ko janbakinta yayi yawa, kananun abubuwa da manya, abinda yake so, wanda bayaso, wata rayuwa ce da in wani ya gani zasu burgeshi, amman rayuwace da sukayi shekaru suna ginawa, ba kuma zaice cikin sauki ba, kowa a cikinsu akwai abinda ya sadaukar dan ganin zaman yayi musu dadi.

“Kinyi kyau…”

Ya tsinci kanshi da furtawa, saita kalle shi da idanuwanta da bacci ya rinar dasu, ta nuna kanta da katon cokalin da ta yake dayan hannunta tana girgiza masa kai alamar maganar bata shigeta ba, kiciniyar bude robar ice cream dinta ma ta farayi, ya taka ya karasa ya karbi robar yana jinta da nauyi, gashi ta dauki sanyi sosai, ya bude ya mika mata, ya kuma kai hannu da nufin karbar cokalin ta janye.

“Karmu fara haka da kai, not my ice cream.”

Cewar Aisha ta zagaye ta gefenshi tana wucewa cikin falon ta samu kujera ta zauna, ta dora robar a saman cinyarta.

“Last I check wani abu na damunka, da safen nan ma da kai kake amsa mun magana, duka satin nan ma, ko ince a watannin nan ka koyi boyemun abubuwa…”

Yanda take maganar yasan ranta yana baci da boye-boyen da yakeyi mata, amman yace mata me? Tunda ya fara tunanin sakin Sa’adatu, ya kumayi sakin wani sashi na sukununshi ya samu tangarda? 

Ko kuma adadin kewar Sa’adatu da yayi wanda shi kanshi baisan yawanshi ba? Idan ya bude bakinshi abinda duk zai fada ba abu bane da zataso taji ya sani. Saboda idan ya auna yawan kishin shi, shi kadai ma saiya girgiza kai ya kara jinjinawa kokarin mata da suke iya zama da mazajensu bayan sun kara aure. Saboda daya hasaso ace shine Aisha, itace shi, tabar gidan taje wajen wani kato, saiya kasa karasa tunanin, kanshi ya sara, jikinshi ya hau rawa, zazzabi ya fara yi masa barazana, har wani duhu-duhu yaji yana neman rufe masa ido.

Daya dawo gidan kuwa, inda duk ta cire kafarta nan ya dinga mayar da tashi, wani irin rashin natsuwa ya dinga fama dashi wajen kwana nawa. Yanzun kuwa zagayawa yayi ya zauna akan kujerar ta dayan gefen yana kura mata ido har saida ta fara mutsu-mutsu, alamar kallon nashi ya soma shigarta

“Aisha…”

Ya kira a tausashe dai-dai lokacin da takai ice cream din bakinta, tana jinshi ya zama ruwa, kamar shima ya narke ne tare da yanayin da Jabir ya kira sunanta

“Abinda ban fada miki ba, abune dana san fadar ba zata amfane mu ba daga ni harke, dan Allaah karkiyi mun wata fahimta ta daban…”

Saita tsinci kanta da daga masa kai, daya kamo hannunta kuma saita ajiye duka robar ice cream din a kasa tana mayar da kacokan hankalinta a kanshi, wani abu da dana sanin yinshi ya  lullubeta bayan Jabir ya bude baki yace mata

“Sa’adatu na da ciki…”

Shima kuma yanayinta daya canza gabaki daya yasa shi hadiye sauran maganar dayayi niyya, maganar watannin cikin da tazarar nata dana Sa’adatun, hannunta dai na cikin nashi har lokacin, kuma idanuwanshi na kanta, numfashi take ja tana fitarwa kamar mai tausayin iskar, kafin ta saka idanuwanta cikin nashi, cikin muryarta data sirance mishi fiye da ko yaushe tayi masa tambayar da bai taba tunanin zatayi masa ba

“Anyi dashen ne daman?”

Sai dai yanda idanuwanshi suka fara rawa a cikin nata yasa zuciyarta wata irin bugawa, bugu ne cikin sigar da bata tabayi mata ba, a rana sau nawa take saka hannunta saman cikinta? Wani lokacin ma sai taji motsi, tana kai hannu kamar abinda yake ciki na mata wasane sai yayi luf yaki kara motsawa, amman yanzun ba motsi kawai ba, watakila da za’a hasko abinda yake cikin nata, juyi ne yayi, juyi mai karfi tare da bugun zuciyar tata, kamar shima yana neman hanya ne don gujewa janshi da zatayi inda tunaninta yake kokarin kaita

“Dashen kwan naka nake nufi, an dasa mata ne daman?”

Da yake a daburce yake, tambayar kuma tayi masa ba zata sai duk wata dabara ta kwace masa, baima san yana girgiza mata kai ba saida ta zame hannunta daga cikin nashi, sai yabi hannu da ta kai jikin rigarta tana gogewa kamar maison goge wani abu da take tunanin riketan da yayi ya goga mata. 

“Tasha…”

Ya kira, kafin ya rufe bakin shi, ta kifta idanuwanta, hawaye na zubowa daga cikinsu, numfashi take ja yanzun kamar mai kokawa dashi, lokaci daya jikin Jabir ya fara rawa, Aisha macece mai tsananin jarumta, shima zaiyi mata wannan shaidar, abinda duk zaiga ya kaita kasa to ya tabbata ba karami bane ba, ko akan maganar matsalar haihuwarta sau nawa yaga tayi kuka? Shisa in dai zaiga hawaye kwance cikin idanuwanta sai yaji gabaki daya hankalinshi ya tashi, akwai mata da yawa a rayuwarshi, tun daga kan ‘yan uwa, na nesa da na kusa, ga kuma abokan kasuwanci. Kalilan din daya ga kukansu a ciki wanda yake da kusanci da sune sosai, kafin ya auri Sa’adatu ma saiya dauka yana daga cikin jerin mazan da basa son kukan mace.

Sa’adatu komai ma a wajenta na kuka ne, idan zai fadawa kanshi gaskiya, yana son kalar da idanuwanta sukeyi in tayi kuka, dukanta ma kyau take masa na daban, ko yace kukanta ba damunshi yakeyi ba, susuta shi yakeyi yaji yana son zabtare shekarun shi ya dai-daita su da nata. Amman kukan Aisha? Aishar shi, kukane da bayason gani ko kadan, rikota yakeyi tana ture hannuwanshi

“Dan Allaah…kinga ba’a son abinda zai daga miki hankali…dan Allaah kiyi hakuri, nine? Nine ko?”

Jabir yake maganar a rude, har lokacin yanaso ya kamota amman tana ta kwacewa, ji take kamar yana rikota da soson waya, ta tabbata inta nutsu zata ga inda ya karceta a hannuwa da yaudararshi. 

“Akwai mata masu kyau Tasha, bance bana ganinsu ba, amman iya shine kawai, ina ganinsu, da idanuwa na…”

Harararshi tayi

“Kana ganinsun dai ai, wata zata burgeka wata rana”

Saiya girgiza mata kai, cike da yarda da kanshi, yardar da ya jawota yana dorata akai, da yaga tana girgidi saiya tsaidata da kalamanshi

“Kuna da bambanci, har abada kina da banbanci da sauran mata, saboda ba idanuwana kadai nake kallonki dasu ba harda zuciyata”

Shi yasa duk idan taga ana magana akan maza da rashin tabbas dinsu saita girgiza kai, tayi murmushi, alfahari ya cika zuciyarta fam, kamar ta daga nata mijin ta nuna musu, lokacin da maganar matsalar haihuwarta ta bullo, da aka tabbatar shi matsalar shi ba matsala bace tunda da an dora shi akan magani zai warke, sau nawa ta kwana tana kuka a jikinshi? Tun tana ganin zai iya juya mata baya har ta daina, musamman daya dinga kallon idanuwan duk wanda yake tunanin ya isa dashi in yayi masa maganar karin aure yana ce musu

“Da nine da matsalar fa? In tace zata zauna dani kune gaba-gaba wajen saka mata albarka da fadin halaccin da tayi mun, me yasa dan nace zan zauna da ita kadai zai zama abinda za’a dinga magana akai?”

A lokacin idan ta hau kafafen sada zumunta taga anyi jam’i ana zagin maza sai ranta ya dinga baci, in taji ance wacce macece zata daki kirji tace namiji ba zai kunyatata ba, ta shiga comment section taga mata na fadin su dai kirjinsu ciwo yakeyi sai taji tausayinsu ya kamata. Taso tace musu suzo su ga mijinta, suzo ga Jabir, hannu ake bukata a daki kirjin dashi ko sanda za’a bata? Ashe yana gefe yana ce mata lokaci yake jira ya bata mamaki, itace ta rufe idonta taki gani. Ko shisa inta taso masa da maganar Sa’adatu sai ya shata mata layi, ya nuna mata ita ta saka shi yin auren gabaki daya ta kuma yi gefe tana barinshi shi kadai, maimakon yace mata tayi gefe ne ta barshi da Sa’adatu yana shagalin shi.

Kawai sai Sa’adatun ta dinga dawo mata a ido, yarinyace cikin shekara sha takwas zuwa sha tara, ko ita tabata wajen shekara goma, amman da yake kishi babu ruwanshi da shekaru gata zaune tana zubar da hawaye akan karamar yarinya, kuma waye yaja mata? Namijin da take ikirarin ba zai kunyatata ba, shine ya dai-daita matsayinta da yar karamar yarinya kamar Sa’adatu, kallonshi tayi ta cikin hawayenta tana neman son da takeyi masa ta rasa, bata jin komai sai kishin da bata taba hango tana da irinshi ba a tsayin rayuwarta. Kuma a haka dan har gaban ka’aba ta tsaya, ta dora hannunta ta nemi sauki akan kishi. Sai take ta godewa Allaah da yasa bata taba tsoma bakinta a duk wani abu daya danganci maganar kishiya ba.

Tana dai kallon masu zaqewa suna fadin Allaah Ya kiyaye suyi abu kaza idan sunga wata tayi, suna tunanin sunfi karfin su nuna kishinsu ta wannan sigar, a maimakon suyi addu’a su nemi sauki tunda baizo kansu ba, ba kuma zasu taba hasaso abinda kishi zai iya sakasu aikatawa ko akasin hakan ba. Da gaske kishi na cikin manyan jarabawa da akayiwa mata. Kokarin mikewa takeyi ko zata daina ganin Jabir

“Aisha please…”

Ya fadi yana rasa yanda zaiyi mata ganin sai ture shi takeyi taqi bari ya riketa, kamar ma bata son ganinshi

“Shisa ka dinga rashin lafiya da ka rabu da ita? To ni meye nawa a ciki? Ai nace maka ka dawo da matarka…”

Take fadi, yanda muryarta ke karyewa da kowacce kalma shi kanshi da takeyiwa maganar yasan bata kai zuciyarta ba, bama daga cikinta take fitowa ba, balle kuma ita da take maganar yanda jikinta ke kara daukar zafi na karyatata. Allaah Ya bata iko ta samu ta mike, Jabir ma ya mike.

“Karka biyoni, wallahi karka biyoni, inka biyoni saina kira Hajja na fada mata.”

Kai ya jinjina mata, ya daiyi tsaye saida yaga ta sha kwana, ya kara matsawa yaga shigarta daki, ta kuma bugo kofar da karfin da yasa shi runtse idanuwanshi, ya kuma rufe masa kofar wani tunani daya fara tsakanin jiya zuwa yau…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tsakaninmu 54Tsakaninmu 56 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 55”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×