Duk safiyar da zata gani, idan ta bude ido, ta fito daga daki da nufin yin alwalar Asuba taci karo da bokitin kullu, sai tunanin inda zata samarwa kanta mafita daga rayuwar data taso a cikinta ta fado mata. Amman zaren duk da zata kama, sai taga tsayin shi yayi mata yawa, tazarar da take tsakaninsu tayi nisan da ba zata iya cimmata ba. In taje makaranta kuma, ta ga yanda take fahimtar duk wani darasi da za'ayi musu, kusan fiye da kowa a ajin, sai ranta ya kara jagulewa. Idan ma tace karatu zata kama a matsayin mafita. . .
Maa shaa Allah sa’adatu a rage kwadayi da dogon buri. fatahAllahu Alaiki
Sa’adatu wannan halayyar taki zata kaiki ta baro fa, lubna Allah ya kara basira