Skip to content
Part 6 of 66 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Duk safiyar da zata gani, idan ta bude ido, ta fito daga daki da nufin yin alwalar Asuba taci karo da bokitin kullu, sai tunanin inda zata samarwa kanta mafita daga rayuwar data taso a cikinta ta fado mata. Amman zaren duk da zata kama, sai taga tsayin shi yayi mata yawa, tazarar da take tsakaninsu tayi nisan da ba zata iya cimmata ba. In taje makaranta kuma, ta ga yanda take fahimtar duk wani darasi da za’ayi musu, kusan fiye da kowa a ajin, sai ranta ya kara jagulewa. Idan ma tace karatu zata kama a matsayin mafita, waye zai dauki nauyin karatun nata? Ga Abdallah nan kiri-kiri ya tare a garejin da alamu suka nuna nan zai kare rayuwar shi. A irin wannan lokuttan Habibu yafi fadowa Sa’adatu a rai, harma da Hajiya, dan tana da yakinin da suna raye inta nuna son karatun zasu kukuta su tsaya mata.

Sana’a kuma Abida ta gama cire mata sonta daga rai, tunda ta taso ta ganta tana sana’a. Amman ita bata ganin amfanin da sana’ar takeyi mata sam, da sun tashi kafin su tafi makaranta zasu tayata abinda zasu iya, da sun dawo ma wani aikin ne kafin lokacin Islamiyya. Ita zata iya rantsuwa ma in dai ba rashin lafiya ba, to bata taba ganin Abida ta kwanta da rana ba, da sunan baccin rana ko na safe dan ta huta ma ranta. Tsaye take kamar hakori tun asuba har wani daren, da tana mamakin yanda take iya tashi sallar daren da ta rigada ta zame mata jiki. Da kuma tayi tunanin irin wahalar da takeyi da rana, wahalar da take ciki ma a rayuwarta, sai ta ga tashi sallar daren kamar dole ne a wajen Abida, a wani gefen kuma babbar dabara ce. Dan zai zama asara ace kayi zaman duniya a wahale kaje lahira inda za’ayi na har abada can dinma kuma a wahale. Gara in baka samu ba anan, to ka samu acan din.

Amman ace tun asuba kake tsaye da sunan neman kudi, amman in aka dagaka aka zazzage babu wani abu na kudi da zai fado, idan aka shiga dakinka babu wani abu da zai nuna cewa bakin rai bakin fama nema kake, ko leshin da zaka fita kunya a taro baka dashi. Nama ma sai kayi watanni bakaji dandanon shi a bakinka ba, ina amfanin irin wannan sana’ar? Shisa Sa’adatu ko a mugun tunani bata son hada kanta da wata sana’a, ko da Fa’iza tayi mata magana, cewar ta bar mata layi daya a fridge dinsu ta dinga kankarar madara tana siyarwa, dariya tayi, itama Fa’izar da take wuni kitimilin zobo nawa ne ribarta? Duk kwana biyu takeyin sabo, ga wankin robobi, kuma da yake su Nana suna tayata, sai ta dauki wani abu a cikin ribar ta basu.

“Nifa ba zan iya sana’ar da a rana ba zata kawo mun ko da dubu daya ba…kokarinki nake gani Fa’iza.”

Da Nana tace ita zatayi, tana da dubu daya, Abida ta kara mata dari biyar, Abdallah ma ya kara mata dari biyar ta hada dubu biyu, ta fara dasu, tana jin Abida na fadin.

“Allah yasa ki fara a sa’a Nana, ita sana’a dadi ne da ita, in kuma ka saba ko aure kayi ka huta.”

A kalmar karshen ne ma tayi murmushi mai dan sauti, don abin ya bata dariya, tausayin su duka kuma ya kamata. Hutu a wajen talaka shine iya sana’a kenan? Ka fara tun daga gidan iyaye, kaje can ka dora? Su basawa kansu fatan samun hutun da basu samu a gidan iyaye ba, su same shi a gidan aure? Ta dauka ma Abida zatayi mata fada kan kinyin kankarar sai taji shiru, hakan yayi mata dadi. A rana daya inta fita zance, wani na iya bata dubu biyu, danma Abdallah ya hanata tara samarin, kuma bata ma haduwa da masu kudi, amman tana jin labarinsu a wajen kawaye a makaranta, yanda saurayi zai iya daukar dubu goma ya baka a lokaci daya. Kuma ba’a dade ba da nan bayan layinsu yarinyar ta auri wani hamshakin mai kudi, lefe ma akwati saiti uku aka kawo. Babu mamakin da Sa’adatu batayi ba da Nana take bata labari, dan ajinsu daya da yarinyar a Islamiyya, kuma sunje ganin lefen tare da sauran ‘yan aji.

“Wai wannan filingar yarinyar akayiwa akwati seti uku Nana?”

Dariya Nanar tayi.

“Saima kinga kayan ciki wallahi, ba na nuna miki wannan turaren da mai ba data bamu, tace shi yace ta rabar da duk abinda ta ga dama, zai kara sai mata…”

Jinjina kai kawai Sa’adatu take cike da mamaki da kuma tayata murna, dan in akwai wani hali guda daya da take dashi shine, bata bakin ciki da ganin wani ya samu, matsalarta tunanin yanda zatayi ta samu irin shi ko fiye da hakan ne abinda yake fara zuwa mata.

“Kingansu an jera a dakin nan nasu da ko leda babu sai tsohuwar tabarma, ke rabo mafa wani abu ne daban.”

Hango dakin Sa’adatu ta dingayi a idanuwanta, da gaske rabo wani abune daban

“Ko ina ta hadu dashi?”

Ta tambaya, mamakinta na ninkuwa da Nana ta amsa da,

“Ance akwai ‘yar uwar Mamanta, to masu kudi ne, a Abuja ma suke da zama, da sukaje ne ta hadu dashi can.”

Maganar sai ta zauna mata, ashe da gangan take tunanin yanda ake bata haduwa da masu kudi irin wannan, to ina zata hadu dasu? Tana cikin Bachirawa, a lungu, gidajen ‘yan uwansu kaf a cikin unguwanni ne irin Bachirawa, cikin lungunan da sai tsananin rabo Samarin cikinsu zasuyi irin arzikin da take hasashe, balle ace ko abokansu zasu dinga kawo musu ziyara, su kuma su hadu da irinsu har a kulla wata alaka. Da Asiya bata watsar da ita ba, sai ta sa ran haduwa da irinsu ta bangarenta. Tun bata san tana da kyau ba take jin mutane na fada, ana magana kan yanda babu me kyanta duk dakinsu, tana girma kuma yanzun tana ganin bambancin da take dashi da sauran ‘yan uwanta, musamman a halittar jiki. Tana da kyawun da masu kudi zasu iya gani su biyota. Ko ta wacce fuska, kowanne zaren mafita ta kama, yanayin rayuwar da ta taso cikine yake kara nisan da yake tsakanin su.

Jikinta ya fara sanyi kuma, wani sanyi da bata da fassarar shi, ko da ta tashi safiyar juma’a bata tsammaci tazo mata da wani bambamcin da sauran ranakun da suka gabata kafin ita ba. Kuma tun safiyar ta kula da haka, kokon da akayi jiya, shi akayi yau, batajin sha, a wajen Fa’iza ta samu ruwan Lipton din data dafa, yana ta kamshin citta da kanamfari, sai ta aiki Sadiya ta siyo mata biskit ta hada dashi ta fita. Data dawo kuma tayi karyar ciwon kai saboda batajin yin wani aiki ta karar da karfinta, shinkafa ce fara da manja da yaji akayi, ko dan ganye basu samu ba, Fa’iza bata dafa komai ba, itama shinkafar taci, Furaira da ba zama ta cikayi ba, tana bar musu komai da zasu bukata. Da yake macece mai sanin ya kamata, kuma su Fa’iza na gaya mata irin dawainiyar da Abida takeyi dasu, kayan abincin tana diba ta bawa Abida tace a kara. Da farko Abida taki karba.

“In dai da gaske an zama daya kamar yanda kike nunawa su Fa’iza ki karba dan Allah, ni dake munsan ba zan taba biyanki da komai ba Abida, ko fitar da nakeyi hankalina a kwance sanin yaran nan na tare dake wallahi ya isheni yi miki godiya kullum, sunce ba wani girki sukeyi ba daban, ki karba mu cigaba da addu’ar Allah ya kara rufa mana asiri.”

A sanyaye ta karba, idan nama Furaira zata shigo dashi to in suka dafa gida biyu take rabawa ta basu Abida rabi, sanin ya kamatanta ne ya hadu da kyautatawar Abida, shisa zamansu ya kara dadi. Ga yaranta ma rashin zamanta tare dasu ko yaushe baisa tarbiyarsu ta samu tangarda ba, Sa’adatu batajin dadin rashin girkin nasu, gani takeyi tunda sunfi su wadata, in zasu dinga girki zai bambanta da nasu, ita kuma zata samu. To an dafa shinkafa da manja, shinkafar ma ta Hausa, da daddare kuma tuwo za’ace ayi ta sani. In ba Abdallah ya kawo mata wani dan abin ba, bata da kudi da yawa a wajenta, ba taci abu mai gina jiki ba, ba zata karar da dan karfinta wajen aiki ba.

“Allah ya kawo sauki, saiki samu panadol ki sha.”

Abida tace mata tana cigaba da gyaran barkonon data baza a cikin faranti, ta amsa da ta sha tun a makaranta ta shige daki ta cire kayan makaranta ta dauko wayarta ta kunna tana bin katifa. Hannunta ya latso wajen kira, sai taga lambar Tahir ta fito a sama, alamar shine karshen kiranta. Sai ta tsinci kanta dasa hannu ta shafi sikirin din wayar, kewar shi kuma tana dirar mata. Tana tuna bai kirata ba jiya, ita kuma bata da kati a wayar, harta karbi wayar Fa’iza ta fara danna lambobin shi saita fasa kuma, haka kawai taji bata son kiranshi da wayar Fa’iza, in ta gama zata iya gogewa, amman shi daga nashi bangaren, bata son lambar Fa’iza a wayar shi. In za’a tsareta kuma bata da wani kwakkwaran dalili daya wuce taji a ranta bata so. Dalilin rashin kiran nashi take ta tunani a ranta har bacci ya kwasheta, saida Fa’iza ta tasheta don la’asar tayi ne tana alwala ta tuna tayi mafarkin Tahir ya kirata. Da tayi sallah sai ta fito tsakar gidan, ganin aiki duk ya kacame musu, sai taji ba zata iya langabewar da taso yi ba.

Musamman hango Abida da mafici tanata fama fifita gawayi, saita karasa tana fadin,

“Tashi kiga Amma…”

Kai Abida ta girgiza mata.

“Ke da bakyajin dadi, gawayin ne wannan buhun duk lema, da daddare zan baza shi kafin safe ya sha iska In shaa Allah…”

Take fadi, Sa’adatu ta mike hannu ta karbe maficin.

“Da nayi bacci kinga banma tashi da ciwon kan ba, tashi kiga, daman kefa Amma ko ba jikakken gawayi bama sai kiyi awa bai kama ba.”

Hararta Abida tayi.

 san dai tun kafin a haifeki nake kunna gawayi dai ko?”

Sosai maganar ta ba Sa’adatu dariya, ta san daman sai Abida ta fadi haka.

“Kuma tun lokacin sai kin kai awa bai kama ba, gawayin ne tunda can ma ya san ‘yar ki zata samu kudi ki koma girki a gas, shisa yake miki gardama…”

Wannan karin Abida ce tayi dariya, akwai wannan bangaren na Sa’adatu, tsokanarta da Abida kadai take gani, sai kuma Abdallah jefi-jefi saboda tana da saurin fusata, bata cika wasa da ssuran ‘yan gidan ba. Suma ba ko yaushe suke sakata a shirginsu ba tunda sun san hali, fadanta dai ba ko yaushe yake rabuwa ba, Abdallah ne kadai idan tana fada yaja hannunta take binshi, amman ko bakin Abida zai tabo bango ba zata daina ba, in dukanta tayi ma a wajen zata kafe ba zata gudu ba ko kasheta zatayi. Tana da wannan taurin kan da kafiyar da Abida ta koma binta da addu’a akai tunda dukan da fada duka sunki aiki. Duk wannan halayen nata, a cikin yaran duka itace take tsokanarta fiye da kowa, ta mayar da ita kamar wata kakarta, kuma zatace a cikinsu duka, Sa’adatu ce idan ta samu abu take nufota kai tsaye, sai dai fadan da take yawan yi mata kan kwadayi ya dakilar da wannan dabi’ar tata. Sai dai wani lokacin zata zo da abu tace mata.

Kudin makarantata ne dana tara Amma, dan Allah kiyi zamanki a daki kici, karki ba kowa.”

Hasashen Sa’adatu na zatayi kudi kuma, duk wani buri da zata furta shi ya iso kunnuwansu to akan irin hutun da zata samarwa Abida ne.

“Amma yarinyarki fa in tayi kudi kullum sai kinci kaza.”

In kayane ta gani a wajen wani zatace,

“Wani leshi nagani Amma, zai miki kyau, bari dai kudin ‘yarki suzo.”

Har wani lokacin saita tankata da

“Wannan kudi Sa’adatu ai tun kafin suzo ma sun gama karewa a lissafi, ni kadai an gama kashemun su”

Ranar kuwa wuni zatayi fara’a in ba wani ya tabota ba.

“Ai suna da yawa Amma, ba kananan kudade bane ba.”

Cikin kankanin lokaci sai ga gawayin ya kama,

“Tuwo za’a ayi ko? In dora.”

Ta fadi tana daga kai ta kalli Abida da ta girgiza mata kai.

“Fa’iza tace Ayyar su tayi waya, mu siyo kuli-kuli a daka, ta riga ta siyo gurasa kuma da yawa, to ita zamu ci da dare.”

Wani kayataccen murmushi daya fito daga kasan zuciyar Sa’adatu ta kawata fuskarta dashi.

“To kije ki zauna kawai, bari in wainar filawar.”

Kai Abida ta girgiza.

“Barni in soya, ki fara gurzamun kwakwa kafin su Nana su gama aikinsu sai su tayaki”

Yau batayi mita ba ta tashi, saboda farin cikin gurasar da zasuci. Amman babu abinda ta tsana irin gurza kwakwar nan, zai wahala kayi ka tashi batare da ka gurje yatsu ba. Daman tun sanda ta kone da suga bata kara nufar inda ake aikin kwakumetin ba, sai dai ta tsaya a gurza kwakwa da taya daurawa. Bata san ko dan sana’ar gidansu bace shisa bata dameta ba, ko bata akayi sai tayi sati cikin jakarta tana ajiyarta. Yau cikin nishadi take aikin, suna hira dasu Fa’iza da take aikin zobonta, tana ganin wani a gefe cikin dan bokiti, yafi sauran kauri da jin sikari dama duk wasu filebo da take amfani dashi.

“Ni dai ina son roba daya, amman na cikin dan bokitin can za’a dibar mun”

Cewar Sa’adatu tana kunshe dariyarta, Fa’iza ta harareta tana dauke kai kamar bataji ba. Ta san wa za’a zubawa na cikin bokitin, Abdallah ne, robobin shi ma daban suke, guda biyu haka zata cika masa, shikuma sai yace saiya bada kudi, haka suke wannan diramar yanzun. Fa’iza ta dauka tana boye abinda takeji akan Abdallah, ta dauka babu komai a fuskarta in yana waje daya wuce matsayin shi na Yaya, ashe ba haka bane ba.

“Kuma kinsan bashi da budurwa.”

Sa’adatu tace mata wani dare suna zaune.

“Wa?”

Ta tambaya zuciyarta na bugawa.

“Yaa Abdallah mana, kuma ni ina jam’iyarki koma yana da budurwa saina rushe gwamnatinta na kafa taki.”

Ta danyi jim, kamar ba zata amsa ba, saboda batama san me zatace ba.

“Nafa gani, kuma banajin ni kadai ce Fa’iza, kowama ya gani, Yaa Abdallahn ne karshe, amman tunda ya ganki shikenan… Alhamdulillah.”

Saita mayar da bakinta ta rufe, kalaman da tayi nufin fadi suka koma mata. Ya ganta? Da gaske ya ganta? Ya kalleta da irin idanuwan da take kallon shi? Anya kuwa? Yanzun yana kallonta in zai mata magana dai, sabanin da, zai amsa gaisuwarta ne a takaici batare daya kalleta ba kuma. Yanzun bayan gaisuwar yana tambayar yanda ta wuni, yana tambayarta Islamiyya, yana dan tsayawa kamar yana neman abinda zai sake tambayarta don su cigaba da magana, jiya dai daya sake shigowa ya ganta yace,

“Zobon yau yafi na kullum dadi, ko an kara wani sinadarin ne?”

Sa’adatu da take gefenta ta rada mata,

“Sinadarin soyayya”

Tana saka wata matsananciyar kunya lullubeta, duk da tasan Abdallah baiji ba, da kyar ta iya girgiza kai tana furta,

“Ba abinda na kara fa Yaya”

Yayi murmushi yana jinjina kai

“Ai kuwa yayi dadi. Allah ya kara kawo ciniki mai albarka”

Ta amsa da amin tana wasa da yatsunta, ta karanta labarai kala-kala na soyayya, haka ta kalli fina-finai mabanbanta. Ta dauka ta fahimci menene soyayya, hasashenta bai hango mata wannan bugun zuciyar da giccin Abdallah kawai kan haifar mata dashi ba,yanda murmushi kawai idan yayi, ta san dominta ne sai jikinta ya dauki dumi, da ake magana ma akan fadawa soyayya daga kallo daya, dariya abin yake bata. Ashe da gaske ne, yana faruwa da gaske. Sunzo gidan nan, filin da aka tanada a zuciyarta don soyayya wayam ta shigo dashi, kawai ta daga ido ta sauke akan Abdallah ta sauke tare da jin shi zaune a wannan filin, ya bude baki muryar shi ta dira cikin kunnuwanta tana sata ji kamar ya sake samun wasu wajaje ne banda iya filin nan, ya mike kafafu sun karasa wani waje da batasan da zaman shi ba. A hankali kuma, ranaku suke wuce mata da mamakin yanda za’ace har yanzun Abdallah yake samun sababbin wajajen zama a zuciyarta, zuciyar nan fa, tilon zuciyarta da bayan shi akwai wasu abubuwan daban, daman tana da girma ne har haka kuma ace a cikin kirjin nata ma ba duka bane ta mamaye?

“Zan samu zobon ko ba zan samu bane in hakura?”

Maganar Sa’adatu ta fisgota daga tunanin da takeyi.

“Yau ban niyyar siyar miki ba to, ki aika gidan Namadi.”

Nana ce ta kwashe da dariya.

“Tafdin, aiko suma nake aka watsamun zobon gidan nan na farfado sai nayiwa jikina sabi uku.”

Dukkansu sukayi dariyar wannan Karin,

“Tsakani da Allah har mamaki nake da mutane ke shan zobon nan kuma su kwana lafiya. Rannan fa naje wucewa naga an siyowa wani mutum, daya daga robar ya kafa kai sai da hankalina ya tashi.”

Fa’iza tace, Sadiya na karbe zancen.

“Su kazantarsu ma tayi yawa, duk unguwar nan banajin akwai yaran da suka kai na gidan nan dauda”

Hira suka cigaba dayi, da suka karasa aikin zobon, suka kamawa Sa’adatu gurza kwakwar, da akayi Magriba kuma dakan kuli-kuli suka hau, wasu na yanka sauran kayan hadin gurasar. Ran Sa’adatu kal take jinshi, da aka aiko kiranta a waje ma haka tace aje ace bata nan, dan bata tuna sunyi da wani zaizo ba, saiya sake aikowa wai dan Allah tayi hakuri ta fito magana kawai zasuyi, taja wani tsaki.

“Kije kiga waye”

Fa’iza ta fadi tana kallonta.

“Ni fa banyi da wani zaizo ba yau.”

Fa’izar dai ta tausheta, dan hijabin Fa’iza ta saka ta fita, girarta a sama, ta turo bakin nan dan bata so fitar ba, ta kuma saka a ranta sallamar shi zatayi ya tafi, sai dai waige-waige ta farayi, dan bata ga kowa ba sai mota da take tsaye gefen gidan nasu, taja siririn tsaki tana shirin juyawa, yayi saurin bude murfin motar yana fadin.

“Sa’adatu…”

Da mamaki ta kalle shi, ya fito daga motar gabaki daya, jikin shi sanye da shaddar da hasken kwayayen lantarkin unguwar ya karawa daukar ido, bakine, mai matsakaicin tsayi.

“Afuwan…”

Ya furta yana karasawa inda take tsaye, saita tsinci kanta da gaishe dashi ya amsa yana sakw fadada murmushin shi

“Kiyi hakuri nayi miki wani irin zuwa…”

Har lokacin mamaki takeyi, itace akazo wajenta da mota yau? Ya akayi tun safe bataji a jikinta akwai bambanci tsakanin yau da sauran ranakun ba? Bama komai da yake fada bane yake karasawa kunnuwanta, ta daiji ya shigo unguwar wajen abokin shine ya ganta, to suna sauri shisa bai tsayar da ita ba, sai yau daya dawo ya bincika aka nuna masa gidansu. Tunani take wanene abokin shi a unguwar su? Akwai masu abokai irin wadannan daman a unguwar?

“Kiyi hakuri ki bani number dinki, in yaso sai muyi magana ki bani lokacin da zanzo”

Ya karasa yana zira hannu a aljihu ya fito mata da wata waya da tasan hasashen tsadarta ya wuce lissafinta. Ta kuwa saka masa lambar, yanayin da take ji na hana mata tabuka abin kirki, sai taji kamar ana kallonta, ta daga ido, ta sauke akan Tahir da zata rantse ta kara rantsewa bata taba ganin fuskar shi a irin yanayin da take ba yanzun, wani yanayi da ya kara ma bugun zuciyarta gudu. Musamman daya ga ta ganshi, yaja hannuwan shi duka ya saka a aljihu yana kafeta da idanuwan shi, sai taji kamar ya kamata tayi wani abune da ba dai-dai ba, kamar babban laifine tsayuwa da saurayin nan da ko sunan shi bataji ba har yanzun.

“Za muyi waya, ga Yaya na nan kar yayi mun fada.”

Ta karasa maganar muryarta na rawar da ta bata mamaki.

“Zan kira, duk da baki tambaya ba har yanzun sunana Yakub.”

Kai Sa’adatu ta jinjina tana sake kallon inda Tahir yake tsaye, sai da ta ga Yakub ya shiga motar shi ya kunna yaja ta sannan ta dan samu natsuwa, sai dai tana kallon Tahir din taga ya juya.

“Yaa Tahir…”

Ta kira tana bin bayanshi da sauri harta kusan kifawa saboda tuntuben da tayi da dutse, sai dai daya juyo saita tsinci kanta da matsawa taku biyu baya, tasan ba zai taba daga mata hannu ba, batama jin Tahir ko kannen shi ya taba duka, yanayin da yake cikin idanuwan shine suka sata son samar da tazara a tsakanin su.

“Yaa Tahir.”

Ta sake furtawa cikin rawar murya, sai dai baice komai ba, kallonta kawai yakeyi, duk wani kwantaccen so da yake yi mata na taso masa. Bai taba rubuta jarabawa da karsashin daya rubuta wannan ba, saboda yanajin itace ta karshe, duk wani buri da yake dashi akanta zai cika, musamman da Bashir yace masa ko yana da ra’ayin aikin force, har ranshi bashi da wannan ra’ayin, baima taba hango shi da kaki ba, saboda mutum ne shi da bayason hayaniya. Amman yanayin kasar na waka sani waya sanka, samun aiki mai kwari wahala yakeyi, ga Aminu nan ya gama bautar kasa, sai fafutuka yakeyi, Baban su dai ya karbi takardun yace wani abokin shi yace ya kawo, za’a samo masa a Gt Bank. Shi kuwa anya zai iya aikin banki? Akwai takura sosai duk da ba laifi albashin su yana da kyau.

“Anya aikin force kuwa Bash.”

Kai Bashir ya jinjina masa.

“Nima maigida ne fa yake mun magana, kasan ana bashi damar kawo sunayen mutane lokaci zuwa lokaci, da yayi mun magana nace zan tuntubeka ko kaima kana so, da mun karbo takardun sai mu bashi.”

Numfasawa ya yi.

“Ina jinjina abinne dan ban taba hangoni da kaki ba.”

Bashir yayi dariya.

“To ni ance maka na taba hangoni ne? Amman Mariya tayi mun halacci, ko kai ka sani, shekara biyar ba nan bace, bayan ga wanda suka shirya nan suna ta fitowa, ta kafe saini, idan na tsaya ruwan idon aiki zan kara sakata jira ne, tunda wannan din yazo watakila shine mafi alkhairi.”

Sosai yake juya maganganun Bashir, sai fuskar Sa’adatu ta fado masa, sai yaji dariyar nan tata a cikin kunnuwan shi.

“Banda dai Police, kowanne amman banda dan sanda.”

Ya tsinci kanshi da fadi, duka saboda itane kuma, wuta mai karfi aka kawo duk tayi musu barna, harda wayar shi a ciki, shisa jiya bai kirawota ba, ya danne zuciyar shine sanin yau din zai ganta. Zai kuma bude mata sirrin da yake zuciyar shi, wani abu kuma na karfafar shi da cewar ba zata tankwabe soyayyar shi ba. Sai ya ganta tsaye da wani, sai ta taso masa da wani kishi da bai taba sanin yana tare dashi ba, dan har wani duhu-duhu yake gani, zuciyar shi na radadi kamar an kara masa kyandir din da yake ci da wuta.

“Yaa Tahir.”

Sa’adatu ta kira da roko a muryarta.

“Kar in katse miki soyayya Sa’adatu, kije kawai.”

Ya iya furtawa idanuwan shi cikin nata da yake hango maikon hawaye.

“Wallahi banma san shi ba, kaga ya tafi, ni bansan shi ba, sai da nace ba zan fito ba, Fa’iza ce tace in fito in ga ko waye…ban san shi ba Yaa Tahir…”

Ta soma koro masa bayanin da bata san daga inda yake fitowa ba, kallon da yake mata na sata jin girman laifin da tayi masa, laifin da bata san zataji tayi ba.

“Me yasa kika fito to?”

Kai ta girgiza masa.

“Kayi hakuri, ba zan kara ba.”

Ta fadi, muryarta na komawa cikin kunnuwanta da wani yanayi, kwakwalwarta na son jefo mata tambayar ba zaki sake me ba? Tsayawa da Yakub? Ko tsayawa da kowa duka? Me kike cewa?

“Bashi kadai ba.”

Tahir yace yana kara saka idanuwan shi cikin nata.

“Kowa ma.”

Ya dora.

“Bana son in ganki da kowa ne…saboda ina son ki.”

Kafafuwanta rawa sukeyi mata, wani yanayi ne ya lullubeta, ba iska akeyi ba, kalaman Tahir na karshene suke fifitata.

“Abinda nazo in fada miki kenan yau Sa’adatu, ince ina son ki.”

Ta ga alama ba kafafuwanta kawai yake neman kashewa ba, har numfashinta yake farauta yau. Sau nawa ta hasaso kanta dashi? Sau nawa ya haska a idanuwanta ya dishe, ya kuma sake haskawa? Sau nawa Abida tayi mata magana akan Tahir din? Ta tambayeta ko soyayya suke saboda tana tsoron abinda zaije ya dawo, tana ce mata a’a, tambayar kuma tana sakata hasko kanta da Tahir din, ko Fa’iza ta sha yi mata magana sai tace mata ba soyayya sukeyi ba, tunda bai taba cewa yana sonta ba, itama kuma batajin tana masa irin wannan soyayyar, yau daya furta mata sai take tana shirin narkewa ta sulale kasa gabaki daya, ya bude bakin shi zai sake magana hon din motar da akayi a bayan shi yasa shi mayarwa ya rufe, yana kuma juyawa don ganin dalilin da zaisa ayi wannan hon din alhalin daga shi har Sa’adatu ba’a kan hanya suke ba.

Sai yaga Bashir, daman sunyi ya same shi anan gidansu Sa’adatu ne, zasu wuce asibiti duba Yayan Bashir din da aka kwantar, numfashi ya sauke yana kallon Sa’adatu da kanta yake a kasa.

“Za muje dubiya da Bash, wayata ta lalace, amman zan kiraki mu karasa magana…”

Ta dago, sai dai ta kasa cewa komai.

“Bari ku gaisa da Bash.”

Ya karasa maganar yana takawa zuwa wajen motar, sai Bashir din kuwa ya gyara packing ya fito yana karasowa inda Sa’adatu take tsaye.

“Malama Sa’adatu, barkanki da dare”

Daga kai tayi ta kalle shi, taji Bash a bakin Tahir harta bace lissafin lokuttan, ta kuma hasaso shi a kanta, sai dai ba haka tayi tunanin shi ba sam. Ta san za’a kalli Tahir ace yana da kyau farat daya, Bashir na daya daga cikin mutanen da idan ka kalle su zaka fara tsamar abubuwan da suke da kyau a tare dasu, kafin inka nutsu zaka hade abubuwan nan duka waje daya kana tunanin kalmar da zata alakantasu da ita, kamar kyau ba zai dauka ba, akwai kwarjini kuma, kwarjinin daya sata sauke idanuwanta. Sannan a madadin Tahir da za’a ce yana da sanyi, sanyin da zaka fahimta a kallon farko, Bashir yayi hannun riga da wannan sanyin, kamar ruwa ne da kankara a waje daya.

“Ina wuni.”

Ta furta da sanyin murya, ya amsa mata yana dorawa da,

“Zan dauke shi, kiyi hakuri, In shaa Allah in zai dawo ni zanzo in sake kawo miki shi”

Murmushi karfin hali tayi.

“Bakomai, yace zakuje dubiya ne… Allah ya kara sauki yasa kaffara ne. Na gode.”

Shima godiyar yayi, kafin Tahir ya kalleta yace.

“Ki koma gida, zan kiraki.”

Jinjina masa kai tayi tana juyawa, sai dai da taji karar tashin motar su saita juyo, sai dai Bashir ne a gefen ba Tahir ba, ta sauke numfashi.

Bashir

Bashir da bata taba tunanin zai taka wani matsayi daya wuce na abokin Tahir ba a rayuwarta.

<< Tsakaninmu 5Tsakaninmu 7 >>

2 thoughts on “Tsakaninmu 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×