Skip to content
Part 9 of 66 in the Series Tsakaninmu by Lubna Sufyan

Fa’iza ce ta shigo dakin da Sa’adatu take zaune, daga can gefe, jikinta sanye da doguwar riga ta atamfa.

“An daura Sa’adatu, yanzun su Yaya Abdallah suka dawo…kinga.”

Ta karasa maganar tana nunawa Sa’adatu fararen goro kal dasu har guda biyu, ta karasa ta kamo hannun Sa’adatun daya sha kunshi ta saka mata goron a ciki tana fadin.

“An daura…kin zama matar Tahir.”

Goron taji da dumi a cikin hannunta, daman idanuwanta na kan wayar da take cinyarta, tana ganin karfe sha daya na safe, taji wani sanyi na ratsa duk ilahirin jikinta, kafin bugun zuciyarta yayi kasa, su biyun suna tabbatar da wani abu mai girma na shirin faruwa dasu. Numfashi taja ta fitar, ta sake ja ta fitar, kafin ta sake jan wani wayar dake jikinta ta hau ruri, tana dubawa taga Tahir ne, dayan hannunta tayi amfani dashi ta daga wayar, dayan na dumtse da goron da Fa’iza ta saka mata.

“Sa’adan Tahir…”

Ya kira, tana jin farin cikin da yake cike da muryar shi.

“Matata…”

Ya sake furtawa muryar shi a karye wannan karin, yanda tsikar jikinta ta tashi, sai taji hawaye ya ciko mata idanuwa.

“Nagode, da kika jure komai, da baki karaya ba, nagode da kika zama tawa. Zamu taho gidan ne yanzun, kice Fa’iza ta kulamun dake.”

Dan murmushi ta iya yi mai sauti, hawayen dake idanuwanta na silalowa, ta sauke wayar daga kunnenta.

“Ki tashi ga kayan da zaki sake can na fito miki dasu.”

Cewar Fa’iza.

“Ina amaryar take?”

Amira kenan data dago labulen tana dariya.

“Ta zama ta zama, yarinya ta zama ta zama…”

Dariya Fa’iza tayi.

“Dan Allah Yaa Amira karki saka mana ita kuka.”

Itama dariyar takeyi.

“Wanne kuka? Ba ita tace tana so ba? Yarinya ke kikace kina so, da baki ce kina so ba…”

Nabila ce ta kama hannun Amira tana janta.

“Ki zo mu kulla alale kika tsaya nan tsokana.”

Nabilar bata barta ta kara cewa komai ba, ta janyeta daga bakin kofar, hakan ya bawa Fa’iza daman kama hannun Sa’adatun itama tana taimaka mata ta mike.

“Da nan kika kawomun kayan ma Fa’iza tunda kinga ba kowa…”

Kai Fa’iza ta jinjina tana ficewa daga dakin, nan ta dauko mata kayan. Doguwar rigace ta farin lace da akayiwa ado da ratsin ruwan toka kadan, ta gama sakawa kenan, yarinyar da zatayi mata kwalliya ta shigo, layi hudu ne a tsakaninsu, ta iya sosai, shisa take yanga, in ba ka isa ba, ba zata bika gida tayi maka kwalliya ba, sai dai kai kaje studio dinta da yake cikin gidansu. Randa sukaje ita da Fa’iza, jininta ya hadu dana Sa’adatu, hira suka dingayi kamar sun san juna. Dole Fa’iza ta koma gefe, taji yanda suke magana suna saka turanci, su duka suna lankwasa harshe kamar zasu tauna shi, kwata-kwata batayi mamakin yanda Sa’adatu take turancinta ba, tunda itama shaidace a zaman da sukayi, na irin nacin Sa’adatu akan koyon turanci.

“Amarsu.”

Salima mai kwalliya bayan ta shiga dakin, hadi da ajiye akwatin kayan kwalliyarta. Murmushi Sa’adatu tayi mata, kafin su gaisa. Da yake tace kwalliyar mai sauki take so, cikin kankanin lokaci aka gama, aka kafa mata daurin daya fito da ita a amaryarta.

“Ma shaa Allah, kinga yanda kikayi kyau kuwa? Kamata yayi ace a studio dina ne yanda zan haska miki hotuna masu kyau.”

Godiya tayi mata, bata wani jima ba ta tafi, tace akwai wanda suke jiranta zatayi musu kwalliya.

“Kinyi kyau sosai Sa’adatu, wallahi baki ga kyan da kikayi ba.”

Fa’iza ta fadi tana daukarta hoto da waya. Hawayen da suke mata barazana take ta kokarin mayarwa. Da taji ana.

“Ga angwayen nan…”

Sai bugun zuciyarta ya karu.

“Allah ya sanya alkhairi Tahir…”

Ta sake ji kafin taji.

“Fa’iza kuna ina ne? Ku fito mana.”

Itama tayi kyau cikin leshinta ruwan toka, duk da batayi kwalliya ba, Salima ta daura mata dankwalinta. Kama Sa’adatu tayi suka fito, kowa nata yaba kyawun da tayi, suka dan tsaya a gefe, saboda anata hotuna da Tahir. Ji tayi an rike hannunta, ko kafin ta daga kai tasan Abdallah ne, ya dan dumtsa kamar yana son bata kwarin gwiwa, kamar kuma shi kadaine ya fahimci girman ranar a wajenta, kamar shi kadai yasan halin da zuciyarta take ciki.

“Idan Yayaa Tahir mijinkine, Sa’adatu saikin aure shi, wallahi babu wani daya isa ya hana auren nan…”

Kalaman shi suka dawo mata.

“Komai zaiyi dai-dai In shaa Allah, bana son wanna damuwar da kikeyi.”

Ta sake jin wasu kalaman nashi sun dawo mata, da kanshi ya jata yana kaita kusa da Tahir, ya kamo hannun Tahir ya saka a cikin nata. Wani yanayi ya kaiwa zuciyarta duka. Komai na dawo mata kamar yanzun yake faruwa.

“Mama taki kwantar da hankalinta Sa’adatu, Mama tana barazanar yi mun baki…”

Tunda aka fara maganar aurensu, tunda kuma Asabe ta rantse ta sake rantsewa sai tayi duk wani kokari wajen ganin bata barsu sun huta ba har sai sun hakura da juna, shine mai karfafa mata gwiwa, shine mai kwantar mata da hankali lokacin da ta fara dagashi, ganin hargagin Asabe ba iya hargagin yake kokarin tsayawa ba, so take ta shiga tsakaninsu, amman ranar sai taji rauni a cikin muryar shi da har rawa take.

“Tace in zaba…”

Ya cigaba yana saka zuciyarta dokawa kaman zata fito waje.

“Tsakaninku, Sa’adatu tace in zaba, ta kasa gane ita dince a saman duk wani abu da addini bai haramta mun ba…ya zatace in zaba?”

Ya karashe cikin karamar murya, kanshi a kasa kamar mai neman wani abu.”Yaa Tahir…”

Ta kira bayan wasu dakika ganin bai dago ba.

“Yaa Tahir…”

Bai dago ba har lokacin, sai da tayi masa wajen kira biyar, ana karshen ma muryarta da take rawa alamun kuka takeyi ne yasa kashi dagowa, wani siririn hawaye ta idon shi na dama ya silalo masa, ya saka hannu ya dauke shi.

“Kiyi hakuri, dan Allah kiyi hakuri, da na san haka abubuwa zasu juye mana, dana soki ni kadai, daga nesa, da ban matso kusa na daga burinki da nawa a tare ba…”

A matsayinta na musulma, mutuwa na fado mata a rai lokaci zuwa lokaci, idan ma taji anyi rasuwa zata iya cewa tana wuni da abin a ranta, musamman ma irin rasuwar nan ta lokaci daya. Ko Habibu tazo yiwa addu’a bayan kowacce sallah sai tunanin tata mutuwar ta gifta mata. A cikin abubuwan da take hangowa zasu iyayin ajalinta, ko kusa babu Asabe, ko da ta fara hargaginta ma bata dauke shi da muhimmanci ba, tunda ta tabbatar da son da Tahir yakeyi mata, itama tasan irin wanda takeyi masa. Ashe Asabe na da karfin da zata iya yin ajalinta ta hanyar rabata da Tahir, tana da wannan matsayin, mahaifiya ce, mahaifiyar da Tahir yake yiwa kaunar da bai hadata da komai ba.

“Da zan iya dana shiga da kaina na yiwa Amma bayani, amman ba zan iya ba, bani da wannan kwarin gwiwar.”

A karo ma farko data shige gida tabarshi a tsaye batare da sunyi sallama ba, ta kuma nufi Abida kanta tsaye tana zama a gabanta, kafin ta dora kanta akan cinyoyin Abida, numfashinta na wani irin fisga, kukane yake son kwace mata, daga kasan zuciyarta da take rarrabewa kashi-kashi take jin tasowar shi, shisa yaketa mata wahalar mallaka, lokacin da ta samu ta kwato shi ya fito fili, kirjinta taji kamar zai kama da wuta saboda zafin da yakeyi, Abida hannu kawai ta dora a bayanta tana shafawa cikin lallashi batare da tace mata komai ba. Kuka tayi har saida zazzabi ya rufeta, anan jikin Abida tayi bacci, ranar a dakinta ta kwana. Zazzabi ta tashi dashi washegari sosai, dan da Fa’iza ta hada mata ruwan shayi ta sha, amai ta dinga shekawa.

Abdallah ya dauketa suka tafi asibiti, jikinta yayi laushi sosai, ko daga zaunen da take ma jiri take gani. Likitan ya dinga fada ganin jininta ya hau.

“A wannan shekarun tunanin me kika saka a ranki haka?”

Kai kawai ta sadda tanajin hawaye na tarar mata.

“Ku me kukeyi mata? Ya za’ayi jininta ya hau haka? Shekara sha takwas…riketa zamuyi gaskiya, sai ta huta sosai, dan ba wani maganin hawan jinin da zan dorata akai tukunna, ta kwana biyu a asibitin muga ko zai sauka.”

Riketan kuwa sukayi, saida aka gama komai tukunna Abdallah ya kira Abida yake fada mata an kwantar dasune, dole suka kullo gidan suka tafi gabaki daya, dan Jidda itama tace ba zata zauna ba, Fa’iza ma haka, ba zaiyiwuwa kuma abar Asma’u ita kadai ba. Kafin yamma har Nana da Nabila sai gasu a asibitin. Ganin yanda suka cika dakin da mutum takwas ne a ciki, kasancewar shi asibitin gwamnati, ga hayaniya da suke tayi, Fa’iza tace ita zata kwana, sai Abida ta hada kawunan su Jidda suka wuce su. Amman a lokacin duk wata hira da sukeyiwa Sa’adatu murmushin karfin hali kawai takeyi, tana kokarin amsa musu ganin irin damuwar da suke ciki.

Abinda bata sani ba shine, Tahir ma yana asibitin, daya koma gida ya shige dakin shi, washegari da asuba, ya fito daga masallaci ya yanke jiki ya fadi. Abdallah ya kira wayar shi, Aminu ya daga yake fada masa, a karo na farko daya tare mai mashin saiya tsinci kanshi da bada kwatancen unguwar da Asabe take aure, ya san gidan, dan ya raka Sadiya da tazo tayi dare, sai dai bai shiga ba, mai adaidaita sahun daya ajiyeta, shi juyawa yayi dashi.

“Ina kofar gida Mama…”

Ya furta muryarshi can kasa bayan ya kirata a waya.

“Abdallah? Wanne kofar gidan? Kofar gidana?”

Kai ya daga kamar tana ganin shi, jin tayi shiru yasa shi kwato.

“Eh.”

Da kyar, daga kasan makoshin shi.

“Ka shigo, kacewa maigadi wajena kazo zai bude maka kofa, bari in fito.”

Ta karasa cike da doki, a harabar gidan suka hadu, fara’ar fuskarta ta dauke ganin yanayin shi da irin kallon da yakeyi mata.

“Lafiya? Abdallah? Me yake faruwa”

Ta jera masa tambayoyin dan ta tsorata da ganin yanayin shi, murnar da take ta zuwan shi, murnar da takeyi ta aikin da akayi mata na kwato shi daga wajen Abida ya fara ci duk ta dauke.

“Yaa Tahir na asibiti, ya fito masallaci dazun da asuba ya yanke jiki ya fadi…”

Kirjinta ta dafe, zuciyarta na dukan uku-uku.

“Na shigesu, faduwa kuma ni Asabe? Wanne asibitin? Ya jikin nashi?”

Numfashi Abdallah ya sauke,

“Sa’adatu ma tana asibiti, me yasa Mama? Menene aibunta? Kince ya zaba…koni kikace in zaba Mama kinsan ba abu bane da za’a auna a sikeli, amman zan rikeki a raina, duk idan na kalleki zanji zafin rabani da ‘yar uwata da kikayi saboda wani dalili da bai kai dalili ba…”

Kallon shi takeyi, mamakin shi na maye mata gurbin tashin hankalin rashin lafiyar Tahir.

“Idan baki tausayawa Sa’adatu ba, dan Allah, dan girman Allah ki tausaya masa shi tunda kinsan zafin shi, zaki cutar dasu, cuta mai girma idan kika rabasu, kuma ina tsoron Allah ba zai barki ba Mama, saboda baki da dalilin baya…”

Marin data wanke masa fuska dashi ya sa sauran kalaman koma mishi.

“Saboda Abida ta shanyeka zaka tsaya gabana kana fadamun wadannan maganganun Abdallah, kai kayi nisan da bacin raina ba komai bane a wajenka ko?”

Kallonta yakeyi, yana neman yafiyar Allah a cikin ranshi saboda kunyar halayenta da ya tsinci kanshi da ji.

“Abinda ya kawoka kenan? To idan ma ita ta turoka, ka koma kace mata bata isa ba wallahi…”

Juyawa kawai yayi batare da ya sake cewa komai ba, ya bar Asabe tsaye tanata bambami.

“Gaskiya kinyi sakaci, matar nan ba karamin lashe zuciyoyin yaranki tayi ba…sai kuma kin tashi tsaye.”

Abinda Malamin Uwani yace mata kenan, da aka kaita gidanta, ita kuma ta kira amintaccen mai adaidaitan ta, ya daukesu, can wani kauyene daga miltara ake dauke hanya, suna shiga suka zauna, kasa kawai ya bata ta dora hannunta akai, ya duba yace mata.

“Akan auren danki ne da bakyaso ko?”

Sai maganar nan tasa ta mika masa ragamar warwarewar matsalarta gabaki daya. Ya bata ruwan magani yace ta kurkure bakinta dashi, in dai tayiwa Tahir magana, ba zaiyi mata musu ba, sai gashi ya tashi daga zaman da yake ya durkusa a gabanta.

“Mama dan Allah, ki saka mana albarka, dan Allah Mama…karkice ba zan aureta ba, wallahi ina sonta, dan Allah ki saka mana albarka, bata da wani hali marar kyau, ko dan bakya gidan ne yanzun? Kin mantata?”

Ita Tahir yake fadawa halayen Sa’adatu, fitsararriyar yarinya mai bala’in taurin kai da zafin zuciya. Saboda shanyewar da akayi masa ba karama bace ba. Daman Malam yace mata an lashe masa zuciya saita tashi tayi da gaske, sai dai duk wani abu kamar yana bin iskane akan Tahir din, randa tace masa.

“Wallahi sai dai ka zaba, koni ko Sa’adatu, ka zabi wanda yafi maka sai inga albarka zan saka maka ko tsine maka zanyi in sallamawa Abida da Sa’adatu…”

Kuka ya rike kafafuwanta yanayi mata, Tahir, kamar yaro dan shekara biyu haka ya dinga mata kuka, kukan da maimakon ya karya mata zuciya saiya kara mata tsanar Abida, ya kara karfafa mata gwiwar koma menene tayiwa Tahir din saita ga karshen shi, har sauran yaran nata ma da take ganin zata iya bar mata su in dai Tahir na tare da ita, sai tabi ta rabasu. Ga Sadiya nan, tunda ta bata ruwan rubutun nan, ko maganar zuwa gidan ta dainayi kwata-kwata. Nana ma ta kirata akan maganar auren Tahir din da Sa’adatu, tayi mata zagin tsamar nama, ta kashe wayarta da fadin.

“Kema saura ke, tunda ba Abida tayi mun nakudarku ba.”

Barinta tayi ta gama da Tahir tukunna, Abdallah ma da alama tunda yana tare da Abida kullum, nashi kamar ma yafi na Tahir din karfi. Haka ta kwana tana juyi cike da takaici da wata irin tsanar Abida da duka zuri’arta. Data tashi da safe harkar gabanta ta cigaba duk kuwa da tafasar da zuciyarta takeyi mata. Da ta kira Alhaji Salihu a waya ya fada masa zataje duba Tahir a asibiti, ca yai mata tabari sai dare, saboda babu direban da zai kaita da rana, haka kuwa ya faru. Data kira wayar Tahir, Aminu ne ya daga ya fada mata asibitin da suke, wani na kudine nan kusa da unguwarsu, ita bata san shi ba, direban ma, saida suka tsaya suka dinga tambaya tukunna. Bacci Tahir yakeyi amman zaka iya ganin ramar da yayi akan fuskar shi, taja kujera ta zauna tana kallonshi, wani daci na taso mata, yaronta, danta mafi soyuwa a gareta, shine kwance a haka sanadin Abida.

Tunda yanzun kenan? Idan kuma ta bari ya shiga hannunsu ta hanyar auren Sa’adatu kuma fa? Ai watakila ganin shima wahala zaiyi mata, yana can yana bauta musu.

“Me likitan yace yana damun shi?”

Manyan idanuwan shi Aminu ya sauke a kanta.

“Da kai nake fa.”

Ta fadi ganin bashida niyyar amsawa.

“Jinin shine ya hau saboda damuwa tayi masa yawa…”

Shiru ne ya ratsa dakin, cikin wata irin murya Aminu yace mata.

“Yanzun idan zanyi aure nima sai yarinyar tayi miki kenan? Nima banda hankalin sanin abinda nake so…”

Bata amsa ba, saboda bata san me zatace masa ba.

“Me yasa sai yanzun? Mama mune muka nemoki fa, baki taba neman mu ba, baki taba zuwa kin duba halin da muke ciki ba, kina sonmu kika kasa hakurin zama da Baba ki rikemu? Tahir ya matsa, shi yace sai munje wajenki, tun tashinmu, zai wahala rana tazo ta wuce baiyi maganarki ba, da muka ganokin fadanki Mama, bai taba sakawa Tahir yayi nisa dake irin yanda nayi ba, nine babba, kinsan sau nawa Tahir ya zaunar dani yayi mun fada akanki? Mama idan na kiraki sau goma, takwas a ciki Tahir ne yasa, biyun ne nayi da kaina…ki kyaleshi, dan Allah ki kyaleshi ya auri yarinyar da yake so tunda shi zai zauna da ita.”

Yana karasa maganar ya mike ya barta ita kadai a dakin, tana juya kalaman shi, hawaye taji yana cika mata idanuwa. Shikenan, banda Uwani babu mutum daya da zai fahimceta kenan? Babu wanda zaiga gatane da soyayya take yiwa Tahir, kwatankwacin soyayyar da yakeyi mata. Itama bata kara jimawa ba, ta mike, dan ko motsi bata ga Tahir yayi ba, a bakin kofa ta samu Aminu a tsaye, batace masa komai ba, shima ko a sauka lafiya baiyi mata ba. A hannun kishiyoyi suka tashi, kuma daga irin labaran da sukaji, Asabe batayi zaman mutunci dasu ba, hakan baisa sunyi musu rikon banza ba. Ba dai kamar ace a hannun mahaifiyarka ka tashi ba, amman kuma ba’a watsar da lamarinsu ko an musu mugunta ba.

Saida ya balbale Tahir da fada.

“Kai ba zaka iya bude baki ka gaya mata Baba ya amince da zabinka ba, ka riga ka gaya masa, ita albarka kawai kake so ta saka maka.”

Cikin sanyin shi yayi wani murmushi da bai kai zuciya ba.

“Uwa ce Hamma, Uwa ce…”

Ya sani, ba saiya tuna masa ba, shisa yakejin wani irin ciwo a zuciyarshi, ya za’ayi ace tana Uwa tana wasa da farin cikin danta haka, rayuwarshi na kan layi amman nata son zuciyar kawai ta sani. Shisa ya kira Alhaji Hashim a waya ya fada masa duka abinda yake faruwa, dan baya gari a lokacin, yaje Abuja.

“Ita Asaben ce tace ba zai aureta ba? Akan wanne dalili?”

Dan daga kafadu Aminu yayi.

“Ita kadai tasan dalili fa, shikuma ya hakura, gashi nan ya yanke jiki ya fadi dazun, likita yace jinin shi ya hau sosai, damuwa tayi masa yawa, zai iya samun matsala.”

Yasan waye Alhaji Hashimu, kusan zaice ma harda soyayyar da yakeyiwa yaranshi duk kuwa da yawansu, yanda bai hadasu da komai ba, yasa suka kara samun riko mai kyau a gidan. Shi da ya saki mace ma akan danta dan ya zame mata gargadi, sai dakyar ta samu ta dawo gidan, ai yasan zai tsaya yayiwa Tahir abinda yake so tunda shi ya kasa.

“Dan zata kashemun? Wallahi bata isa ba, dana barku kuke zuwa wajenta, shine harta samu kwarin gwiwar hanashi abinda ni na rigada na amince…gobe zan dawo ai In Shaa Allah…ka lallaba shi ya kwantar da hankalin shi.”

Bakinshi Aminu yaja yayi shiru, baima fadawa Tahir ya kira Alhaji Hashim din yayi masa bayanin abinda yake faruwa ba. Washegarin kuwa ya dawo, Aminu ya tambaya kwatancen gidan, sai yaji yama san mijin data aura din. Duk da sun kwana biyu basuyi magana ba, hidima tasha kan kowa, yana da lambar shi, bugu biyu kuwa ya daga, sukayi magana. Shi yaje ya samu har gida, a bangaren da yake ganin baki, yayi masa bayanin dalilin zuwan, tunda ba zai yiwu yai magana da Asabe kai tsaye ba.

“Wannan ma ai shirmene irin nasu na mata.”

Cewar Alhaji Salihu, dan sunyi tarayya da Alhaji Hashimu wajen kaunar yaransu, shima bai hada nashi yaran da komai ba, musamman ma da yaji cewa dalilin Asabe ba zai wuce na zaman kishin da sukayi da Abida ba, idan bai manta ba, da bakinta ta fada masa har yanzun yaronta Abdallah a gidan yake, wajen kishiyar, ita take rike dashi, saboda shirme sai tace ba za’a auri yarta ba?

“Ai bama saikayi magana da ita ba Alhaji Hashim, kabar komai a hannu na.”

Haka sukayi sallama kuwa, ya nufi bangaren Asabe, tayi mamakin ganin shi a wannan lokacin tunda ba girkinta bane, mamakinta ya kara ninkuwa jin zancen da yazo mata dashi.

“In dai na isa, a karkashina kike, yanzun nake so ki kira wayar Tahir ki saka masa albarka a auren da zaiyi, in kuma ban isa ba saiki nuna mun insan matakin da zan dauka…”

Yanayin fuskarshi ya bata tsoro, bata son abinda zaisa tayi wasa da auren shi yanzun data fara gane halayen shi da yanda zatabi dashi, ga Sadiya da rayuwarta ta fara inganta, zuciyarta fal da bakin ciki ta kira wayar Tahir din tana addu’ar kar Allah yasa ya daga.

“Mama Na…”

Ya furta da muryarshi a raunane, kafin sallama ta biyo baya, yana hadawa da gaisheta bayan ta amsa sallamar, ya jiki tayi masa.

“Na warware, kawai dai sunki sallamata ne, kina lafiya dai ko? Baki da wata matsala? Hamma yace kinzo dubani ina bacci…”

Wani irin kallo Alhaji Salihu yakeyi mata, jin yanayin muryar Tahir, yasan irin yaran nan ne masu biyayya, irin yaran da iyaye sukafi matsawa saboda sun san ba zasu iya musu dasu ba.

“Lafiya kalau, daman akan zancen Sa’adatu ne, nake so ince maka bakomai, na amince ka aureta. Allah ya sa muku albarka.”

Shiru yayi, wani irin shiru, sai dai sunajin saukar numfashin shi ta wayar da Asabe ta saka a speaker.

“Nagode…nagode Mama.”

Ya samu ya furta muryarshi na rawa.

“Ka kwanta ka huta, saida safe.”

Bai iya amsawa ba harta kashe wayar.

“Nagode. Dan Allah kar in sake jin wata magana kuma daga bangarenki, wallahi zamu samu babbar matsala.”

Kai kawai ta daga masa, dan ta cika, tayi fam, idan tayi magana, kuka zatayi, yana fita ta shige daki tasa mukulli, ta kira Uwani.

“Hajajju matar Alhaji.”

Uwani ta fada cikin raha.

“Zamu je wajen nan Uwani, kizo ki karbi kayan…idan na samu karyar da nayi ya barni fita sai muje.”

Yanayin muryarta ya hana Uwani yi mata shakiyancin data saba duk idan ta bata shawara taki dauka daga farko, daga baya kuma tazo ta amince.

“To shikenan, zan biyo da safe…”

Kayan da take magana, leshine guda biyu masu tsadar gaske da Alhaji Salihu ya bata don tayi fitar bikin Nana dasu, daya ta dinka, dayan yana nan, sai kuma atamfofi guda hudu, bata da kudi a hannunta, shisa zata siyarwa da Uwani kayan ta samu kudin rikewa a hannunta.

In dai ita tayi nakudar Tahir, shida jinin Abida sai bayan ranta…!

<< Tsakaninmu 8Tsakaninmu 10 >>

1 thought on “Tsakaninmu 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×