Skip to content
Part 1 of 5 in the Series Tsinuwar Uwa by Salis M. Reza

Gabatarwa

Shin wai me yake kawo yin tsinuwa? Yaya ma ake yin tsinuwar? Laifin ƴaƴa ne ko laifin iyaye ne? Shin ma wai da gaske ne ana yin tsinuwar? To idan anyi me ke biyo bayan yin tsinuwar? Shin da gaske tsinuwa na kama wanda akaiwa tun anan gidan duniya ko sai an je lahira? To shi wanda yayi tsinuwar yana wanyewa lafiya ko dai shi ba shi da laifin komai? Shin kun taɓa ganin rayuwar wanda iyayen sa suka tsine masa? Idan kun taɓa gani to yaya rayuwar take? Yana yin nasara a rayuwarsa ko dai taɓewa yake yi? Mu buɗe kunuwa mu ɗauki darasi mai muhimmanci a wannan tafiyar,  Kuzo mu shiga cikin wannan littafin na TSINUWAR UWA wanda nai masa taken DAMA TA UKU, domin jin amsoshin duk waɗannan tambayoyin. Bada ɓata lokaci ba duk kanku zai buɗe in sha Allah.

MABUƊI

Gawa ce kwance a tsakiyar gidan wanda mutanen dake kan gawar basu fi mutane hudu ba, tsaye suke kowa fuskarsa babu alamun wannan damuwar da fuskar wanda ya rasa wani nasa ke nunawa na Alihini sai mutum ɗaya da kallo ɗaya zakai masa ka gane yana cikin damuwa. Namijin ne ya ƙara faɗin “Aje a kira maza su zo su fita da gawar nan domin wallhi babu wanda zai mata wanka bare ma wai aje ga yin Salla, idan kuwa ba’a samo masu kaita ba to wallhi tona rami zamuyi a ƙofar gida mu turata ko kuma muje mu jefar da ita a shara, ku mubar mutanen ƙofar gida su shigo susan yadda zasu yi da ita. Ya faɗa yana nuna gawar da kuma hanyar waje da kana iya jin ihun mutane daga waje alamar ana son shigowa cikin gidan. Ɗaya Namijin dake kusa da shi wadda shine mai ɗan nuna damuwa ya ce “Dan Allah ranka shi daɗe mu taimaka ko wanka ai mata kuma mu sallaceta domin nema mata rahamar Ubangiji domin shi mai yafiya ne, dan Allah ranka shi daɗe ka daure? Mutumin da kana gani kasan bashi da alaƙa da gawar ya faɗa yana kallon wanda yayi magana da farkon. Kafin wanda aka kira da ranka shi daɗe yayi magana matar dake tsaye tana wani irin kuka wanda ba zaka gane kukan me take ba, domin babu alamar wannan kukan na alhinin rabuwa da wannan gawar ne. Ta ce “Duk wanda ya sallaci gawar nan Allah ya isa ban yafe masa ba a cikin ku,kai kuma bako, ta nuna mutum da ya gama magana yanzu, idan baka fita kabar gidan nan ba zansa samari suyi maka dukan tsiya, taimako ne na kawota gida kuma ka kawo angode, dan haka ga hanya. Kuma kafin minti biyar wannan gawar ta bar min cikin gida. Matar da kana gani kasan mahaifiyarsu ce ta faɗa idanuwanta duk sunyi jaa, ga wani irin kuka da take yi mai tafiya da imanin mai kallo da sauraronta. Tana faɗa ta shige cikin gidan ba tare da ta ƙara bi ta kan su ba. Ganin da gaske fa mutumin na bazasu suturce wannan gawar bane yasa mutumin  ya fita waje ya tarar da mutane ƴan anguwa duk sun tsaya sai kananan maganganu suke yi, wasu na zage-zage akan sai afitar da gawar daga cikin unguwar, kai ka rantse ba gidan mutuwa suka zo ba. Wasu ma har dariya suke suna kallon waya da alamar dai wani abun da ya sha fi mutuwar suke kallo. Da ƙyar yayi ƙarfin halin kiran wasu samari dake gefe akan su zo a ɗauko gawar a kaita. Samarin da suka zo gurin ba da niyyar kaiwa gawa ba sai domin muna furci da ganin yaya za’ayi da gawar wannan. Cikin iskanci da isgilanci samarin suka fara faɗin “Kai wallhi babu shegen da zai kai gawar nan cikin maƙabartarmu, wallhi ba’a isa ba, dama abun da muke jira kenan mu gani, kawai a bamu ita muje mu yasar da gawar ashara kawai. Ganin yanda suka hayayyaƙo masa ne yasa ya koma ciki da sauri yana zubar da hawayen takaici yana kai co da wannan rayuwar ta wannan yarinya. Sosai mutane ke dukan ƙofar gidan a kan a basu gawar ko su ƙona ko suje su yasar da ita. Yana shiga gidan ya kalli wannan na ɗazun da yace baza’a mata wanka ba ya ce “Yallaɓai dan Allah dan soyayyar ka da Manzon Rahman kuzo mu kamata mu binne ta haka koda babu wankan dan Allah? Mutumin mai suna Bala ya kalleshi ya ja tsaki ya ce “Ai kaji abun da mahaifiyarmu ta ce, kuma ma koda bata ce ba to wallhi babu ni babu wannan gawar da Allah ya tsinewa. Yana faɗa ya juya shima ya bar gurin. Gurin ya rage mutum biyu wato Nasiru wanda ya ke ƙani a gurin Bala sai shi wannan mutumin da ko sunansa basu sani ba. Mutumin mai suna Sani ya kalli Nasiru ya ce “Mu kama ta koda mu biyu ne mu kaita maƙabartan nan please dan Allah. Da ƙyar dai Nasiru ya taimaka suka yi kama-kama su biyu suka ɗauki gawar da babu wanka babu salla, ko makara bata samu damar shiga ciki ba, daga ita sai tsinma da aka naɗe ta a ciki, daga inda kake kana iya hango fuskar gawar wance tayi fari kamar ka kira sunanta ta amsa, sai gefen fuskarta ta ke fitar da jini ƙan-ƙadan.

Haka suka fita da ita waje ai kuwa suna fita samarin nan kowa ya tashi ya fara tofa albarkacin bakinsa. Take gurin ya rikice da hayaniya suna tare hanyar da za’a fita da gawar. Kowa na ƙoƙarin kai hanu domin yakico gawar har dai suka fi karfin su Nasiru take sai ga gawar  ta faɗi tim a ƙasa. Nan ma basu tsaya ba suka ci gaba da fincike ɗan suturar da ta samu na tsinma har sai da suka yage shi, ya rage da ga ita sai kayan jikin ta, shima dai wasu daga ciki ne suke ƙoƙarin rabata da su. “Inna’ilaihi wa inna’ilaihi raju’un, wannan wacce irin mutuwa ce haka wacce tun a duniya babu sauƙi, wannan wani irin tonon asiri ne haka, haba al’umma ba kwa tsoron Allah ne? Shin meye hakan kuke yi, idan ma laifi tayi ai tsakanin ta da Ubangijin tane ba kuba, dan Allah ku dai na wannan abun da kuke yi sam bai dace ba kunji? Cewar wani da ya kutso kai yaga abun dake faru wanda daga gani kasan shima baƙone a cikin unguwar. Ɗaya daga cikin samarin ya ce “Wallhi malam idan ka ƙara magana akan wannan gawar kaima zamu haɗa da kai, baka san komai game da ita ba kawai kaja baki kayi shiru. Haka mutumin yaja bakinsa yayi shiru ganin yadda suka hayayyeƙomasa kamar zasu cinyesa ɗanye ba gashi. Haka dai Sani da Nasiru suka shiga ɗauƙar gawar suna tafiya samarin na ƙoƙarin rabata da kayan jikinta, tana faɗuwa suna ɗauka har suka kusa isa maƙabar tar, daidai anzu kan babban titin wanda sai an tsallaka kafin akai ga maƙabartar ne samarin sukayi nasarar yake mata gefe ɗaya daga rigar jikinta wanda hakan yasa su Nasiru sakin gawar a ƙasa ta ƙara faduwa a kan titin, nan take aka fara dambe da zage-zage a gurin wasu na ganin hakan bai dace ba, wasu kuma na cewar wallhi sai sun wulakanta wannan gawar tun a gidan duniya. Sosai ake kutuntumo ashariya irin ta ƴan iskan anguwa, Sani dai sai kuka yake yana tare duk wanda ke son zuwa ya taɓa gawar. Nan dai al’umma suka ƙara taruwa sosai kasan cewar an zo kan titi, motoci kuwa dole suka faka kowa yana zuwa kallo, duk wanda yazo yaga wannan abun mai kama da almara sai ya yi salati. An kwashe a ƙalla mintoci talatin ana abu ɗaya, akan titunan, ga bayin Allah a mota da mashin an hana su wucewa. Haka dai har suka zo bakin makabartar nan ma dai aka ƙara tsayawa aka yi rikici sosai kafin suka samu damar shiga da ita, kasancewar yanzu masu taimakon ganin an binne gawar sun ƙara yawa, ai kuwa zo kaga al’umma iya kallonka, amma babu abun dake fita daga bakukan wasunsu sai zagi da aibata wannan gawar.  Ana zuwa nan ma dai jefar da ita a kayi a gefen ramin da dama a haƙe yake. Ga shi dai a cikin maƙabarta ake amma anki ayi shiru sai surutu kowa ke yi, su wai a dole baza’a binneta a maƙabartarsu ba, ganin dai bazasu bari a binne ta bane yasa Sani kamo ƙafafuwan gawar ya turata cikin ramin babu ko tsayawa bin ƙaidar yanda ake saka gawa, wani yayi saurin riƙota yana faɗin  “Wallahi baza’a binneta a wannan makaranta ba. Ganin haka yasa Sani saurin turata gaba ɗaya domin a rufe kowa ya huta, ko ina ya shiga sai ya rage gefen kanta da ya tsaya bai ƙarasa shiga wannan tsakiyar ramin ba hakan yasa ya kamo kan kenan sai yaga kamar tana motsi, tsayawa yayi yana bin fuskarta da kallo sai yaga ta sauke wani dogon ajiyar numfashi tana ƙoƙarin buɗe ido. Ai kuwa da sauri cikin tsoro ya sake ta ta faɗa a cikin ramin, kafin ka ce me sai kawai aka fara turo ƙasa wasu harda duwatsu da ganye ana so a rufe ta a haka ba tare da an saka itace ko tukunya ba, shi dai Sani ya rikice domin shi kadai ya lura da abun da ya gani ɗin. Ana ihu na turo ƙasa har an daina ganin ta sai kawai gani a kayi ta ɗago daga cikin ramin ta saki wani ihun da yasa kowa dake gurin rikicewa kowa ya ɗau na kare, wani tsabar rudewa ma cikin ramin ya faɗo yana ihu! Ai kuwa ita da take neman mafita cikin rashin sanin komai ta kamosa, yana   ihu tana ihu gashi taƙi sakar masa riga sai ma ƙara chakumeshi da take yi. Sosai maƙabarta ta rikice da ihun al’umma shi kuwa Sani sai da ya ɗan ja baya sannan ya tsaya ya fara karanto addu’o’i yana kallon ta, ita kuwa gawar da kyar ta iya ɗagawa daga cikin ramin ta saki wannan mutumin ai kuwa ya arce a guje itama ta fito bakin ramin ta kwanta ta fashe da wani irin kuka ta sunkuyar da kanta gashi jikinta duk ƙasa, ga gefen kayanta a fashe, sosai take kuka ko tsagaitawa ma bata yi, haka makabarta ta watse sai Sani dake gefe ɗaya yana ta kallon ta cike da tsoron Allah a ransa ganin ashe dai bata mutu ba har zasu binneta a haka, a fili ya ce “Tabbas Allah na son wannan baiwar tasa tabbas wannan wata aya ce ga al’umma, sannan wata dama ce gare ta ita wannan baiwar Allah, take ya tuno yadda kowa yake gudun ta, yadda kowa keson ganin a wulaƙantata amma gashi daga tashin ta kowa ya gudu, kamar ba ɗazu maƙabartan nan ke cike da mutane ba amma yanzu babu kowa da ga shi sai ita, shima Nasiru ya gudu yanzu haka labari ya ƙarade cewar gawa ta tashi.

A hankali ya tashi ya nufo gurin ta ganin har yanzu bata ko daina kukan ba. Yazo ɗan nesa da ita ya tsaya ya ce “Assalamu’alaikum baiwar Allah? Ba ta ko ɗago ba, kuma bata dai na kukan ba. Ya sake cewa “Ki taso mu tafi ni ɗan uwanki ne”. Nan ma dai bata ɗago ta kallesa ba. Ya ce “Farko munyi tunanin  kin mutu ne, har munzo binneki amma Allah yayi ikon sa kafin hakan ta faru ashe baki mutu ba. Sai a lokacin ta tsayar da kukan da take yi, sannan ta bi jikinta da kallo, sai kuma ta ɗago da sauri ta kalli mai yin maganar, sannan ta fara bin faɗin gurin da take da kallo, lokaci ɗaya ta fara kakkare jikinta tana kallon ko ina dake gurin da take, ai kuwa take ta ƙara sakin wani ihu mai karfi ganinta babu maraba da tsirara kuma a cikin maƙabarta bakin rami, nan take ta zube a gurin sumammiya.

*****

LABARI

Abuja New Aria. Da sallama ya shigo cikin gidan wanda yana shiga ya tarar da duk mutanen gidan zaune a Palo suna ta hira cikin raha da farin ciki. Suna ganin sa fara’ar dake kan fuskokinsu ta ƙaru da lilin ganin babban jigon nasu wanda yanzu shine matsayin uba a gare su, shi ne ke faɗi tashi da su duk rintsi duk wahala.  Su shida ne a ɗan ƙaramin familys ɗin nasu, shi kansa Yaya Bala sai matarsa Anty Zainab sai ƙaninsa Nasiru wanda ke binsa, amma akwai tazarar shekaru tsakanin su sosai, sai ƙanwar Nasiru ɗin mai suna Siyama sai ƙanwar siya ma ɗin wacce itace auta a gidan nasu mai suna Fatima suna ce mata fati. Sai kuma mahaifiyar su wacce itama ke zaune tare da su domin Yaya Bala ya ce baya so yayi nesa da ita, hakan yasa suka saka haya a gidan da suke da wato a salin gidan mahaifinsu sukuma suka tare a nan. A kwai kyakkyawar fahimta a tsakanin wannan family ɗin sosai domin kuwa kansu a haɗe yake, mahaifinsu duk da ba mai arziki bane amma sosai ya jajirce a kan family’s ɗin nasa shi da matar sa har Allah ya dafa musu kan su ya hadu. Idan kaga yanda suke zama ayi hiri abun gwanin ban sha’awa, har da Ita ma Anty Zainab haka suke janta a jiki babu wannan abun na sirikanci, har ma da ita Umma bata nuna mata komai na uwar miji. A gidan Yaya Bala ne ya gama karatu har ma yanzu haka yana aiki a wani kamfani na abokin mahaifinsu, to babu laifi dai baza’a kirasu da masu kudi ba, haka zalika baza’a ce musu talakawa ba, a baya dai kam suna daga cikin talakawan da kallo ɗaya za kai musu ka tabbatar da haka, amma bayan samun aikin Yaya Bala abun yayi sauƙi harma ya mallaki gida wanda ba wani babba bane, dukda aikin nasu sai ya samu ake yi. Shi kuma Nasiru yanzu haka wannan shekarar zai kammala karatun digiri dinsa ya fara bautar ƙasa. Sai itta kuma Siyama da take matakin difiloma shekarar ta farko kenan. Sai auta Fati da take secondary school aji biyu wato kusa da ta karshe kenan.

Da sauri Fati ta ƙaraso gurin Yaya Bala tana faɗawa jikin sa tana masa Barka da dawowa sannan ta amshi jakar hannunsa tayi hanyar ɗakinsa da gudun ta, itama Siyama tasowa tayi ta rungume shi, shima Nasiru yayi kamar yadda tayi, itama Anty Zaibab haka tazo tayi masa kamar dai yadda suka saba. Bayan sun gama al’adar tasu ya samu guri ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Anty Zainab ce ta fara masa magana da faɗin. Yaya Bala yau kun daɗe fa tun ɗazu muke tsammanin ganin ka amma shiru, Allah dai yasa lafiya? Yaya Bala ya ce “Hanm lafiyar kenan, kin san gobe za’ayi wannan gasar da ake yi duk shekara a nan Abuja to kamfanin mu ne zai yi komai na shirye-shiryen abun da za’ayi, to shine fa muka daɗe a gurin ana ta shirye-shiryen tsara komai. Aunty Zainab ta ƙara cewa “Ikon Allah wato dai wannan abun shima har wani muhimmanci ake basa a wannan ƙasar tamu duk da irin halin rayuwar da muke ciki? Yaya Bala ya sake cewa “Wannan karan duk zan kwashe ku domin ku ga irin yadda wannan abun keda muhimmanci a wannan ƙasar, Nasiru dake danna waya shima ya ce “Ni abun da yake ban takaici ma shine … Sai an gama zaɓar ita mai kyau ɗin amma idan ka kalli wacce aka zaɓa ɗin kamar ka yi amai, sai kace makafi ne masu zaɓar wallahi wata kamar jikar aljannu wai a hakan ita mai kyau. Duk suka kwashe da dariya daidai lokacin Fati ta dawo itama ta samu guri ta zauna. Siyama ta tsayar da dariyar maganar Nasiru ta ce  “Haka fa yarinyar da aka zaɓa waccer shekara ga ƙaton goshi kamar gaban mota, ga hanci a shafe ga wani ƙaton baki, kai ni wallhi dariya ma yarinyar take bani har yanzu idan naci karo da hoton ta a social media. Nasiru ya ce “To zaki fara ko? Aunty Zainab da fara dariya ta ce “To ai gaskiya ne waye bai san haka ba, yarinya da ƙaton goshi wai ita sarauniyar kayu. Yaya Bala ya tsayar da hirar da faɗin “To ya isa haka koma dai yaya take Allah ne ya halicce ta, kuma shi ne ya bata nasarar, kuma ai duk kanku dai tafiku kyau. Yana faɗa ya ce “A kawo min abinci na ci tunda gulma ya hana a min tayi, kuma nasan duk kunci naku. Ya faɗa domin kawar da martanin da zasu bashi akan maganar da yayi domin kuwa yasan yanzu za’a fara. Anty Zainab ta amsa da cewar “Dama dai wanka ka fara yi tukun sai a Kawo abincin ko? Ya ce “To duk yanda kika ce Madam”

Haka ta miƙe ta nufi ɗakin sa ta haɗa masa ruwan wanka kafin ta kirasa ya mike ya bar Nasiru da su Siyama a palon. Itama Siyama tashi tayi ta nufi ɗakin su wanda yake mallakinsu su biyu ita da Fati, ta na shiga ta tsaya tana kallon fuskantar a jikin madubin dake cikin dakin. A ranta tana jin cewar wallhi idan ta shiga wannan ƙasar kyawun da keyi Allah ko babu kwalliya sai tazo ta ɗaya, barin idan ta tuno da wacce tazo ta ɗaya a waccer shekarar. Sosai take cigaba  da yin yanda taga ƴan matan na tafiya idan zasu fito gurin, yanda suke jijjuya mazaunansu da ma jikin su. Tana cikin haka Fati ta shigo, ai kuwa tana ganin ta ta ce “To sarauniyar kyau ta gidan Yaya Bala an fara ko? Ta faɗa tana ƙara shigowa cikin ɗakin tana ci gaba da kallon yadda yayar tata ke ta karkarya jiki kai ka rantse da Allah cewar gobe da ita za’ayi wannan gasar tana yin bita ne. Fati ta ce “To Anty Siyama mai zai hana kawai shekara mai zuwa ki shiga wannan gasar ko ke ma za…” Da sauri Siyama ta toshe mata baki domin kar ma wani a gidan yaji. Wannan shine burin ta, wannan shine mafarkin ta, taso ace yau duniya tasan da irin kyawun da Allah yayi mata, ita burin ta tayi zarra da kyawunta, wannan burin ya daɗe a ranta bata so kowa ya sanda shi hakan yasa ta shirya komai ba tare da kowa ya sani ba, tasan za’a sha mamaki idan akaji abun da tayi, tafi so kowa yaga komai a aikace wato gani da ido. Ta sha wahala sosai kafin azo wannan matakin saboda haka dole ta ƙara kiyayewa kar komai ya kwafce mata. Tasan ko a mafarki ƴan gidansu suka ji abun da tayi bazasu yarda ba domin tayi komai ne cikin iya taku da taimakon babbar ƙawa Aida. Sosai ita kanta take mamakin faruwar abun dukda cewar tasan bata bada wata hanya guda ɗaya da wani zai zargeta ko ya gane ta ba, to amma mai zai faru idan aka gano gaskiyar abun da tayi. A zuciyarta ta ce “Babu abun da zai faru a lokacin domin na cika buri na.

Tsinuwar Uwa 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×