Skip to content
Part 2 of 5 in the Series Tsinuwar Uwa by Salis M. Reza

Siyama ta ce “Ke rufa min asiri so kike Yaya Bala ya karkaryani a gidan nan ne ko? Ta faɗa tana sakar mata bakin da ta toshe mata ta na ɗan sakin Itama Fati dariyar tayi ta na faɗin “To ai naga yanda kika ƙwallafa ranki a kan wannan gasar ne, tun fa lokacin da aka gama na waccer shekarar kike lissafin na wannan shekarar, sannan kuma kullum kece ke kushe wacce tazo ta ɗaya last time, to shine nake tunanin ko kina shirin shiga ne kema sai musani ai.Siyama tayi shiru tana tunanin garin yaya har Fati ta gano duk wannan! Dama ta baiyana komai ne! Siyama ta matso kusa da Fati ta kamo hannunta ta ce “Yauwa Fati na tambayeki mana dan Allah? Ta ce “Ina jin ki” Siyama ta yi murmushin da ke ƙara lotsa gefe da gefen kumatunta sannan ta ce “Tsakanin ki da Allah dani da wannan rayinyar da tazo ta ɗaya last time wacece tafi wata kyau? Tayi tambayar har tana wani juya idanuwa kamar mai jin bacci. Fati tayi dariya har tana tashi tsaye ta ce “Gaskiya kike so na faɗa ko karya? “Ai gaskiya na tambayeki ba ƙarya ba” Siyama ta faɗa da ɗan ɓacin rai. Sai Fati ta ce “To idan gaskiya ne tafiki kyau wallhi, idan kuma ƙarya ne kin fita kyau tallahi kawai dai ita goshi ne yayi mata yawa amma badan haka ba ai da ko gefen takalmin ta ma ba zaki gani ba. Tana faɗa ta yi hanyar waje da sauri domin kuwa tabbas tasan abun da zai biyo bayan hakan. Tana fita Siyama da ta gama cika tabi bayanta da kallo tana cije baki. Tana barin ɗakin Siyama ta ɗauko wayarta tana sauri ta danna kira, jin ta shiga ne yasa ta nufi ƙofar ɗakin ta tura ta tabbatar ta rufe sannan ta dawo kan gadon ta zauna, tana zama aka ɗaga wayar cikin masifa ta cikin wayar ake faɗin. “Ke dai wallhi baki da mutunci to ko kizo yanzu ko kuma nima na zare hannuna, haka mukayi da ke, to wallhi bazan ƙara tambayar sa ba. Siyama ta ce “Please mana Aida yayanmu ya dawo gida bazan iya fita ba, kuma ai mun gama komai ɗazu ku da kanku kuka ce sai gobe zamu haɗu ko? Cikin bala’i ta sake cewa “To ni na gaji da riƙon sa, ko kizo ko ya jiƙa miki aiki. Tana faɗa ta kashe wayar. Siyama ta dafe ƙirji tana jin wani sabon lukutin tashin hankali, to tayaya zata iya fita yanzu. Tabbas tasan idan Yaya Bala ya kamata babu wata-wata sai ya karya ta kamar yadda yake faɗa. Shiru tayi tana tunani sai kuma ta mike ta shiga toilet.

Zaune suke dukkansu a gurin cin abinci suna ci suna hira gwanin ban sha’awa kowa sai murmushi yake, kana kallon su zaka ga haɗin kai da ƙaunar juna a tsakaninsu. Yaya Bala ya ce “Siyama gobe zaki zauna a gida tare da Umma ba zai yiwu a barta ita kaɗai a cikin gida ba kin san halin ta. Ya faɗa babu alamar wasa a fuskar sa wanda daga ji kasan umarni yake bata. Da sauri Siyama ta dawo da ruwan da ta ƙurɓa yanzu tsabar wani irin shok da ta shiga har tana kwarewa. Kallonsa tayi ganin yana ci gaba da cikin abincin sa alamar dai ya gama magana, ta mai da kallonta izuwa ga Anty Zainab sai suka haɗa ido. Take tayi ƙarfin halin cewa “Yaya dan Allah ga Fati ita sai ta zauna da Umma saboda…”Saboda ke ban isa da ke ba ko? Saboda ke kin fi ƙarfina ban isa na sa ki ba ko?. Yaya Bala ya katse ta yana kafe ta da ido. Ya ce “Siyama wallhi ina tausaya miki, ke a tunaninki bana kula da duk take taken ki ko? Allah kadai yasan abun da kike shirya wa idan kin je gurin wannan taron gobe, tsrona ɗaya kar kije kice zaki haɗu da wata daga cikin masu wannan gasar ganin yadda kike ta zubuɗi a kai, ɗazu haka naga lokacin da kika fita ban san ina kika ji ba, ke a tunaninki ban ganki ba ko, wallhi Siyama idan na kamaki da wata rawar ƙafa wallhi kin san halina, kuma zuwa ne bazaki yi ba, na gama magana.

Yana faɗa ya tashi ya bar palon ran sa a mugun ɓace.   Aunty Zainab ta ce “Ni narasa irin wannan zumudin naki wallhi, kullum sai kin yi maganar wannan gasar ai dole Yaya Bala ya tsargu, ko jiya sai da yamin magana nace kar ya ji komai ai ke kina da tunani, to kuma sai jiya ya ƙara kama ki kin fita, kawai ki haƙura ku kalla a gida ke da Umma. Nasiru da tun ɗazu yake ta faman surfa lauma yana dariya a ciki-ciki ya ce “Sis na miki alƙawarin ɗaukar komai a waya na nuna miki in sha Allah” Yana faɗa ya tashi ya nufi ɗakin sa yana mata dariya mugunta. Fati kuwa da dariya ta gama cika mata ciki amma tsoro ya hana ta sake su, amma jin abun da Nasiru ya faɗa yasa ta saki a barta tana toshe baki.  Siyama ta tsaya shiru kamar wacce tayi suman tsaye. Ta kai minti biyu a haka kafin ta yi murmushi ta ci gaba da cikin abin cin ta bata ko bi ta kan Fati da Nasiru ba. Aunty Zainab dai sai kallonta take yi ganin bata sake cewa komai ba. Haka dai har suka gama cin abincin kowa ya shiga ɗakin sa. Ta na shiga ɗaki ta tarar da Fati ta kwaso takardun makarantar ta tana ta fama da karatu. Sosai Fati take a tsorace amma taga ko ta kanta bata bi ba, sai ma waya da ta ɗauka ta fara chatting. Tana cikin chatting ɗin kira ya shigo wayar ta, da sauri ta ɗaga ta ce “Ka ƙaraso ne? Tana faɗa ta kashe kiran ta ci gaba da chatting ɗin ta, sai da tayi a ƙalla minti biyar kafin ta tashi ta ɗora wata doguwar riga tayi hanyar waje.

Tun daga nesa ya hango ta fuskar nan a haɗe sai wani cin magani take yi, sannan kaman dai yadda ta saba ko ɗankwali babu a kan ta, daga ita sai doguwar riga, kuma zai iya rantse wa da Allah iya wannan doguwar riga ce a jikin ta. Sosai shima yake mamakin kasan a kan ta. Na farko kamar yadda kowa ke faɗa a anguwar cewar ita ɗin ba sa’ar sa bace, kuma wallhi ba dan Allah take son sa ba, shi ma yasan da gaske Siyama ba ajin sa ba ce, domin ita ɗin irin matan nannane da ake kiran su da wanke hannu ka taɓa. Sannan ita ɗin ta kasance mai yin duk abun da ya raya mata, sannan bata kunyar yin abu idan tasan ya sha feta, amma yadda take nuna masa soyayya yasa ya ƙaryata cewar bata son sa, duk da cewa shi ɗin baƙi ne, kuma talaka ɗan talakawa kamar Ita dai Siyamar. Shi dai yasan idan yasaka ta yin abu tana bari kuma tana bashi lokacin ta da kulawa daidai gwargwado, to meye soyayyar, duk wanda ya samu wannan ai a tunaninsa ya gama samun soyayya amma mutane sunce ba sonsa take, to amma mai yasa mutane suke tunanin bata son sa ne. Shi dai yasan bayan yayanta Bala da mahaifiyarsu da suke tsoro kamar mutuwa, yasan babu wani mutum da Siyama ke jin maganar sa sai shi. Abun da mutane basu gane game da ita ba shi ne, ita tana da wasu irin ɗabi’u ne da ba zaka taɓa fahimtar ta ba har sai ka zauna da ita, shi dai yasan tana son sa kamar yadda take faɗa kuma yake gani a aikace, dukda cewar mutane suna ce masa dole ne shi mara wayo ba zai gane ba, amma shi ya yarda da haka.

Tana isowa gurin da yake ta ce “Tun ɗazu kace zaka zo yanzu gashi har na fara jin barci”. Ta faɗa fuskar nan a haɗe kuma da alamar shagwaɓa a muryarta dukda cewar kusan haka maganar tata take a koda yaushe. Ibrahim ya ce “Yau aikin wata mota muka samu shine ma ya kaimu har bayan sallar isha, yanzu ma fa ko gida ban shiga ba na ce bari nazo na duba ki karki jini shiru. Ya faɗa yana nuna mata jikin sa da yake kamar an fito da shi daga cikin kwalta. Sai a lokacin ta kalleshi taga da gaske ko wanka bayi ba. Ta ce “Ni dai wannan aikin naka wallhi matsala ta ɗaya da shi kawai ƙazanta, kalleka fa dan Allah kamar wani mahaukaci, ni dai kawai ka je gida zamu haɗu gobe kawai, na sha faɗa maka ka daina zuwa idan baka yi wanka ba, dan Allah tayaya zamu sake a haka kana warin baƙin mai. Ya ce “To ai sabo da alƙawarin da yi ne yasa nace bari nazo karki jini shiru kuma kiyi fushi. Te ce “To naji ya aikin? “Aiki fa babu daɗi Siyama ta sai dai muce Alhamdu lilliha! Daga haka tayi shiru shima yayi shiru. Ya ce “Wai me ke damun ki ne yau Siyamata? Yayi tambayar ganin yau gaba ɗaya taƙi sakewa Ta ce “Babu komai kawai bacci nake ji. Ya ce “No kina da damuwa please sanar dani dan Allah Siyamata, kin san bana son ganin damuwar ki”  Ta kalleshi sosai irin kallon da ke sa mutum ya ji ya tsargu irin kallon da idan a kai maka dole kaji kamar an raina ka ne ko ana so a gano wata gaskiya a gare ka. Ta ce “Babu komai fa kawai barci ne ke damuna. Ya ce “To ai gobe Lahadi zan zo da rana sai muyi magana ko? Ta ce “Kamanta gobe…Kamin ta ƙarasa ya ce “Ranar zaɓen sarauniyar kyau ta ƙasa a nan Abuja ko? Tayi dariya ta ce “Ashe dai baka manta ba? Ya ce “Ya za’ayi na manta da abun da kullum sai an min zancen sa, nifa sai nake ganin ko waɗanda zasu yi wannan gasar basu kaiki zumudi ba. Ta ce “Ina son naga mata masu amsa sunan mata ne, da kuma kwalliya da tsan-tsar kyau. Ibrahim ya ce “Ni dai ba zan samu damar zuwa ba, da naje nima, amma zamu kalla a tibi ai ko waya. Ya na faɗa ya miƙa mata ledar da yazo da ita ya ce sai gobe idan kun dawo zan kiraki da safe. Ta ƙarɓa tana godiya ta shige gida ta barsa a tsaye yana bin ta da kallo, shi kansa wata zuciyar na sanar masa da cewar wannan yarinyar tafi ƙarfin sa, domin shi kansa yasan Siyama tana da buri sosai da son wadata, amma idan ya tuno da irin son da take masa sai ya ji  cewar tabbas zai iya.

Lokaci da ta isa ɗakin har Fati tayi barci, sai kawai ta fito Palo ta saka ledar da ya bata a cikin friza ba tare da ta bude ba, domin tasan ba zai wuce nana bane, kuma ita yanzu bata son cin komai. Ta na ajiyewa ta juya ɗaki tana shiga ta kunna wayarta ta shiga chatting.

Washe gari tun da wuri Yaya Bala da anty Zainab da Fati da Nasiru suka shirya kasancewar da wuri zasu je gurin kafin a fara saboda Yaya Bala ne zai kara kula da gyaran gurin. Umma ce ta nufo gurin da suke tana kiran sunan Yaya Bala “Bala.. Bala.. “Da sauri ya amsa yana faɗin “Na’am Umma lafiya irin wannan kira kamar nayi laifi, dama yanzu nake shirin shigowa gurin ki kamun mutafi . Ya faɗa a ɗan tsorace har yana saurin baki, domin tabbas suna tsoron ta sosai. Ta ce “Bance karka ƙara zuwa da kowa gurin wannan shegen takar ba? Yanzu gurin da ake zuwa ana tallan tsaraicin shine zaka kwashi iyalinka ka kai su gurin fatan suma su ɗauko ɗabi’un ko? Yanzu tun da ka fara zuwa da su waccer shekarar shikenan kullum sai wannan yarinyar Siyama ta dame mu da zancen, ga shi daga shigar da take yi ya sauya, shine yanzu zaka kwashe su ku tafi saboda kaima ka zama lalacecce ko, to ban yarda ba. Yaya Bala ya ce “Haba Umma tallan tsaraici kuma, wallhi ba haka bane, kuma ba iya arna ne kawai ke shiga ba har musulmai suna shiga, dan Allah ki yi hakuri mu huɗu kawai zamu je banda ita Siyama ɗin domin nima ina tsoron zuwanta gurin. Cikin Masifa Umma ta sake faɗin “To idan ba tallan tsaraici ba ne me nene duk surar ji a waje, to Gara dai kai da Nasiru ɗin amma ko ita Fatima da matar taka ban yarda aje da suba, suma a bar min su a gida, kuje daga kai sai Nasiru.Da gyar dai Umma ta yarda aka haɗa da anty Zainab. Ai kuwa take Fati ta fashe da kuka tana faɗin dan Allah Umma.  Amma Umma ta ce “Iana taron Allah ina taron mutanen nan kar su ɓatawa yarana tarbiyya. Haka kuwa a kayi su uku suka tafi aka bar Siyama da Fati a cikin gidan fati sai kuka take yi kamar ranta zai fita.

Ita kuwa Siyama wanka tayi ta shirya  sannan ta saci hanya ta fita ba tare da kowa ya lura da fitar ta ba a gidan.

Sosai gurin taron ya cika sai waƙoƙin da aka tanada domin gasar ne kawai ke tashi a gurin da harshen turanci. Sosai holl ɗin ya cika manyan mutane ne zaune kowa ya buɗe idon sa domin basu abinci da kallon kyawawan matayen da zasu baiyana a gurin. Gefe guda kuma ga alƙalai masu tantancewa a gefe sun sha bakaken kaya, ga wasu na’urori a gaban su sai danne-danne suke yi. Ɗaya gifen kuma ga Iyalan gidan Yaya Bala zaune a gefe ma’aikatan gurin kowa shida iyalan sa. Haka dai aka fara kiran sunan jaruman da suka samu damar zuwa wannan zangon na jaha-jaha.  Nan aka fara kiran ƴar jihar Borno. Ta fito tana tafiya kamar ɗawisu, ga ɗinkin dai sai subahanllah! Rabin ƙirji a waje, ga kai babu ɗan kwali, ga shi dinkin doguwar rigar gefen ta a yage har zuwa cinya, tana sanye da wani kyalle mai kamar igiya a kafaɗar ta mai ɗauke da sunan jaharta ta Barno. Bayan ta gama duk wata girgiza da rausaya tayi ɗan jawabi a taƙaice sai aka kira ƴar  Bauchi, itama sanye da irin shigar waccer. Haka dai aka dinga kira har aka zo kan ƴar Jigawa. Itama ta gana sannan aka zo ƴar Nassarawa , itama dai haka tayi nata, ai kuwa ana kiran sunan ƴar Lagos guri ya kaure domin kowa na mata zaton itace zata ci, babu laifi tasha kyau sosai, haka itama ta gama aka kira ƴar Abuja mai kiran suna ya ce “Siyam Olosha from  FCT Abuja. Nan take kuwa ya zuba ido domin ganin wacce halitta ce zata wakilci garin Abuja, domin tabbas wannan shine karo na farko da wata musulma ta wakilci garin Abuja a tarihin gasar. Nan take Siyam Olosha ta fara fitowa cikin takun ta da ta koya tun kafin zuwan wannan ranar, sosai akai mata kwalliya wacce sai ka mata farin sani kafin ka gane ta. Lokaci ɗaya filin taron ya cika da tafi da shewa ganin wata irin halitta mai tafiya kamar shanshani ta baiyana a gurin, sosai kowa ke kallonta ganin ta ƙaramar yarinya. Haka ta iso filin gurin ta fara girgiza ko ina nata tana rausaya haɗi da murmushi, babu alamar tsoro ko kunya a tare da fuskar tata, kallo ɗaya kawai zakai mata kasan tayi kyau bana wasa ba. Ɓagaren Yaya Bala kuwa da Anty Zainab da Nasiru kallo ɗaya dukkanninsu sukai wa Siyama Alhasan su suka gane ta. Dukda kuwa sunji an kirata da wani sunan daban ba wannan ba. Cikin wani irin tashin hankali yaya Bala ke kallon gurin da Siyama ke karkaɗa mazaune, sannan ga duk wani sirrin da Allah yayi mata na ƴa mace nan sun gama fallasa kansu a waje. Bai tashi rudewa ba sai da yaji yadda Siyama ke zubo turanci tana magana tana gaisuwa ga shuwagabannin gasar da manyan mutanen da suka halarta da gwamnonin dake gurin. Shi kansa Nasiru abun neman hana shi nutsuwa yake yi, anty Zainab kuwa ta gama cika da mamaki, badan muryarta da taji da bazata yarda cewar wannan Siyama ce ba. Siyama Alhasan ce ta koma Siyam Olosha! Ta yaya? Anya ma kuwa ita ce, ko dai mai kama da ita ne? To waye kuma Olosha? Haka dai take ta zancen zuci, jin tana neman zaucewa da mamaki yasa ta ce

“Yaya Bala wannan ba Siyamar mu ba ce? inaga mai kama da ita ce dai, domin Siyamar mu wallahi ba zata iya haka ba, kuma ai mun barota a gida ita, dan Allah kira mana Umma ko ita Siyama ɗin domin tabbatarwa. Cikin ihu da wani irin tsawa ya ce “Ya isa haka! Wacce idan ba ita ba, ke a tunanin ki a kwai abun da Siyama zata yi ne na kasa gane ta. Ya faɗa idanunsa na cikowa da ruwa na takaici da ganin irin tozarcin da wannan yarinyar ta jawo musu. Lokaci ɗaya Anty Zainab ta kafe Siyama dake ta murmushi ana daukar ta hoto da kallo, sosai ta kafe ta da ido tana son gano gaskiya. Tabbas ita ce ga yanayin dariyar ta, ga yanayin tsayuwar ta da ɗan dogon hancinta. Lokaci ɗaya itama ta fashewa da kuka. Shi dai Nasiru sai kallon ta yake yana ta tunani, ta yaya haka ta faru a garin yaya.

Sosai a kayi taro na ban mamaki a cikin garin Abuja, wanda yanzu an gama komai sai faɗin sakamako, daga na ɗaya zuwa na uku sune keda kyauta, ta karramawa, sai kuma daga na huɗu zuwa na goma suma za’a basu tasu kyautar wacce bata kai ta ƴan farko ba. Daga na goma aka fara kira zuwa na huɗu. Siyama jin bata ji sunanta a cikin na goma zuwa na huɗu ba yasa ta haƙura domin tasan ta faɗi. Hakan yasa ta ɗaga kai ta kalli ƴan team members ɗin ta da jagororin su sai taga suma duk jikinsu ya mutu. Amma ƙawarta mai ƙara mata kwarin gwiwa tana daga mata hannu alamar in sha Allah bata fadi ba.  Nan dai aka kira sunan wacce tazo ta uku wata Kirista daga garin Benue mokordi. Ana kira aka fara karanto tarishin matar da matakin karatun ta, da irin ƙoƙarin ta. Ana gamawa aka kira sunan ta biyu wato Siyam Olosha. Zo kaga ihu daga gurin ƴan team members ɗin ta harda masoyan da ta samu a gurin. Sosai itama ta fara kukan farinciki da murna. Hakan yasa ta fara ɗaga kai ko zata hango family’s ɗin ta, amma ina duk inda ta duba bata hango kowa ba. Nan aka fara karanto tarishin ta itama da matakin karatun ta da inda take zaune. Ana gamawa aka kira ta ɗaya, wannan ƴar Lagos ɗin. Nan take aka basu takardar yabo da lambobin yabo da zunzurutun kuɗaɗe banda kyaututtukan da ta dinga samu a gurin, daga mota sai kuɗaɗe. Sosai Siyam Olosha ta bada mamaki domin wannan shine karon farko da ƙaramar yarinya kamarta ta shiga gasar, sannan kuma musulma kuma ta wakilci Abuja, sai hakan ya zama kamar ma itace tazo ta ɗayar domin tafi bada mamaki. Haka manyan mutane kowa sai hoto yake son ɗauka da ita ko ina sai kiran sunan Siyam Siyam Siyam ake yi.

<< Tsinuwar Uwa 1Tsinuwar Uwa 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×