Skip to content
Part 4 of 5 in the Series Tsinuwar Uwa by Salis M. Reza

Shiru Siyama tayi a cikin motar tana kallon shigar da tayi. A hankali Aida ta ce “Lafiya dai ko?” Siyama ta sauke ajiyar zuciya ta kawar da kai gefe, ita da kanta tasan shigar da tayi sam bai dace da itaba. Ta ce “Lafiya ina ɗan wani tunani ne” Ka she motar Aida tayi ta juyo ta kalleta da kyau kafin ta fara bata baki har dai Siyama ta sauƙo. Duk da hakan wata zuciyar na sanar da ita bata kyauta ba, amma ta danne suka shiga cikin group din da tun daga bakin get zaka fara cikin karo da manyan motoci na Medels ɗin dake gurin da kuma mutanen da aka ce suna san ganin ta.

*****

Yaya Bala

Cikin tsananin ɓacin ran da ya sarƙe masa zuciya yake tuƙa motar kamar zai tashi sama, Anty Zainab kuwa sai kuka take duk ta rikice da ganin wannan sabon al’amarin. Sosai wata zuciyar tata ke ƙoƙarin ƙin yarda da cewar Siyamarsu ce haka. Shi kuwa Nasiru gaba ɗaya ma shi halin da Yaya Bala ɗin ya shiga ne yafi tashar masa da hankali gashi sai gudu yake yaƙi yayi magana da kowa. Daidai lokacin aka kirasa a waya ai kuwa take ya kai hannu da niyyar ɗauka kuma gashi sun iso kan jakshon, bai ma san sun iso ba hakan yaba wata babbar motar damar hawa kansu, lokaci ɗaya motar ta komatse ta baya, yayin da itama babbar motar ta dungura gefe ɗaya. Lokacin da mutane suka iso gurin Nasiru ne kawai ke motsi, kafin minti biyar har motar agaji ta iso aka kaisu asibiti mafi kusa da gurin. Take likitoci suka tabbatar da mutuwar macen cikin su, sannan suka naimi da a sanar da wani nasu. Cikin ikon Allah kuma waya biyu aka samu ta Yaya Bala da Nasiru, sai dai wayar Nasiru ta fashe hakan yasa aka duba number da ya kira karshe. Number yaran wajan aikin su ne wanda ya kira lokacin da suke tafiyar, koda aka kira aka sanar dasu shine suka zo gurin. Shine suma suka kira number mamar su suka sanar da ita. Koda Umma ta ƙaraso sai ta cika asibitin da kuka, tana kiran sunan yaran nata, sosai ta fita a haiyacinta sai faɗin dama ta hana su zuwa wannan gurin amma suka ce sai sunje yanzu ga abun da ya sake su, sosai take ta zaro magana harma bata san tana yi ba. Sai da likitoci suka tabbatar mata da cewar suna lafiya kafin ta ɗan rage kukan, amma duk da haka bata daina faɗa ba. Ganin halin da take ciki ne yasa likitan bai mata maganar macen da ta mutu ba, sai ma tabbayarta ko zata kira mahaifinsu ko kuma wani Namijin. Jin haka yasa ta bada number Kawu Inuwa wanda aka kirasa shima yazo cikin daren. Nan likitan ya sanar da shi cewar a kwai mace ɗaya a cikin su kuma Allah yayi mata rasuwa. Haka suka je ya ganta sannan ya dawo ya sanarwa da Umma wacce jin haka yasa ta ƙara dawowa da sabon faɗa. “Sai da nace masa kar ya je da ita amma yace yaji ya gani, yanzu dan Allah mai zai cewa iyayenta, wannan wacce irin masifa ce, wannan abun na arna da gaba ɗaya ma saɓon Allah ne, abun da babu wani ɗan musulmi kuma ɗan kirki da ya fito daga gidan mutunci zai bar ƴarsa tayi, shine har kuke ɗaukar iyalai kuje kallo to ga abun da ya jawo muku, ni dai sam ban ji daɗin wannan abun ba, Allah ma dai ya tarwatsa taron mutanen da suka ƙirƙiro wannan kafurcin Allah ya isa ban yafe ba. Sosai Umma take kuka tana face majina, sosai mutuwar Anty Zainab ya taɓa ta, samun sirika irin Zainab a wannan lokacin sai an tona, yarin ya ce mai kawai ci ga na tsuwa, duk da irin faɗan da Umma keda ita amma hakan baisa kana yawan jin kansu ba, gasu a gida ɗaya.

Haka ƙanin Kawu Inuwa ya fita da gawar Anty zaibab ɗin, basu Kaita gida ba sai suka wuce da ita babban masallacin domin tayi kwanan kaso a gurin. Acikin daren aka fara sanar da dangin ta da sauran abokon zama.  Tun a daren likitan ya tabbatar da cewar karaya kawai suka samu ɗaya guri biyu ɗaya kuma guri ɗaya, sai kuma ɗan buguwa da suka samu amma ina sha Allah zuwa safiya zasu farka. Yana cikin barci yake mafarkin matarsa na cikin matsanancin hali, lokaci ɗaya ya buɗe ido da sauri yana bin gurin da aka kwantar da shi da kallo, ganin Umma da Kawu Inuwa ne yasa shi tambayar ina matarsa. Tun da yaga sun fara ce masa ya kwantar da hankalin da ya tabbatar da cewar ba lafiya ba, yana ƙoƙarin rufe ido ya haɗa ido da Siyama, wacce take zaune ta kusa da hannun sa mai karayar. Kallon ta yayi yaga komai na dawo masa. Haka dai bai ƙara cewa komai ba har suka ci abincin da aka kawo musu, sannan barci ya ƙara ɗauke sa bayan an masa allura. Lokacin da ya ƙara buɗe ido sai ya sauƙe a kanta ita kaɗai zaune a ɗakin tana kallon waya tana dariya. Sosai ya dade yana kallonta yana ƙoƙarin haɗa fuskar wannan ta gaban nasa da kuma wacce yaji jiya ana kira da Siyam Olosha. Sosai ya tabbatar da basu da wani banbanci sai dai wannan da take zaune a gaban sa yanzu hijabi ne a jikin ta waccer kuwa marabanta da tsirara babu nisa. A hankali yake lumshe ido yana budewa yana tunanin Allah yasa matarsa lafiya take. Yana cikin haka likitan ya shigo hakan yasa ya lumshe ido kamar mai barci. Yana ji likitan yana mata magana amma bata ji ba. Har sai da ya sanar da ita Nasiru ya tashi kuma abinci zasu ci kafin anjima. Likitan na fita ta shima ya sake buɗe ido.Yana farkawa itama tana satar kallonsa, ganin yana kallonta ne yasa ta fara masa sannu tana tambayar ina ke masa ciwo. Shi kuwa wani irin haushin ta da yake jine yasa ya juya mata baya yana ɗaga  mata hannu yana kawar da kai gefe, sai yaga ta fashe da kuka tana wa Nasiru magana sai kuma yaji tabar dakin da gudu.

Bangaren su kawo Inuwa kuwa washegari aka shirya gawar Anty Zainab ƴan uwanta sukai mata addu’a harda Umma da itama ta zauna a gurin, nan dai ƴan uwanta su kai mata rakiya izuwa gidan ta na gaskiya. Lokacin da Kawu Inuwa ke sanar masa da rasuwar matar tasa sai kawai ya saki murmushi haɗi da hawaye duk lokaci ɗaya, dama ya ji a jikinsa hakan yasa ya kasa yin wani yunguri, amma zuciyarsa wani irin zafi take masa ga shi abun takaici har yanzu babu wanda ya gano cewar Siyama tun da ta fita bata dawo ba. Shi yanzu abun da yafi basa tsoro ma itace Umma, yanzu tana sanin wannan abun shi zata baiwa laifi. Lokaci ɗaya Yaya Bala ya fashe da wani irin kuka wanda yasa Nasiru ma da ke kusa da shi fashewa da kuka. Sosai yaya Bala ke kukan rashin matarsa abar son sa wacce take zaɓar farin cikin sa fiye da nata. Wata zuciyar kuma na nuno masa Siyam a filin taron sarauniyar kyau ta ƙasa! Sosai yake jin ya muzan ta, ya gama zama babban banza kuma ƙaton daƙiƙen da ƙaramar yarinya ta mayar kwandon shara, hannunsa ya kalla ya gani a ɗaure ya cici yatsa. Sosai su kawo Inuwa suke bashi haƙuri har dai ya samu ya ɗan daina kukan. Likita na shigowa Yaya Bala ya ce a sallame shi ya warke, likitan yace yayi hakuri zuwa gobe, amma yaya Bala ya daka masa wata tsawar da tasa likitan rikicewa. Ya ce “Ok ok ok kwantar da hankalinka bari yanzu nasa a rubuta maku takardar sallama. Suna zaune Yaya Bala ya dafe kai, Nasiru kuma ya shiga Toilet yana uzuri sai ga likitan tare da wata noss a bayan sa. Yana zuwa ya miƙawa kawo Inuwa takardar shedar biyan kuɗin su da kuma magunguna da aka sayo musu sai kuma ta sallama. Kawu Inuwa ya amsa yana tambayar na maye? Likitan ya masa ƙarin bayani. Haka dai ba tare da sun fahimci komai ba suka tattara izuwa gida bayan kawo Inuwa ya tare musu mai ɗan sahu.

Yaya Bala yace a saukesa a ƙofar gidan su Zainab kasancewar babu nisa da gidansu. Babu yadda kawo Inuwa bai yi da shi ba amma ina haka ya sauƙa hannu a saƙale bai ko bi ta kan mutanen da ke ƙofar gidan ba ya shige cikin gidan. Koda ya shiga ya tarar da mutane da yawa a ciki hakan yasa ya fara gaisuwa yana hawaye, yana zuwa gurin mahaifiyar Zainab kuwa ya fashe da kuka kamar mace, sosai yake kuka har ya dawo da sabon kuka a gidan. Ƙanwar ta mai suna Zilai da dama tun tuni basa shiri da Yaya Bala domin yarinyar irin marasa kunyar nan ce, shi kuma yaya Bala baya son raini gashi da saurin kai hannu yasa basa shiri da ita, domin kuwa ya sha kwaɗe ta idan tayi rashin kunya a gaban sa. Zilai ta fashe da kuka tana faɗin “Wayyoo Anty Zainab ta tafi ta barmu kun kashe mana ita, to wallahi ba zamu yarda ba, ai ance ba ita kaɗai ce a motar ba amma ita ka dai zata mutu… “Wata ƴar uwarsu ce ta buge mata baki tana harararta. Ohoo shi baima san tana yi ba.

jin abun yaƙi ƙarewa ne yasa baban su Zainab ɗin shigowa cikin gidan ya fita da Yaya Bala. Ganin halin da Bala ɗin ke ciki ne yasa Alhaji Sani wato baban su Zainab fara basa baki hardar yaci nasarar shigar da shi ɗan sahun suka tafi. Koda suka isa gida Umma ce sai matar kawo Inuwa suna kiranta da Mama da matar Husaini suna ce mata Momy, sai wasu daga cikin ƴan uwa. Koda Umma ta gansu tayi mamaki domin ta yi zaton sai gobe ko jibi zasu dawo. Basu jima da dawowa ba sai mutanen gurin aikin su yaya Bala ɗin nan sun yo Mota guda sun zo gidan. Yana aiki da wani karamin kamfani ne irin masu shirya guraren taro ko wani gida idan anyi ko dai filen gabatar da wani taron a nan cikin garin Abuja. Kasancewar aikin ba kullum ake samu bane yasa wani lokaci sukan shiga halin babu, godiyar Allah ma da yasa gidan da suke ciki nasa ne ba na haya ba, domin aikin nasu babu laifi idan aiki ya samu ana samu hakan yasa lokacin da yaji kuɗi a hannunsa sai ya sayi wannan suka dawo wanda suke ciki muka ya saka ƴan haya. Duk da gidan ƙarami ne amma Alhamdu lillah ya ishe su bata tare da takura ba. Bangare biyu ne gidan daya wanda Umma ke ciki, ɗakuna biyu ne sai Toilet daya a gefen ɗakunan babu kicin agurin. Bangaren da suke ciki kuma a kwai ɗakuna hudu da kicin sai kuma kowani ɗakuna guda uku a kwai Toilet a ciki.  Ɗaki daya na Nasiru sai ɗaya na Siyama da Fati, biyun kuma shida matarsa, sai kicin guda ɗaya. Idan sun yi baƙi sai su turasu bangaren Umma, haka suke rayuwarsu babu hangen Dala.

Ganin haka yasa Umma sa Fati ta shiga kicin tayi girki sabo da baƙin, hakan yasa ƴar gidan matar kawo Hassan mai suna Binta tashi ta raka ta suka fara girkin.Baƙin basu jima ba suka tashi suka tafi bayan sun bar masa abu dubiya da suka ruƙo masa. Bayan sauran sun fita ne ɗaya daga ciki ya dawo da alamar dai a bokiksa ne yazo ya fara masa tambayar da yasan sai ya gaji da amsawa. “Wai da gaske ne yarinyar da tazo ta biyu a gasar jiya ƙanwar ka ce? Yaya Bala ya ce “Eh” mutumin yace “Sunanta fa wai Siyam Olosha? Yaya Bala da ya gama kaiwa iya wuya ya ce “Eh itace ” ya faɗa da ƙarfi har sai da hankalin su Umma ya dawo gare su. Shi kuwa mutumin yayi sum-sum ya bar palon. Umma kuwa da tun da suka shigo take son taji ko dai Siyama taje gidan su Anty zaibab ɗin ne ganin bata gansu tare ba ta ce “Lafiya dai kake ihu ga mutumin da yazo duba ka? Yaya Bala ya tashi ya shige cikin ɗakin yana jin hawaye na son zubo masa. Umma ta dawo da kallonta ga Nasiru da shima hannunsa ke maƙale da ƙafaɗa ta ce “Wai ina kuka baro Siyama ɗin ne, ko dai ta tsaya gidan su Zainab ne? Nasiru ya kalli Umma da yasan wallahi babu ruwan ta da wannan ciwon tana jin abun da ya faru shi kenan hankalin kowa ya tashi kenan. Ya ce “Eh tana gidan sai an jima zata dawo koma ta kwana a gurin” Umma ta ce “To ai ta kyauta dama haka ya kamata ace wani yaje gidan nasu. Nasiru ganin haka shima ya miƙe da gyar ya shige ɗaki ya bar palon.

Suna cikin Girkin Binta ta ce da Fati “Wai ina Anty Siyama ne naga ban ganta a gida ba? Fati ta ce “To mun barta a asibiti dai ban sani ba ko kayan ta tsaya kwasuwa. Binta ta ce “Alasarki Anty Zainab wallahi ko ni da ba gidan nan a zaune ba nayi kewar matar tana da kirki sosai ga son mutane. Fati da har ruwan hawaye ya fara taruwa mata ta ce “Da yanzu da ni za’a tafi, Umma tazo tayi faɗa akan baza’a je dani ba, har fa na ke ta kuka ashe dai Allah ya tsara komai ne. Binta ta ce “Alasarki Kinga amfanin bin maganar iyaye ko, yanzu da kin ƙi yarda kin bisu, Kinga ko baki mutu ba ai zaki sha wahala” Fati ta share hawaye ta ce “Ana ganin kamar Umma tana da faɗa har ake ganin hakan yasa bata sakewa sosai da yaran ta, kuma abun da take yi ɗin shine daidai, ni kam daga yanzu duk abinda Umma ta hana ni wallahi ba zan ƙara yi ba. Suna cikin haka wayar Binta ta hau ƙara tana dagawa ba tare da sallama ba wata ƙawarta ta ce “Ke shegiya shiga Whatsapp ki raba mana wannan gardamar ni nace wannan wannan kozin ɗin taki ce Siyama amma su Laila sun ce ƙarya ne. Binta da bata fahimta ba ta ce “Ban gane ba? Ta ce “ki shiga zaki gani ai muna jiran ki”

Ana faɗa aka kashe wayar. Fati ta ce “Wannan Farida ce ko? Binta ta amsa da “Yaya kika gane” t

Ta faɗa tana buɗe datar ta. Fati ta ce “Wannan saurin zagin nata mana, wallahi bana son mutum mai saurin zagi, yanzu fa ji wannan wayar da kukayi ta zage ki har sau biyu kamar wata kafura. Binta ta ɗan yi murmushi ta na faɗin ai Farida da zagi kamar jikar maguzawa. Daidai lokacin Binta ta fara kallon video ɗin da ya gama budewa. Ganin wata kamar Siyama yayarta yasa ta jawo Fati tana faɗin ke duba min nan dan Allah kamar fa Anty Siyama ko? Fati ta amsa tana kallo. Lokaci ɗaya Fati ta ce “Wannan ai ba Siyama ba ce” ai kuwa Binta da farin ciki ya gama kamata tayi hanyar waje da gudu da niyyar nuna wa mahaifiyarta, har tana dariya ta ma manta da cewar zaman makoki suke yi. Ai kuwa suna zaune a gurin gaba ɗaya Binta ta shiga palon tana dariya tana cewa “Umma Mommy Mama kuzo kuga Anty Siyamar mu ta zama tauraruwa. Ta faɗa tana dawo musu da kallon baya. Umma da ta ƙaraso gurin tana cewa wacce Siyama kuma. Nan dai suka fara kallo. Tabbas Siyama ce ga rabin nonuwa a waje, ga kai a bude ga wani irin ɗan banzan ɗinkin da ya gama fitar da mazaunan ta. Sosai Umma tayi sumam tsaye daidai lokacin da Farida ta ƙara kiran Binta… 📝

Muje zuwa masoya, kubi komai a hankali har mukai gurin da kowa zai fuskancin hanya. Yanzu dai kowa yasan abun da ya faru, dama Umma ka dai ta rage…

<< Tsinuwar Uwa 3Tsinuwar Uwa 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×