Nan take Binta ta ɗaga kiran tana sanar musu cewar Siyama ce acikin vedio ɗin, ai kuwa tana jin Farida ta ƙundumawa Lailai wani ƙatoton zagi jin tayi nasara. Jin haka yasa Binta kashe wayar tana ƙara yiwa su Umm ƙarin bayani ganin sun kasa magana. Ta ce “Wai baku gane ta bane? Ina wannan taron da akayi jiya na sarauniyar kyau, to shine fa Anty Siyama ta shiga kuma tazo ta biyu kun gani?” Ta faɗa tana nuna musu takardar shedar zuwa ta biyun da Siyama ta riƙe ana ɗaukarta hoto. Taci gaba da faɗin “kuma Mommy wallahi shi kenan Siyama ta zama..” Wani tsawa Mommy ta daga mata yasa tayi shiru tana bin fuskokinsu da kallon mamakin irin wannan abun farin cikin sukuma duk sun ɓata rai.
*****
Siyama
Lokacin da suka shiga cikin shagon nasu duk wata ƴar team members ɗin su maza da mata duk sun hallara, dama daga ita sai Aida suka rage. Ai kuwa suna shiga gurin ya ruɗe da ihu barin ma ganin irin shigar da tayi. Sosai members ɗin su ke ƙoƙarin nuna mata farin cikin su, amma duk karr take kallon kowa. Haka ta dinga binsu mazan da matan tana runguma suna wa junansu kiss a gefen kumatunsu. Bayan sun zauna Oga Fita ya fara magana cikin harshen Ingilishi. “Muna sake godiya ga Allah da ya ƙara bamu nasara tun bayan shekara shida da muka taɓa zuwa na uku sai yau gashi mun samu ta biyu a cikin mu, kuma nuna san rai shekara mai zuwa mu samu ta ɗaya. Duk suka yi tafi suna amsawa da amen in sha Allah. Ya cigaba da faɗin “Wannan nasarar ba iya ta Siyam Olosha ba ce, nasara ce ta duk wani members da ke cikin wannan group ɗin mai suna wait house (Farin gida). Kuma ina so na sanar daku cewar yanzu haka sabo da wannan nasar da muka samu mun ƙara samu karrama wa ta musamman, sannan mun samu dama guda uku daga kamfanin Baby and me na yin aki damu a matsayin sabbin Models ɗin su na wannan shekara, kuma sun tabbatar da cewar Siyam itace zata gudanar musu da duk wasu tallukansu na kamfanin su muddin ta yarda, yanzu haka sune ke jiran ta a ofec ɗin tan ɗazu”. Ai yana ƙarasa wa suka fara ihu da farin ciki jin abun da suke buri zai tabbata. Aida kuwa kamar ta tashi ta taka rawa tsabar farin ciki, tana son zama Model amma ba irin wannan na ƙaramin kamfani ba, tana so ace irin manyan kasashen duniya su gaiyaceta domin yi musu talla, amma babu laifi idan ta samu wannan ɗin ma Alhamdu Lillah, a hankali watarana zata kai har gurin da take so. Ita kuwa Siyam Olosha farin ciki baki har kunne, dama Oga Fita ya sanar da ita cewar muddin tana son zama Model to wannan hanyar ita ce mafi sauƙi gashi ta yarda tun ba’a je ko ina ba har ta fara zama Model. Adawiya da Badawiya sune suka fara faɗin “Oga Fita amma masu kamfanin babby and me ba wai Siyam Olosha suke so ba, sunce a basu mutum uku ne kawai a cikin members domin ba irin ta suke so a talansu ba. Adawiya da Badawiya sune manya a cikin wannan group ɗin hakan ya Oga Fita baya son rabuwa dasu, domin suɗin sune fitilar wannan taem ɗin, yasan yadda suke nuna ƙiyayyar su akan Siyam, saboda Badawiya ce zata jagoranci team ɗin amma zuwan Siyam da kuma yadda shi Fita ɗin yake ganin zata fi bada abun da ake so ba wai sabo da tafi Badawiya kyau ba, a’a saboda da irin zubin halittar tane yasa ya yarda da ita. Fita ya ce “No ba haka bane, sunce bayan ita a samu mutane uku kuma ke Adawiya ai kina da Contract akan ki, ita kuma Badawiya tace bazata yi aikin Model a ƙananan kamfani ba hakan yasa ban saka sunan ku ba. Na saka Siyama da Nusee sai Sarah da Hafness. Da sauri Siyam ta miƙe jin babu sunan Aida ta ce “Oga Fita banji sunan Aida ba? Oga Fita ya ce “Kamfanin Baby and me kin san basa aiki da baƙin mutum, sunce farare suke so kin ga kuma ita Aida ai bleak biyuti ce, shi ne yasa ban saka da ita ba. Lokaci ɗaya Siyam taji kamar cin fuska ne a kaiwa Aida domin kuwa Aida ai ba baka bace, kuma ma ko bakar ce ai bai dace yace haka ba. Nan take su Adawiya suka fara dariya jin cewar Babu Aida domin sun san abu sai yafi ɓatawa Siyam rai, domin kowa yasan burin Aida kenan zama Model. Haka aka gama taro duk ran Siyam da Aida a ɓace. Sai da tafi komai da ta samu ta saka hannu kafin ta warewa team nasu ita kuma ta tafi gidan Aida da sauran. Kyautar motoci uku, sai kuɗaɗe masu yawa. Sun yi magana da masu kamfanin Baby and me Kuma ta yarda zatai musu aiki amma sai ta shirya tukunna kafin ta saka hannu, domin tana so taje tayi bincike akan irin aikin nasu. Haka suka bar maganar akan zata ne mesu. Koda suka isa gidan Aida sun tara Jamila da jamilu har sun gama abinci sun ci nasu suna kallo. Sannu da dawowa su kai musu suka ci gaba da kallonsu. Ganin Aida bata tada maganar ɗazu bane yasa Siyama faɗin “Ɗazu munyi magana da Fita akan ina so na sanar da iyayena gaskiya dukda cewar lokaci ya ƙure amma ya kamata na nemi yardar su, domin yanzu Kinga zan fara taka wani matsayi da dole ina buƙatar addu’ar iyayena da ƴan uwana, nasan abu ne mai wahala Umma ta yarda nayi sana’ar Model amma idan aka fahimtar da ita zata yarda domin kisan mu Hausawa duk wani abu da bai shafi addini ba gani ake duk mai yin sa ɗan iska ne, so yanzu ina so naji shawarki yanzu na samu damar zama Model, idan sun ce sai na gama karatu ne shima mai sauki ne shekara biyu ya rage min, amma dai na gaji da yin amfani da sunan wani wai Olosha.
Aida taja dogon numfashi, tana haɗeye wani ƙatoton abu a ranta na irin cin mutuncin da a kai mata, wai itace baƙa, sosai ta danne komai kafin ta ce “Kin yi shawara mai kyau, amma gaskiya ina tabbatar miki da cewar babu yadda za’ayi Umma ta yarda kiyi Model, domin yadda suka ɗauki abun ba haka yake ba. Yanzu shawarar da zan baki itace kije gida ki fuskanci komai in sha Allah zasu yarda ni na faɗa miki. Siyama ta ce “Ta sanadiya ta Yaya Bala wanda ya zama kaman Uba a garemu ya rasa matarsa, ya karye a hannu, ga Nasiru ya karya a hannu da ƙafaɗa kuma yana karshen shekara kenan a karatun sa, anny kuwa na kyautawa dangi na. Sosai take kuka tana cigaba da faɗin “Wallahi badan kaina nake wannan abun ba, ina yi ne domin na taimaki su, wannan dama na samu kuma in sha Allah sai nayi amfani da ita. Aida ta ce “Yanzu ni dubeni, badan ina yin wannan sana’ar ba ina zan sa kaina da ƙanne na, da yanzu muna bin gidan ƴan uwa ana cimmana mutunci, a matsayin ki na mace yana da kyau ki kare mutuncin ki, kuma ki tsaya da ƙafafunki babu Maraya sai raggo”. Sosai Aida ta danne nata abun ta bawa Siyama goyon baya da kwarin gwiwa. Haka Siyama ta bar komai a gidan Aida sannan ta shirya da niyyar tafiya sai ga kira ya shigo wayar ta. Ganin sunan Ibrahim ne yasa gaban ta faduwa domin har ga Allah ta manta da shi a gaba ɗaya. Nunawa Aida fuskar wayar tayi suka yi dariya kafin ta ɗaga Aida na cigaba da dariya. “Siyama da gaske wai kece ake cewa kin shiga gasar kyau jiya? Ibrahim ya tambaya a dan rikice. Dariya ta ɗanyi ta ce “Baka taya ni murna bane?” Ibrahim da ransa ya gama ɓaci da kishin ganin video ɗin ta da irin wannan kyawun da tayi yasa yake jin kamar zuciyarsa zata soye, yana kishin abun da yake so hakan yasa yaƙi yadda lokacin da aka nuna masa sai yanzu kuma tazo tana masa dariya. Cikin wata iriyar muryar da baisan yana da itaba ita kanta Siyama ɗin a karo na farko kenan da taji shakkar sa ya ce “Siyama bana son hauka ba wasa nake ba, da gaske kece? Siyama da sai da ta ɗauke wayar daga kunnenta tsabar tsoro tana haɗeye yawu, ta kalli Aida da itama ta tsayar da dariyar. Cikin rikicewa ta ce “Kazo gida muyi magana” tana faɗa ta kashe wayar, ai kuwa sai ga wani kira, take ta kashe wayar tana faɗin “Na shiga uku ni Siyama! Aida karfa wannan mutumin ya zama min masifa fa, naga har na fara tsoronsa. Aida ta ce “Ai ni dama na faɗa miki wannan shirin naki daga baya ke zai dama, kika ce wai babu komai shima ai ba zai gane ba, harda cewa wai wawa ne, bashi da wayo, yanzu dai ga shi kina gani tun bai gano komai ba zai fara kawo mana matsala. Siyama ta ce “Karki damu a kwai kudi idan ya gansu ko da yaji dalilin na a kan sa ba zai yi komai ba idan yaji kuɗaɗe. Aida ta ce “Hamm ayi dai mugani idan tusa zata hura huta” Siyama ta amsa da cewar irin tusar ki kam sai dai ta kashe wutar ma”. Haka Siyama ta fita ta tare mai ɗan sahu ta shiga izuwa anguwarsu, tayi niyyar zuwa asibiti amma tana so ta sauya kayan jikinta, sai ta biya ta gidan su Anty Zainab da ake makoki. Tana sauƙa taga mutanen unguwa kowa na kallonta, hakan sai yanzu ta kalli jikinta taga babu hijjab, da sauri ta shige cikin gida, tana shiga ta tarar da Ibrahim zaune ya dafe haɓa alamar tagumi yana kallon waje. Ai kuwa yana ganinta ya taso yayo kanta kamar wani zaki, sosai Siyama ta tsorata har ga Allah Ibrahim ya sauya sosai. Yana zuwa kusa da ita kallo ɗaya taiwa idanunsa taga sun yi jaa, ai kuwa ta kawar da kai gefe tana jin kamar ya cika gidan nasu. Ya ce “Da gaske kece wannan Siyama? Ya faɗa yana kallon kayan jikinta.
Takurewa tayi a guri ɗaya tsabar wani irin tsoro da ya shigeta, sosai ta matse a guri guda tana jiran sauƙar mari ko kuma taji anyi kutuball da ita, jin shiru ne yasa ta ɗaga kai ta kallesa ya tsaya a gaban ta sai sakin huci yake yi. Lokaci ɗaya ta tuna da cewar Ibrahim ne fa, wanda ta mayar kwandon shara, wannan talakan da ta fake da shi take cika muradanta, sannan yanzu fa ita Siyam ce ba Siyama, zata iya sa a kulle duk danginsa ma ba shi ba, kuma ai yanzu ya gama mata duk wani amfani, lokaci ɗaya taji wani ƙwarin gwuiwa yazo mata, hakan yasa ta sake daga takurewar da tayi ta kallesa cikin ido ta ce “Eh nice wannan da kake kallo yanzu, kuma in sha Allah na fara kenan har zuwa na ciga dukkan burikana na rayuwa, ina son zama Model bama a iya nan ƙasa Nigeria ba har kasashen Turai in sha Allah. Tana faɗa ta kama hanyar gida tana jin mai ma yasa da take neman kada kanta a gaban wannan talakan. Sai dai ko taku uku mai kyau bata yi ba, Ibrahim ya dawo da ita baya, ya kalleta cikin ido, babu wannan tsoron nata yau a cikin idanunsa da ta saba gani kullum, zata iya rantsewa ma kamar ba fuskarsa ba ce.”Mai kike nufi da wannan maganar taki? kina nufin dama ba sona kike ba kawai kina amfani da nine ko yaya? Siyama ta ce “Na godewa Allah da yasa har kayi saurin ganowa da kanka. Sai da ta dawo kusa da shi kafin ta fara faɗin… “Dubeka dubi zubin tsarin halintarka sannan ka kalleni, kai ko giyar wake kake sha har zaka yi tunanin ni Siyama zan iya yin soyayya ta gaskiya da gaskiya da kai, to wallahi bari kaji na faɗa maka, tun da nake tare da kai Ibrahim ban taɓa sonka ba, ban taɓa jin zan iya son ka ba, ina yin amfani da kai ne domin yaya na da kuma mahaifiyata, sannan daga yau ina so na sanar maka da cewar babu ni babu kai, karka ƙara nuna kasanni, kaje kayi lissafin abun da ka kashe min tun daga haɗuwarmu ni kuma zan ninninka maka su, amma dan Allah daga yau karka ƙara nuna ka sanni please, sama tayiwa yaro nisa. Tana faɗa tai masa wani irin kallon sama da ƙasa kafin ta saki wani wawan tsaki ta shiga cikin gidan ta barsa a gurin tsaye yana kallonta, a lamar abun yazo masa a bazata.
*****
IBRAHIM
Duk yadda ya kai da zafin zuciya da zafin rai amma lokaci ɗaya yaji duk sun zube, take yaji jikinsa kamar an zare masa dukkanin lakar sa, babu abun da ya fi taɓa masa rai kamar da tace tun da take bata taɓa jin sonsa ba, kuma bata taɓa masa kallon wanda zata iya so ba. Tabbas jin wannan kalmar daga bakin wanda ka gama yarda dashi ka gama basa amanarka a kwai ciwo. Shi kansa ya sha yiwa kansa tambayar dalilin da zai sa Siyama ta ce tana sonsa, amma idan ya duba yadda take kula sa, kuma take jin maganar sa take basa mutuncinsa sai ya bari akan kawai haduwar jinine, amma ashe ba haka bane. Shiru yayi yana tuna abun da tace wai dama tayi amfani da shine domin cika burinta na zama Model, kuma gashi ta zama, tayi amfani da shi ne domin Yayanta da Mahaifiyar ta. A fili yace “Menene Model! Shiru yayi ya kai minti goma a gurin kafin ya bar unguwar zuciyarsa nata saka masa abubuwa.
Har sai da ya wuce ƙofar gidan su kafin wani yaro ya ankarar da shi, haka ya dawo da baya ya shiga zauran gidan su kafin ya sunkuyar da kansa yana tunani. Bai san adadin mintinan da ya kwashe a gurin ba sai ji yayi ana kiran sunansa. Da mamaki yake kallon zauren ganin duhu alamar dai dare ne yayi sosai, fuskarsa yaji danshin lema, koda ya kai hannu ya shafi sai yaji hawaye ne. Cikin mamaki Hajja ta ke faɗin “Kai Ibrahim meneke gani haka, wai dama kana nan ne ko dai yanzu kazo, tun ɗazu muna ta jiran dawowarka ashe ma kana gidan, me ke faru da kaine?” Hajja kenan kaka ce a gurin Ibrahim wacce ta haifi Babansa yanzu haka tare suke zaune shida ƙanwarsa da ita Hajja ɗin kasancewar iyayensa duk sun rasu, yanzu shi da ƙanwarsa Nana da Hajja suke rayuwa a gidan.
Ya ce “Hajja Siyama ce” Cike da mamaki ta ce “Me ya sami Siyamar? ina ance matar Yayan nasu ce ta rasu, ko itama wani abu ya sameta ne? Lokaci ɗaya Ibrahim ya fashe da wani irin kuka wanda yasa Hajja kwaɗa wani irin salati haɗi da kiran sunan Nana wacce har barci ya fara ɗaukarta. Da sauri ta fito tana tambayar lafiya, haka suka kama shi har cikin ɗakinsa suka kwantar da shi kafin suka fara tambayarsa abun da ya sami Siyama ɗin, domin kuwa babu wanda bai san shi da Siyama ba, daga gidan su Siyama ɗin har gidan su da kuma mutanen unguwa. Ita kanta Hajja farko bata yarda da cewar Siyama tana son Ibrahim ba, domin babu yadda bata yi ba ganin ta raba su, amma ganin yadda ya dage, itama kuma Siyamar har gida take zuwa ta gaidata yasa ta hakura. Ita kuwa Nana dama basa shiri da Siyama kasancewar tana da girman kai ga raini, ko a hanya suka haɗu sai dai ta wuce ta wuce. Ganin yadda suka shiga damuwa ne yasa Ibrahim daurawa ya miƙe yace Nana ta dafa masa ruwan zafi zai yi wanka. Kasancewar akwai wutan nefa yasa ta miƙe domin jona masa. Babu yadda Hajja bata yi da shi ba amma bai ce mata komai ba hakan yasa ta hakura tana ce masa karya sa damuwar mace a kansa fa, ya rufa musu asiri dan Allah shi kaɗai ga resu. Hajja na fita ya ɗauko wayarsa ya danna kiran number Siyama, amma ya jita a kashe ya ƙara kira nan ma a kashe, take ya sauke ajiyar zuciya yana ɗauke babbar wayar abokinsa da ya nuna masa wannan video ɗin. Kunna wayar yayi yaga ta shiga ki, ya cire kin kasancewar yasan ki ɗin wayar, Yana budewa vedio ɗin ya shiga aki kasancewar dama a kai yake, sosai yake ta bin ta da kallo yana so ya gano tayaya haka ta faru, mai yasa bai taɓa lura da cewar Siyama tayi amfani da shi ne domin cika muradanta ba. Yana cikin haka Nana ta shigo ta sheda masa cewar ta shigar masa da ruwan.
*****
Adawiyya.
Kallon Badawiya tayi ta ce “Ni matsala ta dake kenan wallahi shegen jiji da kai, yanzu dan Allah meye laifin kamfanin Baby and me da zaki ce bazayi aiki da su ba, ai ko domin mu wulakanta wannan yarinyar ai kya karɓa. Badawiya ta ce “Ni kaina sai yanzu nake da na sani, domin na bibiyi aikin naga a kwai tsoka, kuma ba wai aikin Contract za’ayi ba, zaka iya haɗa aikin su da na wani ba kamar na Magazing bane da babu dama kayi aiki da wasu har sai lokacin da ka basu ya cika. Adawiya ta ce “You see ni wallahi lokacin da naji Fita na faɗin wai ke kince bazakiyi aiki da ƙaramin kamfani ba abun ya bani manaki domin Baby and me suna biya sosai kuma suna da costoma a ko’ina. “To yanzu yaya kike so ayi domin gaskiya ina son wannan aiki? Badawiya ta faɗa tana kallon Adawiya da ta cika tayi famm. Ta ce “Ai kin gama zubar da damar ki wallahi, amma bari zan samu Fita idan yaso sai a cire wannan Nusee ɗin dan nasan babu yadda za’ayi da zai sa Shara ta fita. Sai a lokacin Badawiya ta ce “To ko dai musan yadda za’ayi a cire ita Munafukar Siyama ɗin sai kawai a saka ni. Adawiya ta ce “Ta yaya? Tayi dariya ta ce “Olusha” Adawiya ta riƙe baki tana dube-dube ko wani ya jisu. Take suka tafa suna ganin ashe ma ga hanya mai kyau da zasu bi su rusa wannan banzar.
******
*SIYAMA*
Duk da irin faɗuwar da gabanta keyi bai hana taji tsoron kar Ibrahim ya shaƙota ta baya ya fara dalla mata mari ba, sosai take tafiya ta ankare da shi, har sai da taga ta shiga cikin palon gidan nasu kafin ta sauke ajiyar zuciya tana jin in sha Allah ta rabu da ƙaya. A fili ta furta “Na tsallake ƙofa ta farko a cikin ƙofofin matsalolin da zan fuskanta. Tana ɗaga kai taci karo da matar kawu Inuwa wato mahaifiya Binta wacce suke kira da Momy. Kallo ɗaya tai mata ta kawar da kai gefe tana ƙoƙarin wucewa domin kuwa basa shiri da matar. Ganin tana ƙoƙarin yin hanyar ɗakinsu ne yasa ta faɗin “Ke Siyama dan ubanki bakya ganina ne da har zaki kama hanya ki wuce ni ko gaisuwa babu? To ke nake jira dama tun ɗazu nake zaune anan an kira number ki bata tafiya, idan har kina son kanki da arziki ki juya mu tafi gidana idan kuwa ba haka ba wallahi sai Ummar ku ta kusan hallaka ki, gata cen babu yadda ba’ayi da ita ba amma taƙi hakura, shi kan sa Bala da baida lafiya bata kyale sa ba, to sabo da haka ki juya yanzu mu tafi. Momy ta faɗa tana ƙarasowa gurin da Siyama take. Siyama da gabanta ya fara dukan goma sha tara-tara jin cewar yanzu kowa na gidan su yaji kuma ya gani kenan. Duk da cewa tana tsoron Umma sosai amma bata jin zata bar gidan nan ba tare da ta nemi amincewar ta akan fara aikin Model ba, ko da kuwa tsriranta zata yi ta cinye to wallahi sai ta tsaya ta ƙwaci yancin kanta. Momy ta ce “Wuce mutafi” Siyama ta ce “Babu inda zan je, yau ko soyani Umma zata yi sai dai tayi, aikin gama ne ya riga ya gama, kawai ki barni” Cikin tsawa da masifa Momy ta ce “Dan ubanki kin san halin da kika jefa ahalinki kuwa? Ina so na tafi dake domin zuciyarta tayi sanyi karta aikata miki abun da zai dameki keda ita amma kina cewa babu inda zaki, Siyama mai kike so ki zama ne, kije kina baiyana kanki a duniya akan kuɗi, to wallahi ina baki shawara akan karki yarda ki shiga cikin gidan nan har ki haɗu da Umma na faɗa miki. Momy na faɗa ta koma ciki ta bar Siyama tsaye idanunta na ta kallon mashiga sashen Umma ɗin…📝
Yanzu aka fara shiga labari, kudai kuci gaba da nuna goyon baya masoya.