Skip to content
Part 10 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Kwana biyu bana jin daɗi ga haushin gogewar da ya yi yasa bana rubutawa. Koda suka koma gida Umman Bashir ta yi ta surfa masa masifa, bai ce komai ba ganin ya yi shiru ta ce ya maidata mahaukaciya, wato ga ta tana magana ya yi burus ya ƙi cewa komai.

“Umma dan Allah me ki ke son ince kince in fita sabgarsu na ce to, yanzu kin dawo kince in auri Bushira, na ji zan aure ta, anman in har ke zaki min komai ki kuma ci damu.”

Tunzira ta kuma yi, “Wato ka mai dani yar iska, inma aure in kuma ci daku in ita waccan yar iskar ce, ai bazaka ce ayima aure ba, nasan da kanka zaka nema ka yi.”

“Ni ai bance ina son aure ba Umma. Sannan mu ba soyayya muke ba, koda ina sonta ban shirya surenta a nan kusa ba.”

Kinsan banda hanyar samu sai ta kanti duk, da cewar nawa ne anman taimakawa a kai aka ban, Inna dauko aure dole in raunana shagon, tunda kuɗin ciki zan ɗiba in ya zamto na ɗebe nai aure kinajin Alhaji Badamasi zai kuma ban wani jarin ne.

In ada ni kaɗai ne na ɗauko mata dole inci da ita, shekara ɗaya ta haihu wani nauyin ga naku. Bacin haka ga karatu na kinsan da kantin nake iya samun kuɗin tafi dashi, inna rusa shagon waye zai bani na kuɗin mota in Alhaji zai biyan na makaranta ba zai juri bani na mota ba kinsani.  Shi yasa in zakimin auren ni bazance komai ba.”

Shiru Umma ta yi kamin ta ce “Tom shikenan, na ji kaje sai ka shirya ɗin aman ka sani wallahi wallahi ko magana ka kumawa yarinyar nan ban yafe ba.”

A firgice ya ɗago ya kalleta, “eh kamaji da wai ni bazan laminta ba, ba kuma zan taɓa janye batuna ba.” Fuuu ta yi ɗaki.

Bashir ya jima agun yama kasa motsi, juya yadda za yi iya zama da sabarwa kansa rashin yima Ummu Hani magana yake, yadda kunnuwansa suka saba da jin muryarta idanunsa suka saba da kallon kyakkyawan murmushin ta.

Ya fi minti talatin kamin ya iya tashi yaja ƙafafunsa da ƙyar ya yi ɗakinsa ransa babu daɗi. Tunda ya shiga ɗaki bai fito ba, yama rasa mai yake tunani da mai yake damunsa.

Washe gari Ummu Hani ba tasa ran zuwansa ba, duk da abin na ranta ta kuma damu duk da ba son sa take ba anman ta saba da shi, aka ce sabo tirken wawa, mutuncinsa da karamcin sa na daban ne, hakan yasa yake da mahinmanci a gareta.

Haka ta yi yinin ranar sukuku, sai dai ta basar dan tun jiya ta fahimci su Aisha na cikin damuwa, kan abin da ya faru batason su fahimci rashin kwanciyar hankalinta su kuma damuwa.

Ranar juma’a tana goye da Muhd zata kasuwar sharaɗa dan siyo kayan miya, da yake su Aisha na gida ana hutu Aishan ce ke zaune gun abinci hakan yasa Ummu Hani ta samu faragar fita tun kan yanma ta yi.

Hangen Bashir da ta yi ne yasa ta faɗaɗa murmushin ta, ta ɗan ƙara sauri dan ta taddashi su gaisa dan ita a saninta Ummansa gidansu ta hana shi zuwa, ba yi mata magana ba.

Shiko hangota da yadda take murmushi duk sai yasa yaji wani iri, abunda ke ransa ya taso, yasan indai ta matso dab da kyar zai iya jure rashin mata magana, in kuma ya yi banza da ita abin zaifi masa ciwo.

Da hanzari ya shiga Masallaci duk da alwala zai yi ya fasa. Ita kuwa Ummu ɗan tsayawa ta yi, tabbas yaganta ko dai bai gane ni ba ta ce ta faɗa aranta, girgiza kai kawai tayi, ta yi gaba yana hangenta ta taga wani abu ya tsaya masa a wuya Umma bata kyauta masa ba, ya ce ya fito ya hau alwala ransa a cunkushe.

Duk ran Ummu Hani babu daɗi kawai ta basar ne dan tana da yaƙinin yaganta haka ta yi siyayyar ta dawo gida.

*****

Zaune take suna hira da Hajiya, dan yanzu da wuri abinci ke ƙarewa duk yawan sa, haka ma fanke su Aisha tuni ana SS 2, rayuwarsu ba perfect bace sai dai suna cikin farin ciki, dangin mahaifin su da na ummansu basa taɓa nemansu, ita Ummu bata nemansu da kyar Hajiya ta shawo kanta ta yadda wani zubin take ɗiban ƙannen nata suje.

Duk inda suka je haɗe musu rai ake, dan kowa zaton su in sun sake fuska yaran zasu buƙaci wani abin daga gunsu.

*****

Hasana da Usaina ne keta faman figarwa Ummu gashi, da sunan suna mata tsifa, yayin da Muhd ya rarrafo ya ture su, shi ala dole su dena taɓa masa Umma.

Hasana sarkin kishi ta make shi, Ummu ta ce lala kika dakar min ɗa, to matsa bana son tsifar taki.

Hasana ta turo baki kamar zata yi kuka. “Bashi ne ba ya raina ni bacin ni ce babba.” Hajiya tace “Kema dai Umma a gaban ki fa ya tsokane ta fa.”

Ummu ta yi murmushi “Gani ya yi suna min mugunta.”

“Ah ba wani mugunta, gani sukai umman tasu ta zama ƙazama gashi duguzun dugunzu.” Inji Hajiya.

Suka sa dariya, Usaina ta ce “Umma in mun tsefe miki ni zan miki kitso ko,” Ummu ta ce tom shikenan yau zansha kitso me kyau.”

“Wai yaushe za ki yaye shi Hajiya ta tambaya.”

“Eh to nima inason yayen anman dai bari zan ya shekara biyun sannan ya fara tafiya.” Umma ta bata amsa.

“Ai in ba gani yai kin yaye shi kin dena tafiya dashi unguwa ba ƙin tafiyar zaiyi, wayone dashi bakiga ba sai ya ga ba kowa yake miƙewa ba.”

Dariya Ummu ta yi, bari dai Hajiya mu ƙara watanni nima ina tsoron yayen nan, bakiga yadda Umman Walid ta yi ba datai yayen nan.”

Hajiya ta yi murmushi “Aikam dai kyayi kya gama, in naga kinƙi yaye shi ɗakina zan maidashi.” Kamar ko yaji, ya kuma lafewa jikin ummantasa yana tsokar mama.

*****

Cikin ikon Allah Muhd nada wata goma sha takwas, Hajiya tasa dole Ummu ta yaye shi, in Ummu zata fita su Aisha duk kukan Muhd sai sunsan yadda sukai dabara suka hana Ummu fita dashi, dan su kam so suke ta samu ta yi aure inda ita kuwa a tsarinta ma ayanzu babu aure.

Yau ma kamar yanda suka saba Aisha ce ta goya shi zata fi ce dan kar Ummu ta ce da shi zata kasuwa.

Ummu na ganin zata fita ta ce “Ina zaki kaishi kin manta zan fita.” “Kai yaya ki barshi a gida yanzu ba nono yake sha ba bare.”

“Kinga ni ki ajen yaro kunfi so infita yayita kuka dan mugunta.”

Kursum da ta shigo ne ta ce “To banda abin ki Ummu nauyi ma ai ya ishe ki yaron ai ya girma ga goyo ga kaya.”

Hararar ta Ummu ta yi, “Ta ina ya girma ni da abuna zan tafi.” Dariya Kursum ta yi, bari in tafi dashi gida in bega tafiyar ki ba ai ba zai kuka ba.

 “Ohni Hani, wai me yaron nawa ya tsare muku?” Kursum ta yi dariya “Ah kawai wahala muke miki tsoro.”

“Ni dabadan a gajiye nake ba ai da na rakaki, daga sch nake lectures ba daɗi, ina dawowa Umma ta ce in kawo miki kuɗin nan karta kashe.”

Ummu ta ce oh umma inta kashe ai ba komai, haka rannan taita bani haƙuri ni wallahi inta nine ma basai ta biya ba, ko yaushe na bata kuɗi sai ta takura sai ta biya.

Kursum murmushi tai, Wallahi bashin ma da kike bamu ba ƙaramin taimako bane Allah ne zai biya ki.

Wanka Ummu ta shiga inda Kursum ta karɓi Muhd da yake ta faman murna za su yawo ta yi waje.

Tsaf Ummu ta shirya cikin riga da zani na atamfa, tasa jan mayafi da ya yi kala da adon atamfar, hoda kawai ta ɗan goga dan rage maiƙo ta sa plate ɗin takalmin ta kamin ta leƙa ɗakin Hajiya ta ce Hajiya ni na fita, dan Allah karsu Hasana su tafi yawo in sun dawo daga islamiyya.

‘Tom sai kin dawo, Allah ya bada sa’a,” Ummu ta ce “Amin” Ta yi waje.

Cikin takun ta mai ƙayatar da mutane, take tafiya, wanda za kai zaton tana sane take yinsa, sai dai ko kusa haka halittar ta take. lokacin da tazo dab da shagon Bashir ta juya suka ma juna murmushi ta wuce, dan tuni Bala yaron sa ya faɗa mata Umman sa ta hana shi mata magana hakan yasa ta daina ƙoƙarin masa magana sai dai duk sanda ya zama dole suka haɗu sukanwa juna murmushi.

Tana tsaye bakin titi motar ta tsaya a hankula aka zuge glass ɗin mutumin ya laiƙo.

Hajiya dan Allah tambaya muke wane titin ne zai sadamu da makwarari. Dagowa ta yi inda ta ɗora idanun ta bisa wani da ke zaune yana dudduba wayar sa, lokaci guda gabanta ya faɗi bugun zuciyar ta ya ƙaru, karo na farko arayuwar ta da ta farajin haka.

Da sauri takawar da idon ta ta ɗora su kan mai tambayar da ya tsureta da ido. Cikin sanyar yar muryarta ta kwatanta masa, na gode yace, yaja glass ya rufe yaja motar ya yi gaba ta saki ajiyar zuciya kawai…

Tana fara magana ya ɗago sabida yadda sanyar yar murta ta daki kunnuwansa. Tunda ta fara magana yake kallon ta yama kasa cewa komai har Umar yaja motar suka bar gurin.

Da sauri ya dubi Umar yace Please mu koma, kallon ban gane mu koma ba u Umar yai masa, Sannan ya ce mu koma ina kuma.

Please juya kar ta bar gun, mtss umar yai tsaki sannan ya ce, kana da matsala Faruk, mu koma muyi mata me? Kasani nasani ba so bane, and she’s not your type ma.

Tsaki Faruk yai shima Please mukoma wallahi inta tafi bazan taɓa yafe maka ba.

Tsaki shima umar kawai ya yi, sannanya juya akalar motar zuwa inda Ummu ke tsaye, sunyi sa’a wahalar mota da ake tasa bata samu adaidaita sahu ba. Adai dai inda take suka parker motar Faruk ya buɗe ya futo.

Kamar ɗazun gabanta faɗuwa yahau yi ganinsa, cikin muryarsa me jan hankalin ƴan mata ya mata sallama ciki ciki ta amsa.

Baki samu mota ba ne? ya tambaya with concerned eh wallahi ta faɗa ataƙaice.

“Ok ko zaki shiga mu ajeki a inda zaki?” “A’a” Kawai ta ce.

Ok shima ya faɗa, a taƙai ce kamin yace ko zan iya sanin sunan. “Ummu Hani” ta faɗa, tana kallon gefe da alamun ƙoƙarin tsaida mota take.

“Ok Ummu da alamu dai a nan unguwar kike ko, eh ta ce yayi kyau ko za’a min kwatance.”

Ba musu ta masa kwatance ba yi ce komai ba ya tsaida me adai dai ta sahu ya ce baki faɗan ina zaki ba, Rimi kawai ta ce.

Shima Rumin ya ce da mai adai dai ta ɗin, yaron ya ce tom ku shiga.

No ita kaɗai zaka kai, make sure you drop her off a inda zaka ta and ka dawo da ita gida.

Shiga ko ya juyo yana kallon Ummu, tama kasa masa musu kawai ta shiga inda ya ciro dubu ɗaya ya bawa me adai dai ta ɗin, sai alokacin ta ce la’ila wallahi basai ka biya ba.

Kaga malan kuje ko me adai dai ta sahu yaja abarsa ba tare da yai musu ba.  A mota kuwa suna fara tafiya Umar ya ce,  Tsaya wai malam me kake nufi don’t tell me wannan karamar yarinyar itama kokarin sata cikin list ɗin yaran da ka yaudara zakai, umar ya faɗa yana duban Faruk.

Murmushi Faruk ya yi  “Ni na faɗa maka and point of correction kasan ni cikin su ba wadda na nema, su suka kawo kansu and am serious this time wallahi, sonta nake and to cut the story short mata ta nake son ta zama.”

Bushewa da dariya Umar ya yi “Dafa bakai bane Allah dai ya tsare musu yarinya. Haɗe rai kawai Faruk ya yi ya maida hankalinsa ga wayarsa. Kamar yadda Faruk ya faɗa mai adai daita sahun ya kaita ya kuma dawo ita dan shi kam riba ma ya samu abinsa.

A gida tunda ta dawo take tunanin mutumin da ko sunansa bama ta sani ba haka ta yi ta kirkiro aiki dan kar tunanin ya addabe ta. Tana hutawa ta hau gyara kayan miya dan kar dare ya yi mata su rasa markaɗe. Ganin har wurin shida su Aisha basu dawo daga Islamiyya bane yasa ta ce da Hajiya zata ta kai tabar mata Muhd.

Tana tafe tana saƙe saƙen mutumin ɗazu aranta ko me yasa ya tsaya mata arai oho ita ta rasa gano dalili.  Sai dai ganin har ta dawo ba wanda ya dawo cikin su Aisha sai hankalinta ya kasa kwanciya ba shiri ta barma hajiya kayan miyan ta ɗora ta yi islamiyar.

Tun daga bakin ƙofa hankalinta ya kwanta hango cewar taro ake na wa’azi sai yanzu ta tuna duk wata uku akan tara daliban amusu nasihoyi. Ganin ɗaliban musanman yan ajinsu duk sai ta ji babu daɗi ada habu abu mafi daɗi agareta irinta ganta cikin uniform ko na islamiya ko na boko gani yan ajinsu da suka fara karatu tare tun yarinta har yanzu sai ta ji tamkar tai kuka.

Har ta juya zata koma ta ji Malam Mahmud cikin lasifiƙa ya ce Ummu Hani shigo mana. Jiki a sanyaye ta shiga ta samu guri kusa da Kursum ta zauna tana sauraron wa’azin da ake yayin da take rungume da Muhd dan ta tawo dashi inta barshi bazai bari Hajiya tai girkin ba.

Tare suka jero da su Aisha da sauran ƴan ajinsu da suka saba tawowa tare lokacin tana makaranta mutun ɗaya ya ƙaru Muhd, tama kasa hirar kawai tafiya take abubuwa da yawa take tunawa a yanzun. Koda suka zo gurin da suke tsayawa suyita hira kan kowa ya yi gida kasa tsayawa tai dan ada in sun tsaya ba abinda suke tattaunawa sai shin me zasu karanta bayan secondry school sai gashi tasan yau in an tsaya bazai wu ce ai maganar me ake karantawa ba.

Sai da safe kawai ta ce musu inda Kursum ta bi bayanta su ka yi gida. Tunanin makaranta duk sai ya rage mata tunanin mutumin ɗazu duk da can ƙasan ranta shi ne fal. Ji take tamkar ta yi kuka sai dai kukanta na nufin tashin hankalin mutane da yawa duk da tasan kuka rahama ne takuma san in ta yi ne zataji sanyi a ranta sai dai bata da gun zuwa ta laɓe ta koka.

Haka ta yi ta yawo da damuwar ta wanda sai da ta gama komai kowa ya kwanta ya ɗauki alƙur’aninta ta hau karantawa a hankula hawayen ke bin kuma tunta jin kukan zai kwace mata ne yasa ta yi maza ta fita ta wanko fiskarta.

Gyarawa su Muhd lilliɓa ta yi sannan ta koma ta kwanta ranta fal abubuwa.

*****

Yau kusan kwana uku kenan da haɗuwar su, sai dai bai zo ba har ta fidda rai da ganin sa tana zaune tana wankin kayan su Usaina, Muhd na gefenta yana wasa da kayan da bata wanke ba yaro ya shigo gidan da sallama, wai ana sallama da Ummu Hani.

Shiru ta yi sai duk sai taji wani iri tunda take yau shine rana ta farko da aka aiko kiranta ko waye oho tama kasa motsawa ta cigaba da wankinta.

Aisha dake dakin girki na kaɗa miya ta lego kaje kace tana zuwa. Sajida Aisha ta kwalawa kira, kizo ki amshi wankin nan yaya zata fita. Ummu Sarkin kunya sai kawai ta tsinci kanta da jin nauyin yan uwan nata.

Hajiya dake gefe ta ce ke Ummu kinfa bar mutun da sauri ta miƙe ta ɗaura zanin ta dan tsaf take gami da zarar mayafin ta tai waje.

Muhammad da yasa kuka ne yasa ta dawo ta ɗaukeshi, Aisha za tai magana ta watsa mata harara ta yi waje kawai ɗauke da Muhd.

Faruk ne sanye da shadda sky blue ya juya baya jikin motarsa yana lallatsa wayarsa, kamar yadda ya saba baima ga fitowarta ba bare yaji isowarta.

Sallamar ta ce tasa ya juyo inda suka haɗa ido ya sakar mata murmushi.

Ahankula ta gaidashi ya amsa cike da jin daɗi dan shikam bai saba budurwar sa ta gaidashi ba.

 Sun jima suna hira kai ka ce sun saba ya amshi Muhd ya yita masa wasa musanmam da ya kasance Ummu akwai tsafta dan tsaf Muhd yake yana ta kamshin humra.

Sai wurin awa guda da zuwansa sannan ya ce zai tafi sallama sukai har ta juya ya ce a’a ina kuma zaki ai bamu gama sallama ba.

Juyowa ta yi yayin da shi kuma ya juya da alamu abu zai ɗauko a mota.

Kamar kuwa yadda ta zata sai gashi niƙi niƙi da ledoji kallon hannunsa a’a ko dai miƙa miki ciki zan dan nasan ba bani Muhammad din zakiyi in riƙe ki miƙa ba.

Da alamun mamaki ta ce “To aikam dai ni bani amsar wannan kyauta na gode.” Haɗe rai ya yi, “What, me kike nufi?”

“A’a ni ba abinda nake nufi kawai dai bazan amsa ba ka gaida gida ta juya ta yi ciki.”

Tsayawa yai kawai yana kallonta yarinyar farko da ya taɓama kyauta taƙi amsa.

Yaro ya samu ya ce ya miƙa mata ciki inda shi kuma yaja motarsa ya bar gun.

Yanayin comment da voting ɗin ku in ya burgeni shi zai sa in posting maybe within this week insha Allah.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ummu Hani 9Ummu Hani 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×