Bayan masu kawo lefe sun watse ne kasancewar a dangin Faruk mutum uku ne kawai suka kawo sai maƙotan su kawu da suka shirshigo, yawan kayan yasa da yawa suka dinga fita suna dawowa da wasu dan kashe kwarkwatar idanunsu.
Akwatu uku ƴan uwa suka juye da sunan wai zasu raba tsakanin su, haka akasa empty akwatu da sauran kayan a dan sahu dan kaiwa gidan su Ummu bayan watsewar kowa.
Ummu bata nan Sai Hajiya kawai, da ƴan biyu, ganin cikin wasu akwatunan babu kaya sai Hajiya ta tsorata dan tasan zuciya bata da kashi, kar ta faɗawa su Ummu ƙarya su dinga tunanin ko ita ta kwashe haka tayi ta alla alla wani cikin su ya shigo kan agama shigo da kayan.
Ilai kuwa ana shigo da akwatun ƙarshe sai ga Aisha, kasan cewar cousin ɗin ta maza aka aiko kawai gaidasu tayi ta shiga ɗaki, ganin Haka yasa Hajiya tace ta fito su mata Bayani.
Salim ne ya ce yauwa inna ta ce an ɗauki kayan akwatu uku, za’a rarrabawa ƴan uwa.
A tsorace Aisha ta kalle shi “Wane irin an ɗauki kayan akwatu uku, wannan ai ba daidai bane in aka kaita tace masa me tayi da kaya har haka.”
Shiru Salim ya yi, inda A’isha tace, “To wallahi bazai yiwu ba, ka faɗa musu wallahi duk wanda yayi anfani da wani abun da ya ɗauka sai ya biya, kawai sabida bamu da gata shikenan Allah ya bata miji wato kanma ta shiga agama zubar mata da ƙima.”
Tsaki Salim yayi ya juya ta ɗan ɗaga murya, “Na faɗa maka bari kaga yanzuma police station zan wuce wallahi da police zanzo gidan nan.” A ɗan tsorace ya kalle ta. Daga masa kai tayi, “Ba wasa nake ba.”
Ko da Ummu ta dawo cewa ta yi kawai a kyalesu, ba komai koma mene zai faru haka Allah ya yi, ita ta gaji da ɓatawa da dangin ta sabida halinsu, ta shirya karɓar koma mene daga gare su da kuma inda zata in sun zaɓi su wulaƙantata sabida danginta ƙanan mutane ne ba zata iya sauya hakan ba.
Haushi ne ya cika Aisha, ta kasa magana ji take me yasa tun kan Ummu din ta dawo bata je ta amso kayan ba anma ba komai.
Shiko Salim da ya koma gida ya tarar da iyayen sa anata rabon kaya, nan ko ya zayya ne musu yadda sukai da Aisha.
Aiko kai kace shine Aishar suka dinga masifa da zage zage, kan wai yaran su Ummu ƴan baƙin ciki ne waye waye.
Haka sunaji suna kallo suka kasa raba kayan, sai zanin gado Inna tasa su ta ɗaure ta hau jiran tsanmanin ganin anzo tafiya da kaya.
Da yanmar da aka kawo lefe Faruk yazo ya sha mamakin ganin yadda Ummu take, jiki suku ku duk kamar ma bata farin ciki damunta da yayi da tambaya ne ta ce masa bata da lafiya, hakan yasa shi cewa ta shiga gida gobe zaizo insha Allah zasu asibiti yanaso suje suyi gwaji.
Kallonsa ta yi da mamaki kafin ta bushe da dariya, “Yo yanzu let say munje anyi gwaji wani abin akwai matsala, ya kenan saki na za ka yi?”
Gabansa ne ya faɗi, “Saki kuma ana zaune ƙalau.” Ya faɗa jiki a salube.
“Eh mana to ni wallahi na manta da wani gwaji, kai kuma da kake sane da tun farko kanma mu saba ya kamata kayi maganar, ai shikenan kome ya faru tunda bani keda lefi ba Allah ya ban juriya takaicin kuma ya ɗora maka.”
Dariya ta bashi “Lallai yarinyar nan baki da kirki wato bakya tausayi na ko.”
“Eh mana tunda kasan da abu kaƙi Magana” Ta yi gaba kawai, kafin ta juyo “Yawwa kuma karka sake ka aikon da komai na faɗa maka.” ta faɗa tana haɗe rai.
Kome ta tuna ta juyo ta dawo, “Duk da munyi magana ta waya anma na haɗo dukkan jarumtata kaya fa sunyi kyau wallahi sun kuma ban mamaki jarumin nawa yayi ƙoƙari Allah ya barmu tare.” Ta faɗa gami yin cikin gida.
Yadda ta yi sai ya bashi dariya, motar sa ya shiga yaja duk da yana fargabar ya goben zata kasance anma kuma sai duk yake jin farin ciki ya cika shi.
Har ya hau babban titi Buk road ya tuna ashe fa abu biyu yaje yi fa.
Wayar sa ya ɗauka ya hau kiran ta, bayan ta ɗaga ne ta ce “lafiya dai ko an fasa gwajin ne.” ta faɗa tana dariya.
Shima dariyar ya yi Ummu akwai zaulaya, ya faɗa aransa afili kuma ya ce, “Ina ai dole ne bakisan yadda Dad ya takura ba nasan in bamuje ba zai iya raba auren nan.”
“To to Allah ya tsare.” ta faɗa tana Dariya.
Amin ya ce, kafin ya ce “kinga mantuwa nayi daman su Anti ne suka ce sun yi mantuwa kayan cikin brown akwatu guda huɗu da na bakko da buhun shinkafa na dangi ne.”
Wani daɗi ne ya cika ta, Bama tasan lokacin da ta hau godiya ba.
Murmushi ya yi kefa ko to “duk mene na godiyar ni da aka ban ɗiya kyauta.”
“Cewa akayi baka ni akayi, kawai dai zan dawo gunka da zama ne ta faɗa awasance…sun ɗan taɓa hira kamar ba ɗazun suka haɗu ba, kafin ya yi mata sallama ya kashe wayar.
Da yanma ta nemo me adaidai ta sahu tasa aka fita da akwatu uku, da buhun shinkafa ɗaya ta haɗa Sajida da su dan tasan Aisha bata da hankali zata iya janyo wata masifar inta je.
Inna na zaune takaici duk ya cika ta, gadai kaya tana gani anma ta kasa anfani dasu kullum sai ta buɗe ta kalla banda kusan kullum sai wata tazo gani anma sun kasa rabawa.
Sadija a mutunce ta gaida Inna kafin ta ce, “daman da wani muke zai shigo da kaya.”
Kallon ta Inna ta yi shigowa ko ɗauka inna ta tambaya.
“Eh duka biyun ne zai shigo da wasu zai ɗauki wasu.” “To” Kawai Inna tace taja gyalenta ta yafa.
Mamaki ne ya cikata ganin akwatuna “Towo” ta faɗa aranta wani lefen ne haka.
Sajida ce ta ce, “Yawwa wai jiya sunyi waya da Yaya Faruk ɗin, ya ce mata an manta ba’a faɗa ba waɗannan ne na dangi da shinkafar nan.” Ta ce ta ɗau akwati guda shi zata bawa dangin ummanmu.
Farin ciki ya cika Inna daman tun farko su taso su ɗauka, wasu suka ce su dauki waɗan can ai shikenan kaya ya tsinke a gindin kaba.
Ɗakin da kayan suke ta nunawa me shigo da kayan suka cicciɓa suka kai adaidaita sahu da ƙyar suka shiga shima sai da dabara.
Sajida ce tace zanin gadon in wani zaizo zai kawo ko in wani yazo sai ya tafi dashi.
“To kawai Inna ta ce ta yi cikin gida rai dik farin ciki.
Sadija na tafiya ta aika Basira ta kirawo kata sauran Faccalolin nata, suka hau kasa kaya.