Skip to content
Part 15 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Washe gari da wuri Faruk yazo dan suje asibitin, kasancewar tun jiyan ta sanar da Hajiya ita kuma Hajiyar ta ce su tafi da Aisha ko Sadija duk da cewar an ɗaura musu aure anma tunda ba kowa ya sani ba kamar mutan unguwa tafiya da ɗaya daga cikin nasu zaiyi kyau.

Tsaf suka shirya duk su biyun sun yi kyau, duk da kasancewar Sadija ƙarama anma kyanta ya gama fitowa dan tafi Ummu kyau sai dai kawai Ummu ta fita kwarjini.

Yana tsaye jikin motar sa, ya zubawa ƙofar gidan nasu idanu hannayen sa harɗe kan ƙirjinsa yayi kyau sosai kana ganinsa kaga angon.

kuwa Ummu da Sajida sun san ya tsure ƙofar gidan nasu da idanu, Ummu ce ta fara fitowa karaf suka haɗa idanu ya sakar mata murmushi yayin da ita ma ta mai da masa, a ɓaɗi ni kuma godewa Allah ta yi domin tasan in da badan ikon sa ba babu abin da zai kawo Faruk ya ce yana sonta har ya iya auren ta..

Ta ko ina ya mata zarra, wani zubin har tunani take ko me yasa yake son ta, in ta rasa amsa ta ce ikon Allah kawai.

Shi gashi mai kuɗi, ɗan mai kuɗi, kuma ɗangata me illimi, ga kyau wanda ko da ace iya shi kaɗai yake da shi da yawan ƴan mata zasu soshi.

Ita kuwa gata marainiya, cikin marayun ma mara gata, ba illimi ne da ita ba gashi ba wani kyaune da ita ba, hasalima duhun fatar ta yasa take ƙara mamakin yadda yake sonta kuma so na gaske, eh mana na gaske tunda har zai iya aurenta.

Yadda ta sani shine matasa munana ma marasa gatan faruk basa son bakar mace bare irin sa.

Ɗan hura mata fuska yayi, ganin tunanin nata yaɗan yi zurfi, “Mrs Faruk tunanin me ake ne haka.”

Murmunshin da bata san ta iya shi ba ta sakar masa, yayin da ya sandare a tsaye ransa cike da abubuwa, ko yaushe da komai na yarinyar birgeshi yake, yanzu sai ya ji inama inama….

Samun kansa ya yi da cewa, “Wai yaushe zaki tare ne?” Murmushi ta yi sai na yaye Muhammad.

A tsorace ya ce, “What, kina hauka ne?” Dariya tasa ta dan zagaye shi ta shiga cikin motar muje ko ta ce dan taga sadija tun ɗazu zaune a baya. Lokacin da tai nisa cikin tunani sajidar ta shiga.

Ɗan langaɓar da kai yayi ya kalleta, gami da girgiza kai, kafin ya zagaya ya shiga shima daga bisani yaja motar.

Ɗan ruko hannun ta ya yi, “yanzu ke bakisan Genotype dinki ba?”  Ya tambaya, kalar tausayi ta yi, “Oh ni sau nawa zan ce maka ban sani ba, nadai san ba sikila ba ce may be As.” Da hanzari ya ce “Ina ke AA ce.” Dariya tayi yadda yayin ya bata dariya shi kuwa sauya topic din yayi zuwa wani

“Wai tunanin me kike ɗazun?” Ya tambaya cike da kulawa, kallon sa tayi kafin ta ce “Kai dai bari kawai zuciya ta ce ta dinga faɗamin yanzu ya zanyi inda matsala a gwajin, nidai inason ka anma fa inason ƴaƴan da zan haifa.”

A tsorace ya kalle ta, “Me kike nufi?” “Nasan ka fahimta anma bari in ma bayani dalla-dalla, ina nufin in da wani abun sai ka turo ka amshi kayan ka a fasa.”

Banza yayi mata yama ƙure radion motar, yayin da ita kuma ta guntse dariya yana kallon ta haushi ya cikashi bai dai ce komai ba har suka isa asibitin Muhammad wase wato Nasarawa.

Da sauri ya fice ita da Sajida suka rufa masa baya, ɗan gaba tayi ta riƙo hannunsa, haba nawan Mijin Ummu bama haka da kai, mene na fishin?, ai ni da kai mutu ka raba.

Juyowa ya yi yana murmushi haba ko da naji da kina wani batun rabuwa ana zaune ƙalau, murmushi mai kashe jiki ta sakar nasa wanda duk yadda Umarancin ya tashi in ta masa yakan manta da shi din Umar ne dan Usman yake komawa.

Office ɗin Abokin sa Umar suka nufa, cike yake da marasa lafiya dan haka baima yunƙurin shiga ba, kawai gefe suka samu suka zauna kafin ya fara neman Number ɗin Umar ɗin.

Bugu guda ya ɗaga, yawwa mun iso ya za’ai kenan?, Faruk ya tambaya ok ku jira am busy zan aiko wanda zai kai ku lab ɗin, umar ya faɗa daga ɗaya ɓangaren ok kawai Faruk ya ce ya katse kiran.

Zaune suke suna hira Ummu da tsokana ta ciyota sai ta rafka tagumi, hankalin sa ne ya tashi wannan kuma na mene lafiya?

Kai dai bari kawai nawan ayyana yadda zan ji nake in muka rabu, wai ke me ke damun ki ne? ba nace banason maganar ba.

Yo to banda abinka ai dole ce, tunda kuwa kai kaja da tun farko anzo anyi gwajin nan da inma rabuwar ce da tuni mun manta da juna.

Allah Ummu Hani ranki zai ɓaci, dariya ta guntse wato Umarancin ya tashi ta faɗa aranta, dan duk da cewar ba Umar ake ce masa ba Faruk ne amma yakan taɓa faɗan su Umar ɗin, abinka da masu iya magana da suka ce suna linzami tabbas ta yadda haka ne kan Faruk ɗin ta.

In dai kaji ya ce Ummu Hani to faɗan ya tashi, dan Ummu ya ke cewa wataran Hani. Dariyar da ta ƙunshe ƙara ƙona masa rai tayi, wato daman ba sona kike ba ko.

Kallon sa tai a shagwaɓance tayaya zan ce bana sonka, kawai dai nafison future ɗin yarana, tsaki yayi to kuwa sai inga mai sawa in sake kin, dariya tasa aiko dole ne, ni kaga ma da takarda ta nake tafe sai mu ari biro gun Yaya Umar tsaki ya saki sai kuma kiyi, gami da miƙewa sabida zuwan yaron da zai kaisu lab ɗin.

Guntse dariya tayi in da ta miƙe su ka bi bayansa.

Sai dai yadda yake ta kumbura yasa ta kasa jurewa dariyar sai da ta fito fili a hasale ya ce wannan wane irin rashin mutunci ne zakizo kina ta wani yiwa mazan waje murmushi.

Hannun ta ta haɗe ayi haƙuri yallabai bazan kuma ba, kima kuma ɗin ya faɗa bata ce komai ba sai murmushi da tayi.

A lab ɗin an gwada su, sunyi jiran kusan awa biyu kafin komai ya haɗu faruk ya rasa me ke masa daɗi, daga ya zauna sai ya miƙe ya koma ya buga tagumi in ya kuma tuno wani abin sai ya miƙe zunbur.

Sajida tun abin na bata dariya har ya koma bata tausayi, ta koma yiwa yayar tata faɗa kan ta dena masa dariya.

Yaron na fitowa riƙe da takardu ta miƙe, Congratulations Mijin Ummu Genotype dina AA blood group A positive.

What! yakalle ta cike da Takaici wato daman kin sani.

Eh mana kawai na kyaleka ne in dan ganya zakayi.

Lalle yarinyar nan, zonan ya faɗa, ta ɗan matsa tana dariya takar dun ya bude kamar yadda ta faɗa haka ne, haka kuma babu wata matsala HIV dinma babu me ita a tsakanin su Farin ciki ya cikashi.

A mota suna tafe suna hira ya ce to me yasa baki damu da batun HIV ba?, murmushi tayi kawai nasa araina babu me ita cikin mu, daman Genotype ne kake As to nasan ba ita bace ni, shi yasa na yadda da me raina ya ce na ɗanyi nishaɗi.

Murmushi yayi ya girgiza kai, ai ki bari kawai ɗazun wallahi daurewa kawai nayi, dan ji na dinga yi kamar ama fasa in sace ki in gudu in yaso Dady dole ya hakura, daga baya kuma da kika kuma ƙonan rai naji kodai inna sace kin in haɗa da zane ki.

Dariya tasa tace oh wayaga miji da sace matar sa.

Gida ya sauke su namma sun taɓa hira kafin ya wuce gida. Sunyi Ummu ɗin zata zo ta gaida Hajiyar sa shima dakyar ta amince sai da yayi ta roƙar ta ƙarshe ta ce shikenan in zata kasuwa zata biya

Yai yai ta yadda yazo ya kaita ta ce bata san zance ba.

*******

Faruk na sauke su Office ɗin Dady ya wuce, ko gida Baije ba ya kai masa Dady yaji daɗi dan shi kansa har tunanin ta yaya zai iya shawo kan ɗan nasa ya yadda ya saki matar tasa in an samu akasi yake. 

Ko da ya koma gida ma da murna ya ƙarasa ɓan garen mum ya sanar mata, itama ta Taya shi murna nanma yake faɗa mata sunyi da Ummu zata zo gai da ta, tayi murna da hakan dan su in tasu ne ko ba kaya akawo yarinyar dan dai kawai basa son nuna zagewa danginta suyi tunanin kamar ƙoƙarin siyen ta suke.

Ka faɗawa mai gadi sunan ta in tazo ya barta ta shigo, kaga mu muna ciki ba sani zamuyi ba kar ya hanata To ya ce gami da miƙewa.

A’a ina kuma zaka Hajiya ta tambaya zanje in faɗa masa ne girgiza kai hajiya tayi tana murmushi yo to yanzu zata zone ta tambaya.

A’a ya ce kawai dai naga gwanda in faɗa masan to kawai ta ce ta shige ɗakin ta.

Baba me gadi na zaune najin radiyo Faruk ya gai dashi, kafin ya ɗan zauna su taɓa hira ya ce yawwa Daman zan faɗa maka ne matata zata zo sunanta Ummu Hani in tazo abarta ta shigo.

Murmushi Baba me gadin yayi to shikenan, ni na ɗauka ma ta kusa tarewa? me gadin ya tambaya.

Eh to muna sa ran wannan watan ko wani Faruk ya bashi amsa.

Tom Allah ya kaimu ya sanya alkairi Baba me gadi ya Faɗa, Faruk ya ce amin kafin ya miƙe ya koma ciki yau kam yayi missing ɗin gurin aiki dole ya haƙura da zuwa.

Yadda Faruk ya dame ta kan cewar ya fa faɗawa Mum ɗin su zata zo yasa ta daure duk da kasan ranta tanajin be dace ba, dan dai kawai ta faranta masa, dan ko Hajiya bata faɗawa ba bare ƙannen ta, ta nufi gidan su Faruk din da zummar daga nan zata wuce kasuwa.

Ba wata wahala mai gadi ya barta ta shiga, dan tana cewa Ummu Hani ce ya ƙara faɗaɗa murmushin sa, sai dai kuma Hajiyar ta fita sai ki kira mai gidan naki ya faɗa mata dan shima ya fita aiki.

To ta ce bayan ta shiga masu aiki suma sukayi ta nan nan da ita, sai yanzu take ƙara kissima girma da iko na Allah da ya bata Faruk a matsayin miji, matsayin su kwata kwata ba ɗaya bane.

Ruwa tasha kafun ta kira ta faɗa masa tana nan fa, ruɗewa yayi ya kashe kiran ya kira masu aiki kan su kakkawo mata abinci yace ta jira gashi nan zuwa ita Hajiya tayi tafiya anma zai kira yayar sa da ƙanwar sa to kawai ta ce ta aje wayar.

Kamar minti goma sha biyar kuwa sai gashi yayi ta nan nan da ita, shine har da zagaya wa da ita cikin gidan duk ya nuna mata ɓan garen kowa. Ƙarshe shine inda zasu zauna.

Gurin yayi mata kyau koda ace iya haka aka barshi ya ishi mutun rayuwa, fita yayi ya ɗebo kayan abinci kafin su zo ataimaka a girkan me zanci.

Kallon sa tayi da mamaki ni da zan tafi, murmushi yayi Allah kinason in kulle ki anan inje in faɗawa hajiya kin ce kin zo kenan.

Ware ido tayi rufan asiri nida Bama tasan nazo ba.

Madafar ta nufa inda ta hau ƙokarin dafa masa, taliya ta dora inda ta fara gyaran kifin da ya kawo dan tasan shi yake so asa tunda ya kawo.

Ba wani girki me wuya tayi ba sai dai kafin wani lokaci falon ya cika da ƙamshi, dan Ummu gwana ce, kasa jurewa Faruk yayi ya taso ya shigo.

Ya jima yana kallon ta kafin ya ƙaraso inda take, hannayen sa ya ɗan zargo jikin ta hakan ya tsorata ta ta ɗan tureshi mene hakan ta faɗa.

Murmushi yayi ba komai kawai kwakwalwa ta ce ta ayyana min haka zan dunga takura miki in kika tare.

Murmushi kawai tayi ba tare da ta ce komai ba.

Me za’a taya ki dashi? Ya tambaya ba komai ta ce, Nama fa gama ta faɗa gami da juyowa sauri tayi ta meda kanta inda yake, batai tsammanin ganinsa ahaka ba singlet ce a jikin sa da short, ko yaushe ya cire kayan jikin sa oho ta faɗa aranta.

Taimaka mun da wannan ta nuna masa plate ɗun da ta zuba abincin ya taso ya ɗauka sukayo waje maimakon dining a falo ya dire, ya je ya dauko ruwa da lemo ya dire musu.
Bisimillah ya ce. Kallon sa tayi nifa bance inajin yunwa ba.

Dariya ya yi mata in kuma kinga kin bar gidan nan sai mun cinye ya faɗa bayan ya matso da abincin kusa da ita.

Yanaci yana murmushi duniya ji yake yafi kowa sa’a ga shi ya samu mace kamila ga iya girki abincin ya masa daɗi.

Tas suka cinye inda ya daɗo musu shima suka cinye, Ummu na wanke kwano ya shigo riƙe da waya ga Anti Farida kuyi magana.

Rokarta Faridan tayi kan ta jira yara take jira su dawo yanzu zata zo samun kanta tayi da kasa cewa a’a ta ce to, sai da ta dawo Falo sannan ta kira Hajiya a waya kan zata biya ta gidan su ƙawar ta Maryam zata jima, to kawai Hajiya ta ce kafin ta ce in baki dawo ba zuwa uku zan fita  sai ki amshi makullun a gidan su Walid to Ummu ta ce sai kin dawo ta katsewa wayar.

Kusa da ita Faruk ya dawo ya zauna ta ɗan Dube shi dan Allah ka canja kaya, to yace muje kiga ɗakinmu banza ta masa.

Dariya yasa ya matso kusa da ita sosai, kasa magana tayi kafin ta ce Allah fa nace maka.

Nima Allah na hadaki da shi kizo kiga dakinmu…

*****

Takaicin duniya ya ishi Ummu ta rasa me yasa ta kasa danasanin zuwan ta gashi kuma ta kasa yin farin cikin zuwan kawai dai gata nan gatanan ne shiko Alhaji Faruk zato yake facci take hannunta ya ruko inda aɗan kuma ya ɗan shafa kanta farin ciki ne fal aransa a zahiri kuma a hankula ya ce Allah ya biya ki taya ni riƙon mutuncin ki da kikai samun kanta tayi da cewa Amin aranta.

Bugun kofar ɓangaren nasu yasa shi tashi ya fito yayin da Ummu ta ka bude idon ta ahankula takaicin duniya ya ishe ta Allah dai yasa koma waye kar ya shigo ta samu ta rarrarafa ta tafi gida.

Da alamu addu’ar ta bata karbu ba dan kuwa muryar mace taji tana cewa Wallahi Faruk baka da kirki wato shine kayiwa ƴar mutane fyaɗe ko sosai kai yayi yana dariya kai yaya mata ta ce fa Allah ba inda zata ma ni ta tare.

Ware ido Ummu tayi ta yun ƙura zata tashi itakam bazata zauna ba sabida ita ta kawo son miji duniya kawai sai ta kawo kanta tace ta tare, sai dai duk jarumtar ta sai da taji babu dadi.
Tsaki Farida ta yi gami da shiga ɗakin ita ta taimakawa Ummu ta yi ta mita dan me zata buyewa Faruk sai alokacin ta samu ta sa kuka.

Shigowa yayi haba Yaya dan Allah kawai sai kisa yarinya kuka hararar sa tayi ya juya ya fice kan tayo kansa da masifa.

Ruƙo hannunta Ummu ta yi dan Allah Yayarmu karki faɗawa su Hajiya nama zo dan Allah.

Karki damu bazata sanu ba Faruk ya ce kasuwa zaki muje sai ib sisiyo miki kayan in yaso sai in sauke ki hakan kuwa ba karamin daɗi yayiwa Ummu ba.

Koda ta fito Faruk na tsaye ya yi saurin tako watsa masa harara tayi inda motar yaya Farida take.

Shi komai tayi birgeshi take bai ce komai ba ya koma cikin gida yayin da Farida taja motar suka fice.

Yadda ta faɗa ɗin haka ne ya faru a mota tabar Ummu ta fita ta siyo mata abinda ta ce danma Ummun ta yi ta roƙonts karta ƙara kan abin da ta fada mata da siyayya sosai zata mata.

A gida ta sauke Ummu ɗin yayin da Umnu ta aika aka amso mata makullin Yaya Faridan ce ta sauke mata kayan sukai sallama ta tafi.

Bata jima ba aka aiko Khadija da Muhd yako sha kukansa ya more tausayin sa ya cikata.

Ta rungume shi a ƙirjinta tanajin ajiyar zuciyarsa, zataje ta roƙi malamin su Aisha gaskiya in dai zata fita ba tare da Muhd din ba gwanda Aishan ta tafi dashi makarantar tunda yaƙi sabawa da maƙotan.  

******

Zaune take tun inda ta zauna tun shigiwar ta ta kasa tashi gyaran tattatasai take inda akai sallama.

Amsawa tayi kafin ta juya dan gano me sallalar dan bata ɗauki murya ba. Matashiya ce da ba zata wuce shekaru ashirin da biyar zuwa da shiga ba. Fara ce doguwa kyakkyawa sanye take cikin jan bakun lesi mai adon golden wanda ya dace da kalar fatar ta da sauri Ummu ta nuna ma Hasana kujera ta ce miƙo mata.

Sai da Matashiyar ta zauna tukunna suka gaisa da Ummu kafin kowa yayi shiru.

Tabbas kam yarinya ce Matashiyar ta faɗa aranta yayin da take kissima shekarun Ummu tasan ta girmi Ummu ita a tunanin ta ma ta bata shekaru bakwai zuwa takwas ta ce dole Faruk ya rikice yaga yarinya duk da yadda take jin irin son da Faruk kewa yarinyar tayi zaton zata ganta wata tsaleliyar Mace.

Ummu ce ta katse mata tunani sai dai ban gane ki ba ko gun Hajiya kika zo.

Murmushi tayi a’a gunki nazo ke ce Ummu Hanin Faruk ko Matashiyar ta tambaya.

Eh ni ce Ummu ta faɗa gami da faɗa ɗa murmunshin ta dan tayi zaton ko ƙanwae Faruk ce musanman ma ganin kalar su tazo ɗaya.

Sunana Fatima matashiyar ta faɗa ni tsohuwar budurwar mijin ki ce ko in ce dadiron sa.

Cike da mamaki Ummu ta kalleta Dadiro kuma ba kece Fatimar Gidan Aminin baban su Faruk ba ya ban labarin ki amma ni bai faɗan wani aibu daga Tarayyar ku ba.

Murmunshin Fatiman tayi yo daman ta ina zai faɗa miki, nima da nazo in faɗa miki ne sabida abu guda wato kishi amma da na ganki sai tausayin ki ya kama ni baki can canci miji irin faruk ba.

Ɗaga mata Hannu Ummu tayi koma dai mene yanzu shi ɗin miji nane kome yayi ya wuce ya kuma tuba.

Dariya Fatima tasa au daman ai haka zai ce miki bari kiga ta zaro wayar ta ta ɗanyi danne danne ta miƙowa Ummu.

Wannan da kike gani jiya ya faru, kallo ɗaya Ummu tayi ta kautar da kai Domin yafi ƙarfin idon ta innalillahi wa’inna ilaihirraji’un ta faɗa mijin ta da wata ba ita ba kiri kiri tama kasa magana ta kuma kasa miƙawa Fatima wayar.

Yayin da ita kuma Fatima ta zuba mata ido dan son gano me yarin ke kullawa aranta….

<< Ummu Hani 14Ummu Hani 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×