Skip to content
Part 16 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Miƙa mata wayar Ummu Hani ta yi, kafin ta ce, “haka ne bancan canci miji kamar Faruk ba sai dai kaddara ta zaɓa min shi, na karba Allah yaban ladan hakuri zan cigaba da yi masa addu’a, shidin mijinane an riga an ɗaura bacin haka ma yanada wani bangare nasa na gari zan kalli wannan ɓangaren in ci gaba da zama dashi, karki damu ina ji a raina zai daina ko me yake.”

Sakato Fatima ta yi tana kallonta ada ta raina shekarun yarinyar tana zaton tana nuna mata zata rushe da kuka ta tubure sai ya sake ta, sai yanzu ta kuma yadda mace da wayon ta ake haifanta ba wai shekarunta ba.

Shiru su kai na wani lokaci kafin Fatima ta ɗan yunkura, “Ni zan wuce anma dai ki sake tunani.”

Murmunshin Ummu Hani ta yi, “Ki gaida gida, na gode ta bawa Fatima amsa ba tare da ta bata amsar mai ta ce ba.”

Da kyar Fatima ta iya kaiwa motar ta yadda ƙafafunta su kai sanyi tama rasa me ke wakana aranta, ta jima a motarta kafin ta iya janta ta bar layin.

Tana barin layin ta faka motar yadda ta ji bazata iya tuƙin ba, wayar ta ta ɗauka ta hau laluben lambar da take son kira.

Bugu ɗaya aka ɗaga kamar kiran nata ake jira, kana ina ta faɗa a kasalance banji me ɗayan ɓangaren yace ba sai ji na yi tace ok ina inda ka min kwatance ta aje wayar.

Kamar minti biyar ya iso, Matashi ne da ba zai wuce shekaru talatin da biyu ko uku ba, Ba fari bane sai dai bama ce masa baƙi ba kyakkyawa ne dogo ba can ba, sanye yake da manyan kaya na Hausawa ruwan madara duk da a rikice yake bazaka kasa gano kamalar sa da tsantsar nutsuwar sa ba.

Daga dan gaba kaɗan ya aje motar sa ya ƙaraso inda motar Fatiman take har da ɗan gudun sa.

Kishingiɗe take jikin kujerar motar idanun ta a rufe sanin halinta yasa bai kwankwasa ba ya buɗe yadda ya zata a buɗe kuwa motar take, cikin muryar sa mai cike da kwarjini yace me ya faru bana ce kar kizo ba.

Hararar sa tayi tace ni buɗen baya kwanciya nake sonyi bai ce komai ba ya buɗe mata, ta miƙo masa hannu alamar ya tai maka mata ta fito kamar bai san me take nufi ba ya juya baya.

Ɗan ƙaramin tsaki tayi ta fiti ta koma baya ya rufe ƙofar ya koma mazaunin driver gami da jan motar.

Tafe suke kowa da abin da ke wakana aransa kamin matashin saurayin ya ce, “Wai me ke damun ki ne.

“Ban sani ba.” Tace inda ka damu da me ke damu na ai da ka taimakan ka dawo dani baya anma tsabar wuƙanci ka wani juyar da kai.

“Wai dan Allah Fatima ke wace irin mutun ce, sau nawa zance miki azabar Allah ta tabbata ga wanda ke taɓa jinsin da ba muharramin sa ba.”

“Kaga malam wannan lalura ce ba wa’azi nace kamin ba.”

“Ba wata larura…” Katseshi ta yi cikin faɗa “fitar min a mota.”

Bai kuma cewa komai ba ya faka motar a gefen titi ya fita, inda ita kuma ta dawo gaba taja motar ta tabar gun a guje. Girgiza kai kawai yayi ya hau ƙoƙarin tsayar da Ɗan sahu.

Mansur kenan da ga Alhaji Muktar hamshaƙin ɗan kasuwa da ya yi ƙaurin suna a fannin sa. Mansur yaro ne dan gata abinso ga iyayen sa a nutse yake ga hankali da sanin ya kamata duk cikin abokanan mahaifinsa kowa burin sa inama Mansur yaron sa.

Shi kansa Mansur zamu iya cewa ya shahara a nasa fannin dan ba irin yaran nan bane masu dogaro da abun iyayen su tun yarinta Allah ya yi shi da son neman nakansa.

Sauƙin kansa ba zai sa kayi tunanin shi din wani bane. Tun tasowar Fatima Allah ya jarabce shi da son Fatima sai dai ita ko kaɗan bashi bane a gabanta hasalima bata kallon sa a matsayin namiji.

Duk da cewar yasan abinda suke da Faruk, sai dai ko sau ɗaya zuciyar sa ta kasa tsanar ta shi kullum burinsa ɗaya ne ta shiryu ta zama ta kwarar ta so shi ko da ƙimar ƙwayar zarra cikin kason soyayyar da yake mata ne.

*****

Fatima na fita Ummu ta sa kuka dauriya take tun ɗazun tasan da Fatiman ta kawo yanzu a gidan nasu da tabbas kukan nan zai iya kwace mata a gaban Fatiman kamar yadda ya kwace mata yanzu.

Muhammad ne ya sa hannu ya hau goge mata hawayen yana gwalan gwanton su na yara, goge hawayen ta yi sai dai ba alamun zai tsaya Usaina ta kalla ta ce karku fita karki bari Hasana ta daki dan ƙani to Usaina tace ta cigaba da fige tattatasan da take kar kace wata babba ce.

Ummu na shiga ban ɗaki kukan ya kuma kwace mata kuka ta yi mai isarta da tayi shiru sai abin da ya faru da ita da Faruk a gidansu ya tasomata gami da abin da ta gani a wayar Fatima duk da aranta bata yadda jiya a kai video ɗin ba anma tanajin wani ɗaci aranta ganin mijin ta da wata a gado.

Sai da taji faɗan su Usaina daga tsakar gida sannan ta tuna bafa iya tata rayuwar ce mai mahimmanci ba akwai ƙannen ta a ƙasanta. Wanke fuskar ta tayi ta fito da sauri dan jin yadda faɗan ya gauraye Muhammad na kuka Hasana na kuka.

Ilai kuwa Usaina ta gani na haki riƙe da kwano wanda da alamu bugawa Hasana ta yi, kwanon ta amshe kafin tayi ƙarfin halin cewa mai yasa zaki buga mata kwano bana hanaki mugunta ba ke bakisan Yayar ki bace.

Cikin rawar murya Usaina tace “Allah Umma ita ce muguwa nace mata karta daki dan ƙani taƙi wai dole sai ya bata tumatirin da kika bashi bacin ga wasu nan da yawa nace ta ɗauka a ciki taƙi shine ta makeshi nima na make ta.”

Murshi Ummu Hani ta yi yaran akwai rikici Muhammad ta ɗauka ta hau lallashi yai luf aƙirjinta, ta hau rarrashin Hasana da haka ta ɗan samu damuwar ranta tayi sanyi suka cigaba da gyaran kayan miyar.

Suna nan zaune su Aisha suka dawo ta ce bari ta kai markaɗe Khairiyya da Sajida su kai sukai ta bari su kai kamar yadda suka saba tace ita zata kai tanason zuwa gidan su Ummul Kairi dole suka kyaleta badan sun so ba.

Ba inda zata kawai tana son samun sa’ida aranta ne dan tasana in ta fita zata iya jin sanyi a ranta.

Tafe take tafiyar ma juriya kawai take zuciyar ta babu daɗi yanayin garin da yanayin zuciyar ta sai in gizata suke tasa kuka anma tana daurewa.Kamar ance ta kalli gefe karaf sukayi ido biyu da Bashir murmushi ya sakar mata daurewa tayi ta maida masa bayan yaƙi datai da hawayen da ke ta yun ƙurin sai ya zubo kuncin ta.

Tasowa ya yi yayo inda take ba haka taso ba  dan ko kaɗan bata shirya yin magana ba a yanzu sai dai Bashir ya wuce ta ganshi ta wuce.

Gaidashi ta farayi kafin cikin sauri tace Dan Allah karka min magana banson bakin Umma ya kamata ta dalili na. Yadda tayi din yasashi dole tsayawa inda ita kuma tayi gaba wani abu ya kuma zuwa mata wuta ya tsaya ji take tamkar ta rushe da kuka inda tasan zata ga Bashir da tabbas bazata fito ba maimakon zuciyar ta ta yi mata sanyi sai ma wani baƙin cikin da ya kuma cika mata zuciya.

Da kyar ta iya ƙarasawa gidan markaɗen tana ajiyewa ta yo waje dan ƙarar injin bata mata rai kawai yake kuma yi ta jima a kofar gidan markaden kafin ta shiga ta dauko bayan an markaɗa.

Shiko Faruk kwana ya yi cikin farin ciki minti kaɗan Ummu yake tunawa, wani lokacin ma sabida farin ciki har yan wake wake yake. Yanzu haka ma yana haɗa tea ne yana hadawa da yan wake waken sa na love, ji yake tamkar yaje ya dauko Ummun sa shikam dan kawai ta nace ne da shikam in ta shine sa yaye Muhammad din tare.

Zumbur ya mike bayan ya ajiye kofin da ke hannunsa zuciyarsa ce ta fada masa anya kuwa Ummu na lafiya musamman da ya tuna yadda sukai jiya da yadda ya mayar da ita jikin ta ba kwari, ɗan dukan goshin sa yayi gami da yin tsaki ni din ina da matsala ya faɗa, me yasa ban bari sai da ta tare ba yadda zan kula da ita sosai.

Makullin motar sa ya zara yayi gidan su Ummu ɗin, a inda ya saba aje motar ya Parker hango mutane a kofar gidan yasa ya tuna ashe fa yanzu lokacin cinikin Ummu ɗin ne. Daga inda yake yana hangen ta tana zuba abinci, ido ya zuba mata yanayin Fuskar ta ya nuna kawai daure wa take yadda ya hango ma kamar damuwa ya hango ba kasalar da yayi tunani ba.

Kasa jira yayi a mota kawai ya fito ya nufi gidaan yana san tabbatar wa da idanunsa, kai tsaye gidan ya shiga inda ya gaida Hajiya kafin ya fito inda Ummun ke sana’ar.

Kwata kwata hankalin ta bai hango mata shi ba lokacin da yake tawowa ba, sai kamshin turaren sa ne ya sanar mata da zuwansa kasa ɗaga ido tayi ta kalleshi, wani bacin rai taji ya kuma ziyar tarta daurewa kawai ta yi ta ci gaba da zubawa Umar abincin da ya bukata.

Inda Ummu din take Faruk ya dawo ya zauna bayan ya fito daga gidan a nutse yake nazarin ta, yaga alama bawai kunyar sa takeji kamar jiya ba yau din rashin san kallon nasa na bacin raine, duk da baisan mai ke damun nata ba hankalinsa ya tashi dan yaga alamun ta ga zuwansa anma baijin yaji sanda ta gaidashi hakan ya nuna masa dashi ake fushin.

Kukan da Muhammad yake ta faman tsalawa yasa Faruk mikewa yace ta bashi shi, in ta kalleshi to kular da ke gaban ta ta kalleshi. Bai damu ba yasa hannu ya dauki Muhammad din ya hau jijjigawa nan da nan yaron yayi shiru.

Yana nan zaune abincin ya kare ta dinga shigar da kayan kafin ta matsa kusa dashi ta mika masa hannu bani shi tace murya adashe tamkar wadda tasha kuka. Mai ke damun ki ya ce cike da kulawa, watsa masa wani mugun kallo tayi wanda ya razani shi badan wai tsoron ta ba sai dan bai taɓa ganin ta masa irin wannan kallon ba, ka bani shi tace murya a kausashe kallon ta kawai yake ya kasa mika mata yaron ganin haka yasa ta mika hannu zata ɗauki Muhammad din.

Ruko hannun yayi ya dan jawo ta daf dashi har sunajin futar numfashin juna ya dago Fuskar ta da tai kasa da ita kafin yace Please Ummu ki fadan meke faruwa kokarin fuzge hannu ta tayi sai dai karfin namiji ba daya yake da na mace ba, kasawar da taine yasa tasa kuka nace ka sakeni da hanzari ya saki hannun dan kalmar ta bashi tsoro Daukan Muhammad ta yi kawai tayi cikin gida.

Kasa motsi Faruk ya yi hankalinsa duk ya tashi tunanin duniya ya kasa gano me ke damun Ummu, shi dai yasan lafiya suka rabu ya kuma san Ummu duk da yarinya ce amma da hankalinta yasan dan abinda ya mata jiya bazai sa ta canja haka ba, tunda tasan ai shi mijin tane tunanin hakan da ya yi yasa ya cire tunanin da zuciyarsa ta sa masa na kaddai Ummu ko da ta dawo gida tayi zaton shi din dan iska ne ya mata fyade.

Mikewa ya yi ya shiga gidan shikam in bai shawo kanta ba baijin zai iya bacci dole su dai dai ta yace ma ransa.

Duk jiran duniya Ummu taki fitowa daga banɗaki sai gajiya yayi ya fito kawai badan yaso ba.

Daren ranar yini yayi yana kiran wayar ta anma taki dauka ya rasa meke damunta yadda yasan Ummu in tana fishi dashi to bata barin wayar ma a kunne in ko ta bar ta bugu biyu ta daga sai gashi yau ya kira yafi Sau dari taki dagawa ta kuma ki kashewa.

Ita kuwa Ummu tanaji ya fita ta fito Hajiya ce ta dube ta, tace, “Ummu me ya hadaki da Farukun ne, murmushi Ummun ta yi kamin tace bafa komai Hajiya cikina ne kawai babu daɗi shi yasa na jima ban fito na.”

Ai shikenan koma dai mene ya kamata ki dunga tunawa yanzu mijin ki ne, gaban Ummu ne ya fadi yayin da a lokaci guda kuma idanun ta suka hango mata Faruk da wata a gado, bata ce komai ba kawai ta dauki Muhammad ta yi ɗaki.

Zama ta yi ta hau bashi nono, sai a lokacin ta tina bama fa ta kashe wayar ta ba, hannu ta zura ta dauko wayar miss calls ta gani rututu na Fatuk da sakon ninsa.

A hankula take bi tana karantawa a sannu hawaye ke bin fuskar ta, yayin ɗa Muhammad da ke shan noni ke zuro hannu na goge mata, magan ganun faruk kullum nasa taji aranta tamkar bata da wanda zai taɓa sonta kamar sa, ayanzunma duk da cikin fushi da takaici take tanajin tamkar gaske yake faɗa sai dai wani ɓarin na ranta na faɗa mata ƙarya yake yana dai son kawai itama ya tsotse tane ya watsar.

Sakon da ta bude ne taji tanason bashi amsa sabida irin magiyar da ya dinga mata na ta faɗa masa meke damun ta.

Ba wani dogon sako ta tura masa ba kawai cewa tayi ” Ni dai dan Allah da zaka taimaka da ka sakeni, sannan abin da kamin zaifi kyau ka tambayi Fatima”

A ruɗe Faruk ya mike daga gadon da yake kai, dan ya ɗan farka ne daga baccin da baisan ya sace ba ya ci karo da sakon Ummu, da murna ya buɗe yayi zaton ko ta huce ne sai yayi karo da bakin cikin da yafi na baya, baiyi zaton matsalar takai yarin yar ta nemi saki ba.

Yana tafe yana zura riga haka ya fito da Dady sukai karo a falo yake tambar sa inda zashi da sassafen nan, cikin hanzari yace ina dai zuwa Dady ya fice.

Kai tsaye gidan su Fatima ya wuce. Ba wani tambaya mai gadi ya buɗe masa gidan ya shiga, Bushira ya aika ta kira masa Fatiman minti kaɗan yarinyar ta dawo wai tace tana zuwa to kawai yace yaja ya zauna.

Yana nan zaune Mansur Ya shigo sama sama suka gaisa shi tun yana jin haushin irin maita ta Mansur ɗin yadda ya nacewa Fatiman duk da yasan yarinyar mazinaciya ce ba kuma sonsa take ba har ya dena musanman a yanzu da yasan mene ne so, ayanzu ya fahimci so ba ruwansa da mutum waye dan yadda yake jin son Ummu ko me take zai jure.

Ganin yafi minti talatin Fatiman ta ki fitowa yasa ya miƙe yayi dakin nata.

Tana kwance tayi rigingine daga ita sai yar shimi da gajeron wando ta bazo gashin ta baya dan ita din akwai gashi yadda take ya tabbatar masa bama tayi niyar fitowa ba daman.

Tanajin shigowar sa ta wani mike tana girgiza tamkar wata karuwa ta karasa daf dashi sorry na saka ka jira ta fada murya a kasalance, hararar ta yayi cikin kaushin murya yace me kika je kika ce da Ummuɗita haushi ya kamata wai ummunsa kai lallai ma mutumin nan.

Matsowa tayi daf da girjinsa dan ya fita tsayi tana faɗin haba kai kuwa mene na fushi kan karamar yarinyar.

Tankaɗa ta yayi gami mannata da bango ya shako wuyanta ke ki shiga taitayin ki wallahi shegiyar yarinya shaidaniya na jima da dawowa daga rakiyar ki, hannu tasa cikin salon yaudarar ta ta rufe masa baki cikin ko zafin nama irin na namiji ya cire hannun gami da murdeshi nace ki fadan uban me kika ce mata.

A tsorace ta ce kawai video na nuna mata, ganin yadda jijiyoyin kansa suka tashi idanun sa suka yi ja yasa bama tasan ta fadi haka ba dan ita tunda take dashi over 20 yrs bata taba ganin ko tsawa yayi bare fishi ba.

What ya kuma faɗe cikin tashin hankali gefe ya watsar da ita inda ya dauki wayar ta ya hau dubawa ya riga yasan password dinta bai bi takanta ba ya hau bin cike.

Hankalin sa ne ya tashi ganin video din da ya gani wayar Fatiman cikin kunar rai ya ce wannan kika nuna mata jiki na ɓari tace eh, kawai waje yayi da wayar baima bi takanta ba.

Mansur Yana ganin Faruk ya fita ya shigo dakin dan duk yanajin yadda sukayi yanayin da yaga Fatiman ciki ne yasa shi juyawa jikin sa na bari dan shi bai taɓa ganin ta a haka ba hasali ma shi a matan Hausawa bai taba ganin wata a haka ba.

Kunya ce ta rife Fatiman ta zura abaya kawai ta biyo shi, kamar bai ji komai ba suka gaisa ya ce daman nazo muyi sallama ne inason zan danyi tafiya.

Ok safe trip Allah ya kiyaye hanya ya dawo mana da kai lafiya. Duk da ransa a jagule yake yaji dadi zai iya cewa karo na farko kenan da ya taɓa jin yarinyar tayi masa kalami mai daɗi.

<< Ummu Hani 15Ummu Hani 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×