Skip to content
Part 17 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Tun a hanya Faruk ke faman gwada layin Ummu Hani sai dai bata shiga sitiyarin motar ya murda bisa titin da zai sada shi da gidan su Ummu din, ransa a bace yake hankalin sa a tashe yake ji yake kamar ya yi tsuntsu yaje ya fadawa Ummu ba yaudarar ta yake ba hasalima shi ya jima da tuba.

Wayar sa da ta hau ruri ne yasa shi saurin dauka dan azaton sa ko Ummun ce ta biyo kiran kamar yadda ta saba in taga missed called din sa, sai dai kash! ba ita din bace, Fatima ce dan Allah Aliyu ka tsaya muyi magana nasani na yi kuskure abin da ta faɗa kenan, cikin zafin nama da bacin rai kai kace Fatiman na gabansa ya taka burki Allah yasa babu wani mai binsa abaya da sai haɗari ya afku.

Cikin kausasa murya yace “Ke dallah malama dakata, karki sake kirana” ya fada rai ɓace kafin ya kashe wayar, ya jima yana ta tunane tunane wanda shi kansa baima san takai mai mai mai yake tunani ba kafin yaja motar sa yayi gidan su Ummu Hani ɗin.

Batayi zaton ganin sa a yanzu ba ta fito zubda shara cikin buhun da suke zubawa a zaure juyawar da zatai ta dora idanun ta bisa nasa da sauri ta zube sharar ta koma cikin gida.

Ya Allah Faruk ya faɗa bayan ya ɗan dungule hannu gami da naushin iska shi a yanzu ma baisan ta inda zai tunkari Ummu ba gabaki daya haushin kansa yake ji, ga kunyar ta da ta cika masa rai yanzu kawai ganinta da yayi sai da gaban sa ya fadi, ya jima a tsaye kafin yayi sallama zuwa gidan su Ummu din.

Tanajin yadda yake sallama tai biris dashi, bayan da Hajiya ta fito ne tace ya shigo Ummun ta mike tayi dakin su inda Muhammad ya bita abaya dan tuni ya fara tafiya abinsa duk da kasancewar sa a ido bama zaka c9e ya fara rarrafe ba.

Tun jiya Hajiya ta fahinci Ummun na cikin damuwa wannan yasa da suka gaisa da Faruk ɗin bata kwalawa Ummin kira ba tace kawai ya shiga dakin, aikam yaji dadyi dan yasan da ta kiratan ma ko ta zo bazata ce masa komi ba.

Tana zaune ta rafka tagumi Muhammad na cinyar ta Faruk ɗin ya shiga bata ko motsa ba sai amsa salmar sa da ta yi wadda iya labbanta ne kawai suka motsa Faruk din bai damu ba ya matsa kusa da ita a hankula ya samu guri ya zauna har tana jiyi hucin sa dan dab da ita ya zauna.

Ɗagowar da ta yi da zummar yi masa masifa sai taga duk yayi mata kwarjini wannan yasa tayi ƙasa da idon ta kawai ba tare da ta ce komai ba, ya fahimci ta ɗan yi la’asar cikin sanyaryiyar murya can ƙasa yake magana dan baya son Umma ta ji wani abin.

“Ummu Hani” ya kira sunan ta a nutse bata amsa ba ta ɗago ta kalleshi kafin ta yi ƙasa da idon ta, bai damu da rashin amsawar ba ya ci gaba.

“Nasani yanzu kin tsane ni anma inason dan Allah kimin adalci ki yadda dani ki sake tunani, wallahi tun da nake ban taɓa kokarin cutar da ke ba, ni har raina wallahi sabida Allah nake son ki ki fahimce ni.”

Miƙewa tayi kafin ta ce, “Adalci dai kake so in ma ba, to abu ɗaya ne shine inaso ka daure ka taimaka ka sake ni.”

Da hanzari ya kamo hannunta, “wallahi Ummu bazan iya sakin ki ba, kedin rayuwata ce, ke din kin riga kin zama wani sashen na jiki na, ke ce farin ciki na, ki fahimce ni wallahi video din da ki ka gani yafi shekara uku ki yadda dani.”

Taɓe baki ta yi kafin ta hau ƙoƙarin kwace hannun ta yayin da shi kuma ya riƙe su gam ganin yafi ta karfi yasa ta kurma ihu, cikin kuka, “Na ce ka sake ni ta faɗa rai a ɓace.”

Da sauri ya saki hannun ta tsugunna tasa kuka shima kukan yasa ganin haka yasa ta miƙe ta share hawayen ta, kafin ta ce Malam zoka bar mana gida ta faɗa, bai ce komai ba ya goge hawayen sa da baisan sanda suka fara zuba ba ya yi waje.

Duk abinda suke Hajiya na jinsu sai da ya fita sannan ta shigo ɗakin ta yi ta rarrashin Ummu din kafin ta fara tambayar ta mai ya faru ganin taƙi faɗa yasa ta koma yi mata nasiha.

Shiko Faruk ya jima a mota kafin ya iya jan motar ya bar gun shikam ko mai Ummu za ta yi wallahi bazai sake ba ya fada a ransa.

Da mangariba bayan ya yi Sallah gidan su Ummu din ya koma kamar dai ɗazun bai samu wata fuska ba kukan dai ta sa masa sai dai shi yanzu ya daure bai yi kukan ba sai hakuri da ya yi ta bata.

Kusan tun daga ranar kullum sai yazo sau wurin uku ko hudu, kwata kwata ma ya fita sabgar ta in yazo in tana gun abinci zai ɗauki Muhammad ya shige cikin gidan su, in kuma tana ciki zata shige daki shi kuma ya yi zaman sa tsakar gida su sha hirar su da Hajiya da kuma su Aisha.

Yauma kamar kullum Ummu na zaune cikin ƙannen ta suna ta dariya Faruk ya shigo ta miƙe gami da ɗaukar Muhammad taja ƴan biyu suka yi ɗaki suna shiga Hasana ta kwace hannun ta gami da fitowa ta faɗin ga Baba, Muhammad ma kuka yasa ta dire shi yabi bayan Hasana. Haushi ne ya cika Ummu Hani, Usaina ce kawai tazo gefen ta ta zauna.

Tana ɗaki tana jiyo hayaniyar su cikin farin ciki sai rarraba musu tsaraba yake, a fusace ta fita da zummar yi masa masifa Hajiya ta ce Ummu ki yi ma Faruk godiya fa baya gajiya da hidima.

Rai a ɓace Ummu Hani ta kalleshi ta ce an gode ɗaga mata gira yayi gami da sakin murmushi kawai takaici ya cika ta juyawa kawai ta yi ta koma ɗaki.

Tun Ummu Hani na basar da Faruk gami da tashi in ta ga ya shigo har ta gaji dan ta fahimci abun nasa bana kare ba ne tunda kullum in ya tafi aikin da ta tashi ta bari sabo yake dawowa wannan yasa take zaman ta tai aikin ta.

Tun amsa sallama ke haɗa su har ta kai ta kawo takan gaishe shi wannan yasa ya kuma dagewa wurin zuwa burin sa shi kam ya samu yarin yar ta dena fushi dashi.

Zaune ya ke suna hira da yayar sa ta ke tambayar sa Ummu Hani din yayi murmushi, “Ki bari kawai Yaya Ummi na fiku matsuwa yarinyar ta tare kawai ban son in mata dole ne.” Harar sa Yaya Ummi ta yi kafin ta ce “So kuma na nawa nan ina ka kawota gida kayi abin da ka so.”

Ƙasa yayi da kan sa yaɗan sosa ƙeya, kallon sa tayi na ɗan mintina, “Ni tsorona wallahi karka yiwa ƴar mutane abin da kayiwa Fatima.”

Cike da tsoro ya kalleta “haba yaya taya kike tunanin ni zan cutar da Ummu Hani wallahi bazan iya ba.”

“Hmm Faruku kenan dafa ba kai bane.” Ta faɗa tana kallon sa.

“Allah yaya ki yadda dani kuma kunsan inason Ummu Hani kuma kunsan bana son Fatima tunda duk da kanku kun sani ni ban taɓa ce muku inason ta ba kullum ma ku kai maganar son ta nake ina jadda muku ba soyayya muke ba, Ummu Hani kuwa da kaina na roƙa aka je aka nemar min auren ta aka kuma ɗauro auren.”

Shiru yaya Ummi ta yi kan ta miƙe hmm Faruku nifa ban yadda da kaiba zanje kawai in samu Hajiya ta yi magana asamu ku tare dan kar aje yarinyar nan ta samu ciki kaga yau zamu wuce America dole in fita hakkin Ummu Hani kar in tafi ka yi wani abin.”

Da sauri ya miƙe ya riƙo ta “Haba yaya bama haka da ke,” kallon sa ta yi kafin ta kwace hannun ta, “ai ba wannan zancen na faɗa maka zanyi tafiyane dan haka dole in tabbatar yarinyar ta tare na kuma yi yadda bazaka iya korar ta ba.”

Na ji wallahi na amince in dai tarewa kike son tayi shine babban burina, abu ɗaya ne dan Allah karki faɗawa su Hajiya abinda kika gani badanni ba ko dan banason su sa ni, a’a sai dan ita yarinyar nasan bazata so ace surikanta sunji kan ta tare kuma a cikin gidan su tayi irin haka ba.”

Shiru yaya Ummi ta yi naɗan mintina, kafin ta ce tom shikenan naji wannan bazan faɗa ba, Murmushi yayi “yawwa yaya ta a bar sona.”

Hararar wasa ta watsa masa kafin ta mike “bari inje nasan su Amira sun kusa gama haɗa kayan su” “tom shikenan sai naji yadda kukai da su Hajiyan.”

Faruk ne zaune gaban mahaifinsa inda Abban ke ce wa “munyi magana jiya da yayar ka ta ce min ka takura kanason ayi magana yarinyar ta tare.” A ɗan sauri Faruk ya ɗago kai kafin ya sunkuyar da kan nasa kunya duk ta rufe shi wato tanan Yaya Ummi ta ɓullo.

Kafin ya ce wani Abu Abba ya kuma cewa na yanke shawara ko bata yaye yaron ba kawai zanwa kawun nan ta magana ta tare ɗin tunda ai daman ko ta yaye shi anyi tare da su zaku zauna.

Farin ciki ne ya cika Faruk har hakan ya kasa ɓoyuwa a fuskar sa sai dai ya kasa magana Fahintar haka yasa Abba cewa shikenan kaje kuyi magana da ita nanda sati uku sai ka faɗan ya kukayi in yaso sai muji yadda kukai daga baya.

Kansa a kasa yake ta zuba godiya ɗadi ya cika Abba wai yau Faruk dinsa ne a nutse haka ya kuma yadda aure na kintsa mutun.

Duk da farin ciki ne fal cikin Faruk sai dai ɓari guda na ransa na tsoron yajewa da Ummu Hani maganar tarewa musanman da ya tuna da har yanzu fa bata gama hucewa ba.

*****
Fatima ce kwance abin duniya duk ya isheta ji take tamkar ta yi hauka kishi da haushin kanta ya cika ta, ta rasa ada wanne irin hauka ne ya sata bawa Faruk kanta duk da kuwa tana mutuwar sonsa sai yanzu ta fahinci ba karamin kuskure tayi ba tunda kuwa gashi ya gujeta ya auri yarinya karama.

Ganin ta rasa abinda take tunani yasa ta fitowa daga falon nata wayar ta da ta gani a center table da ke main falo yasa ta tuna rabon da ta kunna wayar ankai sati sai a lokacin ta tuna da Mansur tsaki ta yi yayin da afili ta ce ni na rasa ma uban me ya gani ajikina yake sona.

Har ta wuce kuma ta dawo ta kunna wayar kamar yadda ta zata sakon sa ta fara gani na ya sauka lafiya.

Har ta goge sakon sai kuma ta tsinci kanta da son tura masa da amsa.

“Ok, sannu da sauka.” Kawai ta iya cewa cikin saƙon nata kafin ta fi ce daga falon zuwa harabar gidan nasu.

A hankula take shawagi duk da ranta babu dadi sai dai iskar da take kaɗa bishiyun farfajiyar gidan ta sanya ta jin wani sanyi a ranta bata san lokacin da ta hau kissima in da Faruk mijin ta ne a irin wannan lokacin suna tare da yaran su da Allah kaɗai yasan farin cikin da zata shiga.

Tuni Fatima ta yi nisa a tunanin dokin rano sai ji tayi ana cewa baby na lafiyar ki kuwa da hanzari ta dawo hankalin ta gami da ƙaƙalo murmushi “lah Dad sannu da zuwa.”

Kallon ta Dady ya yi cikin da damuwa “Meke damun ki ne duk kinyi baki,” dariya ta yi kafin ta ce “lah, Dady weather din Nigeria ce fa,” kallon ta Dad ɗin yaɗan yi kafin ya girgiza kai, “ni dai na faɗa miki ki faɗam ko mene karki samin kanki a damuwa.” Murmushi ta yi kafin ta ce Allah dad ba komi.

“Kin tabbata” ya faɗa yana kallon ta eh Dad ta faɗa cikie da murmushi, ciki kawai ya shige yabar ta nan inda ta kuma komawa dunitar tunani.

*****
Ummu Hani ce zaune ita da ƙawar ta Salma suna hira wadda kusan duk a kan karatun Salma ne, yawwa ban faɗa miki ba, Salma ta fada Ummu Hani da ta miƙe dan zubda ruwan wankin salak din da ta gama yankawa ta ce inajin ki.

Admission ya fito na farko ba sunana, da hanzari Ummu Hani ta dawo subhanallahi ta faɗa fuskar ta cike da damuwa.

Murmushi Salman ta yi kafin ta ce kema dai ai list ɗin farko ne, to Allah yasa asamu Salma ta ce amin.

“Anma zanwa Faruk ko Umar magama ɗaya daga cikin su ya taimaka ko yana da hanya.” Inji Ummu Hani.

“A’a dan Allah karki musu magana nasani bakyason nemam alfarma.”

Tsuke fuska Ummu Hani ta yi ni ɗin wace ce da zance banson neman alfarma bacin ma haka ai Faruk mijina ne karki damu ko me zakice sai na tambayeshi.”

Murmushi Salma ta yi kafin ta ce, “tom mai miji an gode.” Suka sa dariya baki ɗaya.

Hasana da ta yi waje da gudu yasa Ummu Hani cewa kinji ɗan halak ana maganar sa ya zo.

“Kai ah lallai na yadda soyayyar nan ta gaske ce wato tun kan ya shigo kinsan shine wato har sautin motar sa kin sani.”

Murmushi Ummu Hani ta yi “wallahi bana ganewa wani zubin saima ya shigo nake sanin yazo kawai fahimta na yi indai naga Hasana ko Muhammad wani ya yi waje da sauri to nasan shine.”

“Hhh lallai matar nan ni zaki rufe cikin zani to mene a ciki dan kina son mijin ki,” “Ni kinga karki min sharri.” Ummu Hani ta faɗa kafin ta yi sauri ta ɗauko Muhammad da ke ƙoƙarin faɗuwa sai dai Faruk ya riga ta ɗaukan sa da tuni sun shigo inda yake rike da hannun Hasana.

Cin karon da sukai ne yasa ta dafe kai inda ta ɗago rike da gun ya yi saurin ƙarasawa, “Ya rikota mugani ba dai kiji ciwo ba ko?” ya faɗa a tsorace.

<< Ummu Hani 16Ummu Hani 18 >>

1 thought on “Ummu Hani 17”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×