Skip to content
Part 18 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Mugani ya ce bayan ya riƙo ta, muryar Salma da suka ji tana faɗin eyye ah lallai masoya tana faɗi ne cikin dari ya sa da sauri Ummu hani ta ture hannun sa shiko bai damu ba yake faɗin badai kiji ciwo ba ko, turo baki tayi yo dana ji ciwo ai da kuka zaka ga nasa.

Ajiyar zuciya yayi ta wasa ah to Alhamdulillah har na fara tunanin kiran Umar muje asibiti, dariya Ummu hani ta yi kawai kafin ta koma ta zauna.

Shima ɗin guri ya samu ya yiwa kansa mazauni sai da ya zauna ɗin tukunna Ummu hani da Salma suka gai dashi.

Hajiya bata nan ne ya tambaya eh sunje unguwa ita da Khairat.

Mikewa Salma tayi bari in tafi tun kan afara korata da sauri Faruk ya ce da ko kin kyauta wallahi, eyye ƙawar tawa kake kora inji Ummu hani, kafin ya ce wani abu Salma ta ce ah ni bashi ya koreni ba ke ce naga kina ta harara ta alamar na takura muku.

  Harara Ummu hani ta watsa mata kan ta ce wani abu Salma ta ce a’a kika kuma to kin jawo sai na faɗa masa.

Da sauri Faruk ya ce mene? faɗamin, dariya Salma ta yi ai ka bari kawai tunda nazo gidan nan magana ɗaya take min shine na yadda take sonka.

Daɗi ne ya cika Faruk ya wani washe baki zan bawa khairat Tukwicin ki ta baki ki gaida gida.

Eyye wato korata kake ko, Ummu tasa dariya bake kike goyon bayan sa ba.

Samun kansa yayi cikin Nishaɗi da kallon yadda Ummun ke dariya, dariyar da ya jima baiga tayi ba duk da sun koma Normal yanayin ta yana nuna masa da damuwa aranta sai dai yau daɗi ne ya cika shi yadda yagan ta cikin farin ciki.

   Ai dole kiyi dariya tunda kun haɗu keda mijin ki kun kore ni zamu haɗune ta faɗa kafin ta wuce.

Aɗan kasalan ce Faruk ya dubi Ummu hani Ya akwai abin da zanci kuwa yunwa nake ji.

Ɗan kunbura fuska tayi wato so kake Umma ta ce na hanaka cin abincin ta ko, Ni kinga in rowar taki ce ta motsa kawai ki faɗan in miƙe in san nayi.

Murmushi tayi ni karka min sharri ta faɗa tana ƙoƙarin zaro kofi a kwando.

Sai da ta kuma ɗauraye kofin kafin ta zubo masa kunun tsamiya ne ban sani ba ko kana sha.

Hararar wasa ya watsa mata ina ludayi da sauri Hasana dake gefensa ta miƙo masa yawwa ta wajena, Usaina ta turo baki ni ta wajen Umma ce tana nufin Ummu hani, duk suka sa dariya.

Indai Faruk yazo gidan bazakai tsanmanin shi ɗin wani ne ba yadda yake maida kansa tamkar yaro yana biyewa yarintar ƙannen Ummu hani da ita kanta Ummun.

Yana shan kunun tana kallon sa yana ɗaya daga abinda yasa ta haƙura taji tana son zama dashi taji zata masa Addu’a Allah ya shirya shi, saboda yadda tun kusan farkon haɗuwar su bai taɓa nuna musu kyama ba.

A kullun in ta tuna da wani zuwan su shida Umar ta kawo musu ruwa da lemo Umar yana faɗin towo to ina ganin sai dai ni ɗin,aa dan mutumin naki kyankyami ne dashi kofin sa na gida ma shi yake wanke abin sa.

Karki damu karya yake ni inma zan kyankyami ai bazan kyankyanmin abin da nake so ba, mutumin da zaka aura mene na kyankyamin sa.

Tuna haka yasa ta Samun kanta  da yin murmushi sai ji tayi yana faɗin kunun yayi daɗi nasan Hajiya ce tayi ko.

Kana shan abu me zafi kace Hajiya ce tayi bacin na ce ma tun safe ta fita.

To gaskiya wannan nasan Hasana ce tayi ya faɗa cike da zaulaya.

Ah wannan sedai Muhammad, ummu hani ta bashi amsa.

Ni fa ince ko da naji suka sa dariya.

Duban sa Ummu hani tayi bayan ya gama shan kunun ta ce yawwa kaga inata zuci zucin in faɗa ma.

Yadda tayi maganar ya gane yanzu da mahinmanci maganar da zata yi.

Inajin ki mene ne?.

Yawwa daman ɗazu muke magana da Salma ta ke faɗan Admission list ya fito ba ita, shi ne muke neman alfarma dan Allah ko zaka samu cikin waɗan da ka sani ka nema mata alfarma ko zata samu Admission ɗin.

Yanzu wannan ne yasa kike ta wani ƙasa da murya da sun sun da kai se kace wani babban abu na sha faɗa miki ko mene komai wuyar sa ki dinga tambaya ta kai tsaye.

Yanzu gobe ki amso takaddun ta zan bawa Abban su Umar insha Allahu zata samu musanman ma da yake ta ci komai ɗin ta.

Yadda take ta zuba godiya yasa Faruk miƙewa ni kinga bari in tafi.

*****

Fatima ce duk abin duniya ya isheta musanman da saƙonnin Mansur suka isheta ayanzu bata son Dad din ta yasan da Mansur ɗin yana son ta dan tasan zai iya roƙon ta alfarma ta haƙura ta auri Mansur ɗin.

Tun jiya take tunanin mafita bayan Dad din ta ya faɗa mata Alhajin su Faruk ya masa maganar yanaso zasu je suyi magana kan tarewar Faruk ɗin da ummu hani.

Ta rasa abinyi sai dai tanajin in dai har Faruk zai tare da wannan shegiyar yarin yar ita kam ita da shi ko alahira tasan zasuyi hannun riga ne, ita kuma dashi ta tsara rayuwar ta.

Zuciyar ta ce ta bata shawara tana kuma jin jaymar shawarar zata mata amfani.

Wayar ta da ke gefen gado ta sa hannu ta ɗauko Number ɗin Alhajin su Faruk ta danno kami da danna kira.

Bugu ɗaya ya ɗaga Fati na ya a kai ne ya faɗa Fatiman ta ce daman dan Allah Abba alfarma nake nema amma nafi son sai nazo kana gida ne.

A’a na fita anma yanzu zan dawo ki tawo kan kizo na dawo tom ta ce ta kashe.

A shirye ta ke Mayafi kawai ta yafa tayi bangaren Antin su.

A’a Fatin Dady unguwa za’a eh ta ce kafin ta ce zani gidan su Faruk ne.

A’a kaga kirjin biki ana bikin aminin ai dole kiyi ta zarya, haushi ne ya cika Fatiman kafin ta ce ni na wuce zan kira Dad in faɗa masa.

Ok tom ki gaidasu inji Antin ta faɗa tana maida kanta.

Alhajin su Faruk yana zaune a falon sa yana cin abinci Fatima ta same shi bayan sun gaisa ya ce itama ta zuba ta ce ita ta koshi lemon kawai tasha.

Inajin ki mene ne Alhajin ya faɗa.

Daman Na jima ina yiwa Dad Magana kan yayi maka magana inason Faruk anma ya ce tunda Faruk baya so na shi bazai masa auren dole ba.

Murmushi Abba yayi karki damu tunda ya zaɓi wadda yake so ɗin, kema zaɓin ki zan aura miki sai ku tare ku biyun keda wadda yake so ɗin.

Ran Fatima ba daɗi ba haka ta so ba anma dai dole ta hakura, ba kishiya a tsarin ta, sai dai akan Faruk ko ata huɗu ne zata je bare ta biyu…..

Fatima ce ta ce shikenan Abba Nagode anma dan Allah ka faɗawa Dady da kanka.

Murmushi Abban yayi kan ya ce karki damu zan masa waya yanzu ina gama cin abinci ki je kiyi shirin ki, nanda sati uku Faruk din zai tare shida Hani ɗin in yaso duk sai ku tare lokaci guda.

Tom ta ce bayan ta ɗauki Tufa guda biyu na tafi da wannan, murmushi Abban yayi ki zo ki daɗa.

No ta ishe ni wannan ɗin ta faɗa kafin ta bar falon zuwa cikin gida dan gaida mutanen gidan.

Tana Fita Abban ya kira Dad din Fatima ya ke tambayar sa ko yana gida, a’a ina shago sai dai in zan wu ce gida in biyo in abun mai mahimmanci ne inji Dad ɗin Fatiman.

No karka damu ba wani abu bane daman faɗa maka zanyi na yiwa Fatima miji nan da sati uku zata tare.

Ok tom Allah ya nuna mana inji Dad din Fatiman, ba tare da ya tambayi ko waye mijin ba.

Mutuncin da ke tsakanin mahaifin Fatima da Faruk yayi girman da duk yadda Alhajin Su Fatima yakai ga son Fatima ya hakura da yadda take son Faruk ya ki goyon bayan ta dan baya son zumun cin su ya ɓaci tunda ya fahinci shi Faruk ɗin ba son ta ya ke ba.

Ko ayanzu sam shi bai kawo aransa cewar Faruk ɗin ake ƙoƙarin auren da shi ba, yana son tambaya sai dai baya son ya nunawa aminin nasa iyakar sa kan Fatiman.

*****

Miƙewa ummu hani ta yi tana faɗin bari in maka rakiya har ransa yaji daɗi dan rabon da Ummu ɗin ta masa rakiya tun kan Fatima ta shigo musu rayuwa.

Ajikin motar tasa suka jingina kafin ya ce inata son in faɗa miki wallahi amma tsoron ki nake ji ya faɗa yana ƙasa da murya.

Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un ta faɗa yanzu ni kake tsoro karka sa duniya ta zageni mana ace mijina ya na tsorona.

Ki bari kawai nima har mamaki nake ace wai wannan yar halittar nake tsoro ya faɗa cike da zaulaya.

Haɗe fuska tayi lallai ma mutumin nan ni ce yar halitta, murmushi yayi kin gani ko shi yasa kike ban tsoro tamkar wahainiya kike wallahi yanzu sai ki birkice ki tadawa mutum hankali ya kasa bacci.

Ni yanzu a bar maganar tsoron nan mene kake son faɗamin kake ƙunbiya ƙunbiya.

Eh to daman wallahi dai bani bane, kin san Allah bani bane yaya Ummi ce da su Abba sun takura sai kin tare.

Tsuke fuska tayi kaga malam karka yiwa su Abba sharri, Allah ba sharri na musu ba yadda yayi  yasa yatsan sa a leɓe gami da nuna shi sama tamkar wani ƙaramin yaro da bai wuce sa’an su Hasana ba sai ya bata dariya.

Murmushi ta yi kan ta ce tom shikenan na ji yau shene suka ce tariyar ta tambaya tana kallon sa.

Sosa kai yayi kan ya ce shidai Abba maganar Sati uku yake anma in tani ne yanzuma ki tawo mu tafi kawai wallahi.

Harar wasa ta watsa masa shikenan, ka ci darajar su Abba zanje in sanu su kawu in faɗa musu, su sanya rana in yaso sai in faɗa ma yadda mukai.

Cike da murna da ɗoki ya kamo hannun ta dan Allah Ummu da gaske kike kin yadda zaki tare.

Aɗan tsorace ta kwace hannun ta, a fa waje muke ta faɗa.

Sorry Madam yace yana murmushi ni wallahi nama manta nan waje ne.

Ke imma wajen ne wata tsiyar mukai ke ɗin ai matata ce kowa ya sani.

Dariya tayi badai kowa, ni karka ma ban haushi wallahi se wani zumuɗi kake tamkar wata sabuwar amarya za’a kawo ma.

Ke lallaima yarin yar nan sabuwa ce mana, kedai bari kawai wallahi raina yau ɗinnan tas.

Uhum adaiyi shiru bayan ka riga ka……se kuma tayi shiru.

Kallon ta yayi ido cikin ido har seda taji kunya kan ya ce me nayi faɗamin.

Oho kawai ta ce.

Ci gaba ya yi da kallon ta kafin can ya ce oh wai kina nufin dan rannan kinzo munyi…..kai lallai ma mutumin nan ta faɗa bayan ta rufe masa baki.

Hannu yasa ya cire hannun ta kan ya ce kin san Allah ko ada ni kawai nasan ina mutuwar sonki anma san kasan cewa da ke ya karu ne kuma yana kan ƙaruwa tun daga ranar da bakya son in faɗa, ummu hani dina ta daban ce ba ƙaramin sa’anayi ba.

Hannun ta da ke hannun sa ta fizge kan ta ce ni kafi karfina tayi cikin gida.

Dariya yasa ya bita da ido ransa fal farin ciki kafin ya ce cikin ɗan ɗaga murya ki amso takar dun fa zan dawo anjima.

Bata bashi amsa ba ta shige gida yayin da shi kuma yaja motar sa yayi gaba.

*****

Da yanma lis su Hajiya suka dawo suna dawowa Ummu hani ta fi ce zuwa gidan su Salma dan amso takar dun.

Bayan Mangariba Faruk ya dawo aiko tana jin sa ta shige ɗaki ta bawa Aisha takardun ta ce su ce tayi bacci.

Yasan da gayya ta shige ɗakin hakan yasa ya leƙa tana kwance Muhammad na jikin ta su Hassana na gefe duk suna bacci.

Wutar da aka kawo ce tasa ya matsa daf da ita ya ɗan tsunguna yafi minti biyu yana kallon ta ransa fal abubuwa yayin da faduwar gaban ummu ya ƙaru batayi zaton zai shiga ba shi yasa ko tunanin sanya hijabi batayi ba.

Ahankula ya mike ya kunna musu fanka kafin ya fice yama su Aisha Sallama yabar gidan

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ummu Hani 17Ummu Hani 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×