Skip to content
Part 2 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Suna ƙoƙarin kamata su fita, Inna ta ga alamun haihuwa ta ce, cewa tai da Ummu Hani ta yi maza ta kira mata matar nan jami’ar asibitin, to kawai Ummu Hani ta ce, ta miƙe a hanzar ce, ko tsoron masifar matar babu aranta.

Matar har ta fara bacci Ummu Hani ta taɓa ta, kamar ɗazu cikin masifa take faɗin “Malama lafiya bana ce muku ni bazan iya komai ba?”

Kuka sosai Ummu Hani tasa.

“Dan Allah nurse ki tai maka, kizo.” Shiru matar ta yi kamin ta yi tsaki, ta miƙe

“Muje” shine abin da ta ce.

“Kinga munyi ƙoƙarin ɗaukanta sai nake ganin kamar haihuwar tazo, inna ce mu tafi komai zai iya faruwa a hanya, ga dare shi ne nace ko za ki kyale mu ta haihu anan.” Duk wannan Inna ce ke ma primary health care worker ɗin Bayani.

“To ya zanyi tunda ƙaddara tasa kunzo nan, abu na gwamnati ina ni ina korar ku.” Matar ta faɗa jiki ba kwari rai a ɓace.

Habule ta kalla “Malam yi waje.” Da sauri ya miƙowa Inna wayar da suke haskawa, ya yi waje dan shima ɗin jira kawai ya ke ace ya fice ɗin, dan shi kam bayason yaga yadda ake haihuwa.

Juyowa ta yi ga Ummu Hani kema bishi, Inna ce tai saurin cewa a’a, ta ɗan matsa can dai Habule da na ne anman ban yadda su zauna tare cikin daren nan ba a kuma waje, yaron yanzu sai Allah.

Kamin matar ta kuma cewa wani abu tuni Ummu Hani ta koma inda ta taso matar ta zauna, hankali a tashe bakinta fal addu’ar samun lafiya ga Umman nasu.

Da taimakon Allah, Ummansu Ummu Hani ta haife yaronta namiji, sai dai fa tasha wahala sosai.

Sai da matar ta gyarashi ta naɗe a zanin da Ummu Hani ta bata sannan tace suyi sauri su kaita asibiti dan da alamu tana bukatar jini sosai.

Ummu Hani ce rungume da baby, inda Habule da Inna suka tallafi Ummi suka yi gurin adai-daita ɗin.

Kansu je babban asibitin murtala Umma ta jigata sosai sabida ɓacin hanya.

Sai dai me suna zuwa nanma mai gadi ya hanasu shiga, sai dai su fito su shiga a ƙas kwana biyun nan ansa dokar shiga da ada-daita sahu..

Ummu Hani ta fito riƙe da baby ta yi ciki har gun security ɗin, tana zuwa tasa musu kuka suzo suga halin da ummanta ke ciki, bazata iya tafiya ba in suka ce zasu jata kuma zafi ciwon zai yi.

Tai mugun sa’a shugaban securities na asibitin, yana kan round ya ce ta yi shiru suje ya gani, sosai tausayi ya kamashi, ya basu takadda da damar su shiga Ummu tai ta masa godiya kai kace Ummanta ta warke.

Kai tsaye suka wuce E and A, sai dai ba gado, nurse ke faɗa musu kawai su canja asibiti, dan kaf nan babu gado hankalin Ummu ya tashi, ta dubi jaririn da ke hannunta yana bacci, da Ummanta da ke kwance jikin inna babu alamar tana da rai.

Fitowa ta yi daga adai-dai ta ɗin, ganin wani zai shiga motarsa riƙe da kayan ma’aikatan asibiti da alamu likita ne.

Tsaidashi ɗin da tai ne yasa shi tsayawa yana kallonta, cikin rawar murya tace likita dan Allah yadda Allah ya taimake ka, ka tamaka mana ka duba mana mara lafiya, ba tare da wani tunani ba yace muje inganta.

Yadda yaga Umma hankalin sa a tashe ya ce ina zuwa, minti kaɗan ya dawo shida nurses da gadon tura mara lafiya,  sanya ta suka yi akai, kai tsaye office ɗinsa suka wuce da ita dan ba inda zai sata.

A gadon office ɗin yasa aka ajiye masa ita, ƴan binciken su irin na likitoci ya yi kamin ya fito Ummu ya duba ina mahaifinku? Cikin sanyin murya ta ce ya rasu, to sauran ƴan uwa fa, eh da ya ke dare ne bamu da waya ba wanda ya sani.

To yanzu tana buƙatar jini, kin san group ɗinta ko sai munyi gwaji, cikin sauri Ummu Hani ta ce nasani A negative ne.

Subhanallahi negative, Ɗazunnan kaf asibitin babu shi, cikin sauri tace akwai a family ɗinmu, yawwa in basu da nisa ya kamata kije kizo dasu, daɗewa zai iya jawowa ta rasa ranta.

Yanzu kawo baby ɗin kamin ku dawo mun duba shi ok ta ce, ta miƙa masa baby ɗin tabar Inna Mai Ɗan Wake ita kuma su kayi waje ita da Musa.

Kaitsaye kwandila suka wuce gidan kawunta, yayan Umma ne jininsu iri ɗaya ne, shima A negative ne, bugu kaɗan aka buɗe, Cikin kuka ta masa bayani ai kamin ta gama ya hauta da masifa.

Bakya ganin bani da lafiya, wato memakon kije ku samo na masu lafiya sai ni, ɗan jinin da ya ragemin ku tsotseni in ƙare in mutu, ku kun rasa uba ni ma ku sa nawa yaran su rasa.

Baima ƙarasa batun nasa ba Musa yazo yajata daga inda take durkushe tana kuka, ya ja adai-dai ta sahun yace yanzu ina zamu.

Da hanzari tace tarauni, su uku ne kawai masu irin jinin, naga kuma sunfi shaƙuwa da kawu kuma shine namiji, shi yasa na ce mu zo nan, anman muje gidan gwaggo lami, to kawai yace mata suka wuce.

Sai dai me kamar gidan kawu, nanma Inna masifa ta yi ta yi, tana cewa, Inba hauka ba irin na Ummu Hani ina ta taɓa ganin cewar an ɗebi jinin mace, kuma me shekaru.

“Ni yanzu bani da lafiya kuje da safe innaji dama dama zanzo, in dubata.” Shiru kawai Ummu ta yi dan kasa kuka ma ta yi, wai wannan itace wadda suke uwa ɗaya uba ɗaya da Ummanta.

“Kin sanme, yanzu muje a gwada nawa in yayi sai in bada nawa dan gaskiya bansan mene group ɗina ba.” Wannan duk Musa ne ya faɗa.

Ɗago kai ta yi, ta ce, “Na gode” Suka wuce ranta fal baƙin ciki, wai yau ace jininka ba zai iya maka komai ba sai maƙoci, yau ta kuma yadda da cewar sa’ar maƙoci babban rahama ne arayuwa. 

<< Ummu Hani 1Ummu Hani 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×