Skip to content
Part 21 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

A hankula ya sake ta jin zuciyar sa tana raya masa abubuwa da dama, miƙewa ya yi yana faɗin “Bari inje nasan ana ta jirana a office sai na dawo anjima.” “Bari in je in faɗawa Hajiya ta zo ta yi godiya.” Inji Ummu Hanin.

“Kin jiki dan Allah ki kyale ta ai ba wani abu bane.”

Murmushi ta yi masa, “Tom shikenan nawan Allah ya kiyaye hanya.” “Amin” Ya ce yayin da Ummu Hanin ta ce, “Yawwa anjima zani in ma Salman albishir.” “Ki ce kawai za ki yawo Malama.” Faruk ya bata amsa.

“La’ila daman Salma ta faɗa ba zaka dinga barina ina zuwa ganin su ba.”

Murmushi ya yi, “Ah ki ce zuga ki take tom zan haɗu da ita ne.”

“A’a fa mijin Ummu Hani kaima kasan dai ba zuga bace tunda yaushe rabon da in tambaye ka unguwa yau daga tambaya ka ce yawo.”

“A’a dai ko shekaram jiya kinje gidan Kawu,” Ya faɗa yana tsure ta da ido, dariya ta yi “Yo wannan ai fitar ka ce, kaine kasa naje in tani ne a shekara ba’a tare ba, kaine sarkin rashin haƙuri.”

“Ah lallai yarinyar nan, ai wallahi ki bari kawai baza ki gane banda hakuri ba sai…” “Ni dai inje dan Allah?” Ta roƙa cikin sanyayyiyar murya, “Na ji ki je anma karki jima kuma banda cin ado.”

Riƙe haɓa ta yi tana kallonsa, dariya yasa, “Ni dai na faɗa miki banason ana gane min gayunki.”

“Yo to banda abin mijin Ummu Hani ai Ummun tasa ba wani haɗuwar da intayi gayu zataja hankali ta yi ba.”

“Kai ah lallai ma ke kinsan yadda kike da jan hankali kuwa musanman in kina wanna takun.” Yaɗan gwada tafiyar ta, salati tasa cikin dariya shima dariyar yasa ya ce “Muje ki karɓi Admission letter ɗin ya yi waje yana dariya, itama tom ɗin  kawai ta ce cikin dariyar gami da zarar mayafi ta fito tsakar gida ɗakin hajiya ta leƙa ta ce Hajiya zan amso takar da a motar Faruk.”

“Tom karki daɗe Hajiya.” Ta ce.

Bayan Faruk da tuni ya yi waje Ummu Hani tabi dan karɓo takardar, a cikin mota ta same shi ta ɗan matsa kusa dashi ya miƙo mata takardar ta amsa tana murmushi sai da ta karanta sannan ta hau godiya hararta ya yi, “Ke dai bakya gajiya da godiya ni bara in wuce.”

Har ta juya ya ce “kinga nama sha’afa wallahi.” Dawowa ta yi da ido ya nuna mata ta shiga motar. Zagayawa ta yi ta shiga dan tuni yaɗan zura hannu ya buɗe mata.

“Shaf daɗin abincin ɗazu ya mantar dani shekaran jiya naje na miki registration na WAEC tunda a SS2 kika dena zuwa na kuma miki registration na lessons kafin ayi exam ɗin.”

Kasama magana ta yi sabida farin ciki, kamar yasan abinda ke ranta kenan sai dai tana ganin ya wuce tasa shi ya yi abinda baida ra’ayi kodan iya halaccin sa na ɗaukan ƙannen ta tamkar nasa koma tamkar ƴaƴan sa.

“Ba kice komai ba niyata tunda exam din May/June ce in kika tare a gida sai masu lesson din su dinga zuwa suna koya miki da nace can sch din zaki dunga zuwa sai suka ce suna private service ma.”

Kawai kallon sa take tana murmushi ta rasa mai zata ce ta ko ina Faruk rahamane a rayuwar ta a yanzu da take kuma kallon sa hasaso irin sa’ar datayi na samun sa a miji take.
Matsowar da yayi daf da ita ne yasata saurin kallon sa. Belt ya hau sa mata ta ce ah me kake haka, ɗaga mata gira yayi gami da sakar mata murmushin da yasa tsigar jikin ta tashi tayi saurin kawar da kai.

“Tafiya zan da ke,” A tsorace ta matsa “ina kuma?”

“Tun ɗazu nake magana kinƙi magana, kawai kallon ki da nake ɗan mintoci kina murmushi sai zuciya take faɗan sati shida yayi yawa wallahi.”

Basar da shi tayi ta hau godiya, “Ni kinga ba godiya zaki min ba,” “ai godiya ta zama dole, na gode Allah ubagiji ya saka da Alheri,” rufe mata baki ya yi, “Wai mene na godiya kefa matata ce nemar miki illimi dole nane. Ni dan Allah ki yadda mu tafi kawai gobe nazo in tafar miki da kayan ki.”

Dariya ta yi gami da ɗauke hannun sa abakin ta, kan ta ce, “Yanzu dai goben da yaushe zamu gun registration ɗin da ka ce za’ai finger print ɗin.”

Kallon da yake mata yasa ta buɗe motar sai anjima ɗin in ka dawo zamuyi maganar.

Binta ya yi da kallo sai sa ta ɓacewa idanun sa sannan ya tuno da batun da sukayi da Abban sa shikam bai san ta yadda zaiyi ya faɗawa Ummu Hani wai da kishiya zata tare ba, kuma wai Fatima shi bai san ta yadda zai iya faɗa mata cewar auren dole ne za’a masa ba.

Koda Ummu ta koma gida da gudu ta shige ɗakin Hajiya cikin murna take nuna mata Admission Letter ɗin murna Hajita tasa itama ta hau sawa Faruk albarka.

Sai da suka gama murnar Hajiya kewa Ummu Hani faɗam me yasa bata faɗa mata tun Faruk yana nan ba ta yi masa godiya.

“Wallahi Hajiya na ce zanzo in faɗa miki kinsan Halin sa ya nuna wai ai ba komai bane, anma ai yace anjima zai dawo sai ki masa godiyar.”

“Tom shikenan Allah ya dawo da shi lafiya yayi masa albarka yasa ku anfani juna a zaman nan na ku.”

“Amin, Hajiya nima ya ce ya biyamin kuɗin exam yace zan ci gaba da karatu.

Murnar Hajita ta yanzu har ta fi ta ɗazu dan tasan yadda Ummu Hani ke som karatu kawai sabida ƙannen ta ita ta watsar da nata burin.

Nan tayi ta sawa Faruk albarka yayin da Ummu keta faman amsawa da amin.

Wurin huɗu Ummu Hani ta yi wankan ta tsaf ta yi kyau sosai ta ɗauki Muhammad suka yi gidan su Salma bayan ta faɗawa Hajiya zata je ta kaiwa Salma admission letter ɗin.

A kofar gida ta haɗu da Faruk mamaki ya cika ta badai har ka dawo ɗin ba.

Zuwa na yi ko ki tawo mu tafi ki tare yau ko ni in dawo gidan nan kawai.

Ɗan zaro ido ta yi tana kallon sa kan ta ce wani abu ya zagaya bayan mota ya fito da jaka, “These are my things it’s either ki ɗauko kayanki ko ni in shigar da nawa ciki na dawo nan in sati shidan ta yi ma tafi tare.” Sakato ta yi tana kallonsa ya ce, “Oya am waiting what’s your answer?”

A hankula Ummu Hani ta matsa kusa da Faruk a lokaci guda tana tunanin me zata ce masa. Hannunsa ta kamo ta shigar dashi mota kafin ta sunkuya dedai kunnen sa tayi magana, juyar da kai ya yi kafin ya ce, “nifa kome zaki ce se kin zaɓi ɗaya cikin zaɓin da na baki.”

“Haba mujin Ummu Hani kar muyi haka da kai fa, yanzu fisabilillahi me zaka ce da su Abba in ka dawo gidan nan da zama.” Ta faɗa a yayin da ta yi narai narai da ido.

“Yawwa kawai to ki zo mu tafi ɗin,” Zaro ido ta yi, “Haba mijin Ummu to su kawu fa ai se suce an maidasu ba komai ba tunda sun riga sun sa rana kawai sai aje ace musu na tare.”

Ai ba ɗaurin aure bane Hajiya yanzu fa a ƙarƙashin ikona kike ba su ba ke ɗin mata ta ce.

Nasani ai shi yasa yanzu nima nake ce maka mijin Ummu dan Allah ka bar maganar dawowa nan ko binka.

Da ƙyar Ummu Hani ta shawo kan Faruk ya yadda ba za’ai ɗaya cikin zaɓin nasa ba.

Kallon sa ta yi kafin ta ce bari inje ni inda zani.

Kallon ta yayi what ina zaki dariya tayi a hankula dan tasan Faruk rikicin sa yayi yawa in ta yi wani abun zai iya dawo da maganar zaɓi.

“Wai tsaya daman bani kika fito tara ba, ya faɗa rai a ɓace.”

Girgiza kai ta yi, “Allah mijin Ummu ko me iya zama da kai se ni, inbanda abinka yaushe mukayi waya har ka ce min kazo da zan fito tarar ka.”

Gyaɗa kai ya yi, “Hakane fa anma tsaya wai kina nufin duk wannan gayun a haka zaki unguwa.”

Kallon kanta ta yi kan ta dube shi ita dai bata ga wani gayu a nan ba.
Gaskiya in a haka zaki ki kawo takardar kawai in kai mata da kaina Faruk ya faɗa fuskar nan a tsuke.

Ina zuwa ta ce ta koma cikin gida.

Hijab din Hajiya dake kan igiya ta sanya, Hajiya ta ce, “Wannan ai ya cukurkuɗe ina za ki badai har kin dawo daga gidan su Salman ba?”

Murmushi Ummu Hani ta yi kan ta ce “a’a banma je ba, da Faruk na haɗu a ƙofar gida shine ya ke cewa wai na yi gayu.”

Dariya Hajiya ta yi kan ta ce “Ina wani gayu kawai fitar ce baya son ki yi.”

Murmushi Ummu Hani ta yi kan ta ce shi yasa ai nazo in canja hijabin.

Waje ta yi yana tsaye jikin motar sa idonsa kyar bakin kofa, da alamu fitowar ta yake jira.

Suna haɗa ido suka sakarma juna murmushi.

Bari naje kar dare yamin ta faɗa masa alokacin da taje dab dashi.

Ko inzo in miki rakiya ya faɗa idonsa akanta.

A’a kasan mota bata zuwa layin su in kuma mukaje a kafa zakai ta jira ne a kofar gida tunda zamuyi hira da ita.

Tom shikenan ki gaida ta ki ce mata ban manta da Tukwicin ta ba zan bawa kairi ta kawo mata.

Tom kawai ummu hani ta ce kan ta yi gaba kar ya canja shawara.

A dedai gidan Balaraba mai markaɗe Ummu Hani ta haɗu da Bashir a kai rashin sa’a suka haɗa ido murmushi ya sakar mata wanda yasa bata da zaɓi face itama ta mayar masa da murmushin.

Da sauri tayi gaba badan batason ganin sa ba sai dan abu biyu, maganar mahaifiyar sa da kuma auren da ke kanta.

Koda ta yi gaba tausayin Bashir ne ya cika ta duk ya yi baƙi ya rame ya wani zama ɗan ƙauye, kamar ba Bashir ɗan gayu da ta sani ba, Bashir ɗan gayu fari dan duk farin ɗin ta Bashir yafi shi fari zan iya cewa har kyauma kawai gata da kuɗi Faruk ya fi Bashir.

A ranta duk sai taji ta damu ko me ya maida Bashir haka oho kwanaki dai ta ji ance ya auri wadda mahaifiyar tasa ke so.

Shikam Bashir bai ji haushin wucewa da Ummu Hani tayi bata masa magana ba tunda yasan yadda Umman sa ta yi yasani sabida shi yasa Ummu Hani taki masa magana.

Shigar Ummu Hani gidan su Salma yasa ya a je tunanin yanayin data ga Bashir a ciki da Sallama ta shiga cikin gidan.

Da Salma suka fara cin karo tana wanke wanke, suka sakarma juna murmushi kafin Ummu ta ce “ina Umma.”

“Ban sani ba.” Salma ta ce, “Wato ki yi wata da watanni baki zo ba sannan yau kizo memakon ki fara nemana ko.”

Dariya Ummu Hani ta yi kan ta ce yo ke ba gashi na ganki ba.
Umma ce ta leƙo ta tagar ɗakin ta tace kinganni nan Ummu kyale ja’irar yarinyar nan.

Murmushi Ummu ta yi ta shiga ɗakin sai da ta rissina cike da girmamawa ta gaida Umma kafin ta miƙa mata takardar Umma ta ce “yo banda abin Ummu ni ina zan iya karantawa.”

Dariya Ummu ta yi ta ce au haka ne, “Kinga Admission ɗin Salma ne ɗazun Faruk ya kawo.”

Murna Umma tasa gami da Hamdala a lokaci guda Salma ta shigo da gudu ɗakin tana faɗin, “Lallaima yarinyar nan kai wato a kawo tun safe se yanzu zaki kawon, ba kya kirawo ni a waya inzo in amsa.” ta faɗa cikin murna.

Murmushi Ummu Hani ta yi kan ta ce “da yake ke kika ban kudin kati ko.” Suka yi dariya duka.

Umma kan se faman sawa Faruk albarka take harma da Ummu Hani.

Ficewa suka yi daga ɗakin zuwa ɗakin su Salma suna shiga suka saka ihun murna kamar wasu yara.

Sai da suka gama murnar Salma ta karanta takardar wani farin ciki ya kuma lulluɓeta ji take tamkar yau ɗin riƙe ta ke da certificate ɗin ta.

Duban Ummu ta yi ta ce “Wai da gaske Ummu niɗin ce riƙe da Admission dina na BUK kuma a College of health ba faculty ba.”

Dariya Ummu Hani ta yi kan ta ce, “Yo to banda abinki mene Allah baya yi.”

Haka ne Ummu ba abinda Allah baya yi shi yasa da ya ɗauke mana Abbanmu sai ya bani ke a matsayin ƙawa ina gode masa ina gode miki, keɗin jigo ce a rayuwata.

Tsaki Ummu Hani ta yi kan ta miƙe Hajiya ni bari na wuce goben dan Allah kizo da wuri mu tafi kinsan Halun Faruk da mita in muka makara, tom Salma ta ce ta ciga da godiyar ta.

Washe gari Aisha bata je makaranta ba dan wurin tara su Ummu suka yi zasu wurin registration ɗin dan Haka Aisha ta zauna gurin fanke Ummu Hta shirya, takwas da rabi a gidan su Ummu Hani ta yi wa Salma ya zama Faruk kawai suke jira.

Wurin tara sauran minti goma Faruk ya iso suka tafi, sai da ya karya wurin goma suka ɗauki hanya, tunda suka gaisa da Salma take godiya gajiya yayi da godiya ya canja hirar.

“Ai Ummu ta faɗan zugata kike kan karta tare.” Zaro ido suka yi duk su biyun wato Ummu da Salma.

Ummu ta ce, “A’a dai mijin Ummu yaushe mu kai haka.”

“Jiya mana ko har kin manta kika ce tace in kin tare bazan dinga barin ki zumunci ba.”

Dariya Ummu Hani ta yi yayin da Salma tayi ajiyar zuciya ta ce, “Oh nifa sharri tamin kawai ce mata nayi in namiji ya fiye son matar sa yana kishin ta sosai in ya fiya kishin kuma yana kulle.”

“Ani nasan daman sharri ta miki nima wataran tana min.” Suka sa dariya duka.

Har suka ƙarasa office din suna ta hira abunsu gwanin ban birgewa

Sai wurin sha biyu da rabi suka dawo dan an fara kiraye kirayen sallah a ƙofar gidan su Ummu Faruk ya ajiye su, Salma ta shiga cikin gida yayin da Ummu Hani ta tsaya.

Duban sa ta yi kan tace “mijin Ummu bazaka tsaya kaci abinci ba.”

“No ki bari can anjima insha Allahu zan dawo insha Allahu yanzu ana jira nane, saidai pls ɗan matso, ba tare da sanin me zaiyi ba ta matsa dab dashi.”

Rungume ta ya yi sosai a jikinsa kasa cire jikin ta ta yi koda yake bama tayi ƙoƙarin cirewar ba sun jima a haka kan ya saketa.

“Kinsan Allah dankin ƙi yadda ne da tuni mun tare ko anan ko gidanmu.”

“Tariya ta nawa kuma, ka cika mantuwa banda abinda ka yi?’

Dariya ya yi, “Ai ni so nake ya zama kullun muna tare inta abinda na ke so.”

Basar dashi ta yi kan ta ce, “Duba agogo ta ce tunda bazaka ci abincin ba sallah fa?” Ta tambaya tana kallonsa.

“Kan inje bakin titi nasan sun tayar sai in tsaya inyi miƙon ruwa in alwala.”

Tom ta ce masa ta shiga cikin gida. Yayin da shi kuma ya fito daga motar.

Kallonsa take yana alwala a hankula ya ɗago ya kalle ta, ya ce ko kema kinajin abinda nake ji, da ido ta tambaye shi alamar me kake ji.

Kawai ji nake wallahi kamar kar in tafi, wata irin kewar ki nake ji.

Dariya tayi kan ta ɗauki butar, “Kai dai ko kaje ka anjima ɗin mayi magana kar a gaji da jiranka.”

Dariya ya yi tom sena dawo ɗin.

Ade dai tsallaken masallacin ya parker motarsa kafin ya fito daga motar ya tsallaka ya shiga.

Ana idar da Sallah ya yi lazimi da addu’oinsa wanda kusan duk na Allah ya basu zaman lafiya ne da Ummu Hani ne, ya bashi ikon faɗa mata umarnin mahaifinsa.

Da hanzari ya fito daga masallacin ganin kiran office sai shigowa yake yasan sun gaji da jiransa, sai dai me a kokarin sa na tsallaka titin ne farar motar ƙirar Honda tayi gaba dashi kan kace mene wannan tuni jini ya malale bakin titin.

A can gefe motar da ta bige Faruk din ta dakata yayin da mutanen da ke zaune bakin shagunan su da masu fitowa daga masallacin sukayi kan Faruk dake kwance cikin jini.

Wani Matashi sanye da kayan College of health ne ke ƙoƙarin bashi taimakon gaggawa.

Sai dai me a hargitse matashin ya miƙe yana faɗin bafa ya nufashi kamar ya mutu.

Wani dattijo ne ya matso jikin Faruk ɗin ya hau taɓa shi cikin tashin hankali yake faɗin “yafa mutu…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ummu Hani 20Ummu Hani 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×