Skip to content
Part 23 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Kai tsaye ɗakin Faruk Fatima ta nufa sai da ta isa bakin ƙofar sashen sannan ta tuna ashe fa yanzu bata da makullun shashin nasa, tsaki ta ɗan ja kafin ta juya zuwa main cikin gidan umman su Faruk ta gaisar sukai ɗan hira kafin ta fito ta zauna a verenda tana duba waya yau kam taci aniyar dole sai ta ga Faruk.

Tana zaune magariba tayi duk da ta gaji anma haka ta daure ta shiga cikin gida tayi alwalawa tayi sallah, dakin da ta saba kwana in taje gidan kwana ta koma zaman jiran Faruk.

Ganin har goma tamyi yasa ta fito dan tafiya, Halima ta tambaya ko Abba ya dawo tace mata eh to kawai ta ce ta nufi falon Abban.

Yana zaune suna kallo shida Umman su Faruk Umma ta ce “Ba dai ba anan zaki kwan ba?” Murmushi Fatima ta yi kan ta ce eh umma Dady baisan zan kwana ba, Abba ne ya yi murmushi ki “yi zaman ki zan fada masa ni nace ki kwan.”

Murmushi ta yi ai banzo da kaya ba ba, shima Abba murmushi ya yi yace “Badai kyason kwanan ne.” Kin ci abinci ne, murmushi ta yi eh Abba bari in wuce.

Ok ki gaida gida inji Umma, gashi kuma mutumin naki bai dawo ba har yanzu murumushi kawai Fatima ta yi kafin ta bar falon.

Tana barin falon Umma ta dubi Abba ta ce “Nifa tun safe banji duriyar Faruk ba, ko ka aike shi ne? Taɓe baki yayi “ina kuwa zan aike shi, zaizo ya samen ne.”

Sai dai me har ɗaya Umma na jiran ganin dawowar Faruk ba shi ba labarin sa, wayar sa kuwa ta kira yafi sau dari bata shiga shikam Abba tuni yayi bacci.

Tunanin da Umma ta yi na ko ya dawo bai shigo gun su ba duk da ba ɗabi’ar sa bace haka yasa Umman dauko key ta fito zuwa shashen Faruk ɗin, a kulle yake makullun hannun ta tasa ta bude ɗakin.

Babu alamun an zauna a Falon sai dai tasan tsaftar Faruk kai tsaye bedroom din sa tanufa baya dakin sai dai da alamu ya kwashi kaya dan ga wasu nan a ajiye kan gado an sauke akwati kuma, gaban ta ne ya faɗi da tayi tunanin ko dai ya bar gidan ne sabida ya Fasa auren Umma Hanin, salati tasa kafin ta fi ce ko rufe sashen batayi ba ta koma sama gun Abba.

A tsorace ya farka “Lafiya dai kike min irin wannan tashin cikin dare haka,” Idon ta duk ya ciko da ruwa muryar ta na rawa ta ce “Abban Ummi da alamu fa Faruk gidan ya bari tsorona kar ko yarinyar da ya takura aka daura masa aure da ita ya fasa aure.”

Tsaki Abba ya yi, “Shine dan ya bar gida zaki zo ki tashen haka kinji yadda gabana ya fadi yaje tunda haka yaga ya fiye masa, anma wallahi aure ne tsakanin sa da Fatima dole sai an daura in zai shekara dubu a inda ya je in ya dawo sai ya zauna da ita.

A tsora ce Umma ta zaro ido aure da Fatima kuma, eh jibi nake son Fada miki ki fadawa yaya Balaraba zasu kai lefe inason ita Ummu din da Fatiman su tare lokaci guda.

“Haba Abban Ummi ta ya zaka haɗa auren da ba soyayya sufa ba soyayya suke ba kasan ɗan yau.” Tsaki ya ja, “karma suyi soyayyar aure ne sai anyi” ya koma bacci abinsa.

*****

Ita kuwa Ummu Hani tunda suka rabu da Faruk ta koma gida gaban ta ke Faɗuwa ta rasa me ke mata daɗi wannan yasa take ta anbaton La’ailaha illah anta Subhanaka inni kuntu minazzakimin tana faɗe tana ayyukan ta.

Ko da ta gama abincin siyar wa Faruk ta ɗorawa abincin tunda ya ce zai dawo abinda ya fiso ta dafa Masa wato shinkafa da taliya ahaɗa masa gu guda, ta dama masa koko dan indai ya ci abinci yana son yasha koko, sai da ta zubawa Muhammad kokon Sannan ta fita ta kira mai fitar mata da abincin kofar gida.

Kasa zama ta yi sai Aisha ce ta zo ta zauna haka kawai ranta ba dadi wani iri ta ke ji tamkar tayi ihu dam dai ita ɗin ba gwanar complain ba ce, in abu na damun ta a rayuwa ta riga ta saba ta kuma sa aranta akwai wasu akasan ta in bata zama jaruma ba su waye zai kula da su.

Tun tana tsanmanin Faruk har ta dauko waya ta kira shi, sai dai waya bata shiga ita din tasan shi ba gwanin kulle waya bane duk rintsi yana da caji ko meeting yake in ka kira zata shiga sedai in ya fito ya biyo kiran.
Tun tana tunanin zaizo ko kira har ta dena haka kawai take samun negative feeling akan rashin zuwan ko ɗaga wayar sai dai ta rasa me take tunani aranta game da haka.

Bacci kam kasawa ta yi ta zubawa wayar ta ido ita ba Number ɗin kowa nasa ta ke dashi ba sai Umar gashi dare yayi bare ta kira shi haka ta dauro alwala ta hau salloli tana fatan ya zama lafiya kalau ya ke.

*****
A can asibiti mutunin da ya buge Faruk sai kai kawo yake ya rasa abinda ke masa daɗi yayin da a office ɗin likitan, likitocin da matashin likitan ya kira ke ta dube dube Dr Colins da ya kasance likitan zuciya ne yayi ajiyar zuciya kafin ya ce he is alive but we need to move him out of this room.

Suna tsaye aka fito da Faruk a kayi ɓangaren ƴan zuciya da shi a can aka dauko sauran abubuwan da ake buƙata aka gwargwada shi tare da masa scanning na internal da external organ gami da kwakwalwa.

Bayan dogon nazari da bincike akan suka gano abinda zasu gano sannan matashin likitan ya fito dan yiwa mutumin bayanin binciken sun.

Mutunmin na hango Likitan yayo gunsa likita ya dai yana raye ko mutumin ya tambaya a ƙagare, share gumi likitan yayi kafin ya ce yana raye anma sai sai wani ikon Allah ɗin rayuwar sa, kwakwarwar sa ta haɗu da jini samnan lakar sa wato central nervous system ta taɓu ko ya rayuwa zaiyi mugun wahal ya iya komai da jikin sa da ya wuce magana kawai yana cikin dogon suma yanzu mun sashi a injin da zai tallafa masa yayi nufashi yana bukatar a maidashi Aminu Kano.

Ajiyar zuciya mutumin yayi kafin ya dubi likitan to yanzu wanne processes za’a bi wurin maidashi can ɗin yanzu ka biyo ni Sir.

Sai alokacin mutumin ya ce ni kuwa kasanni ne kake ta faman Sir, ɗan ƙaramin murmushi likitan ya yi sannan ya ce eh ka koyar da mu phycology a Buk during our second year at University.

Oh Allah sarki ya ce kawai dan har lokacin hankalin sa a tashe yake shi kam ba haka yaso ba shi baiso ya zama silar nakasar wani arayuwa gabaki daya ransa a jagule ya ke.

Sai da aka gama komai inda duk inda za’a sa hannu police ɗin ne kesa hannu sai da aka sa Faruk ɗin a motar asibiti da zata wuce dashi Aminu kano sannan mutumin ya tuna dole fa yaron yana da dangi.

Shida mutanen da suka kawo Faruk ɗin aka hau kacaniyar neman waya sedai babu ita babu labarin ta an sace.

<< Ummu Hani 22Ummu Hani 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×