Skip to content
Part 24 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Neman duniya anyi wa wayar Faruk ba’a same ta ba, ran bawan Allah ɗin da ya buge shi ya mugun ɓaci a ce mutane bazasu taɓa zama masu tausayi ba daga buge mutun sai a ɗauke wayar sa wannan wanne irin rashin imani ne, ganin ba’aga wayar ba yasa mutumin ɗaukar niyar in nanda sati biyu bai samu sauki ba zai sanya cigiya a gidan Tv.

Ita kuwa Ummu Hani da bata san sanda bacci yayi awon gaba da ita ba firgigit ta farka ba komai ya farkar da ita ba fa ce mafarkin da ta yi Faruk ya na ta kiranta bata samu ta ɗauka ba, da sauri ta miƙa hannu zuwa inda wayar ta take sai dai babu ko alamar miss call faɗuwar gaban ta ne yaƙaru dan kam zuciyarta ta gama yadda ba lafiya ba dan tun randa suka fara haɗuwa da Faruk bai taɓa awa goma bai kira ba yanzu kuwa da aka ɗaura musu aure baya iya tafiya gida bai zo ya ganta ba.

Agogon wayar ta kallah shida saura yanzu tasan dai ko Umar bai ta shi ba in ta kira shi ba zai yi tsanmanin bata kyau ta masa ba na hanashi bacci tunda dole wasu mintina kaɗan dole zai tashi.

Da’alamu ma idon sa biyu don bugu ɗaya ya ɗauka a’a matar mu ko magagagin bacci kike ne ba angon naki ba ne ya faɗa cike da tsona, bata iya murmushi ba dan bama ta fahinci wasan ya ke ba, haka kuma ta manta da batun gaisuwa dama Tambayar ka zanyi  ko jiya magana da Faruk kaga tun jiya da safe da muka rabu ya ce zai dawo bai dawo ba inata kiran wayar sa akashe.

Gabansa ne ya faɗi dan yasan haka kawai Faruk ba zai rufe wayar sa ba, yasan ko maganar auran Fatima ce ba zai sa ya gujewa Ummu Hani ba dan shi da ya kira bai same shi ba yayi tsanmanin ma ko gidan su Ummu din ya gudu.

Rasa mai zai cewa Ummu ya yi sai can dabara ta faɗo masa, “Eh to bamuyi magana ba anma ina tsanmanin ko wayar tasa aka sa ce bari gari ya sha zan je gida in muka haɗu zan haɗa ki dashi.”

To kawai ta ce duk da can ƙasan ranta hankalin ta bai kwanta ba tasan Faruk baya zuwa inda mutane keda yawa bare a sa ce masa waya kawai dai zata jure anjima din ta ji mai Umar ɗin zai faɗa mata.

*****

Ita kuma Umman Faruk ganin da gaske Faruk ɗin baya nan kuma wayar sa bata shiga ɗakin ta kawai ta koma ta kwanta da zummar gobe zata kira Umar tunda tana da tabbacin ko me Faruk zai haɗa dole ne ma sai ya sanar da Umar.

Washe gari bayan ta gama lazimin ta ta kira umar sai dai line busy dole ta aje wayar ranta cike da addu’ar Allah yasa ɗan nata lafiya.

Umar na gama waya da Ummu hanin Umman Faruk ya kira dan yaga kiranta lokacin da suke magana da Ummu hanin.

Bugu ɗaya Umma ta ɗaga ya gai data cike da girmamawa ta amsa kafin ta ce Umar ka faɗawa Faruk ya buɗe wayar sa kuma wallahi ya dawo gida in ba so yake in ci mutuncin sa ba, hankalin Umar fa ya tashi baya son tadawa Umma hankali daurewa ya yi murmushi tom shi kenan bari ya fito daga bayi zan faɗa masa, ajiyar zuciya Umma ta yi har ranta kam taji daɗi tunda ɗan nata na lafiya.

Suna gama waya Umar ya zari makullun motar sa sai ma’aikatar su Faruk ba kowa sai mai gadi masinjan Faruk ɗin ya kira nan ya sanar masa aifa jiya faruk kam baizo aiki ba, yama kasa tunanin wacce irin matsala ce ta faru da Faruk ɗin bare ya yi tunanin mafita.

Duk inda yake tunanin zai ga Faruk yaje baya nan yasan koda Faruk zai gudu sabida karya auri Fatima to tabbas zai tafi da Ummu Hani baya son yin wani tunani dan baya ma son zuciyar sa ta raya masa cewar wani abu ne maras kyau ya sami aminin nasa.

Ita kuwa Ummu Hani ganin har 7 ba kiran Umar sai tasha jinin jikin ta ba ko wanka bata yi ba ta zari hujabin ta kai tsaye ɗakin hajiya ta wu ce, Hajiyan na zaune kan sallaya ta gai da ta sannan ta ce, “Dama zani gidan su Faruk ne tun jiya hankalina yaƙi kwanciya.” Shiru Hajiya ta yi kafin ta ɗan nisa sannan ta ce, “Tom ki ɗauki Aisha ko kairat ku je ta re.”

“A’a da gidan su Salma zani sai mu tafi tare ita Aisha suna da exam, eh to hakan ma ya yi Allah yasa muji alkairi Hajiya ta faɗa Ummu hanin ta ce Amin sannan ta fi ce goye da Muhammad dan tasan in ya farka bata nan ihu kawai zasu sha.

Daga gidan su Salma ɗin sukayi bakin titi kasan cewar safiya ce babu wulgawar Ɗan sahu sosai wannan yasa dole sai sun fita main titin unguwar. Suna tafe Salma na bawa Ummu baki yayin da ita kuwa Ummun shiru kawai ta yi ji take tamkar ta sa kuka anma ta kasa.

Motar Faruk da suka hanga bakin tsallaken masallaci yasa su karasa wa jikin Ummu na ɓari ta hau leƙa motar sai dai a kulle motar take ba kuma alamun da mutun a ciki, wani dattijo ne da ya ƙaraso yake faɗin, “Ah kunsan mai motar ne tun jiya da mota ta bige shi ba’a samu ƴan unwan sa sun ɗauke motar ba.”

“Bige shi kuma?” Ummu ta faɗa cike da tashin hankali, “Eh yar nan anma kai shi asibiti tun jiyan.” Girgiza kai kawai Ummu take cike da tashin hankali Salma ce tai farar dabarar faɗin Baba kuma wanne asibiti aka kaishi. Nisawa Dattijon yayi sannan ya ce eh gaskiya ban sani ba da yake duk bamu bi su ba.

Riƙe hannun Ummu hanin Salma ta yi taja ta bayan ta ce ma tsohon sun gode, ba su fasa zuwa gidan su Faruk ɗin ba duk da kuwa ita Ummu hankalin ta ma a tashe ya ke inda ita kaɗai ce bana ce ga inda zata ba.

Mai gadi ba ganin su ya gaida su dan ya shada yar baƙar yarin yar ita ce matar Faruk ba wani tambaye tambaye ya musu iso ciki, suna shiga aka kaisu main parlour ɗin gidan ko zama kasawa Ummu ta yi dan a lokacin ita kam bata san mai ya da ce ba tashin hankalin da ke zuciyar ta Allah ya yi yawa da shi.

Hajiyar Faruk na ɗakin ta dan tun jiya Haushin Dadin su Faruk take ji naƙin nuna ko in kula ga Faruk ɗin Ai na faɗa mata cewar Ummu Hani ce tazo ta fito hankali ta she tsoron ta kar dai yaron nan sakin Ummu yayi kafin ya gudu.

Yadda taga yarin yar ta kuma yadda da abin da zuciyar ta ke faɗa mata ta karasa jiki a sanyaye bayan Salma ce ta gai da ita inda ta samu gu ta zauna sannan ta dubi Ummu, ki zauna kinji Ummu komai zaizo da sauki kinji ta faɗa murya a raunane.

Kallon ta Ummu ta yi kafin ta ce bai ji ciwo da yawa ba ko Mami ta faɗa murya na rawa, tsoro ne ya kama Hajiyar Faruk, “Ciwo kuma?” Ta tambaya cike da mamaki, “Eh a wanne asibitin yake?” Ummu ta kuma tambaya cike da ƙagara.

Wai mai ya samu Faruk ɗin ne mami ta tambaya, sai a lokacin kuka ya zoma Ummu Allah sarki Faruk ɗin ta ashe ba ba wanda yasan halin da ya ke ciki ko yaya ke yanzu oho nan kukan ya kuma kwace mata.

Sai Salma ce tama Mami bayanin da tsohon ya musu hankalun ta ya tashi cike da Fargaba ta bar falon zuwa ɗakin Alhaji yana ta barcin sa hankali kwance cikin fushi ta tashe shi ta faɗa masa abinda su Ummu suka faɗa masa hankali ta she ya mike ya baro ɗakin sa.

Waya ya fara yi ga yaran sa kan su bazu asibito ci dan naimo inda Faruk ɗin yake, shima ɗin bai tsaiya ba asibitin da ke kusa da su ya kufa.

Umar ma jin aminin nasa yayi haɗari yasa shi bazama asibiti. Kusan dai duk asibitin da ke kano sun karaɗe shi private dana gwamnata babu Faruk babu bayanin sa wannan yasa aka sanya cigiya ko wani ya ganshi ko jin labarin sa.

Baifi wasu awanni da sa cigiyar ba aka samu Faruk ɗin dan Prof din da ya buge shi ɗin ne ya zo da kansa har gidan su Faruk ɗin, duk da Iyayan Faruk da Ummu basu ga Faruk ba anma samin tabbacin yana raye yasa hankali ɗan kwanciya.

Faruk ɗin an masa transfer zuwa asibitin Zariya ne dan masa gashi sabida matsalar laka da ya samu, cikin yinin ranar suka shirya har Ummu zuwa zariyan dan kowa ya ƙagu ya ga yadda Faruk ɗin yake, Ummu tabar ƙannen ta gun Hajiya ne inda ta tafi da Muhammad kawai.

Hankalin kowa ya tashi Ummu kasa tsaiwa tayi kafafun ta kasa ɗaukan ta sukai ɗora idanun ta bisa Faruk dake kwance tamkar inji bisa taimakon engine kai bazaka ce Faruk ɗin da ke iya yawo shekaran jiya ba ne kuka tasa a lokacin da ta zube kasa yaraf hankali tashe.

<< Ummu Hani 23Ummu Hani 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×