Satin su biyu kawai da zuwa Zariya Ummu Hani duk ta bi ta rame ta kuma baƙi in ka kalli fuskar ta tayi fayau da ita abin tausayi baka ganin komai sai dogon hancin ta da manyan idanun ta da suka kuma girma sabida kunburin kuka da sukai dan waccan Jarumar Ummu Hani wadda bata kuka ta jima da suma dan kuwa wannan Ummu Hanin ko yaya ta ɗora idanun ta bisa mijin nata hawaye ne ke wanke mata fuska.
Zuciyar ta cike take da tausayin mijin ta in ta ganshi a kwance tamkar gawa zuciyar ta kuma tsinkewa. . .
Fatan Alkhairi Gareki Kanwa Allah ya karawa Rayuwa Albarka da Nisan Kwana By Journalist Talksay
Amin ya rabbi na gode sosai, Talksay ya raba zumunci