Skip to content
Part 28 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Zaune suke Fatima na doguwar kujerar dake ɗakin inda Ummu ke zaune kujerar dake kallon Faruk suna hira kasa wannan ya kara batawa Fatima rai ta mike a fusace zata bar ɗakin Faruk na kallon ta har ranta Ummu taji daɗin haka sai dai me ji tayi Faruk na faɗin,

“Ummu dan Allah ɗan bamu guri zamuyi magana da Fatima.” Ranta ne ya baci ta dubi Faruk din sai ta kasa magana dan ya mata kwarjini kwafa kawai tayi ta bar dakin ranta na mata suya sosai haka kawai taji bata son Ayatullah ya ganta cikin ɓacin rai sai dai kuma bazata iya shanye fishin ta ayanzu ba wannan yasa ta kawai zama a saman benen tana bin kasa da kallo a hankali ta fara jin sa’ida a ranta kusan minti goma Fatima bata fito daga ɗakin ba wannan yasa Ummu sauka ƙasa dan ta ji sanyi yanzu a ran nata.

Tana tafe tana tinanin ko yanzu Ayatullah ya gama aikin sa oho ita bama ta taɓa tambayar sa a wanne sashe yake ba da taje ta gani kamar yasan mai take tunani ya matso dab da ita dan tun ɗazu yake Binta ya mata Sallama.

Juyowa tayi cike da annurin fuska ta ce ashe kana kusa murmushi yayi eh wallahi na fito zan je canja kaya in wuce gida na hangoki, murmushi tayi eh wallahi miji nane zasuyi magana na fito in ɗan basu wuri, gaban sa ne ya faɗi jin ta anbaci wani da mijin ta duk da cewa yasan tana da mijin anma dik sanda ya tina hakan sai ransa ya susu yanzu da ta kara kiran mijin sai yaji faɗuwar gaba da tashih hankalin nasa yama fi na da.

Kasa zama yayi da suka ƙarasa ransa fal ɓacin rai ya dai daure bai bari ta gane ba ya ce bari inje in mun kuma haɗuwa insha Allahu zaki rakani in dubo yayan namu, daɗi taji har ranta tace tom na gode sai Allah ya haɗamun ya ce to kawai Allah ya kara sauƙi kan ya bar gun.

Ta jima agun kafin ta daure tabar gun sai lokacin ranta ya kuma ɓaci da kamar karta koma ɗakin sai ta tuna kome Faruk ya mata ya wuce ta ki komawa tunda baida lafiya yana bukatar ta akalla in tananan dole Fatima bata da dalilin taɓa mata miji da sunan kula dashi.

A hanya dai inda zata shiga lifter ta haɗu da Fatima duk ta canja ba kamar ɗazun ba idon ta yayi jajur da alamu kuka tasha tana ko ganin Ummu ɗin ta kuma fashewa da kuka ta riƙo hannun Ummu ɗin kin sani kema take faɗe cikin kuka, tsoro ne ya cika Ummu cikin ruɗani ta dubi Fatima Mutuwa yayi? ta faɗa tama kasa kukan.

Maganar da sukai ɗazun da Faruk ɗin ce ta dawowa Fatiman ta kuma rushewa da kuka wato Ummu na barin ɗakin Faruk ya kira sunan ta Fatima ya ce ta ce na’am kin san SCI kallon sa tayi dan bata gano mai yake tambayar ba bai damu da kallon da take masa ba ya cigaba, may be it’s because we are not meant for each other shi yasa Allah ya ɗora min spinal cord injury, gaban ta ne ya faɗi haba Faruk dan baka sona basai ka dorama kanka wannan masifar fa.

Kuka yasa ko bana sonki bazan taba so in zama haka ba kodam in rayu da Ummu bazan so haka ba Fatima ki manta dani a rayuwar ki kedin ba mata ta bace ki barni inji da iya hakkin yarin can da ke kaina da bazan iya saukewa ba basai kin doran wani ba dan Allah.

Girgiza kai ta hauyi haba Faruk nasan halin ka sarai wallahi bazaka yaudaren ba kai tsaye gurin da ake aje information na Patient tayi ta sa a duba mata bayani kan Faruk hankalin ta ya mugun tashi dan abinda ya ce din shi ɗin ta gani a record ɗin mai ke damun sa.

Hankalin ta ya tashi sosai kasa komawa cikin dakin tayi ta jima abakin kofar dakin tana kallon sa ta glass tana kuka tasan tana son Faruk anma zucuyar ta kasu gida biyu bata jin zata iya jarumtar auren sa abin sai ya mata yawa gashi baya son ta ga rashin Lafiyar da bata warkewa.

Mai ya samu Faruk ɗin mutuwa yayi Ummu ta kuma tambaya girgiza kai Fatima ta hau yi bai mutu ba kema kinsan bazai warke ba, ajiyar zuciya Umma tayi in har yana raye ina ganin sa hakan yafimin komai girgiza kai Fatima tayi tare da sakin hannun Ummu hani tabi Ummun da kallo tama kasa yin wani tunanin arziƙi.

Ummu ranta duk ba daɗi tausayin Faruk ya cika ta ɗakin ta nufa sai dai baya nan ta hau dube dube bata ganshi ba fitowa tayi da nurse ta ci karo take tambayar ta ina na ɗakin yake nurse ɗin ta bata amsa da an je a masa wasu gwaje gwaje ne dan gobe ake son fara masa gashi.

Godiya Ummu din ta yi ta koma ɗakin ta zauna sanyi take ji sosai ga kwannafi duk yabi ya dame ta bama wani abinci ta ci ba har ta zauna taji tana jin amai ta miƙe ta koma toilet dakyar ta samu ta iya wani amai mai tsami wanda ya kuma kara mata kasali jiki ba kwari ta wanke gun ta hau wanke baki, tana toilet ɗin ta jiyo alamun ana shigo da gadon Faruk ta hanzar ta fito.

Yana ganin ta ya hau murmushi itama murmushin ta masa har kin dawo kenan ina ta jiran ki, jiki nane ba daɗi nace bari in sha iska kan ku gama hirar, dariya yayi oh Ummu sarkin kishi to maida Wukar Faruk naki ne ke ɗaya dan ina tabbatar miki ba wadda zan burge ahaka.

Tsuke fuska tayi inji waye ai ina tabbatar ma mata sai dai in basu ganka ba anma Tuni zasu rude sai mijin Ummu, tuni ta manta da ɓacin ran ɗazu hirar su suke gwanin ban birgewa, har ta gama masa alwala da zaiyi Salla kan ya tayar ta ce, ina Ayatullah da nake baka labari.

Murmushi yayi eh na tuna shi ɗazun muka haɗu a waje yake cewa zaizo dubaka ta faɗa, murmushi yayi aiko da naji daɗi yaushe zaizo, eh to gaskiya ban sa ni ba yadai ce in mun sake haɗuwa, to Allah ya nuna mana ya ce gami da tada Sallah ɗin.

Ita kuwa Fatima tayi kuka sosai bayan ta koma masaukin su tuni ta haɗa kayan ta gami da fara naiman visa dan tayi tunanin may gwanda ta tafi gida zai fiye mata kafin dare kuwa ta samu washe gari da Sassafe ta bar kasar sai Nigeria.

Shi ko Faruk washe gari Aman Ummu ne ya tashe shi da ɗan ɗaga murya yake ta tambayar mai ne lafiya dai ko hankalin sa tashe ji yake tamkar yasa kuka shi yanzu mai ne amfanin sa yana kwance tamkar gawa ace matar sa bazai iya taimaka mata ba.

Fito tayi tana murmushi ta ce ba komai fa zazzabi nake may be ko fitar da nake bakin bishiya ne yasa sauro ke cizo na, hankali tashe yake faɗin kuma kikai shiru bari Hajiya tazo zansa ta kaiki gun likita, rokonsa ta hauyi dan Allah kayi hakuri zanje da kaina wallahi bana son abinda zai sa in rage ganin ka kasan intaji banda lafiya hanani zuwa zatai tace in huta.

Shiru yayi kafin yace eh to kuma fa nima bazan so in daina ganin ki ba dan Allah ki daure ki je tom shikenan nawan kar ka damu suna haka nurses suka shigo dan zuwa dashi ɗakin gashin.

Kusan tun safen nan har yanma Ummu na jiran dawowar Faruk bashi ba labarin sa sai Wurin shida Dady ya zo ya hau mata Nasiha yadda taganshi da yadda yake mgn sai hankalin ta ya tashi Dady mai ne ya same shi, duk dauriyar Dady sai ya kasa jurewa yana son Faruk yana tausayin yarin yar, kinsan dai Allah ya fimu sonsa da ya amshi abinsa ya fimu sonsa.

Kuka tasa ta riko hannun Dady tana Faɗin dan Allah karka cemun ya mutu wallahi Faruk da ransa ba yanzu zai mutu ba, jan hannun ta yayi zuwa ɗakin da Faruk din yake da gudu ta karasa bayan kwace hannun ta tahau jijjigashi tana kuka dan Allah ka tashi ka ce musu baka mutu nasan da ranka.

Doctor din da ke gefe ne ya matso ahankula ya zare robar da ke hancin Faruk din gami da tura injin gefe ya zama sai Faruk din kawai kafin cikin harshen turanci ya fara bata hakuri ta kuma sa kuka.

Dakyar Dady yasa ta bar asibitin tana kuka a inda sukai masauki ta tarar da Mami suka hau kukan su biyu tashin hankali tsoro da tausayin kan ta ya cika ta. Washe gari Dady ya zo ya ce ya gama musu komai zasu tawo shi zai zauna ya gama processing din tafiyar da gawar zuwa Nigeria.

Ummu ta yi ta kuka ita abarta da gawar sai da Dady ya yi mata tsawa da faɗa sannan ya samu ta tafi shima sai da ya kuma mai da ita taga Faruk din ta yi kuka iya kuka dakyar aka kwace hannun ta suka nufi Filin jirgi.

Da yanma lis suka iso Nigeria, Umar ne yazo ya ɗauke zuwa gidan su Faruk ɗin, makil gidan ya cika kai kace lokacin za’a Sallaci gawar, duk da Ummu taga gawar Faruk tun acan yanzu ta kuma yadda tabbas Faruk ɗin ta ya tafi duk dauriyar ta kuka ta kuma fashewa da shi.

<< Ummu Hani 27Ummu Hani 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×