Kai tsaye asibitin suka wuce da musa, office ɗin likitan suka wuce batare da wani biye biye ba, dan su Faɗawa likita ga Musa yana so su gwadashi.
Ba ƙaramin tashin hankali Ummu ta shiga ba, da likitan ke faɗa musu sai dai suyi haƙuri Allah yaima Umma cikawa, kukanma kasayi tai, baby ɗinsu ta amsa ta rugumeshi cike da tausayi.
Da taimakon likita, da su Musa aka basu gawarsu suka yo gida da ita, Ummu gani take kamar Umman kawai bacci take, tama kasa yadda da cewar wai Umman gawa ce.
Kusan da asuba suka dawo gida, kwata kwata Ummu bata rintsaba, ita da inna da su Umma Balara maƙotan su suka yiwa Ummanta wanka, ita ta tsefe mata kai ta gyara mata shi, duk gani take Umman zata farka ba mutuwa tai ba, kawai faɗe likitan ya yi.
Tun asuba gidan ya fara cika yan uwan Umman da na Abban su, duk sun hallara jira ake kawai gari ya yi haske a kaita.
Har lokacin Ummu ta kasa kuka riƙe take da baby ɗinsu, ta shiga ɗakin da Umman ke kwance cikin likkafani, ahankula ta zauna ta bude mata fuska.
Fuskarnan ta yi wasai, hancinta toshe da audiga, a hankula tasa hannu ta cire audigar, ta dora jaririn a cikin Umman, ita kuma ta dora kanta akan ƙirjin Umman, tana shakar turaren almiskin da aka fesa mata, Umma ya zanyi da jariri, dan Allah ki tashi nasan baki mutu ba, ta faɗa a hankula.
Ke mai kike haka cikin faɗa kawunta ke faɗe, tashi ki fita bata ce komai ba ta ɗauki jaririn da tun jiya ba’a sanya masa kaya ba tai waje.
Takwas dai dai masu ɗaukan gawa suka shigo, tana kallo suka ɗauki Umma su kayi waje, ta kuma rungume jaririn ranta na mata zafi, wato ashe ma hawaye rahama ne, yau da ta kasa kuka ji take tamkar ana tafasa zuciyarta, sabida yadda take mata ciwo da raɗaɗi.
Wajen tara Inna Mai Ɗanwake ta sa Muklisa ta je ta ɗebo su kairiyya a gidanta, dan ta hana akawo sune dan karsu ga gawar Umman nasu hankalinsu ya tashi tunda yara ne.
Tare suka shigo da Muklisa, tana ɗauke da Usaina inda Aisha ke ɗauke da Hasana, Khairi na riƙe da hannun Sajida ajere suka shigo, sai alokacin Ummu Hani ta ji kuka ya dawo mata, ganin ƴan uwan nata.
Daurewa tai ta shanye kukan, da sauri Usaina ta sa zillo sai Muklisa ta sauketa, tana direta tayo gun Ummu tana kuka, tana cewa, yaya wai Ummanmu ce ta mutu shiru Ummu ta yi, bata ce komai ba kawai ta rungume ta, tanasan kuka anman tasan in tayi zata raunana ma ƙannen nata zuciya, hakan yasa ta yi shiru dan yanzu tasan tana buɗe baki kuka zai tawo mata.
Wurin goma Alhaji Bala maƙocinsu ya aiko da buhun shikafa har uku, da galan ɗin mai, kan kace me har mutane sun ware anata girke girke.
Sosai gidan ya cika, kai bazaka ce gidan mutuwa bane, hira kawai kowa yake ciki kuwa harda shaƙiƙan Umman, wanda ya kamata ace bayan su Ummu Hani, su zasu fara jin mutuwarta anman da alamu ko ajikinsu.
Batun dangin Abbansu Ummu Hani kuwa daman su ko oho, dan bason Umma suke ba, dan haka mutuwarta ba damunsu ta yi ba.
Zaune suke a ɗaki, Ummu Hani na rike da baby, wanda duk cikin dangin nasu babu wanda ya yi ƙokarin yace zai sa masa suna, dai dai da ɗaukansa babu wandai ƙoƙarin yi, bare jin lafiyarsa.
Hasana dake manne jikin Ummu Hani ce, cikin muryarta ta yara ta dubi Ummu ta ce yaya, wai wannan ƙaninmu ne? Ummu Hani ta yi murmushi, eh ƙaninmu ne, to ya sunansa yarinyar ta tambaya.
Duban yaron Ummu Hani ta yi, sai yanzu ta tuna, anafa sawa jariri suna, bakinta tasa akunnensa ta yi masa huɗuba, sannan ta dubi Hasana ta ce sunansa Muhammad.
Yeee muma munyi Muhammad, Hasana ta faɗa, Ummu tai murmushin ƙarfin hali.
Ummu Hani da kanta taiwa Muhammad huɗuba, dan taga iyayan nasu da alamu sun mance da anbar jariri, tunda har biyu ga mutuwar, dai dai da biyu da haihuwarsa sun kasa bi takansa, kayan da take saka masa ma makociyarsu ta ɗebo cikin kayan jaririnta sabbi da kwance ta bawa Muhammad ɗin.
Ranar biyu ma sai da wani ya kuma kawo shinkafa, buhu guda sai dai me kaf zuwa uku dangi sun dafe ta sun kwashe wata.
Da yanma haka kowa ya tattara kayansa, da yaransa sukayi gaba da zummar sai ranar bakwai.
Ummu hani ta yi zaton ko mutun ɗaya ne zai zauna tare dasu zuwa bakwai, ararrabasu dan tasan dole sai dai kowa ya dauki daya ko biyu, anman sai taga babu ma wanda ya yi maganarsu.
Haka ita da kanta cikin dare taje ta rufe musu ƙofa, ko bayan rasuwar Abbansu bata taɓa zuwa ta rufe ƙofa ba, Umma ke rufewa, asoro ta durƙushe tasha kukanta, tun mutuwar sai yau ta samu ta yi kuka, abinda ya tsaya mata a maƙogwaro ya ƙi gaba ya ƙi baya sai yau ta samu yaɗan motsa, yabar inda ya tokare mata, duk da cewar bawai ya yi kasa bane, sai dai taɗan ji sanyi aranta.
Washegari rasa me zasuci ta yi, dan ko kwayar shikafa babu agidan, bugun kofar dataji ne yasa ta yi saurin buɗe gidan, Imrana ne yaron maƙotansu rike da kwanon sha, wai gashi inji Ummanmu da ɗi ya kama Ummu Hani, dan yanzu tunaninta me zata ba su Usaina.
Kan goma sun samu abinci sosai na maƙota, masu kawowa gidan mutuwa.
Madara kamar kullin ta dafawa Muhammad, yasha rabi ta bawa su Hasana rabi, dan in bata basu ba in suka hau rigima, mai rarrashinsu sai ya shirya, Umma kawai ke iyawa yanzu kuma babu ita.