Skip to content
Part 30 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Washe gari da wurwuri Ummu Hani ta tashi da niyar yin aiki kafin ta wuce asibiti dan duba Dady sai dai jikin ta ba ƙwari dole ta yi wanka tukunna da ruwan zafi mai zafi sosai ta shafe jikin ta da Rub kafin ta yima Muhammad wankan da shi da yan biyu da kyar ta iya dama musu koko tabar ma sauran a botiki kafin ta goya Muhammad ta leƙa ɗakin da Hajiyan su da Umman su Salma suke kwance bata so tashin su ba sai dai bazata so su tashi kawai suga bata gida ba, bayan an kwanta da ita.

A nitse ta tashe su ta ce ita zataje asibitin dan tana son jin mai Dady zai ce tom suka ce Umman su Salma ta ce ta taso Salman ta rakata tunda yayi sassafe tom kawai ta iya cewa ta fito daga ɗakin, Kaya ta samu Salman na canjawa sannu ya jikin Salman ta faɗa, da sauki ta ce kawo Muhammad ɗin in goya naga jikin naki ba daɗi sosai sauko shi tayi bacci ma ya ke dan haka bai kuka ba Salman ta goya shi.

Sai dai me kuka su Hassana suka sa su lalle sai sunbi Umman su duk yadda Ummu ta yi siyi shiru kinyi sukai dole tana ji tana gani ta sa su a gaba suka tafi aiko yaran sai murna suke.

Da sunyi tafiya kaɗan Salma sai tayiwa Ummu sannu har haushi Salman ta fara bata ita dai tasan ko ramewa batayi ba sannan ita ba gwanar Ragonci bare ta ce shi tayi shiru kawai ta yi dan abinda ke ranta yanzu sam bata da lokacin yin faɗa ko ƙorafi.

A kofar Ɗakin Dady ɗin jama’a ne da dama da suka so duba shi wasu ma basu san Ummu ɗin ba sai Mami ce ta nuna musu ita aiko tausayin ta ya cika su, Ya Farka ne Ummun ta tambaya bayan ta gaida su, eh tun ɗazu yanama ta tambayar ki zaku iya shiga tom ta ce ta miƙe ayayin da zuciyar ta ke dukan tara tara.

Dady yana jingine jikin filo idanun sa a rufe suka shiga ganin haka yasa Ummu faɗin Bacci ma yake muje kar su Hasana su tashe shi, buɗe idanun sa yayi a nutse sannan ya ce Ummu idona biyu ya faɗa cikin sarƙaƙƙiyar mursu ta manya.

A nutse ta koma ita da su Salma suka rissina suka gai dashi ya amsa tun da nafarka nake son ganin ki, eh naje gida ne sabida nan ɗin da yan jinya can kuma ni kaɗai sai yake ta samin tunane tunane, haka ne ya ɗan gyaɗa maza kiramun Umman taku yana nufin Hajiyan su Faruk, miƙewa tayi su Salma suka biyo inda suka fi ce.

Su Salman gu suka samu suka zauna inda ta faɗawa Mami kiran Umar da Abban su Fatima da yayan Dady ne suka biyo ta kusan dai su goma ne suka shigo ɗan da Dady ɗin yake, gyara zama yayi kafin ya ce dama bari nayi tazo sai in faɗa mu nasan dik kun ƙaƙu kuji inda Gawar Faruk take.

Gaban Mami ne ya faɗi gawa kuma kenan ya mutun ɗin daurewa tayi ba ta ce komai ba Dady na nisa kafin ya ce, kusan tun tafiyar ku ciku cikun tawo da gawar nake sai dai abu ya xi tura yadda aka tabbatar mun da na matsa ma shine zai iya ɗaukan wata guda yama zo da wuri kenan wannan yasa na samu Lamiɗo ya nema mana transfer ak akai komai tamkar Faruk nada rai na mai dashi asibitin su Lamiɗon daga nan muka binne shi a garin da Lamidon yake ya faɗa yana share hawaye.

Kuka mami tasa ta yanzu Alhajji kama Faruk adalci ace gawar sa ka rasa inda zaka binne ta sai nesa inda ba zamu iya dinga kaimasa ziyara ba ni ka dawon da ɗana ta faɗa tana kuka, itama Ummu kuka take abinda Mami take faɗa shine aranta dan dai kawai Dady ne yayi hakan shi yasa bazata iya magana ba.

Ce miki akai dan inaso ne gatan da zan wa gawar Faruk kawai kenan gaggauta binne ta shi kansa nasan da zai iya magana sai ya roƙi hakan kuma batun ziyara ai Allah yana ko ina addu’a zamu dinga masa Anan take ko acan ita yake bukata bawai zuwan mu ba.

Dakyar aka lallashi Mami ita kuwa Ummu anyi anyi taƙi shiru itakam da tasan haka ne da bata tawo ba wallahi. Dady da kansa yayi ta bata baki yana mata Nasiha da ban baki.

Sati guda da dawowar Dady ya kira Ummu ita da Salma kamar kullum suka tafi gidan sosai tasha mamakin ganin kawunnan ta har uku a gidan falon kusan mutun takwas ne ciki, kawunnan ta Abban su Fatima, Dady, Mami da yayan Dady sai mutun biyu bata sansu ba.

Bayan sun gaisa ne Dady ya ce yawwa Ummu batun Gado ne ganin Faruk ya kwan biyu da rasuwa naga kyautuwar sauke masa nauyi na gado, nayi bin cike ba’a binsa bashi ba kuma ya bi sai dai ke kaɗai kika rage ban tambaye ki ko kina binsa ba.

Tsikar jikin ta ce ta tashi tsoron wannan rayuwar ya cika yanzu wai shikenan da gaske Faruk ya rasu, girgiza kai tayi ni bana binsa gaskiya, to Alhamdulillah ni dai na yafe nawa gadon na barma ita matar tasa Dady ya faɗa, ɗagowa Ummu tayi t
Kalleshi bai ce komai ba ya cema ɗaya cikin mutanen da bata sani ba Malam bisimillah zaka iya rabawa yanzu magadansa ga sunan banda ni ya nuna Mami.

Mami ma kuka tasa ta barma Ummu cikin kuka Ummu ke fadin ni nafison adawon da Faruk mu rayu ko ba sisi dukiya jin daɗi basu da anfani a guna in har babu shi.

Dakyar tayi shiru akai bayanin abin da ya bari, yadda kowa zai samu da kuma matsayin barwa Ummu da sukai, Kawunnan Ummu sai gyaɗa kai suke ganin lokacin kaɗan Allah ya azurta Yarinyar ji suke inama ace ta wajensu ce ta samu wannan daula.

Na fahin ci kin fi son zaman ki can inda kuka taso wannan yasa ban miki dole ba wurin zama damu nasan kinason ragewa kanki damuwa anma duk sanda kika samu sanyi cikin ranki ko ji kikai kinason zama damu mu ɗin masu amsar ku ne keda ƴan uwanki, nasan ita Kanta Khadija in bakwa kusa yanzu sai tafi saurin samun sanyi cikin ranta tunda tunawa da Faruk ɗin zai mata Sauƙi Dady ne mai wannan maganar, gyaɗa kai kawai Ummu take tana share hawaye godiyar ma ta kasa Mami ma kukan ta take har Ummu suka fi ce.

Bayan sun dawo ne Kawu Musa ya ce su Ummu su tattaro kayan su, su dawo gidan sa tunda an kore su daga inda suke yayin da shi kuma Kawu Uba ya fe banda abin Yaya ai bazaka iya rike su ba ni yafi dacewa, cikin Faɗa Kawu Musa ya ce ni nace ma bazam iya riƙesu ba eyye.

Takaici ne ya cika Ummu tasan mai sukewa cewa ta yi ai kusan tun tafiya ta ma wata guda mun dawo nan da zama tunda mun riga mun saba danan kuma ina sana’a ta anan unguwar ɗin har yanzu bata mutu ba, basai munje ko ina ba.

Shiru kawai sukai dan sun san halin yarinyar tunda ta ce bazasu tafi ba ba kuwan zata bi kowa ba, Kallon gidan Kawu Isma’il yayi yanzu to mu ya da ce ki kawo takardun kadarar taki mu aje miki nan gidan baimun kama da yana da security ba bare ma duk ku ɗin mata ne. Sai alokacin ta juya ta cewa da Salma bashi dan tunda suka tawo suna gun Salma, ki bashi in zan wani abin dasu maje mu amso ta faɗa ranta babu dadi kafin ta shige cikin gida tana jin haushin abinda iyayen nata suke musu kuɗi wato ya fiye musu jini.

Salma ce ta ce wannan ba zan bada ba zan maidawa shi Abban Faruk ɗin ya aje mata duk randa ta kuma aure ko taji zata amsa sai taje gunsa ta faɗa kafin ta shige cikin gidan.

Kawu Musa ne ya mara mata baya yana masifa Aisha dake Tsakar gida na gaidashi baima gane ta ba dan ta kuma girna shi idon sa ya rufe, Hajiya ce ta ce mai ya faru ne Salma ta mata bayani, amsa ta yi ta ce haba Malam ku yanzu ba’abin kunya bane mijin yarinya ya rasu anma ta abjnda ya bari kuke, ku barta taji da ciwon ran rashin mijin ta mana.

Ummu ce ta fito tana share hawaye “Hajiya dan Allah ku basu, suje suyi duk abinda zasuyi da su ni wallahi Faruk ya fiye mun duk wannan abin da aka ban, nama rasa shi na ke raye bare kuma dukiya, shima da wanda ya tara mutuwa yayi ya bari bare ni da bani na sha wuya akai ba, dan Allah kubarni inji da abinda ke damuna dan Allah..”

<< Ummu Hani 29Ummu Hani 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×