Ummu na faɗin haka ta shige ɗaki tana kuka ranta kwata kwata babu daɗi itakam da zasu mata adalci su barta kawai taji da ciwon mutuwar mijin ta, yayin da Hajiya kuma ta dubi Kawu gami da ɗaga takardun badai wannan bane to wallahi bazan bada ba in kunga cewa lallai lallai sai kun amsa to ku kai kotu sai hukuma ta amsar muku tunda naku ne.
Jiki ba kwari suka fi ce daga gidan dan sun san su da kansu sunyi kuskure na rashin ɗaukan yaran yanzu da suna gunsu ai da dole au za’a bawa ajiya kuma suyi yanda suke so dasu dukiyar.
Ummu duk ta faɗa ga jiki kullum bata jin daɗin sa, rayuwar ta ta koma wata iri wannan ummun nai magana dariya da faran faran ta jima da bacewa inda sabuwar Ummu ta samu wadda bata cika son magana ba aikin ta kullum shine kuka da zama cikin kuryar ɗaki.
Kusan su Hajiya sukan mata nasiha yayin da wani zubin sukan kyaketa ta koka dan sun san kuka rahama ne in kama samu kana yin sa kakan samu sukuni cikin ranka.
Yayin da lokaci ke gudu haka ma zafi da dacin da muke ji bisa rashin da mukai kan ragu a sannu tun in mun tuna mukan yi kuka da hawaye har takai wataran na zuci muke gami da yima mamacin mu addu’a asannu kuma har mukan iya tuna lokacin muna cikin farin ciki dasu muyi murmushi mu ce Allah sarki wane Allah ya jiƙan ka, haka abin yake gurin Ummu Hani tun tana tunanin rayuwar ta tazo karshe har ta hakura ta fara fitowa tana taya yan gida aiki duda cewar har yanzu bata kai matakin dena kuka ba anma akalla takai matakin yadda zata iya rayuwa ko da ba Faruk a doron kasa duda ta aminta rayuwar kawai zatai anma Farin cikin ta ya tafi dashi.
Kusan kwanakin nan sosai suke cikin kuncin rayuwa da talauci abinda zasuci ma gagarar su yake wannan yasa Ummu ɗauko wasu cikin kuɗin da Mami ta danka mata ta bawa Aisha da Salma sukayo musu cefanen kayan abinci da sauran abubuwan da zasu bukata na komawa sana’ar ta tada wato sai da abinci.
Umman su Salma ita ta dauku ragamar girkin inda A’isha da Salman kan fita dashi dan sosai Ummu kejin jiki daurewa kawai take anma duk da dauriyar tata sun gano ta wannan yasa Umman da kanta ta ce ta bari ta gama takaba tukunna.
Kusan Fara jami’an da Salma tayi wanda Faruk ne sila da lesson ɗin da su Aisha suka fara yasa Ummu nacewa ita zata dunga futa da abinci koma hakan zai sanya taji sanyi aranta da kyar ta shawo kansu Hajiya suka amince.
Kusan kamar yadda ta faɗa fitar ya taka rawa sosai wurin cire mata damuwa bani bani ya kan dauke mata hankali dan sosai suke ciniki kasancewar basu da nisa da gidan su nada duk tsoffin customers din ta sun biyo ta.
Rayuwa na rafi lokaci naja kwanci tashi yau watan Faruk huɗu da Mutuwa yayin da cikin Ummu keda wata bakwai yana shirin shiga na takwas kibar da tayi sosai yasa yan gidan nasu har yau basu san da cikin ba yayin da ita kuma bata sanar musu ba kasan cewar bata san mai zata faɗa musu ba.
Haka ma gidan su Faruk tun tabbacin da ta samu na tana da ciki bata kuma zuwa ba cikin ikon Allah suma ba wanda ya naimeta duk da tana son sanin halin da suke ciki anma tana tsoron su ce abin cikin ta ba jinin su bane in kuma sun aminta nasu ne tana tsoron su ce zasu kwace shi dan tasan tabbas in sun aminta da wuya subar jinin su ya taso cikin talauci abinda ita kuma bazata iya jurewa ba shine a kwace mata jinin Faruk daya tal da koda ba ita ta haifa ba zataso ta riƙe bare nasu ne ita dashi.
Tana zaune a ɗaki tayi shiru tana ta sake sake Hajiya ta shigo Ummu tunanin ke kike?, Murmushi Ummun ta yi ba komai Hajiya kawai hutawa nake, Kallon ta sosai Hajiya ta yi Ummu wai da gaske ciki ne dake a tsorace Ummu ta kalleta ciki kuma Hajita ni nake dashi inji wa.
Ajiyar zuciya Hajiya tayi haba koda naji ni nasan karya ne in ba haka ba muna gida ɗaya ace kina da cki bamu sani ba, kibari kawai mutan unguwa keta yamadidi suna faɗin wai cikin shege gare ki haihuwa ko yau ko gobe.
Gaban Ummu ne ta faɗi abinda take tsoro zai faru kenan a hankali ta ce ah ni bani da wani ciki, kyalesu Allah ya saka miki dan kansu Hajiya ta faɗa kafin ta fi ce tabar Dakin, kololuwa hankalin ummu ya tashi yanzu fa in al’umma suka sheganta cikin ta shikenan ya shegu innalillahi wa’inna ilaihirraji’un abinda ta iya faɗa kena yayin da ta cire hannun ta daga kwanon abincin dan Bama zata ita kara loma ko ɗaya ba.
Duk damuwae da take ciki ta kasa yin danasanin zuwa gidan su Faruk da bari da tayi ya kwanta da ita duk da basu tare ba ada tana danasani anma bayan mutuwar sa da ganowa tana da ciki da tayi taji daɗi sosai akallah zai samu mai masa addu’a akalla zata dinga ganin jinin sa da ya samu ta tsatson ta.
Washegari tana zaune tana tuyar kosai wasu dattijai suka same ta, kusan ta gane su masu gidan da suke ciki ne wato su ne suka bawa su Salma haya, bayan ta gai dasu daya ciki ya ce ina Umman taku yi mata magana tom ta ce ta mike ta shiga ciki.
Umma na zaune suna hira da Hajiya ya sanar mata zuwan baƙin ton tace gami da zarar mayafi ta biyo ummu din ta ce mata ta ce musu si shigo zaure.
Ummu daga inda taje takan iya jiyo Muryar Umma na bada hakuri inda dayan tsohon ke faɗin eh to ai danma karkuji rana ɗaya mun tashe ku gida dai an saida wata guda ya isa ku naimi gun konawa adalcin da zamu muku kenan.
Gaban Ummu ne ya fadi a lokaci guda cikin ta ya wani murɗa mararta ta riƙe azaba tamkar ranta zau fita tama kasa motsi dan yunkurin da tayi na kokarin tashi tuni ta nemeshi ta rasa.