Daurewar da marar tata ta mata ne ya ɗan saki da kyar ta yunkura cike da juriya ta miƙe gami da karasa cikin soron kuma gaida mutanen ta yi sannan ta ce “dan Allah bawan Allah ku taimaka ku kara mana lokaci wata guda bai isa mu samu wani gidan da zamu koma ba koda wata uku ne ku taimaka mudin bamu da gata bamu da inda zamu in lokacin ya cika in har bamu samu wani gun ba maimakon azo ku kuna korar mu, mu kuma muna ganin baku mana adalci ba da zaifi kyau ku sa mana. . .