Kamar kullum Ahmad na zaune kofar gida kusan shekara biyun nan yaƙi gajiyawa da zuwa yayin da ita kuma ta kasa kaishi gun hukumar, da sauri yabi bayan ta cikin faɗa ta ce, “Wallahi ka dena bina tun kan inma rashin mutunci.” Rokon ta ya hau yi dan Allah ko kaita ne ta yadda yayi yadda duk ya rame yasa ta ce to dauko motar ya bata tausayi sosai ita da kanta tasan yana sonta sai dai bazata je dangin da basa son ta ba tasan yadda Umman su tasha wahala sosai gun dangin Baban su.
Kan ya matso da motar ta canja shawara tuni ta hau Babur ɗin adaidaita sahu ta ce ya kai ta kurmi, inda Sabo Ahmad ya saba da halin Ummu sai dai ya kasa dena sonta sannan zuciyar sa kullum tana faɗa masa in ka kasa janyewa yayin da kake nema wata rana zaka samu abu da kake so.
Kai tsaye kasuwar kurmi aka kai ta sosai ta yi siye siye ta aje kayan gun Ibrahim kan shi zai tawo mata da su gida ta wuce kasuwar rimi, yau kasuwar cike take gurin traffic ne sosai na mutane dana motoci rike take da Muhammad inda Faruk ke baya sai dai ganin ana ture su yasa ta sabi Muhammad sukai gaba, Ayatullah da ke mota cikin traffic ɗin dan a asibitin Murtala yake aiki, lokaci lokaci yana jan tsaki idon sa ya kai kan Ummu dake tafe riƙe da yaro tabbas ita ce farin cike ne ya lullube shi ya da kyar ya matsa gefe ya fito da sauri ya hau kutsawa cikin mutane da karfi ya kwala mata kira Ummu Hani ya ce baima san ya kira ba cak ta tsaya tasan muryar nan but bata iya tunawa ko tawaye ba, kusan ba ita kaɗai ta tsaya ba mutane da yawa ne kafin kuma kowa ya cigaba da harkar sa.
Juyowa tayi taiko sa’ar ganin sa ya sakar mata murmushi itama murmushin ta masa ta matsa kusa Dr ta faɗa daɗi ne ya cika shi ashe dai kedin ce wallahi ni ce banyi tunanin ganin ka ba kuma ban tunanin zaka gane ni ba, dariya yayi kawai kafin ya ce badai Muhammad bane wannan shi ne wallahi miƙa hannu yayi zai amshe shi ta mika masa ledar hannun ta ungo dai wannan kiwa ce dashi kuka zai sa in ka dauke shi dariya yayi oh har yanzu yana kiwar kenan ka bari kawai sai abinda ya karu tunda aka masa kanne yake kishi. Gaban Ayatullah ne ya faɗi sai dai bai ce komai ba yabi bayan ta. Kusan komai shi ya rike mata sai da ta gama siyayya sannan ta tuna bafa ɗan dako ta ɗauka ba ta hau bashi haƙuri dariya yayi muje in kai ki kasa yi masa musu ta yi tabi bayan sa har zuwa inda motar tasa take.
Har kofar gida ya kai ta, sai a lokacin suka samu damar yin magana sosai ta sauko da Faruk ta ce kaga yaron nawa su biyu ne ɗan uwan sa na gida murmushi yayi Allah sarki Allah ya raya muku su ya kuwa jikin mijin naki koda shike tunda ma kuka dawo ai ya warke, ajiyar zuciya tayi ta kwana biyu mutuwar bata mata ciwo irin yanzu ba girgiza kai ta yi ai ya rasu tun kan in haife su, rasa me ke wakana a ransa yayi ya dai san ba farin ciki ne ba tausayin ta ne ya cika shi yayi ta bata baki kafin suyi Sallama ya tafi. Kusan yau kwana uku ke nan da Ayatullah bai samu kan sa bare ya Kuma zuwa gidan su Ummu duda kullum tana ransa yayin da haka kawai Ummu taji tana fatan inama ya dawo duda bata san dalili ba.
Ita kuwa A’isha daga batun Film biyar har ta doshi goma sha lissafi ma ya fara kufce mata ita kam ta samu abin da take so dan sosai Film din ke garawa da ita ga kuma followers din ta na Tiktok da Instagram kullum cikib karuwa suke wanda shi ne burin ta tafi kowa followers, tana biye da batun Ayatullah duda har lokacin taki dawowa anma tasan baya kula kowa wannan ya kwantar mata da hankali dan gani take tabbas ita yake jira ta dawo musamman ma yanzu da ta zama superstar ta kuma kyau ta goge maza ke faman binta suna nuna mata so tasan dole shima ya kyasa in tana wannan tunanin dariya take. Ban in ce oh ni Fayau wannan yarinyar bata san dawar garin ba.
Da kyar Ayatu ya yakice ayyukan sa ya nufi gidan su Ummu tana shago tana bada abinci dan yau akwai customers dan kullum weekend gun cika yake da mutane masoya ma’aurata da sauran su sam bata yi tsanmanin ganin sa ba order kawai ta nufi gun dan dauka dan sabbin ma’aikatan nasu da suka ɗauka basu da sauri sosai tana son sallamar kowa on time.
“Sannu ko Malam mai za’a kawo ma.” Ta faɗa cikin sanyayyar muryar ta. Dagowa ya yi a hankula ya ce, “Duk abinda kika ga ya dace dani musamman wanda ke kika dafa shi.” Da sauri ta kalleshi, “Lah Dr.” Suka haɗa ido ya sakar mata murmushi itama ɗin murmushin ne kan fuskar ta. Tom kawai ta ce ta juya da sauri.
Sakwara ta zubo masa miyar agushi da zobo mai sanyi kawai yanayin sa ya mata kama dana Faruk yau ɗin sai taji bari ta zubo masa abincin gargajiya dan tasan shima Faruk bai son abincin zamani, mamaki ne ya cika shi ganin me ta zubo masa dan yana son doya da duk abinda akai da ita, kamar kinsan abinda nake son ci kenan har zan wuce gida in ce sumin ita na ce badai inzo mu gaisa. Murmushi ta yi amma fa naji daɗi ka kuwa kyauta bari in zo dan Allah ta yi inda sabbin mutane suka zauna yanzu.
Duk inda ta yi yana kallon ta goye take da Faruk inda Muhammad ke can gefe zaune yana bin ta da ido shima sahun Muhammad ɗin ya bi yana cin abinci yana bin ta da ido. Koda ya gama ci ta dauko Muhammad suka fito tare kuɗin ya zaro bafa a fadan na nawa na ci ba, dariya ta yi kaima dai Dr wallahi bazan amsa ba, au haka ne ya maida kuɗin sa aljihu ai ko nidin dan son banza ne in kika ce haka zamuyi sai in karya ki dan kullun zuwa zanyi.
Dariya ta yi ai kam danaji dadi indai zaka zo kullum din, tsayawa ya yi dan Allah da gaske kike ah Allah da gaske nake tom shikenan kuwa ki shirya ganina danni da abinci 5&6 ne tom sai kazo. Faruk ya kalla ya hau yi masa wasa yaron ya juyar da kai dariya ya yi ya ce kai dai akwai kiwa to ba ɗaukan ka zanba, dariya Ummu ta yi ta ce daba dan wannan ɗinma dan rikici ba ne ai da na aika ya kirawo Umar murmushi Ayatullah ya yi ai tsoro yake karki tafi kubar shi.
Suna tsaye suna hira Husaina da Umar suka fito Umar na hango Ummu yayo gunta yana murna yana faɗin Umna mun fito murmushi ta yi ta ce ina zaku cikin gwaranci ya ce taiten mu da akai wai aiken su akai Ayatullah sai da ya kuma duba na bayan kamar su daya irin su daya sai dai da alama shi Umar ba ɗan rikici ba ne, Husaina ce ta gaida Ayatullah shima Umar cikin gwaranci ya gaidashi kafin su wuce. Wai dama yan biyu ne dariya Ummu ta yi eh biyu ne shi wannan baya yadda da kowa shi yasa nake yawo dashi bashi da sauri kamar wancan shi yasa kawaj nake goya abubana dariya Ayatullah ya yi Halan ke ya gado nasan kema haka kikai kina yarinya. Murmushi ta yi ina sam kanwata Kursum ya gado har yanzu haka take Though ta ce ita ba ita yayi wai Babansa ya yo duk suka sa dariya sun ɗan jima suna hira kafin ya tafi.
Ahmad na kallon su tun fitowar su daga shagon har jimawar da sukai suna hira kishi da takaici ya cika shi ji yake tamkar ya je ya make Ayatullah dan yadda yaga walwala fuskar Ummu abin ya kuma bashi takaici da tabbacin yafa rasa ta tunda ko lokacin da ta amince zata aure shi bai taɓa ganin ta haka ba sai yanzu kuma abin takaici daga haduwa da mutun har ta ji ya kwanta mata haka inaga in sun jima. Ya jima yana tunani kan ya bar gun.
Tun daga ranar kullun sai Ayatullah yazo har in lokacin zuwan nasa ya yi baizo ba sai Ummu taji ba dadi har tsoron yadda ta shaku dashi ta ke wani zubin har tsoro take ji kardai ta fara sonsa bacin da shi ko sau daya bai taɓa cewa yana son ta ba wani zubin har tunani take karfa dai yana da mata yayin da wani barin zuciyar tata kan ce mata to in yana da mata ai sai yafi tunda dai ke bazawa ce saurayi ba sa’an auren ki bane. Yayin da shi kuwa Ayatullah kullum cikin tunanin yadda zai furta mata yake anma ya kasa kwarjini ne da ita sosai da ya ganta sai ta cika masa ido sai dai suyi hira ya tafi kawai. Ya gama shirin sa tsaf na aure kawai so yake ya tattara kwarin gwiwar sa ya sanar da ita.
Daga gidan su Ummu gida ya wuce kai tsaye toilet ya wuce yayo wanka ya sanya kaya marasa nauyi kafin ya wuce dakin Hajiyar su tana zaune tana kallo ita da jikokin ta. Ammar ne ya yo kansa yana murna ga Uncle ga Uncle ya cafe shi ya juya shi kam ya dire shi sauran ma suka ce sai an ɗaga su yabi ya ɗaga su kafin ya gaida Hajiya, yau ka dawo da wuri eh wallahi zuwa na yi muyi magana murmushi ta yi Tom muje ciki ta miƙe suka shiga bedroom.
“Dama so nake dan Allah ki fahimce ni karki fahimce ni baibai.” Murmushi ta yi tom ina jinka ina kwana ki da na ce ki tayani addu’a Allah yasa inga yarin yar da naji inaso murmushi ta yi Ummu Hani ka ce min ko yawwa ita fa to addu’a din ki ta amsu amma ita din ta taɓa aure har tana da yara biyu though tana cewa biyar ne anma a binciken da nayi duk kannen ta ne biyu ne nata suma yan biyu ne.
Shiru Hajiya ta yi kafin ta nisa ta ce mai ya kashe auren nata hadari mijin ya yi shi ne ai lokacin ina Argentina muka haɗu nasan sunan ta ashe mijin suka kai, murmushi Hajiya ta yi ka ce kaima sunna zaka raya tunda da bazawa zaka fara ajiyar zuciya ya yi baiyi zaton zata amince ba duda yasan ita din mai illimin addini ce har ya miƙe ya koma amma kuma girgiza kai tayi karka damu indai yan uwanka ne ba abinda zasu ce haka Abban ku duk zasu Amince kai dai Allah ya baku zaman lafiya amin ya ce but zaman da yayi so ya yi ya faɗa mata yaran Ummu ɗin fa da yawa suna cewa shegu ne amma shi sam bai amince ba kasa faɗa mata ya yi ya fice daga ɗakin.
Koda Abban su ya ji ya ce zaiyi bincike tukun kan ya amince nan tsoro ya cika shi sai dai bazai iya cewa kar ya yi ba tsoron sa kar suma su amince yan shegu ne su Umar shi koda mene ma yana son yaran har ransa ko dan su kadai ko baya son Ummu zai aure ta dan su jin su yake tamkar nasa duda can kasan ransa yanajin nasa ne tun da na Ummu ne ai agunsa jinin ta kuma yayan ta ai nasa ne.
Koda Alhajin Ayatullah ya gama binciken sa kiran Ayatun ya yi sannan ya ce yawa ko zan iya sanin dalilin da yasa ka ce zaka auri yarinyar nan shiru yayi Kafin ya de ada sabida inason ta ne duda har yanzu ina sonta fiye da ada dinma anma dalilin ya canja, yanzu sabida ita din tana da halaye da yawa masu kyau da kowa zaiso ya zaɓa ma yaran sa ita a uwa kenan yanzy sabida zurriya ta zan aure ta ba iya so ba.
Shiru Abba ya yi kafin ya ce anma ai kasan zargin da ake akanta ko, shiru Ayatullah ya yi gabansa na faduwa Abba ya kara da faɗin nasan dole ka sani tunda nima nasani wani da nake son ka sani shi ne shaidar mutane wani abu ce a rayuwa duda nida kai mun yadda yaran na halak ne amma sauran mutane fa, shiru Ayatullah ya yi kan ya ce dan girman Allah Abba ka amince.
Murmushi Abba ya yi karka damu koda ace da gaske ne ba yaran halak bane zan amin ce kasan me yasa, girgiza kai Ayatullah ya yi sabida sadaukarwar ta ga rayuwar mutane da yawa ya cancanci ta ta samu miji na gari, godiya Ayatullah yayi ta yi kafin Abba ya ce ka same ta ku tattauna yaushe zamu zo batun auren.
Yau kam Ayatullah ya cire tsoro ransa tas ya nufi gidan su Ummu suna cikin hira ya daure ya ce yawwa Ummu na ce ba ta kalleshi alamar inajin ka ya ce zaki aureni zuru ta yi tana kallon sa yaushe zan turo ya kuma faɗe kafin ta ce wani abu, dariya tasa amma dai wasa kake ko dan Allah ki fadan yaushe zan turo zaton ta ita duk wasa yake tace gobe mikewa yayi ya mika mata Faruk dan yanzu yaron na yar da dashi dan har murna yake inya ganshi kafin ya ce tom sai na turo ci gaba tayi da dariya kawai ta shige cikin gida.
Kai tsaye gidan Kawu Musa ya wuce kawun su Ummu ya ce masa shine manemin Ummu ta kuma ce ya ce su turo gobe kawu Musa ya ce shi bai ce ba anma su zo ran Lahadi, daɗi ya cika Ayatullah yaje ya samu Mahaifin sa ya sanar masa.
Ran Lahadi suka je aka sa ranar daurin aure Sati huɗu kusan tun daga lokacin Ayatullah bai kuma mata batun aure ba haka su kawu basu sanar da ita anzo ba wannan yasa tunda ta manta da batun nasa bata kuma bi takai ba duda wani zubin in tana zaune ita kadai na ji aranta inama da gaske yake.
Ranar da suka sa daurin auren aka daura auren Ummu da Ayatullah kawu ne yazo har gida shida sauran kawunnan ta suka bata sadaki da kayan lefe suka ce mata wani satin zata tare mamaki ya cika ta ta ce wai wacce Ummun kuka daurawa auren ne dariya kawu yayi kar ki ce mun ba ke kika turo Ayatullah ba wata guda kenan yazo yace kin ce ya turo. Tadanji sanyi aranta jin waye aka daura auren dashi cewa tayi wai dama da gaske ya dauki maganata, Kawu Bala ne yace ah to ance miki ana wasa cikin aure ne kuma wallahi karki sake kice wani abu dan nikam na gaji da kananun maganganun da ake akanki.
Faɗa sosai suka mata kafin su tafi abin mamaki sam Ayatullah yaƙi zuwa ta kasa kiransa, sai washe gari yazi da IV na dinner wanda yake son ta rarraba kasa ma masa magana tayi ta rasa abin cewa shi kuwa sai tsokanar ta yake duk sai ta nemi fada da masifar da ta tara zata masa ta rasa wata irin matsanan ciyar kunyar sa ce ta cikata fahimtar haka ya kuma zakewa.
Ita kuwa Aisha tana Abuja ta samu labarin bikin Ayatullah hankalin ta ya mugun tashi ba shiri ta hau shirin tafiya sai dai dole ta tsaya zuwa jibi ayi last shooting da ita dan kam dole ya saki koma wace ya aureta.
Sosai Su Salma su Aisha su kai rabo kusan duk kawayen su ne dan Ummu bata da kawaye ita sam ba wani shiri da take sune suke komai sun dage sai gyara amarya suke da magunguna da gyaran jiki tayi kyau sosai Umma da Hajiya ma ba’abar su abaya ba ta ko ina ta hadu ummu yau take dinner tun rana su Aisha suka tafi da ita gidan kwalliya dan tun jiya suka kaita gun kunshi ita dariya ma suke bata sai wani umarni suke bata kamar iyaten ta.
Biki yayi biki amarya ta yi kyau iya kyau ango kawai suke jira yazo ya wuce da ita gun dinner in ka ganta bazaka taba cewa Bazawara bace inma ance maka bazawara din ce zaka ce karty ne bare kuma ace ma tana da yaya sai kace karya ne, ita da kanta mamaki take wai ita ce ake bikin ta har yau ta kasa yadda.
Kaf kannen ta dana Salma shiga iri daya su kai suma sunyi kyau sosai Muhammad da su Umar ne a gaban amarya da Su Hasana kannen Ayatullah dasu Aisha masu take musu baya. Kowa nagun amarya da angon nata sun birgesu sun musu kyau haka yan yaran da ke gaba. Kusan tun shigowar su Ummi ke bin yaran da kallo kasa hakuri ta yi koda amarya suka zauna ta miƙe ta karasa gun ta kalli yaran sosai Ummu ta gane ta yayar Faruk ce sauri ta yi ta kauda kai zuciyar ta hau harbawa yadda taga tana kallon yaran nata innalillahi wa’inna ilaihirraji’un kawai ta ke fada har Ayatullah ya fahimta ya cika da razani ya ce mene cikin rawar murya take rada masa yayar baban su Umar ce kar ta ce sai an basu yaran.
Shima ya shiga tashin hankali amma shi ya nutsu yace karki damu ai ke ce uwa a musulunci raino na gun uwa ciyarwa ce kan uba, dan haka bazan taɓa bari su amshe miki yara ba ajiyar zuciya tayi gami da murmushi mutane da yawa tun dazun sun kuma burgesu dan zaton su batin soyayya suke.
Ita kuwa Ummu kai tsaye gun gate ta nufa ta amshi kati tabbas sunan amarya Ummu Hani tasan ita ce duda sau daya ta taba ganin ta randa Faruk yazo da ita indai kuwa ita ce tabbas yaran da ta gani jinin su ne yaran Faruk ne motar ta ta dauka ta nufi gida.
A gida dakin Hajiyar su ta nufa dan tasan iyanzu suna tare da Abban su a nutse ta musu bayani ta ce Hajiya dama na faɗa miki abinda Faruk yama yarinyar nan nasan kin tuna dai ko Hajiya tai murmushi bansa abin Ummi ai ya wuce ina an gama wannan maganar Alhaji ne ya ce wacce yarinya kenan Hajiya ta ce Ummu Hani wai take nufi kasan can kwanaki tun da lafiyar Faruk na fada ma dan yaga an daura musu aure shine ya dauko musu diya ya kwanta da ita, murmushi Abba yayi ai ya wuce kuma ai matar sa ce, ajiyar zuciya Ummi ta yi ba’a gama ba, bai wuce ba munyi kuskuren biyewa Faruk na kin bi takan yarinyar dan kuwa ta haihu kuma wallahi yaran Faruk ne kamar su daya su biyu ne yau ake bikin ta ina kanin Mansura Hajiya ta ce kina nufin Ayatullah eh shifa inji Ummi, to shine mijin, cike da Farin ciki Alhaji ya mike muje dakin Faruk din.
Faruk dake zaune kan wheel chair ya juyo yana Murmushi ya ce lah Abba bana ce kuje ku huta ba yau daya sai ku huta murmushi Abba yayi Ummi yi masa bayani Ummi ta zayyana masa komai ji yayi tamkar ya mike yaje yaga jinin sa ashe dai zaiga jinin sa kafin ya mutu.