Hannun Ayatullah Ummu ta ture gami da faɗin, “Na faɗa ma ni ba matarka bace dama sanadin kana da wasu ɗabi’un nasa yasa na amince zan rayu da kai amma tunda mai ɗabi’un asalin ya bayyana dashi na zan rayu.” Ta faɗa cikin kuka.
Faruk ne cikin rarrauniyar murya ya ce, “Ummu ki kalleni ba Faruk ɗin da kika sani ba bane aurena dake ba mai yiwuwa bane inna zauna dake nauyi kawai zaki ɗoramun dan Allah ku fahince ni zama na dake shi zaifi samun damuwa fiye da rabuwa ta dake, da hanzari ta rufe masa baki. “Ni kai nake so da kuma kai zan zauna karka ɓata bakinka wurin yimun bayani.”
Kuka yasa, “Ummu in dai ba so kike ki ga damuwar ki tasa mun ɓacin ran da zai kashe ni ba ki bar maganar auren nan dan Allah tun asali abinda na guda kenan a lokacin dana farfaɗo Dady yake faɗa min kun bar kasar gawa ta kawai kuke jiran ya tawo da ita nasan in har ya dawo ya ce muku ban mutu ba, ko in muka dawo tare hakan zakiyi shi yasa na zaɓi mutuwa na zaɓi in ace na mutu dan dukkan mu muyi rayuwar farin ciki, Dady yaƙi yadda da abinda nazo dashi anma da yaga na cije haka ya hakura ya yi.”
Girgiza kai ta yi ni abinda ya damen yanzu shine mujina yana raye mai ya faru ada ba shine ya damen ba, shiru kawai Faruk ya yi shi da kowa na falon kafin ya ce, “Ya Ummu kaini ɗaki dan Allah.” Abinda kawai ya ce kenan. Ya Ummi ta matso ta tura keken nasa. Da hanzari Ummu ta bi bayan su har tazo shiga Dady ya ce karki shiga in kika takura masa ciwon sa zai iya tashi cak ta tsaya har lokacin hawayen take wannan wacce irin jarraba ce ta rayuwa sai a lokacin ta hau kiran innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, dalilin ɗan jin sukunin zuciyar ta kenan.
Har yaya Ummi ta juyo zata bar Ɗakin Faruk ya ce Ya Ummu dan Allah ku kori Ummu daga gidan nan karku bari tazo inda nake, Shiru Ya Ummi kawai tayi bata bashi amsa ba ta juya abinta, da makulli ta kulle ɗakin ta kuma cire makullum abakin ɗakin Ummu ta zube tana kuka shima kukan yasa dags inda yake sai dai bazai iya koda motsi ba bare ya bar inda yake zuwa inda take dan lallashin ta.
Dady ne ya dubi Ayatullah da ke tsaye tamkar dutse ya ce gwanda ka tafi gida dan kar a gaji da neman ka dare ya raba insha Allahu zamuyi kokarin shawo ma kanta zata fahimta,” “To na gode” kawai ya iya cewa kan ya bar gidan ransa cike da tashin hankali a yadda yaga Ummu ayadda idanun ta da yadda take acting ya tabbatar bawai wasa take ba yana kuma jin shawo kanta zai matukar wahala.
A can gida kuwa koda Ayatullah ya dawo tambayo yi kalala a takaice ya zayyana musu abinda ya faru mamaki ya cika kowa wai mijin ummu na raye. A dakin sa kasa komai ya yi juyi kawai ya ke bisa gadon nasa zuciyar sa cike da tunani marasa kan gado tunawa da ya yi su Aisha ƙannen Ummu zasu tashi hankalin su bisa rashin dawowar yayar tasu yasa shi ɗauko wayar sa ya fara kiran Salma dan ba zai iya tuƙa mota zuwa gidan su Ummu ɗin ba.
Bugu ɗaya Salma ta ɗaga ina Ummun take ina kuka tafi ta faɗa duk a lokaci guda, ajiyar zuciya ya yi tana gidan su Faruk ta ƙi tawowa towo mai ya faru Salma ta tambaya a kasalance ya musu bayanin komai dukkan su suma sun cika da mamaki harma da tsoro wai Faruk bai mutu ba.
Washe gari da wurwuri Ayatullah ya bar gidan dan kam shi tun jiyan bai wani bacci ba ya riga ya yanke shawarar zuwa zaiyi ko mai Ummu zatayi sai ya ɗauko ta, Mai gadin ma Bacci ya ke lokacin da Ayatullah ya iso, buɗe masa gidan ya yi a hanzar ce ya gaida mai gadin ya shige cikin gidan inda ya barta jiya nan ya tadda ta zaune anma tana bacci wato kofar ɗakin Faruk da alamu data sha kukan ta bacci ne ya sa ce ta. Hannun ta ya kamo taso mu tafi ya faɗa a ɗan tsorace ta buɗe idanun ta tako hau ƙoƙarin kwace hannun tana faɗin ni na faɗa ma ba inda zani.
Dady da ya jiyo hayaniyar su ne ya fito ganin Ayatullah ne ya hau yi masa faɗa yanzu bana ce kaje ba zamu kawo ma ita, Faruk fa baida lafiya da kyar yake bacci yanzu in baccin yake ka masa adalci kenan ya tashi a firgice, Ayatullah tsuru tsuru ya yi yana kallon Dady shi saima duk kunya ta cika shi shi yasa ake gudun bin abibda zuciya ta ce dan gudun dana sani.
Hakuri ya bawa Dady sannan ya bar gidan kai tsaye gidan su ya wuce aiko tamkar jira ake ya dawo Dady ya aiko kiran sa. Dady ne da Kawu zaune ya gai da su kafi Dady ya fara da jiya Aisha taje gun biki kun haɗu kai da yan uwanka kun ci mata mutunci abin bai isa ba sai da kuka haɗa da ɗauko musu hukuma.
Yunkurawa Ayatullah ya yi zai fara bayani Dady ya ce karka min wani zance da na yanke gobe zan ɗaura muku aure to ɗan kawun naku yazo ya ce a bari sai wani satin tunda auren farin da zai fara ne yanason ya yi gayya dan haka ka shirya zama da ita da kuma matar taka.
Anma Abba…. Anma me na riga na gama magana kaima lokacin da zaka auri waccan yarin yar alfarma ka nema in ma Kuma na na dan haka kaima alfarma nake nema bawai umarni ba baka ba in alfarma ɗin ce ban isa ka min ba sai ka faɗan, tamau Dady ya kulle shi harda jijiyoyin sa dole ransa ba daɗi ya ce shikenan Dady Allah ya bamu zaman lafiya Amin suka ce yabar ɗakin ransa kwata kwata babu daɗi ji yake tamkar ya faɗi.
Kusan kwanan Ummu huɗu a gidan su Faruk kullum tana ƙofar ɗakin ba wanda yake mata magana itama gaisuwa kawai ke haɗa su sai wani zubin in ta gaji da zama ta fara ma Faruk dake cikin ɗakin hira wanda duk hirar da ɗin su ce lokacin suna ckin farin ciki ita ala dole sai ta karya masa zuciya yaji ya amince su cigaba da zama tare, Yau bayan Ummi ta fito daga ɗakin nasa zaton Ummu zata rufe ɗakin kamar kullum sai dai bata rufe ba da sauri Ummu ta shiga yau a kan gado yake kwance, a nutse ya ce ɗan gyaran labulen iska ta yi yawa da hanzari ta gyara labulen ya ce filon ɗan ɗagon da kaina ta gyara filon tayo sama da kansa.
Sai kuma ta yi shiru ta kasa magana zauna mana ya fada yana nuna mata gefen gadon da idon sa, guri ta samu ta zauna Ummu Hani ya kira sunan ta da sauri ta ɗaga muryar tasa ta nuna mata buƙatar hankalin ta gare shi yake.
“Kin san wani abu?” Girgiza kai ta yi murmushi ya yi kafin ya ce ban taɓa takaicin wannan ciwon nawa ba, ban taɓa jin me yasa na haɗu da wannan kaddarar ba sai cikin kwanakin nan ada a kullum ina tunanin tawa kaddarar ce a haka ina fatan Allah yasa jarrabar nan ta zama silar aljanna ta, anma shekaran jiya zuwa kinsa na fara tunanin ke yasa ni me yasa kowa yake da lafiya yake zaune da iyalin sa cikin koshin lafiya sai ni, ban son in faɗa miki duk abinda yazo kaina anma wallahi sanadin abinda kikai kinsa na kusa fita daga addini na kinsani damuwa maras adadi.”
Ɗagowa ta yi a tsorace ta kalle shi, “eh ba wai na faɗa miki bane dan kawai ina son ki kyaleni ni da kika ganni nan nafison rayuwar mu ta ɗore anma kaddarar mu ta raba mu, a shekaran jiya da Yah Ummu ta faɗan ina yara ji nake tamkar ba yani cikin farin ciki da ɗoki na ce ta kaini in gansu da ace nasan yadda zakiyi kenan da wallahi bazan je ba da hakura zanyi yadda kika mallake yaran in bar miki su nasan a kallah zaki musu addu’a.”
Kuka tasa, “to ya kake so in yi na faɗa ma bazan iya rayuwa babu kai ba.” girgigiza kai ya yi kayya Ummu babu wani da bazamu rayuwa ba wai sai da shi ko kuma in bashi muce bazamu rayu ba, ke misali ce kin rayu ba mahaifi ba kuma mahaifiya ki iya rike wasu kuma ina tabbatar miki suma ɗin ko ba ke zasu rayu kamar yadda ada da kike zaton na mutu kika rayu haka yanzun ma zaki iya farin ciki koda ina raye.”
Zata kuma magana ya ce, “Ni yanzu ba surutu ne na kiraki muyi ba rokon ki zan dan girman Allah badan ni ba ki tausayamun ki barni wallahi hakan shi zaifi samin kwanciyar hankali ki daure ki koma gida kuyi rayuwar ki da mijin ki, yana sonki kema kin sani.” Bata kuma bashi amsa ba ta miƙe tabar ɗakin tana kuka yana kiran sunan ta ko juyowa batai ba.
Kai tsaye gida ta wuce su Salma su kai ta murna dan tun shekaran jiyan basu koma gidajen mazajen su ba sun kuma kasa zuwa gidan su Faruk ɗin dan su tawo da Ummu ɗin. Bata ce musu komai ba ta shige ɗaki bata tsaya duba wanne Umar ko Faruk ba ta goya ɗaya ta saɓi daya tana yo waje Muhammad ya biyota yana kuka ta riƙe masa hannu sukai waje ba tare da ta tsaya bada amsar tambayoyin da ake mata ba.
Kai tsaye gidan su Faruk ta wuce a ɗaki ta tadda Mami tana gyara masa gado yana ina Ummu ta ce Ummi ce zata koma gidan ta shi ne ya tafi rakiya ajiyar zuciya Ummu tayi sannan ta ce ni zan koma bayan ta dire na hannun nata gashi nan sun san sunan su Umar da Faruk ne in sun ɗan saba dashi kwana biyu zanzo in tafi dasu.
Tuni Mami ta aje abin da take ta ɗauki Umar farin ciki fal cikin ta wai yau ita ke riƙe da ɗan Faruk a nutse ta kalli Ummu kuma zasu zauna yaƙe Ummu ta yi eh na hannun naki zai zauna wannan ne dai in ya farka yaƙi zama sai a dawo dashi, shine Faruk ɗin, murmushi Mami ta yi oh kuma shine me halin Faruk ɗin.
Hannun Muhammad Ummu taja zata fi ce yasa kuka ƴan biyun su sakin Hajiya ce ta ce kyaleshi in suna ganin sa sai sunfi zama murmushi Ummu ta yi ɗan rikici ne ba zams zai yi ba, abin yaro fincike hannun ya yi ya koma gun hajiya duk suka sa murmushi inda Ummu tabar gidan.
Ta jima abakin layin a zaune dan har sai da motar su Faruk ta dawo ya ganya ya juyar da kai dan yasan rikicin ta da yayi sa’a ma tabar gidan hakan ya masa daɗi, kamar bazata bar gun ba ta kuma miƙe ta yi gaba abin ta kafin ta tsare ɗan sahu ta koma gida, A kofar gida ta tadda Ayatullah da alamu waya aka masa aka ce ta dawo yana ko ganin ta yi inda take, a nutse ta gaida shi kafin ta ce dan Allah ka bari anjima muyi magana Tom ya ce yayin da ita kuma ta shiga ciki. Faruk yayi murna sosai na ganin yaran nasa dady ma haka sam basuyi zaton ganin yaran Umar abokin sa ne ke tura keken yayin da Dady ke mara musu baya ba wanda ke magana cikin su dan kowa jimamin Abinda ya faru yake suna shiga yaran sukai arba da su suna ta wasan su Faruk ne dai can zaune bisa cinyar Mami tana bashi madara da alamu kuka yasha ya koshi.
Faruk babba bai san sanda ya saki dariyar farin ciki ba Umar karami yayo gunsu da gudu yana taɗa keken Faruk ya dubi Umar babba ya ce dan Allah bama kama, dariya sukai duka ai basai ka faɗa ba wannan kawai rayuwa sukai a cikin ummu anma kaine kanana ke yawo inji Dady murmushi Faruk ya kuma yi doramin shi a cinya ya ce da Umar babba Umar ya ɗoro masa shi Faruk ya ce ya sunan ka ya faɗa yana duban yaron.
Da sauri cikin gwaranci ya ce Umar sannan ya nuno ɗayan dake cinya ya ce Faruk sunan sa kallon juna Umar Babba da Faruk sukai gami da yin murmushi Dady ya ce ashe takwarori ta muku Muhammad ne ya matsa da gudu yana faɗin shima a ɗora shi dariya Faruk ya yi yaron ya kuma wayo kamar sa Ummu sai fitowa take ikon Allah wanda ta haifa basuyi kama da ita ba sai kanin ta.
Faruk karami da ke shan madara shima ya taso Mami ta ce ah lallai na yadda jini ba wasa bane yaron nan kinyin shiru yayi sam shi sai a kaishi gun Umman sa ganin da nayi kamar baici taje gida ba kuma tunda bikin ta ake zaifi kyau in basa taren na ɗan kwana biyu shi yasa ma naƙi sawa a maidashin.
Murmushi Faruk ya yi kyake shi a sannan zai ware sauke Muhammad da Umar Faruk yasa Umar ya yi sannan ya sa ya ɗora masa Faruk aiko yaron ya yi luf a jikin sa daɗi ya cika Faruk.