Shi ko Ahmad tun da yaji an ɗaura auren Ummu Hani yayi baƙin ciki iya baƙin ciki yasan yayi rashin mace tagari mace jajirtacciya ganin a koyaushe ya fita zuciyar sa ingiza shi take ya nufi unguwar su Ummu wani zubin ma sai ya je kofar gidan sai ya hau salati yayi sauri bar gun wannan yasa ya haɗa kayan sa tas ya koma Zariya inda yake masters ɗin sa a can dan yana jin in har yana garin kano mantawa da Ummu ɗin zai masa wuya. Kusan matakin da ya ɗauka ya rage masa kewar Ummu dan kuwa da yaji zai fara tunanin ta yake ficewa ya tafi inda yake research ɗin sa.
Aisha kam rabon ta take cike da kwanciyar hankali gami da farin ciki Baliƙisa ke rakata yauma sun dawo daga rabon Balkisa ta ce yanzu dai Aisha aure za kiyi” dariya ta yi “ga zahiri kuwa hmmm ki bari kawai ni da ace Isah type ɗina da wallahi tuni na aure shi da bama zan biki ba time ɗin da kika sa muka tafi.”
Dariya Aisha ta yi nasa muka tafi ko kika sa muka tafi a’a karki mun sharri kin manta da nake miki complain ɗin ni zan tafi inbar gida in aka kwan biyu na dawo sabida bana son Isah aike kika ce kawai muje muyi film ɗin da aka mana tayi.” “Yawwa to wai me yasa bakya son Isah?” Aisha tambaya.
Kwafa Balkisa ta yi “ki bari kawai wallahi banson namiji ɗan jijjida kai bafa yamin magana sai na masa wai shi ala dole introvert dan kawai yana ganin shi mai kyau ne.” Dariya Aisha tasa ni kuma kinga abinda yasa nake son Ayatullah kenan irin su Bama su da lokacin wasu matan sai nasu matar dan kamar ma tsoron kula mace suke.”
Dariya Balkisa tasa ai shi yasa naga har yaje ya auri wata dariya Aisha tasa itama bazaki gane ba ne dan dai niɗin cusa masa ni akai ne shiyasa, eyye wato kinma san baya sonki inji Balkisa, eh nasani anma ina tabbatar miki inhar yayi kuskuren aurena ba boka ba malam sai yaji niɗin kaɗai da ita zai iya rayuwa kema sheda ce wuyar ta mutun yasan wace ni Aisha ta faɗa cike da kuri, kedai kibi asannu karkije wannan yarinyar ta kasa ki gurin sa dan da alamu ba kyalle ba ce. Kinga mubar wannan batun mu koma na film Aisha ta faɗa.
Kinsan yanzunma daurewa kawai fa nayi nabar film dinnan dannasan shine last chance ɗina in ba haka ba nasan nida Ayatullah har abada anma irin ta waccan ɗin ake tayi wallahi. Towo tayin films ɗin ne dai Baliƙisa ta tambaya kedai bari manyan kamfani fa ko jiya sai da FKD sukamin mgn ta handle ɗina na twitter akwai role ɗin da suke ganin zanyi a film ɗin su kinsai dai yadda manyan jarumai keson harka da su.
To kuma me kika ce kusu taɓe baki Aisha ta yi ke kuwa zan ce cewa nayi aure zanyi na aje film, shiru Balkisa tayi kan ta ce bayan su mutun nawa kika faɗawa a industry, tab ai ba adadi, Salati Baliƙisa tasa to Allah dai ya rabaki da sharrin su wallahi kinsan su Jaruma Mubarak sun kafa miki kofa da kin sani baki faɗa sai dai kawai a nemeki a rasa, shewa Aisha tasa yo to me zasu iyamun ai ni nasha dubu sai ceto, dariyar Balkisa ta yi yayi yayi ta waje na ta faɗa.
Yau take daurin aurin auren Ayatullah da Aisha sam shida yan uwansa basa cikin farin ciki ga kuma abinda Ummu ta ce eh zata zauna dashi anma zata fi jin dadi yaje ya amso mata takardar sakin ta gun faruk koda yaje Faruk ya faɗa masa shi tun tuni ya sake anma dole Ayatullah yasa ya bashi takarda ya kawo mata koda ya kawo cewa tayi yanzu kam sai ta gama idda zasu kuma haɗuwa shi tsoron sa ba wai iddar ko rashin zuwa gun nata ba tsoron sa kar cikin wata ukun ta kuma juya masa baya.
Yana ɗakin sa a zaune abokin sa ya shigo kan yazo su tafi gun ɗaurin aure yace shi wallahi bazashi yai yai dashi yaƙi dole shi da sauran abokan Ayatu ɗin suka tafi.
A gurin ɗaurin aure masallacin Alfurkan ne da ke kano liman ya dubi waliyin ango da amarya ya ce ina gwaji kallon sa waliyan sukai kafin Dady da ke matsayin waliyin Amarya ya ce ai duk su biyun yaran mu ne nine baban ango na jini anma kaganni nan ni mahaifinta ya naɗa na zama waliyin ta ƙanina ne.
Murmushi Liman ya yi wannan bashi kaɗai muke dubawa ba ai baku da tabbas kan ƴaƴan ku sannan kuma in genotype ɗin su nada matsala shima ya kamata a haƙura tunda dai kuna buƙatar jikoki masu lafiya. Kawu ne ya ce aje a kirasu anjima da karfe biyu ayi ɗaurin auren bayan gwaji.
Kai tsaye asibiti Dady da A’isha da Ayatullah suka wuce inda akai gwajin blood group, genotype, HIV, da sauran cututtukan da za’a iya ɗauka, Ayatullah dai kam ba wani ciwo jinin sa ne dai As yayin da Aisha keda HIV hankalun ta ya tashi dan bama tasan tana dashi ba tayi ta ihu tana kuka haka suka rankayo sukayo gida.
Dady ne yayi ta mata nasiha ya kuma tabbatar maganar aure babu ya nuna mata ita da Ayatullah duk ɗaya ne agunda koda Ayatu ne keda cutar bazai yadda ya aura mata shi ba, takaici da bakin ciki Aisha ta yi shi sosai dan ta tabbatar da ta riga ta rasa Ayatullah. Zaton Ayatullah zaiyi farin ciki in an fasa auren ban sai dai jini ɗaya yafi ƙarfin wasa tausayin Aisha ne ya cika shi sam babu kwayar zarra ta farin ciki aransa ga tsoron da ya shiga ransa kar dai jinin Ummu AS ne dan ko kaɗan shi bai bawa Ummu zata samu transmissible disease ba.
Wata guda da fasa auren Aisha ta koma harkar ta ta film sosai film ke garawa da ita kamar da babu wanda tayi kuskuren faɗawa tana da HIV ko Balkisa bata faɗawa ba abin iya family ɗin su ya tsaya shima na kusa kusa. Jin haushin da mubaraka kewa Aisha ya yi yawa dan kuwa tazo lokaci kaɗan ta mata fintinkau wannan yasa take ta ƙulle ƙullen sai tasan yadda ta yi ta koreta a harkar.
Yau suna wurin shooting film Aisha taga sai kallon ta ake ana duba waya cikin tsiwa ta dubi Ib mai bada kayan sawa ta ce Malam lafiya dai kake mun irin wannan kallo haka murmushi ya yi ya matso kusa ya miƙa mata waya,ita ce cikin wayar yadda mahaifiyar ta ta haifeta ta kuma gane ɗakin wanda suka je da sabon saurin da tayi hankalin ta ya tashi cikin firgici take tambayar sa ina ya samu ya ce a twitter aka sa yanzu ya yaɗa ko ina, harda Tiktok ta tambaya da sauri, eh har can.
Da hanzari tabar gurin sai dai duk inda ta yi yan jaridu ne dakyar ta samu ta tawo gida nan ɗinma masu tambayar ne kuka tayi sosai koma waye ya mata wannan ya cuce ta sam bai mata adalci ba, sai dare can ta iya shiga gida aiko Umman su kamar tasa zata zo idon ta biyu ta hauta da masifa dama yanzu Aisha cutar nan da kika ce a reza kika ɗauka ƙarya kike. Kuka Aisha tasa yo Inna Koma a me na ɗauka ai kece sila tunda ke ce kike nunan tun asali komai nake so komai nake yi shine dai sai fuu ta shige ɗaki salati kawai Umma tasa tama kasa magana Malam najin su bai ce komai ba dan shikam ji yake tamkar zuciyar sa ta fito sabida baƙin ciki.
Rayuwar tama Aisha zafi sam ta tsani harkar film dan tasan komai ya same ta sanadin Tiktok da film ne da ace bata ba su yaddar ta ba da tuni yanzu tana gidan mijin ta cikin farin ciki kai koda batai aure ba da tuni tana gidan su da mutuncin ta, maganar video ya lafa anma irin yadda ake neman ta da sam ba’ai Balkisa dama sanadin ta ake sata yanzu itama ɗin ba samu take ba, yanzu Aisha ta kuma yadda duniyar shahara ba komai bace face wahala.
*******
Nifa a gaskiya Umma kin takurawa rayuwa ta nagaji haba tunda na auri Bashir na rasa waye nake aure ke ko shi, kuka Umman Bashir tasa yanzu Yar nan ni kike faɗawa haka ina da ban haifeshi ba na kuma sa ya auren ki ya rufa miki asiri da tuni ina ta gararan ba a gari.
Tsaki Bushira taja yo kema da bakin ki kin faɗa sawa kikai ya auren yadda ya auren baya sona haka nima da kuma kike batun rufan asiri mene abin birgewa a auren Bashir aure duk wahala abinda zaka ci ma sai anje an nemo tukunna. Kwafa Umma ta yi eh duk lefi nane wallahi yaro nason yarinya mai kashin arziki uwarki ta zugani na tubure sai ke wallahi nayi dana sanin hana bashir Auren yarinyar can Ummu hani.
Shewa Bushira tasa ai kam dai Ummu hani ta miki nisa surukuta da ita ba sai dai kiji ana yi muɗin dai mune dole ki ganku ki kyale mu, Bashir da ya shigo ne ya tadda mahaifiyar tasa da matar tasa suna rikici bai ce komai ba ya ɗauki ɗiyar sa ya shige ɗaki masifa Umma tahau yi wai ya zama soko yana kallo Matarsa na zagin uwar sa ya gaza cewa komai.
Faɗan ne ya rincaɓe lokacin da Umma ke ƙoƙarin ɗaukar ledar shinkafat da Bashir ta ajiye aiko Bushira ta hankada ta kan tukunya nan ta sa ihu da gudu Bashir ya fito kallon Bushira ya yi zo ki tafi gidan ku sai na nemeki, ruko kwalar sa ta yi sake ni dan wallahi bazai yuwu da an kwan biyu ka ce in dawo ba nagaji, murmushi ya yi shikenan na sake saki ɗaya, jikin ta ne ya yi sanyi dan batai tsanmanin zai iya sakin ba.
Ɗaki ta shige ta haɗo kayanta haɗe da ɗiyar ta zata bar gidan yasa hannu ya amshe yarinyar ai kema kinsan bada ita kika zo ba haka suma sun san ba basu haɗoki da ita ba, waje kawai ta fi ce tana sanbatu yayin da Umman sa ma ta juya zata fita a hankali ya kira sunan ta Umma ya faɗa cikin murya mai sanyi ungota ya miƙa mata yarinyar, cikin hargagi take faɗin kasan dai ni bazan riƙe jinin waɗancan natsiyatan ba, girgiza kai ya yi jinin mune Ummu kin manta ɗiya ta ce ta halak tunda kin sa na kori Babar ta ke ta dace ki riƙe ta har in samo mata wata mahaifiyar.
Amsar yarin yar ta yi sannan ta ce Allah ya baka mace ta gari danma kace mun Ummu hani ɗin tayi aure da wallahi ita zan je in roƙa ta aure ka dariya yayi ai ta yi aure anma zaki iya zuwa ku gaisa ki bata hakurin abinda kikai mata baya, shikenan Bashir zanje karshan ta ma abinda na mata ne ke binka ta faɗa kan tabar gidan ya shige ɗaki bayan ya kullo gidan haka kawai yaji tamkar ya saukewa kansa wani nauyi mai yawa.
**********
Kusan wata huɗu kenan da batun auren su Ayatullah satin nan aka kuma sawa dan ɗaurin aure kusan kaf rayuwar su Umar ta koma gidan Su Baban su Ummu na kewar yaran ta amma tausayin mahaifin su wato Faruk yasa ta kasa zuwa koda ganin su ne dan tsoron kar ce sai sun biyo ta.
Yau ta kirawo kawunnan ta harda Ayatullah suka nufi gidan su Faruk kamar wancan lokacin mutanen da aka tara yauma sune harda malaman sai dai wannan karan da Faruk zaune sam ta kasa haɗa ido dashi abubuwa daban daban ke zarya a ranta, ita ta fara bayani batun gadon dana ci ne na dawo dashi tunda wanda aka raba gadon nasa yana raye abu ɗaya ne gidan mai na siyar shima gida na siya ga takardun gidan wanda muke zaune a ciki ne ta faɗa lokacin da take miƙo takardun.
Ƙarawa ta yi da faɗin sai miliyan biyu da tayi sauran cikin kuɗin da aka saya nan dubu ɗari takwas ne insha Allahu zan ciko sauran a sannu sune wanda muka buɗe shago da abinda na rabawa ƴan uwana sai alokacin Faruk ya yi magana. Sai batun gidan da muke ciki za’a mana taimako dan Allah a bamu haya, Ni na yafe basai kin kawo ba sannan suma waɗannan ɗin wallahi baki nayi ni da kaina nasa bawa Dady ya baki.
Sai a lokacin ta ɗago ta kalleshi sai kuma tayi ƙasa ta kanta wannan abinda kake dashi ne musulunci ya mana hani da kyautar da dukiyar mu duka dan haka bazan amsa ba kana da magada ka adana musu. Shikenan gidan ku zauna har tasowar su Umar duk yadda suka yanke kan gidan shikenan Faruk ya faɗa. Shiru ne ta ratsa na wani ɗan lokacin kafin Malam su rufe da addu’a kowa yabar gun.
Sam Ummu bata nemi taga yaran ba daga falon gida ta wu ce Taf taga gidan su dan gobe ne ɗaurin auren nasu ita kam duk sanda ake shirin bikin ta ba ta taɓa shirin wani abu ba ƙannen ta ne kawai ke yi wannan karan sai ta samu kanta cikin farin ciki ganin dangin Umman su dana Abban su duk sun hallara kuma wai duk sabida ita. Washe gari wurin goma Ayatullah ya kirata ya faɗa mata an ɗaura dan tuni sunyi gwaji abin su liman na neman takardar gwaji aka nuna, taji daɗi sosai na ɗaura auren sai dai da ta tuna da Faruk kuka ne ya kwace mata dakyar aka lallasheta.
Da daddare a shirya dan tafiya dinner wadda daga can za’a wuce da amarya gidan ta, amarya da ango sunyi kyau sosai fiye waccan dinner ɗin lokaci lokaci suna magana tsakanin su gwanin ban birgewa, sam batayi zaton ganin sa ba sai muryar sa taji lokacin da ake ta hotuna yana faɗin ko ba’a hoto dana zaune ne.
Da sauri ta juya dan tayi zaton gizo Muryar ta mata sai dai shi ɗin ne Faruk ne rau rau tayi da ido zata sa kuka ya girgigiza kai kajiki kuma mene na kuka, Ayatullah kuzo muyi hoto Faruk din ya faɗa a dake, Ayatullah ne ya matsa inda Umar abokin Faruk ɗin ya turo keken kusa da Ayatullah sai Umar karami Ummu ta ɗauke shi Faruk ƙarami kuma yana jikin Baban sa Ayatullah kuma ya ɗauki Muhammad ba wanda zuciyar sa batai sanyi ba a gun. Sunyi hotuna sosai kafin Faruk ya ce Umar ya tura shi kujerar da Fatima ke zaune ita da angon ta Mansur, sosai suke hira shida su Fatima lokaci lokaci yana ma Faruk karami wasa wanda sam yaƙi saukowa.
Kusan tare aka tashi bikin da Faruk duda ya riga su Amarya tafiya ganin da yayi su Umar sun fara barci har su Hasana ya haɗa ya tafi dasu sai da ya koma gida Faruk da Dadin sa suka kwantar dashi bisa gadon sa sukai sallama sannan dauriyar da yake ta masa kaura sosai kuka ya kwace masa anma kasancewar ya ɗauki aniyar mantawa da Ummu matsayin wadda yake so ne yasa ya daure sosai naƙin yin kukan sosai. Ankai Amarya gidan angon ta inda aka barta daga ita sai shi sai halin su.
Rayuwa mai kunshe da farin ciki Ummu hani suke da mijin ta yadda yake nuna mata kulawa yasa ta cire komai itama take kulawa da abinta sai dai babu wani lokaci da zaizo da zatayi addu’a bata sanya shi ciki ba shida mijin ta da yaran ta.
Shagon abincin su kuwa ya kuma haɓaka dan har sun buɗe rassa wannan yasa take ƙara ganin girman Ayatullah sam bai hanata kasuwancin taba haka kuma ya bata dama duk sanda tana son ganin Yaran ta da ƙannen ta su Hasana dan tun ran bikin ta suma rayuwar su Hasana ɗin ta koma gidan su Faruk, ya bata dama ta ɗauko su inma gun ta take son dawo dasu shi ya ce mata sam bashi da matsala.
Ayayin da yau da gobe ke shuɗewa a sannu kuma shekaru ke tafiya yau su Faruk ƙarami ke bikin gama degree ɗin su, sun zama manyan samari in ba ce maka akai wannan shi ne wannan ba to bazaka iya banbance waye umar ko Faruk ba sai dai in ta yawan dariya da surutu duk wanda yasan Faruk baya dariya sam.
Faruk Umar ne ya shigo ɗakin wai kai har yanzu baka gama shirya Dadin bane, Faruk da ke shirya baban su wato Faruk ya harare shi to so kake in zama inji kome, matsowa Umar yayi ya ɗauki hula ya ɗorawa Faruk yawwa Dady wannan tayi kyau, ya tsina fuska Faruk ya yi (Baban nasu) ni matsala ta dakai Umar u don’t have fashion sense kwata kwata, kwafa Umar yayi shi dama nasani kafi son Wannan kurman, suka sa dariya, tare su biyun suka daga mahaifin nasu suka ɗora bisa keken nasa sukai waje.
Usaina da ta sakko daga bene ne ta ce ni zan tura shi gaskiya, Faruk karami ya ce ni gaskiya Anti Usaina banason abinda kikemun kawai sai ki dunga ma mutun kina kwashe masa lada, harar sa ta yi dalla ni matsa ta faɗa lokacin data karɓe marƙin keken dan turawa Faruk ya zunɓura baki yabi bayan su.
Faruk (Babba) yaji daɗi sosai ganin wai yau yaran sa ne suka kai haka ya kuma ga girman su ya kuma yi masa tarbiyya shi kam ko iya haka ya gode Allah, Umman su ma tazo wato umma hani haka Abban su wato Ayatullah da sauran ƙannen su wanda Ummu ta haifa a gidan Faruk in kagan su a gun convocation ceremony ɗin zasu birgeka sosai, Muhsina da Uman ta Fatima da Abban ta Mansur da sauran ƙannen ta da suka zo ne akai ta tsokanar Faruk Ƙarami sabida tana zuwa suka gaisa da kowa ta koma kusa da Faruk ɗin ta zauna.
Faruk Babba ya ce ah kaga masoya ana ta soyayya ko Umar Ƙarami ya matso ya ce ah Dady soyayya kuma dariya Dadin (Faruk) nasu yayi eh mana tun kwanaki yake faɗan in faɗawa Dada (yaka nufin baban sa wato kakan su) aje a nemo masa auren ta, What Umar ya faɗa ya akai ya rigani nimafa na fidda mata ya faɗa lokacin da ya kannewa Zainab yar gidan kawu Umar ido ta sun kuyar da kai. Ummu hani ta girgigiza kai dai wallahi Ummaru akwai rashin ta ido aka sa dariya duka.
Sai yanma lis suka watse kowa yayi gida Faruk da ɗan uwan sa Umar suka ɗauke mahaifin su sai gida sai da suka gasa masa jikin sa sannan suka kwantar dashi gefen gado suka zauna suna hira abin su irin ta ɗa da mahaifin da suka shaƙu sosai.
A gidan Ummu kuwa bayan sun tabbatar yaran su sun kwanta ummu ma bayan yaran tabi ta kwanta dan tasan halin baban sa aiko dai ɗakin ya biyo ta fuska a cakule tamkar wani karamin yaro ya ce wai me kike nufi kinsan dai baba iya bacci ni kaɗai ko hararar wasa ta watsa masa to kai jariri ne, ni Allah zan sa muki kuka ya kuma kwaɓe fuska salati ta saka gami da dariya oh ni Ummu ace ayi mutun sam baya tsufa ka kallafa kwanan nan zaka fara jikoki, hannu yasa ya jawo ta daga gadon ni taso mu tafi bacci nake ji nagani da magana, cikin dariya ta miƙe tabi bayan sa inda suka rufewa yaran kofa sai da suka leƙa ɗakin Abubakar da Aliyu sannan suka tabbatar sadiya ma tayi bacci sannan suka wuce ɗakin su…
Alhamdulillah labari ya zo karshe na fara rubuta shi 26/7/2020 na kammala yau inda yai dai dai da 16/7/2022.
Akwai dalilai da yawa da yasa na rubuta littafin mafi girman dalili shi ne a rayuwa Maraici ba zai taba zama sanadin da zamu lalace ba naji wasu na fadin ai marayu sau da dama suke lalacewa su addabi al’umma duk dan basu da mai kwabar su duk dan basu da mai ci da su, Ummu hani mace ce yarin ya da bata wuce a ci da ita ba sai dai da yake zuciyar ta bata gurɓace ba sai ta jajirce ta nemi sana’a yes ba wai dole a rayuwa sai munyi degree, NCE ko Diploma zamu ci gaba ba rayuwa ba dole sai muna wani babban aiki ba sannan zamu kai inda muke so, Ummu ko secondry bata gama ba anma ta kai inda wasu da dama masu zurfin karatun basu kai ba.
Zanso so inji naku ra’ayin kan wanne irin daraji kuke tunanin littafin ya koyar da ku ku daure ku rubutan Nagode sosai sai mun haɗu a sabon littafi
Good